Showing 177001 words to 180000 words out of 193443 words
Chapter 60 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt
tafi.." He said as he unzipped her clothes, Sarah tayi lamo jikinsa taƙi yarda ta kallesa, bata san mene take ji ba, tasan kawai za taji babu daɗi, Losing him near her is like losing her happiness, ƙasa yyi da murya still holding onto her yana shafa mata fuskarsa yace "Saa... rahhhhh" still shiru tayi masa, idanunta rufe yana jin zuciyarta na bugawa sosai, gently ya leƙa fuskarta tayi saurin juya fuskarta tare da ɓoye ta a ƙirjinsa, He couldn't speak to her, he was hugging her more and her compassion was overwhelming him, Bata son ya tafi amma ba zata iya faɗa masa haka ba, hannunsa yasa a hankali ya ɗago fuskarta yana binta da kallo Kafin speaking clamly yace "What happening?" Shiru tayi masa, ya Lumshe idanunsa yana jin gaba ɗaya kamar ya ɗauke ta su tafi, cikin breaking voice yace "Talk to me Sarah, dan Allah" idanunta ta buɗe kaɗan suka haɗa idanu, zata ɗauke kanta yyi saurin kama fuskar yace "Mene? Me kike so?" Kasa basa amsa tayi sai kawai ta fashe masa da kuka da iya ƙarfinta tana ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, "Ya Rabb!" Abeed ya faɗa a kasalance, rabuwa yyi da ita sai da tayi kuka ta gaji, kana ya wani ƙanƙameta sosai yace "It will be the last day that your tears will come out, it will be the last day that you will cry in your life, I don't want to see you cry Sarah" ita dai shiru tayi tana shassheƙa, a hankali ya ɗura bakinsa a kunnanta yace "Being in love with you, I have got to be the luckiest girlfriend in the world, you're strong, kind, Intelligent and Mine" She keep nodding her head and smiling a ɓoye, maganganun da yake faɗa mata suna shiga har ƙasan Zuciyarta, Abeed ya kama fuskarta a tafin hannunsa idanunsa akan jajayen laɓɓanta muryarsa can ƙasa yace "Meeting you has been the highlight of my life. I want to spend all my tomorrow finding out more and more reasons to be in love with you" ajjiyar zuciya ta shiga yi kukanta ya tsaya, a hankali ya sanya hannunsa yana goge mata hawayen cikin Muryar raɗa yace "Are You Okay?" Muryarta na rawa tace "bana son zama a nan" Abeed ya ware fararen shanyayyun idanunsa With so surprised yace "It is your grandparents' house, you will live with your grandmother, grandfather, brother, sister and other relatives" tai masa shiru a hankali yace "ok, today is Friday, I will come on Sunday, hk yyi?" Kasa Mgn tayi sai cute smile data saki tana ɓoye fuskarta.. special light kisses yyi mata a wuya da forehead zuwa lip's yace "Zanyi missing" yana faɗin hakan ya janye ta daga cikinsa tare da jan hancinta, tafiya ya fara yi yace "koma" yana faɗin hakan ya nufi compound na gidan, ganin zai mata nisa cikin siririyar muryarta tace "Uncle..." Tsayawa yyi da tafiyar tare da juyawa daga inda yake yana kallon direction ɗinta... Walking slowly ta fara takawa zuwa inda yake kanta a kasa cikinta har ya fara bayyana a fili, tana zuwa dab dashi ta tsaya, he just looking at her face kafin yace "what?" Idanunta ta ɗaga taga babu mutane a wajan da ɗan sassarfa ta nufesa tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da rungomesa tace "Thank you... Allah ya tsare ya kiyaye ka" Murmushi yyi yana manna mata softness lip's ɗinsa a cheeks ɗinta yace "Amin Ya Rabbi Queen.." kasa cikasa tayi tai lamo a jikinsa shima kuma bai saketa ba, baya jin kuma zaice ta cikasa, footsteps da Sarah taji yasa ta fara ƙoƙarin zame jikinta, Abeed yaki sakinta Zain dake tsaye dab dasu fuskarsa ba yabo ba fallasa yace "Is this what you forgot?" Gira Abeed ya ɗaga yana kashewa Sarah idanu wacce kunya ya gama kamata, Zain ya juya yana faɗin "You have no shame" Da sauri Sarah ta kwace jikinta bata tsaya jiran Abeed ba tayi shigewar ta cikin gida....Da daddare Mrs Zain na kwance akan bed idanunta rufe Sarah ta shigo cikin bedroom ɗin cikin wasu pech ɗin pyjamas da D&G couples slippers mai kyau a ƙafarta, ta ɗura hula saman sumar kanta, hannunta riƙe da wayarta ta nufi kusa da Mrs Zain "How long have you been lying in bed alone?" Sarah ta faɗa tana zama kusa da Mrs Zain, a hankali Sairah dake kwance ta buɗe idanunta tare da kallon Sarah,kafin gently ta tashi zaune muryarta can ƙasa tace "Not long ago" Sarah tana danna wayarta tace "Ina tunanin halin da mijinki zai kasance, He wants to be with you, and Abba wants Zain to give you divorce papers, na shiga damuwa" Mrs Zain ta buɗe idanunta muryarta can ƙasa kamar mai shirin kuka tace "I was just thinking the same" Sarah ta ajjiye wayar hannunta gaba ɗaya attention ɗinta ya koma kan Sairah tace "What's in on your mind?" Mrs Zain tayi ƙasa da kanta hannunta dafe da cikinta daya girma tace "I don't want to be separated from my husband, sbd cikin dake jikina na kasa tantance halinda zuciyata take ciki, naji dai bana baƙin ciki koda Zain ya sakeni, amma bana son haka sbd Ubangiji ya haɗa haihuwa tsakanin mu" shiru tayi hawaye na sakko mata tace "What should I do twin? Na kasa fahimtar komai, Du'a is like a mother to me zan iya sadaukar mata, Wlh ban taɓa kishin taba tun farko kallon ƴar uwa nake mata, to yaya zan? Tana son mijinta ina son zama dashi Nima" ta ƙare magana kuka na ƙwace mata, shiru Sarah tayi can tace "Look Sairah, kin san har abada Zain ba zan taɓa sakin ki ba? why are you bothering yourself? Eh? Ki daina damuwa kodan kare lafiyarki dana babynki ok?" Sarah ta faɗa tana sharewa Sairah hawaye kafin tayi Murmushi tace "Do you remember?" Mrs Zain tace "What?" Sarah tace "D promised".... "What promised?" Sarah tayi Murmushi tace "On that day, I made a promised to you that I will give you happiness, I will live with you, I will even replace you as a mother, father, and siblings" shiru tayi sai kuma tace "ban samu damar haka ba, I know you are angry with me na tafi na barki, ban san meke faruwa dani ba a lokacin, kawai ban san Wacece ni ba ina jina kamar sabon mutum bazan iya tuna abubuwan dana aikata a Time ɗin ba, I am sorry ki yafe min na kasa cika maki Al'ƙawari Twin" girgiza kai Mrs Zain tayi tace "No, at all. Baki komai ba nina aikata maki laifi, na maki sharri akan kece kika cakawa Abeed wuƙa, banyi haka dan a ɗauki mataki a kanki ba, nayi haka ne sbd ki fita daga cikin Zahel, baki da lafiya ba zaki jure zama ba, kin fini taurin zuciya za'a iya aikata maki wani abu, shiyasa na ɗura laifin caka masa wuƙar a kanki, but i kne i made a mistake daga baya... Baki da kowa kuma har yanzu ina riƙe da al'ƙawarin ki na cewa mu cire Daddy daga matsayin Uba" duk shiru sukai, can Sarah tace "I need to know why Daddy took us to the forest, Mene yasa yace ba shine ya haifemu ba?" Yarima Yashim da yake tsaye bakin ƙofa yace "Sbd ɗaukan fansa..." gaba ɗaya Sarah da Sairah suka ɗaga kai tare da kallon yayan nasu, a hankali Yaa Yashim ya nemi waje ya zauna kafin Clamly yace "Babu abinda Sir Salam yake so a duniya sama daku Twins, sometimes yana ɓata lokaci shi ɗaya a office akan tunaninku, wata rana har kuka yake, yace yana son ganin yaransa yana son jin ɗumin yaransa kusa dashi, babu wacce yake jin tausayi sama da Sarah, a koda yaushe ciwonta zai iya dawowa idan bata samun kulawa, ba haka Kurum ya kaiku dajin Zahel ya zube ba, hakan tsararren abu ne, kuma yace Allhmd Sairah tayi rabin abinda ake so, kada kuji haushin Sir Salam yana sonku da ƙaunar ku" ya faɗa yana kallon Sairah domin sam ya kasa kallon direction ɗin Sarah,yana jin nauyin all abubuwan da suka faru a baya, silar Kilishi yyi soyayya da biological sister sister ɗinsa, What a shame! Mrs Zain tace "Mene yasa ya kaimu,wane aiki?" Yaa Yashim ya ɗaga shoulders yace "till now bai ce min komai ba, but yana tsananin kewarku" Sarah dai kanta a ƙasa taƙi cewa komai, Mrs Zain tace "Kai fa? You are also your father" Murmushi yyi mata yace "frgt about me, ni da man ban sanshi ba, ban shaƙu dashi ba, haka ban san Wacece mahaifiyata ba... Silar aiki tasa na san shi, amma tun a time ina jinsa a raina ina tsoran ɓacin ransa" Mrs Zain tayi can tace "Nima na aikatawa wani laifi a Zahel, ina son zuwa garin" Yaa Yashim yace "is not necessary" yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da yi musu good night, da kallo Sarah tabi bayansa tana sauke ajjiyar zuciya.... Cikin dare suna kwance akan bed duk suna bacci, but baccin Sarah rabi da rabi ne, sbd zazzaɓin da yake damunta duk dare ita nata kalar laulayin kenan, A hankali Fulani Bilkisu da Sarki Al'khasim Abubakar Wahab suka Turo ƙofar ɗakin tare da shigowa, gaba ɗayan su idanunsa akan Grandchildren ɗin nasu yake, Sarki na kallon Sairah data ɗura hannunta saman cikinta, Fulani Bilkisu kuma idanunta akan Sarah data kwaɓe fuska kamar Zatai kuka tana tura baki gaba, ta rungome pillow amma yanayin saukar numfashinta ba daidai yake ba, walking slowly Fulani Bilkisu ta nufi wajan Sarah tare da zama kusa da ita a hankali ta ɗura hannunta saman forehead ɗinta, sosai taji zafi Sarki yyi ƙasa da murya yace "What's going on... U looks so worries" cikin ƙasa da murya tace "She has a fever and a headache" ta faɗa cikin sanyin murya, Ganin Sairah Bacci take a nutse yasa Sarki nufar wajan Sarah yana zuwa ya dafa kanta yaji zafi yace "What are you waiting for? check her body temperature, ko injection ki mata" girgiza kai tayi tace "Komai yana Cikin chemist, dole ai mata scanning may be ko awo basa zuwa" jinjina kai yyi Fulani Bilkisu ta kalli Sarah sosai sai kuma ta kalli Sairah tace "Ikon Allah, nafa gasa gane wace Matar Abeed wace matar Zain, I mean wace Sairah da Sarah tsakanin su" Murmushi Sarki Al'khasim Abubakar Wahab yyi kafin yace "haka mazan nasu suke ai" A Hankali Sarah ta mirgina tana ƙara ƙanƙame pillow bakinta na motsawa tace "Un... Uncle" ta faɗa tana kwaɓe fuska, Fulani Bilkisu ta shafa kanta tace "Ga wata ta fallasa kanta da Uncle, sorry Granddaughter, Uncle baya nan sai Grandparents" Sarki dai na tsaye cool water ta ɗauka ta shiga shafawa Sarah, hakan yasa Sarah tayi shiru tana sauke ajjiyar zuciya domin duk zaton ta Uncle ne, suna zaune har wajan Subhi time ɗin zazzaɓin Sarah ya sauka, a hankali Fulani Bilkisu ta gyara mata rufa kana tabi bayan mijinta tana cewa "Girman cikin Sarah tsoro yake ban, kalli har cikinta yafi na matar Zain girma dole a kula da ita"....... After 1week Zain na zaune saman carpet kansa a ƙasa sai Amma, da kuma Yaya Rooma A hankali Abba yace "Sbd kada nayi maka Mgnar saki kabar ƙasar? Haɗa baki kukai dakai da warin naka?" Zain ya girgiza kai yace "No Abba, Abeed has a lot of work to do,Even a phone call doesn't get a chance to pick up, The son of the German president was klled yesterday, abin ya ƙara tsamari domin hadda ƴan mata ashirin aka sace, Da Abeed da Daddy Salman sun yi busy yanzu haka suna can Jamani, kuma ana shirye-shiryen bada award ga best Singer na duniya" Shiru Zain yyi Abba yace "Allah ya kyauta" Naila dake zaune tace "Yanzu uban mene ya faru ne kayi masa kiran gaggawa ni naga ma duk ya zuƙe wallahi, idan ba hali kawai ka dawo da matarka nan ina dalili,kuma zanje can Zazzau ɗin ƙafa da ƙafa na bawa Shisham hqr wlh na ɗauka Shege ne bashi da Uba, huhuhuhu su Zulfa'u za'a kwashi kunya wlh zan so naga idanun azababbiyar matar nan, a to muguwa ce fa yanzu dai sai ta ɗauki Wannan ƴar shilar ƴarta ta bawa Shisham ɗin Allah dai yasa ita bata yin ciko" sai kuma tayi shiru can tace "Abin nan ya tsaya min, shekara ɗaiɗai shekara ɗari da goma nayi a duniya amma ban taɓa ganin al'mara irin wannan ba, Wlh ko Leges dana kira sunce ba'a haka to yaushe ma ake haka? Wlh mace tayi cikon nono acan kura ce kawai domin bata ɗauki lasisin zama ƴar iska ba, kasan tif tif suke dashi ko wanne da kalar iskanci su" Shiru dai gaba ɗaya sukai mata Yaya Rooma tana da riƙe dariya ta, Naila ta girgiza kai cike da al'mara tace "Wlh abin ya girgiza tunani na, na kaɗo ainu to me zaka ce? Ɗan yau ne fa shiyasa wlh nai shiru ba um ba u'm "uhm da ƙyar dai nace Allah ya shirya" Abba ya numfasa yace "Ka ruhutu Divorce paper?" Zain yace "Abba dan Allah kayi hqr Wlh ba zan iya sakinta ba" Naila ta ware Idanunta tana dafe ƙirjinta tace "Auzubillah, saki, saki dai na aure dana sani? Wanne irin saki ana ƙoƙarin shigowa Ramadana? To akan me? Waye zai saki wa kuma za'a saka? Inji dai ba Shalale ba kuma ba matarsa ba?" Zain ya juya ya kalli Naila tace "Grandma, dan Allah ki faɗawa Abba ina son zama da matata Sairah ga cikin dake jikinta" Naila ta saki baki sai kuma ta kalli Mai martaba tace "Banga ne ba? Kayi min dalla dalla akan mene za'a saka yaro da masifa? Zaka zauna da Wannan ƙaton rawanin naka kana gasa masa azababbiyar Mgn meye ne saki?" A hankali Abba yace "Eh, Hajiya Du'a ita ce matarsa ta farko idan aka saketa ba'ai mata adalci ba wlh" Naila tace "Tab...." Sai kuma ta rushe da matsanancin kuka tace "A Gsky ban taɓa ganin Mai rawani mara adalci irinka ba, yanzu yarinya fara ƙyakƙyawa mai hqr da sanyin hali zaka saka ya saketa? Allah na tuba gamai ciki wa yake ta Juya? To Wlh akan wannan cass ɗin ba ruwana sai na tattara kaya na naje duk inda Allah ya kaini" shiru tayi tana Matse hawaye tace "Yanzu kenan cikin ya zama gantalalle ko mene? Yanzu ko ɗan cikin da bai zo duniya ba baka tausayawa? A Gsky Mai rawani ban taɓa sanin baka iya mulki ba sai yau, banda kada na tona asiri kawai dana faɗawa hisba su kuma su sanarwar freedon rediyo kowa yaji kalar naka mulki" Abba yyi shiru Naila ta harɗe ƙafa tace "Ziff kake kowa? Maza ɗakko takarda kazo nan" Miƙewa Zain yyi Abba yace "Kada kace zaka saki Du'a" Naila ta miƙe tsaye tana runste idanunta tace "Alkur'an sai ya sake ta, Kai wlh sai na ɗaga maka nono kowa ya huta kai ne ka ƙulla auren ko menene? Ya kake neman kashewa yara rayayyen auren su gashi Ubangiji ya ƙulla rabo mai girma, haka kurum yaron tun yana ciki a fara yi masa gori ana nunasa da baki ana cewa, gashi can an saki Uwarsa tun yana ciki? To ba zan zama Uwar banza ba, saina saka a tsige maka rawani mu huta da azabar ka" tana faɗin hakan ta juya kan Zain tace "Huce mana, kai ma badan halinka ba jiya jiya ya shiga yyi min sata fa? Raguwar alkaki na tass ya sacesa" sai kuma ta fashe da kuka tace "Wlh ban taɓa tunanin Ziff ya Shahara a sata ba sai jiya, yanzu dan Allah me zan cewa Laure? Yadda na dinga bata daɗin alkakin nan da irin sigarin da aka saka masa, wlh sai ta ɗauka ƙarya nake ko tace ni talaka ce" babu dai wanda ya kulata, Zain dawo hannunsa riƙe da paper Naila ta amsa ta ware tass, Takardar ta bawa Yaya Rooma tace "Karanto muji" Yaya Rooma ta amsa tace "Ni Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas na saki matata Du'a Al'khasim Abubakar Wahab saki biyu ba tare da laifin komai ba" sai kwanan wata da rana, Ƙwace takardar Naila tayi tana bawa Zain tace "Raguwar guda ɗayan da aka barsa yana lilo a duniya na mene? Kai ma kaso iskanci wlh kai da zaka rubuta saki uku a jere rerass......Zain did not speak, cos He's speechless.. har yanzu yana riƙe da Divorce paper ɗin, Dr dake tsaye akan Du'a wacce take kwance akan gado hannunta maƙale da Drip, A hankali Dr ya gama dubata yace "Ta samu hawan jini, da bugawar jini a brain ɗinta, at anytime zata iya samun shanyewar ɓarin jiki" Amma dake zaune akan kujera tace "Subuhanallahi, Hawan jini?" Dr yace "E, idan ana kula da ita, babu wata damuwa a Zuciyarta komai zai daidai" Zain daya kejin komai ya fita akansa yace "In sha Allah, thank you" Dr yace "I have to go" yana faɗin hakan ya tattara kayansa, har lokacin Mai martaba dake tsaye baice komai ba, gently ya miƙe tsaye not looking at them, a taushashe yace "Follow me... Zain" Zain yabi bayan Abba har zuwa haɗaɗɗan sashin sa... Abba ya kalli Zain yace "Are you happy now? Everything that happens to her, kai ne sila" Zain dai yyi shiru Abba yace "Mene yasa Ubangiji ya samar da iyaye ga yaransu? Mene yasa Ubangiji ya samar da Babba kafin ƙarami? Mene yasa Ubangiji ya samar da Ayar Suratul Nisa'i 34 ayet?" Allah maɗaukakin sarki yana cewa;
"اَلرِّجَالُ قَوَّامُوۡنَ عَلَى النِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ اللّٰهُ بَعۡضَهُمۡ عَلٰى بَعۡضٍ وَّبِمَاۤ اَنۡفَقُوۡا مِنۡ اَمۡوَالِهِمۡ ؕ فَالصّٰلِحٰتُ قٰنِتٰتٌ حٰفِظٰتٌ لِّلۡغَيۡبِ بِمَا حَفِظَ اللّٰهُ ؕ وَالّٰتِىۡ تَخَافُوۡنَ نُشُوۡزَهُنَّ فَعِظُوۡهُنَّ وَاهۡجُرُوۡهُنَّ فِى الۡمَضَاجِعِ وَاضۡرِبُوۡهُنَّ ۚ فَاِنۡ اَطَعۡنَكُمۡ فَلَا تَبۡغُوۡا عَلَيۡهِنَّ سَبِيۡلًا ؕاِنَّ اللّٰهَ كَانَ عَلِيًّا كَبِيۡرًا"
Abba yaja numfashi yace "Mene yasa Ubangiji ya saka maza a gaba da mata? Mata suna da rauni, mu maza bama tsayawa musan mene raunin mace? Muna amfani da son zuciyar mune, Ubangiji ya samar da iyaye akan yaransu saboda sauke wani haƙƙi, da nace maka ka saki Sairah ba haka Kurum bane,