Showing 39001 words to 42000 words out of 193443 words
Chapter 14 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt
yana tsaye yaji Sallamar Amintacciyar kuyangarsa tana nemawa Dad Waziri da Uncle AY iso, kasa magana yyi can ya nisa yace "kece ina hutawa ne" yana faɗin hakan ya shige bedroom. Amma na shiga part ɗin ta, ta haɗe kai da gwiwa ta shiga rera kuka kamar yarinya, ita kam wace zata tara da wannan mgnar? Ko Anuty Zulfa zata kira? Ko kuma ta kira Rooma? Wlh ta shiga uku wajansu idan ta kira, Zulfa ba taƙi ta tashi jet yanzu ta sauka a 9ja ba. Har kusan Subhi tana zaune bayan tayi sallah ta dinga addu'a Ubangiji ya kare mata ɗan ta ya zaɓa masa abinda yafi masa alkairi a rayuwarsa. Washegari da safe tun wuri Zain ya shirya yabar gidan, domin gidan yyi masa zafi sosai, he can't believe cewa yau baya tare da Biyuninsa, tsanar Riya ya ninku cikin zuciyarsa. Sara na part ɗin ta sai ta gaji da zaman ta ɗan leƙo wai taga ko Abeed ya dawo. Abeddeen na fita kai tsaye airport ya nufa, yaso ya samu jirgin da zai tashi a daran zuwa anywhere na country amma babu, dole ya nufi Tahir hotel ya amshi key ɗin room, kowa na mamakin ganin Abeed, domin sun ɗauka ɗa ɗaya ne da Mai martaba ba, ba'a taɓa saka photon Abeed da Zain su biyu a media ba, abu ɗaya suka sani duk Acct ɗin da suke using suna saka ZAIN ABEED. Rufda ciki yyi akan bed tare da rufe idanunsa yana sauke numfashi a hankali, gaba ɗaya baya samun iska wadatacciya tamkar wanda Numfashinsa ya cushe haka ya keji. Miƙewa yyi ya nufi wajan window tare da tsayawa ya shiga shaƙar fresh air dake kaɗawa, har lokacin idanunsa jajir suke, sai ajjiyar zuciya yake Saukewa. Yana tsaye a wajan har Subhi kana ya shiga bedroom yyi wanka tare da yin alwala, bai iya shiga Masjid ba, a nan yyi sallah ya zauna, yana jiran gari yyi ya sake ya duba Flight ɗin da zai tashi. Naila ce zaune ita da wata tsohuwa mai shekarunta tace "Ai Hanne ban san lalacewar ki takai haka ba, sam babu zumunci acikin lamarinki, dan kina talaka ai ba cewa nayi bazan ƙawance dake ba" Hanne dake fama da naman kaza tace "A'a, ai kana zaune ne kawai da mutum baka san zuciyarsa ba, Lalacewa dai a lalace bai kai ki ba" Naila tace "Niba wannan ba, ko ki tambayeni shalele" Hanne tace "Ai tunda Allah ya nufa naman nan ya ɗauken hankali na manta komai kiji na faɗa maki, yana ina ne? Nasan yanzu ya zama zabgege" Naila tace "Ai kiji na faɗa maki, ya zama babban mawaƙi a Kano, kin san Kano tafi duniya girma fa, to babu wanda bai san shi ba" Hanne ta riƙe baƙi tace "Kice Allah? waƙa dai wacce ake ji a rediyo ake gani a talabijin?" Naila tace "To ai ban zama gantalalliya ba, har yanzu da raguwar imani na, bare na fara ƙarya"Hanne tace "Ikon Allah, kuma bama yafi kowa iya waƙa a kano bama a duniya ba? Kin san girman da kano take dashi duniya bata dashi fa" Naila tace "Daman, ai duk masifar daza kiji anyi a Kano da Nijeriya ai Ba'ayi a duniya, ita duniya ai mutanan cikinta ka ɗan ne, shiyasa burin kowa yazo Kano fa" Hanne tace "Bawai, ke dai kakarki ta yanke ƙaga, ɗanki sarki jikanki mawaƙi a kano ki gode Allah wlh ina faɗa maki" Naila ta ɗauki nama ta saka a baki tace "To ai zuciyar ce a tsarkake bana nufin kowa da sharri, imani ne ai ba duk musulmi ba shiyasa ai har yanzu mutuwa ta gagara ɗauka ta" Hanne tace "To yanzu yana ina,kira mana shi mana" Naila ta ɗauki sanda ta miƙe tace "Biyoni muje" Bayanta Hanne tabi hannunta riƙe da nama. Sashen Amma shiru babu kowa sai ƙarar t.v da Sara ta kunna, shigowa gidan Naila tace "A'a ya naga wayam? Ina mutunan gidan suka bar tangamemen gida haka a buɗe" Sara ta ɗan leƙo da kanta daga wajan dining room, Naila tace "Algunguma ashe kina ji, kike zare ido, ina jama'ar gidan" Sara da tayi raurau da idanu tace "Kowa yana part ɗin sa" Naila tace "Bawai, ƙila shalele na opis, to ina faɗa maki wannan ita ce matar da Junaidu zai aura, to ba sai dai muce Allah ya kaɗai fitina ba" Hanne tace "Alkur'an ƙyakƙyawa da ita, kamar ita tai kanta" Naila tace "Sai dai kyan ɗan macici, dan dai bana gulma dana cewa maki ita arniya ce" Hanne ta dafe ƙirji tace "Arniya fa? Bata sallah" Naila tana yin gaba tace "A'a bana son gulma kowa bada ƙaddararsa ba, to wlh bata Sallah masifa ce kawai Junaidu ya ɗauko mana" haka sukai gaba Hanne hadda juyawa ta sake kallon Sara tana faɗin "Bawai shiyasa gata nan jajurr wlh" Suna fita ta fito daga dining room ɗin hannunta riƙe da Apple, gaba ɗaya zaman gidan ya isheta, duk kowa ya shige Amma haushin Mai martaba ta keji, Mai martaba kuma fama yake da ciwon kai, yayinda Zain yyi ficewarsa. Tana sanye da duguwar riga Abaya blue wacce tayi mata kyau, ƙafarta sanye cikin flat show, tafiya ta keyi harta bar sashen su Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ta zagaya can baya gidan sarautar, wata ƙofa ta gani da alama ba'a fiya shigewa ta cikinta ba, samun kanta tayi da fita ƙofar, sosai tayi mamakin ganin wani kwantaccen titi mai masifar kyau, ga wasu red ɗin fitilo dake duhu ya fara, kamar daga sama taji ƙarar tsayawar wata baƙar mota a gabanta, baya tayi da ɗan sauri tana dafe ƙirji, buɗe motar akai aka fito wani dugun Mutum ne ya fito, fuskarsa rufe baƙi ne sosai, aka ƙara buɗe motar aka fito gaba ɗaya mutanan suka kalli Sara ɗaya yace "Ina tunanin itace wacce muke nema" Ɗayan Mai suna Gaza yace "Bari mu ƙara tabbatarwa" Wayarsa ya buɗe photon Saraa ya bayyana, ya kalli photon ya kalli Sara yace "Billahi itace, Kutumar uba duk wahalar nan da muka sha ashe tana garin Kano" Ɗayan yace "Gaza ma lokacin ɗauko ta muje kawai" jin hakan yasa Sara sakin kuka tare da yin baya ta rasa sunan waye zata kira can ta ƙwalla ƙara tare da faɗin "Twin......
_Zain Abeed isn't free.... Kiji tsoran Allah ki sani ba haƙƙin ki bane.....zamu haɗu wata rana..08119237616 for more information_
Barka da juma'a❤️❤️ai weekend lafiya😍
[08-15 08:45] +234 703 831 1110: *17 Nimcyluv*
Baki Sara ta buɗe zata saki ihu, Gaza yyi saurin sanya hannunsa tare da rufe mata baki ya ɗauke ta cak zuwa cikin motar yana faɗin "Don't scream, calm down" Gaza ya faɗa bayan ya sakata a motar, suka ja motar da gudu tare da barin wajan. She can't cry sbd har yanzo bakinta yake a rufe, tsoro da fargaba sun cika mata ciki, tunani ne a ranta, domin a hankali nutsuwar ta ke dawowa jikinta, sbd ƙarfin addu'a da ruwan da take sha wanda Abeed ya bata, shiru tayi cikin motar tana sauke ajjiyar zuciya, bayan ta zame jikinta daga hannun Gaza, tunani ta fara da Zuciyarta, _Listen to your breathing Sara, Easy. Don't force it, Just concentrate. Listen_ wata ƙyakkyawar ajjiyar zuciya ta sauke Zuciyarta na bugawa da ɗan ƙarfi _What am i going to do now? How am i going to survive? Will i ever see Twin Again? What used to be my real life back in Nasarawa?_ Jin wasu tunani na zuwar mata ka wanda ya jima bata yisa ba, ya sanya tayi shiru dalilin sarawar da kanta yake mata, a haka har bacci ya ɗauke ta cikin motar suna sharara gudu. Wayar Gaza ta ringing da sauri ya ɗauka yace "Hello!" Shiru yyi can yace "Owk, we are on our way...." Kashe wayar yyi ya kalli driver yace "Heyyy, driver faster.." . Zain bai shigo gidan ba sai wajan 1:4 na dare, gidan shiru babu motsin komai har lokacin babu wanda yasan cewa Sara bata ciki, part ɗinsu ya shiga yay shower, kana ya shirya cikin kayan bacci, har ya kwanta yaji gaba ɗaya ɗakin yyi masa girma sosai, Miƙewa yyi gently ya fito Main Parlo ya kwanta, ya jima a haka kafin bacci ya ɗauke sa, Kiran Assalatu ya sanya Zain buɗe idanuna a hankali, ya miƙe bakinsa ɗauke da addu'a, part ɗinsu ya shiga yyi alwala, kana ya sauya kaya zuwa Jallabiya, a can mosque ya haɗu da Junaid da Dad Waziri sai Abba, ana idar da sallah bayan ya gaishe su, yayi tafiyarsa zuwa part ɗin Naila, domin ya ɗauke mata kewar Abeed, domin Abba yace kada wanda ya sake ya faɗa mata cewa baya gidan. Misalin 10 na safe Amma ta fito zuwa part ɗin Sara ganin har yanzu bata fito ba, tura ƙofar tayi shiru babu komawa a hankali cikin nutsuwa ta shiga kiran sunanta "Sara! Sara! Sara!" Shiru, ƙarasa shiga tayi sosai tayi mamakin rashin ganinta ciki, fita tayi ta gama zaga babban sashen nasu amma babu Sara, da sauri ta kira Jakadiya Abar, Jakadiya na zuwa ta zube bayan ta gaisar da Amma, tace "Uwar ɗaki na, naji kira na amsa" Amma tace "Ba kiga motsin Sara ba?" Jakadiya Abar na ƙara yin ƙasa da kanta tace "Allah ya ƙara girma Fulanin Bilhira rabona da Sara Tun shekaran jiya" Dafe goshi Amma tayi cikin kaɗuwa tace "Ya Salam, please ki duba ko ina ki sanya hadimai da fadawa su duba ta..." Tana faɗin hakan ta juya da sauri da ƙyar take kallon hanya sbd ciwon da kanta ke mata, hawan jininta na neman tashi, Amma nada hqr sosai, shiyasa hawan jini ya kamata in one time. Part ɗin su Zain ta nufa, bata tsaya jiran iso ba ta shiga bakinta ɗauke da sallama, time ɗin Zain na zaune akan kujera idanunsa akan system, amma zuciyarsa babu daɗi, ganin Amma ya sanya ya ajjiye system ɗin yace "Amma lafiya?" Amma ta kallesa kana ta kalli parlon tace "kaga Sara?" Ware idanunsa yyi yace "Sara?" Tace "Eh, i was looking for her, amma kakaf gidan babu ita wlh" Miƙewa yyi tsaye yace "Subuhanallahi, gaba ɗaya na mance da ita, kin san kanta ba saiti zata iya yin wani wajan" Amma wace take cikin tashin hankali tace "Dan Allah Zunaiddeen kada na rasa Sara please, ita nake gani ma dadin ɗan uwanka" kallon Amma Zain yyi, this is the first time da take Mgn akan Abeed, hakan na nufin she missed him irin sosai ɗin nan, ajjiyar zuciya ya sauke yace "In sha Allah,tana nan Amma" gaba Amma tayi tace "I hope so..." Ta faɗi hakan yana dafe kanta, baya tayi zata faɗi sbd jirin da take gani da sauri Zain ya sanya hannunsa ya riƙeta yana faɗin "Be careful Amma" Hannunta ya kama zuwa Main Parlo ganin yadda take ɗan ya motsa fuska, daidai nan Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ya fito sbd tuni ya samu labari wajan Jakadiya Abar, Amma na ganin Abba tayi saurin juyawa zuwa part ɗinta, da kallo kawai ya bita, yasan haushinsa ta keji, shi kansa bai san lokacin da ya furta hakan ga Abeed ba, Abba yace "Ka ganta?" Zain yace "Yanzu zan duba Abba" juyawa Abba yyi zuwa sashinsa, Zain kuma yyi waje, duk inda ake tunanin ganin Sara amma babu ita, kowa kuma aka tambaya zai ce bai ga fitar ta ba, Zain cikin tashin hankali ya koma kai tsaye ya nufi wajan Amma samunta yyi kwance akan bed jikinta na rawa, da alama zazzaɓi,abin yyiwa Zain yawa, fita yyi ya ɗauki wayarsu tare da yin dailing number Junaid. Junaid na zaune saman kujera yana sauraran abinda Dad Waziri yake ce masa, shafa kai yyi yace "Dad, mene yasa za'a zubawa yarinyar nan idanu? Wait wama yace tana da ciwon zuciya? Haka masu ciwon zuciya suke, duk wani sign na masu ciwon babu tattare da yarinyar nan" Ummi dake shigowa Parlo tace "Ke nan ni zan maka ƙarya? Tunda baki na dana likitan yake shaida min ciwon zuciya ne da yarinyar nan, haba Bama dole ciwon zuciya ya kamata ba, Wannan tsana da kke nuna mata tame ce, nina haifi ƴarta dan haka ka saurara mata haka nan, daman kai tuntuni ai na sallamawa Saratu kai, tun ta fini a wajanka" Junaid ya kalli Ummi yama rasa me zai ce, Dad Waziri yace "Mene yasa kika haka ke Sadiya? Junaid fa shine babba idan Bama raye waye zai kula da Riya?" Ummi tace "Duk al'ummar duniyar nan sai na rasa wanda zai kula da ita sai Junaid, a'a wlh wannan ma zance ne" Junaid yyi ƙasa da kansa yana mai jin takaicin abinda Ummi keyi, yana ƙoƙarin Mgna Wayarsa ta fara ringing, zaro wayar yyi daga aljihunsa ganin sunan Zain ya sanya ya miƙe da sauri, a tunaninsa zai ce masa Abeed ya dawo, yana picking yaji Zain yace "Where are you, Junaid?" Junaid yana ɗan satar kallon Ummi yace "At home, something new?" Zain yace "Sara, is missing" Da sauri Junaid har yana ƙoƙarin yarda wayar yace "What? Sara missing? When? How?" Ya jera tambayar yana waje, tashin hankali na bayyana akan fuskarsa, Zain yace "Kazo dai, wannan dalilin yasa hawan jinin Amma ya tashi" kashe wayar Junaid yyi ya nufi babban sashen dake cikin Masarautar Bilhira, Ruwa da drip Junaid ya sakawa Amma, Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas na zaune gefen bed ɗin Amma, ya kama hannunta ita dai tana jinsa ba tace komai ba, har su Junaid suka fita, Abba yana riƙe da hannun Amma yace "It's all my fault Hajiya Sarah, akan all these kike son kashe Kanki? Ni ya kamata kiyi punishing ba kanki ba, I'm the reason behind anything" Shiru Amma tayi masa, domin a wannan karan kawaicinta ya ƙare, hawayen dake sauka akan fuskar Amma, Abba ya sanya hannunsa kai taushi ya share mata yana ɗan share mata zufar goshinsa yace "I'm sorry wify, i hate your silence is hurting me" juyawa tayi ta kallesa suka haɗa idanu Mgn take sonyi amma ta kasa, da ƙyar tace "My Own child..." Sai kuma tayi shiru sharrr hawaye ya zubu mata, hawayen Mai martaba ya goge mata yace "It's okay, sleep" ya faɗa yana da shafa kanta idanunta ta rufe tana jinsa ya sumbaci goshinta..... Tafiya kawai Junaid yake cikin mota for almost 45 minutes not knowing that party direction she's heading to...He just can believe Sara is gone, ina zata? Wata sani a faɗin garin nan? Parking yyi a gefen titi lokacin kusan dab da magrib ne, kansa ya kifa akan string motar yana sauke numfashi, kafin a hankali yace "A karo na biyu na sake rasata..." Bayan sallar Issha Abeed ne zaune cikin Room ɗin daya kama a Tahir hotel, ya faɗa lokacin ɗaya idanuna ya fito sai kuma ya ƙara kyau, yana zaune akan kujera hannunsa riƙe da bottle water, tun ɗazo ya ɗauko zai sha amma ya kasa, damuwa tayi masa yawa, korar iyaye masifa ce, ace uban daya haifesa shine zai koresa daga cikin gidansa, ji yyi zuciyata tayi zafi tare dayi masa nauyi, idanunsa yaja ya rufe kafin a hankali ya ɗan sha ruwa, Wayarsa mai ƙirar iphone 13 pro max ta fara haske, ganin sunan Dr Adyan ya sanya yaja tsaki, wajan kira biyar yyi masa bai ɗauka ba, notification ne ya shigo wayar gently ya miƙa hannunsa message ne Dr Adyan yyi masa yace _Please Yariman Bilhira pic the call.....I went talk to you_ yana gama karantawa kiran Dr Adyan ya shigo, answering yyi tare da mannawa a kunansa yace "Uhm" Dr Adyan yace "Yarima try to understand abinda kke son aikatawa ba daidai bane..." Da sauri Abeed ya tsayar Dr Adyan cikin tsawa yace "Shut up, Adyan! I asked your advice because I respect your intelligent. I can't believe you're talking like one of those old Guy's....Uhm" yama kasa ƙarasa Mgnar sai ɗan cije bakinsa da yyi kawai, Dr Adyan yyi ƙasa da murya yace "Yarima kana tunanin zan cuceka?" Abeed na ɗan jan numfashi yace "Especially If someone's trying to run you over" Dr Adyan yace "But kasan ba zan maka haka ba, ina zaune dakai da zuciya ne ɗaya ne Yarima Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas, kawai ina faɗa maka gsky ne" Tsaki Abeed yaja yace "Bye..." Yana faɗin hakan ya kashe kiran baki ɗaya, Wayarsa ya duba yaga 10:45 ajjiyar zuciya ya sauke, zuciyata take samun nutsuwa ji yake kamar yyi ta ihu, idanuna ya rufe dif! dif! Haka zuciyarsa ke bugawa a haka bacci ya ɗauke sa ba tare daya shirya ba. Washegari da safe bayan Riya tayi breakfast ta ɗauki mayafin ɗinta ta saka, iso ta nema wajan Mai martaba, yana zaune saman darduma gabansa cike da kayan marmari yana sha, fuskarsa shima ta ɗan faɗa, ya ɗan saki Murmushi yace "How the you feeling now?" Riya tace "Feeling much better Abba" shiru tayi tana tunanin abinda za tace, Abba dai kallonta yake bai magana ba, can tace "Abba daman na fasa auren Abeed ɗin ne, akwai wani wanda ke sona shi nake son aura" da mamaki Abba ke kallon ta, ya daɗe a haka kafin yace "What made you change your mind?" Riya tana sakin kuka tace "Abba, ina son Abeed amma na fahimci baya sona, kona auresa ba zan farin ciki ba, gashi dalili na ka kore sa hakan bai min daɗi ba, yanzu idan ya faɗa wani mugun hali ba? Ba zan yafewa kaina ba Abba, bana son zumunci ya samu rauni saboda ni" Abba yyi ta kallon Riya wlh bai san tana da hankali har haka ba, yace "Abeed zai dawo, na san ba zai wuce Dubai, ko U.k ba ko Mascow daina kuka" Riya tace "Abba dan Allah kace ya dawo" kai kawai ya ɗaga mata kafin ta miƙe tsaye tayi waje. A Main Parlo taga Zain zaune ya gama shirin office damunsa tayi yana waya yana faɗin "Don't worry, calm down Sweetheart. Give me a minute to think ok" Du'a ta ɗan shagwaɓe fuska tace "Gaba ɗaya saura kwana uku bikin mu, amma baka taɓa zuwa inda nake ba" ta faɗa kamar zatai masa kuka, shi kam sbd kada ya kula Riya