Showing 93001 words to 96000 words out of 193443 words
Chapter 32 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt
akai mata wlcm, ɗaya daga cikin ma'aikatan wajan suka ce me za'ai mata, zama tayi Idanunta akan Sara wacce bata ɗago kanta ba sbd bugun zuciyarta daya ƙaro, Ma'aikaciyar na ƙoƙarin zame liƙab ɗin Fuskar Ayyana tayi saurin riƙe hannunta tana girgiza kai tace "gyaran ƙafa" ta faɗa tana sauke ajjiyar zuciya, Idanun Ayyana akan Sara da tsananin mmki kafin tayi saurin ɗaukan wayarta wacce ba kowa ya san tana da ita ba, wata number ta kira wacce ko Sarki Mabus bai san da ita ba, ana ɗagawa tace "Yarinyar nan tana Zahel?" Shiru tayi can tace "Ok, thanks" kashe kiran tayi mmkin ganin Sara ya kashe ta daidai nan kuma aka gama cirewa Sara henna ɗin wacce tai wani kalar jaa mai ɗaukan hankali, haɗa idanu sukai Sara da Ayyana, Ayyana tayi saurin ɗauke Idanunta tana gyara zaman liƙab ɗin ta, sosai Sara take bin matar da idanu can ta miƙe tsaye tana ɗaukan handbag nata zata bita, ma'aikaciyar tace "Ki jira sa mana" Girgiza kai tayi tace "kice naje gida" tana faɗin hakan ta fita, da sauri Ayyana ta miƙe tsaye itama Sara na gab da fita tayi saurin riƙe hannunta, ajjiyar zuciya Sara ta sauke tana bin matar da idanu, Ayyana ta ware idanu kafin tace "Akwai Manyan dog's a hanyar kibi ta baya" Sara ta waro idanu tsoro sai kuma ta saki cute smile tace "Thank you Mom..." Kasa magana Ayyana tayi sai kawai ta ciro wata paper a jaka tace "Ki bawa brother naki" tana faɗin hakan ta juya Sara da bata san sunan Ayyana ba ta shiga ƙwala mata kira "Mom! Mom.." Ganin ta shige bata tsaya ba yasa Sara jan tsaki tace "I don't even know her name, Just Mom is ok for me" tana faɗin hakan ta nufi ƙofar tare da samun mai tacsi tace makarantar su zai kaita, shiga tayi ya tafi da ita, Sarki Mabus da yake tsaye bakin ƙofa hannunsa riƙe da gun yana jiran fitowar Sara amma yaji shiru can kuma yaga Ayyana ya fito ita ɗaya, Kallonta yyi yace "Tana ina" ware hannu Ayyana tayi tace "Akwai matsala a Zahel zamu komai some day's, sai mu Turo neman haɗin gwiwar Companyn, na nema mana tickets" tana faɗin hakan ta shige cikin motar yaja tsaki tare da shiga motar suka bar wajan.... A hankali Sara take tafiya kamar daga sama taji Auta ta fasa ihuu tace "wlcm dear" wata frnd ɗin su Nadiya tace "Ai naji babu daɗi,kinzo daidai yanzu zamu fara Auta bata kayanta ta saka" Murmushi Sara tayi ba tare da tace komai ba, wani hall suka nufa ashe duk ƴan matan suna ciki ana yiwa wasu make up wasu ana musu vedio wasu na photo, wasu na tictok duk classes beb ne a ciki, wata red lace gwon aka bawa Sara, cikin wani waje ta shiga tana saka gwon ɗin ta fito "Wow!" Gaba ɗaya ƴan matan wajan suka shiga faɗa sbd wani irin kyau da Sara tayi ga gyaran kai ga kuma henna da akai mata, make up akace za'ai mata tace bata so, gaba ɗaya girls ɗin wajan suka ce bata ita ba, dole ta zauna akai mata make up tare da wani ɗaurin tauban, nan da nan kowa ya zubawa Sara Idanu wasu da suke kishi da ita suka shiga jan tsaki musamman wata mai suna Feedy, ita kanta Sara sai da tayi mmkin yadda make up tayi mata wani irin mugun kyau, farar new gucci bag ɗinta Auta ta bata with white hill shoe na Gucci, sai white vail siriri, photo na akaiwa Sara ita bama ta kula ba domin mai make up ba kowa ta kewa photo ba, amma Sara har vedio ta mata, 6 daidai suka nufi babban hall ɗin da ake patyn d.j ya cika wajan, Sara tayi rau rau da idanu sbd tarin Madam sclh ɗin data gani gaba ɗaya sun sanya white and black na suit, iya haɗuwa wajan yyi juyawa tayi da sauri tare da nufar wani waje ta zauna ita kam ba zata iya shiga wajan ba, tana zaune taji ance "Sarahh" Idanunta ta ɗaga suka haɗa idanu da Yarima Yashim da yake tsaye cikin wata white ɗin Alkyabba wacce tayi masa bala'in kyau, ya ɗan faɗa ba sosai ba yace "Are You Okay?" Ta ɗaga masa kai kafin tace "Ina yini" bai amsa mata ba kansa a sama yana duba sararin samaniya kafin yace "It is too cold here" ta miƙe tsaye sai a lokacin yyi baya yana ƙare mata kallo frm head to toe yace "Ma sha Allah, kinyi kyau sosai Princess" Murmushi tayi tace "Thanks" yace "No need future wife" ya faɗa yana kama hannunta saurin kwace hannunta tayi ya shafa fuska yace "Sorry, Abbana yana nan so get ready" ta ware idanunta sai kuma tace "Ok,bari naje" yace "Zanzo ciki anjima, i have something to do now, love you princess always you're in my heart and prayers" da idanu ta bisa yana barin wajan kira ya shigo wayar Auta dake hannunta ganin sunan Jaan ya sanya tayi saurin zama tare da manna wayar a kunnanta tana wani narkewa tare da shagwaɓe fuska tace "Nayi fushi" Abeed dake zaune cikin mota a harabar wajan idanunsa akanta baice komai ba yana bin jikinta da kallo idan ransa yyi dubu to ya ɓaci, jin shiru yasa Sara turo baki tace "Baka ki rani ba" a hankali ya sauke breathing a nutse yana gyara Murya yace "Ni ne kike turawa baki?" Ta waro Idanunta sai kuma ta miƙe tsaye tana kallon wajan tace "where are you, dan Allah kana ina please" shiru yyi mata ita kuma ta shiga duba wajan yana kallo ta shige ta jikin motarsa can yace "Sanyi yyi yawa,ki koma I'll call you later" yana faɗin hakan ya katse wayar Idanunta ya cika da hawaye, ta daɗe a wajan kafin ta shiga wajan hall ɗin, daidai wajan M.c na cewa muna buƙatar namiji ɗaya da mace ɗaya wanda zasu taka a fili z wanda ya kasa rawa idan macace namijin zai mata kiss idan namiji ne ya kasa macan zata yanka masa adadin kuɗin data keso, wani handsome guy mai suna Aryan ɗan gidan vice president ya miƙe tsaye, iya haɗuwa Aryan ya haɗu ga kuɗi da aji, hakan yasa M.c yace "Yes, d lady is here" Sara da bata san meke faruwa ba ta tsaya a wajan tana waro Idanunta, M.c kowa ya ɗauka Miƙewa tayi tsaye hakan yasa gaba ɗaya mutanan hall ɗin suka hau ihuu, sbd izza da izza sun haɗu, wanka da wanka ya haɗu, kyau da kyau ya haɗu waye zai zama winner waye zai zama loser? Nadiya ta miƙe tsaye tare da ƙara sawa wajan Sara ta kama hannunta zuwa kusa da Aryan da Idanunta ke ƙasa fuska ɗaure, M.c yace "What a match, what a lover, ba tare da ɓata lokaci ba zamu fara" yana faɗin hakan aka saki wata cool Indian songs Pal ik pal, gaba ɗaya aka zubawa Sara da Aryan idanu hadda Malaman schl ɗin, Aryan ba wata kunya ne dashi ba dan haka ya fara ƙoƙarin kama hannun Sara da niyar yin Indian dance da ita amma ta haɗe fuska, ta kame shi kam a hankali yake zagaye ta da wani irin salo burinsa daman bai shige taƙi yin rawar ba, har aka gama waƙar Sara bata motsa ba, dan haka M.c yace "Aryan yyi mata kiss kamar yadda tsarin gasar yake, amma idan akwai wanda zai iya fansar Sara da kuɗi da yawa yana iya yi sai a sallama masa kiss ɗin" waje yyi Shiru hakan yasa Aryan ya fara ƙoƙarin yi mata kiss daga bakin ƙofa suka ji ance "1.2m" Cak Aryan ya tsaya gaba ɗaya suka juya Yarima Yashim ne tsaye hannunsa zube cikin Aljihu fuskarsa akan Sara, M.c yace "Yanzu za'a bawa Teacher dama" Aryan yyi Murmushi yace "1.56m" ya faɗa yana yiwa wani yaronsa alama daya kawo kuɗin domin kowa a nan zai zube, Yarima Yashim bashi da cash iya su ke nan, hakan yasa ya wani ƙurawa Sara idanu M.c yace "yaro ɗan masu dashi,kana da iko akan Sara yanzu, idan akwai wani mai ja to" shiru babu kowa hakan yasa Aryan ya nufi Sara tana ja baya yana biyo ta har suka isa ƙarshe, a hankali ya kama fuskarta Yarima Yashim ya runtse idanunsa sosai sbd wani bugawa da zuciyarsa tayi Aryan na ƙoƙarin haɗe bakinsu yaji ance "200.10B"
Zain Abeed isn't free contact to subscribe...... 08119237616 it's 500.... Ai weekend lafiya sai Allah ya kaimu Monday, Wanda ba zai iya jira ba mu haɗu a Arewabooks🥰🥰Allah yayi wa iyayen mu albarka👏🏻*****40***⚫⚫⚫40
Zain Abeed it's not free contact to subscribe.... 08119237616.
Aka faɗa ana cillo jakar kuɗin cikin hall ɗin juyawa sukai baki ɗaya domin ganin wanda ya sanya wannan mahaukatan kuɗin akan kiss ba millions ba Billions, yana tsaye bakin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya haɗu cikin Three-piece dinner suit, hannunsa maƙale da Diamond Rolex, ƙafarsa cikin Black Leather shoe, sumar kansa sai ƙyallin Ginger Geminal Oil-hair, ya zagaye sumar da black bandana, ga ƙamshin Hugo boss dake tashi a jikinsa yana kaiwa hancin Mutane ziyara, fararan shanyayyun idanunsa sauke akan Sara yana binta da wani irin hargitsastsan kallo wanda babu wanda zai iya fahimtar wanne kalar kallo yake jifanta dashi, nutsuwarsa da kwarjinin sa da kuma tarin haibar dake jikinsa, sun haɗu waje sun ɓoye dukkan wani yanayi dake sauke akan fuskar ABEDDEEN ABDUL-JABBAR ABBAS. Sara da itama take kallonsa with so much surprise, na yaushe yazo? Yaya akai yasan tana wajan, dalilin hakan yasa ta kasa motsi sai idanu take binsa dashi, Gaba ɗaya hall ɗin ya koma kan Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas, hatta Yarima Yisham bin Abeed da kallo yake ganin babu ko ɗigon harama akan fuskar Abeed ɗin, Walking slowly still looking into her face yake tafiya zuwa tsakiyar hall ɗin, yanayinsa ya sanya Sara ɗauke kai jikinta yaso bada ita sbd rawar tsoran Abeed daya fara, tsaiwar Abeed a tsakiyar hall ɗin ya sanya all students ɗin buga wani uban ihuu suna faɗin "Rockstar, the super Man, the best Singer in the world, ZAIN ABEED" gaba ɗaya hall ya hargitse wanda ya sanya Abeed motsa fuskarsa kaɗan yana taɓe baki,sbd ihun na neman rusa masa ragowar jin dake tattare dashi, ihu da tafi irin wannan ya saba ganinsa tun bai kai haka ba, M.c ya gyara zaman speaker yace "Wonderful, Amazing, yau mune muke ganin Rockstar Zain Abeed a gaban mu? What a beautiful day, we're a biggest fans nka Zain Abeed, please just for the love kayi mana song sbd tarin soyayyar da muke maka, bamu da inda zamu ganka bamu da kuɗin da zamu je wajan show naka, Please Rockstar Zain Abeed" gaba ɗaya hall ɗin aka ɗauka "Zain Abeed, Zain Abeed, Zain Abeed" no one knows his Real name, sai makusancinsa, Sara da mmki ya gama kashe ta a tsaye kawai tabi Abeed da idanu, wanda shima ke tsaye hannunsa zube cikin Aljihu duk tarin mutanan da suke wajan wallahi babu wanda Abeed ya ɗaga idanu ya kalla sai His little Pinky Saransa, Dama mawaƙi ne? Shine tamabayar da take wa kanta, idanunsa ya lumshe tare da buɗewa tamkar wanda ya bata amsar abinda ke mata yawo a zuciya, Aryan Vice President's son shi kansa was shock da ganin Abeed, mutumin daya jima yana son yyi masa Birthday song amma ko wanda yake bada appointment na ganin Zain Abeed bai samu damar ganinsa ba, sai yanzu yau ya gansa dalilin Sara, who is she to him? Mene Matsayinta a wajansa, koma dai menene she's very special to him, ta zama wani ɓari ne na rayuwarsa baki ɗaya shine abinda kawai zai ɗauka.... Auta da Nadiya na zaune suna kallon ikon Allah, Nadiya tace "I love his style, I luv his golden voice, I luv him completely.... Billahil lazi Auta" Auta tayi Murmushi tace "Yaa Abeed ɗin kike so?" Nadiya tayi fari da idanu tace "Of course YES, is there any problem with dat?" Auta ta watsa hannu tace "Kawai it's difficult shine, naga ko mu baya damuwa daya kalle mu bare yyi mana magana" Nadiya tace "Pardon! Do you know him somewhere before?" Auta tace "In sha Allah, ɗan gidan ƙanwar Mami ne, babban abun bayan shi mawaƙi ne kuma Yarima ne ɗan Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas na Masarautar Bilhira" Nadiya ta waro ƙananan Idanunta tace "Stop kidding me, Auta" Auta tace "I'm telling you Nadiya Ahmad Bala" duk mganar da suke feedy na jinsu, M.c yace "Please Zain Abeed, muna buƙatar jin waƙar ka a zahiri ba'a waya ko t.v ko redio ba" A lokacin Abeed ya gama ƙara sawa gaban, ya jima yana kallonta cikin kamewar sa, da mmkinta sai taga ya miƙa hannunsa tare da amsar speaker ɗin hannun M.c, still idanunsa akan Sara a hankali kamar fitar amon wani sauti mai ɗauke da sarewa Sara taji yace.
MAKOMATA...
Ya faɗa yana kama hannunta tare da matse tafin hannunta ya sanya yatsarsa guda ya shiga shafa tsakiyar hannunta kamar mai mata tafiyar tsotsa, hakan yasa ta nemi yin baya ya ɗanyi saurin janta sukai very close da juna Idanunta da sukai rau rau da hawaye, Students abin nema ya samu kusan kowa na wajan iphone yake using suka shiga kunna Camera tare dayin playing na vedio. Cikin daddaɗar Muryar da a kullum masoya Abeed take ƙara narkar da zuciyarsu ya shiga yin waƙar sa cikin baitoci kamar haka.
Zuciyata tai wa kidnapping
Sam na gaza yin dragging
Kullum ga ni cikin crying
Bari zancen selfdepencing
So shi ne maƙurar attacking.
Farkon fari ni ke prauding
A so can sama na yi rising
Na gagara babu diminishing
Na ƙetara hanyar deforming
'Yammata koyaushe thrilling.
Na ruɗu da yayi ina smiling
Na bi waccan ina crushing
Da hango wata sai betraying
Ta rasa sukuni tana ta begging
Nai biris buƙatarta nai refusing.
Tana kuka ni ko laughing
Ba batun wani regretting
Babu jin ƙai ina ta waving
Wai ni Cele ina ta feeling
Da kwanciyarta nake exulting.
Baby numfashina is undulating
My sense's link is almost breaking
Ga Lambun zuciyata is drying
Please ko borehole zo ki drilling
Neman ceto ne ya sa nake squealing.
A sama hotonta ne yake flying
Bakina harshenta yake ta sensing
Mami ta yi faɗan ta yi warning
Na gaza bi zuciya na obfuscating
A gaskiya yunwarta nake kui believing.
Abokai don Allah ku tayan pleading
Wallahi I'm insane zan yi hooking
Ku taimake ni kada na yi loosing
Ku yi gaggawa na kusa deceasing
Idan ba a ita life ba sauran dreaming.
Yana kawowa nan,ya saki speaker M.c ya tare da gudu, Hall aka shiga ihu ana faɗin "Wlh you're the best Singer in the town, Zain Abeed we love you" kafin kace me Caaa an rufe Abeed da ruwan kuɗi ana masa liƙi hadda Aryan Vice President's son dake neman ganawa da Abeed ɗin, Abeed dai sai ya tsuna fuska yake, can ya zame tare da kama hannun Sara ya jata zuwa waje, ganin hakan yasa Auta Miƙewa tana ɗaukan handbag nata, Nadiya tace "Help me Auta.. Wlh ina sonsa" Auta tace "Jeki faɗa masa to" ta ware idanu tace "Wlh i can't tab, Wannan babu macan da zata iya kawo masa wargi" Auta dai bata sake magana ba tayi waje, Yarima Yashim kasa motsawa yyi sbd wani irin sarawa da kansa yake masa, Zamewa yyi kaɗan tare da zama yana kama kansa dake ƙoƙarin rabewa gida biyu. Abeed na zuwa ya buɗe gaban mota tare da cilla Sara ciki ya rufe, Auta na zuwa ya haɗe rai hakan yasa da sauri ta juya ta nufi motar ta, Abeed na tsaye ya harɗe hannayensa a ƙirji yana duba Diamond Rolex ɗinsa, not too long sai ga bodyguards nasa su wajan miyar manya manya dasu, sun sako Aryan a gaba wanda yake ce musu "Menai muku?" Ganin Abeed tsaye jikin mota idanunsa akan waya yana dannawa, yasa yyi shiru da bakinsa sai daya gama abinda yake kafin ya ɗago idanunsa daya fara sauya launi tare da kallon Aryan dasu, ɗaya daga cikin guards ɗinsa ya kalli Aryan yace "Hanyar da Mrs Abeed tabi kada ka sake binta, balle kayi tunanin wani abu,duk ranar daka sake ɗaga idanu ka kalli Mrs Abeed zakai ladamar kasancewar ka a raye" da Mmki Aryan yace "Am vice President's son nima ina da iko" wani ƙyakƙyawan mari guard ɗin ya sakar masa yace "How dare you? Ehh who are you mene vice president waya sonka Ubanka aka sani, shi kasan waye shi?" Aryan yace "Matarsa ce ko mene?" Wani marin za'ai masa a hankali cikin kakkausar murya Abeed yace "Nooo!" Hakan yasa aka fasa Marin Aryan a hankali Abeed ya taka gaban Aryan tare da ɗura bakinsa a kunnan Aryan ɗin ya shiga yi masa magana, da sauri Aryan yace "Am sorry, am so sorry please ban sani ba" Abeed bai sake bi takan Aryan ba, ya buɗe gaban motar suka haɗa Idanu da Sara, wacce hawaye ki sakko mata ɗauke idanuna yyi tare da kama hannunta ya fito da ita, da sauri guards ya buɗe masa back seat, ana buɗewa ya saka Sara ciki a hankali Shima ya shiga ciki aka rufe musu,sai a lokacin Khabeer ya ƙarasa wajan ya shiga driver seat, sauran bodyguards ɗin suka shiga nasu motar, cikin nutsuwa motocin suka fara bita all abinda ke faruwa akan idanun Yarima Yashim wanda yake ƙoƙarin rasa ransa, tafiya suke amma Ƙamshin Hugo boss ɗinsa ya gama cika mata hanci har bata iya buɗe Idanunta, tana haka taji wayar hannunta ta Auta tayi ƙara alamar notification ya shigo, buɗewa tayi messages ne daga number Jaan, da sauri ta kalli Abeed taka idanunsa rufe sai Wayarsa take hannunsa, Idanunta ta mayar kan wayar ta fara duba saƙon _“stop hurting me, ur tears mean anything to me, stop crying Pinky, take this💋as rarrashi ok”_ da sauri ta ɗaga kanta suka haɗa Idanu da Abeed dake bin screen ɗin wayar da kallo hakan yasa tayi saurin ɓoye wayar, gently ya miƙa mata hannunsa ta kallesa tace "Wayar Auta ce" baice mata komai ba ya ƙara miƙa mata hannunsa tayi baya da wayar, inda ransa ya ɓaci bai fiya magana ba hakan yasa ya daka mata ƙyakkyawar tsawa dalilin hakan ne