Header Ads
Showing 57001 words to 60000 words out of 193443 words

Chapter 20 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Hawaye na zubu mata ta buɗe baki ta amsa, ta naci tana kuka har taci da yawa tace "Na ƙoshi" sakin fuskarta yyi ya nuna mata ruwa sha tayi tace "Hannunka ya ɓaci" bashi da kuzarin tashi sai kawai ya miƙa mata hannun tissue ta ɗauka ta riƙe hannunsa a hankali ta goge masa tass ta ajjiye hannun, tagumi tayi tana kallon sa ido ya buɗe suna haɗa ido ya zare mata ido yace "Uhm, go and sleep" zatai Mgn ya ɗaga mata hannu, tashi ta nufi bed ɗin tayi lamo kamar jira ake bacci ya ɗauke ta. Abeed ya jima a wajan kafin ya miƙe ya nufi bed ɗin, wata paper da piro ya ɗauka hannunsa yana rawa ya shiga rubutu cikin handwriting ɗinsa mai kyau ya jima yana rubutu ya nayi yana kallon Sara dake motsi har ya gama, ninke paper yyi tare da zirawa cikin aljihun wandon dake jikin Sara, kwanciya yyi idanunsa na kallon sama a haka bacci ya ɗauke sa.


Wajan Subhi Dr Haris na zaune a office ɗin sa yana duba wasu files da wani bayani da aka tura masa ta e-mail, ajjiyar zuciya ya sauke yana gamawa ya miƙe zuwa mosque, tare da Khabeer ya dawo cikin ward ɗin yana ta so ya tambayi Khabeer family na Abeed amma ya kasa, suna shigowa ward ɗin na'urar dake room ɗin Abeed ya fara ƙara da wani irin sauri, gaba ɗaya ya cika ward ɗin kusan likitoci goma ne suka fito time guda suna tafe suna magana da juna a gurguje, room ɗin Abeed suka shiga lokacin har ya gangaro ƙasa bai idda faɗuwa daga bed ɗin ba, hannunsa riƙe dana Sara wacce ke bacci, gaba ɗaya yyi aman jini akan bed ɗin ya ɓata jikinsa dana Sara, jikinsa na rawa yana wani irin mimmiƙewa Numfashinsa na fuska fuskar nan tai wani irin fari tas, gaba ɗaya likitocin tsayawa sukai suna kallon yadda computer dake kula da Numfashinsa ke tafiya daga 100 zuwa ƙasa, Abeed Sara yake son tashi amma ya ƙasa wlh duk wanda ya kallesa a lokacin sai yyi kuka domin duk wani ƙwararran likitan yasan Abeed lokaci kawai ake jira, Dr Haris ne ya share zufa tare da ƙara sawa wajan ya shiga tashin Sara da sauri ta buɗe ido tana tashi taji muryan Abeed na faɗin "Saaaaa, Saraaarh" zumbur ta miƙe zaune a rikice tace "U..... Uncle...." Bama tasan kalmar ya fito mata ba, kuka ta sanya Abeed kuwa ganin ta farka ya Sanya ya riƙe ta a jikinsa ƙam ƙam tamkar zai tafi lahira da ita, wata irin runguma yyi mata wanda duk mai hankali zai gane cewa baya cikin hankalinsa yana tare da Mala'iku masu yiwa ransa mara ba, fita Dr Haris yyi da gudu ganin alrdy Numfashin daga 100 ya dawo 76, yana zuwa waje Dr Zulfa na shigowa yiwa wata mata operation, da sauri Dr Haris ya ƙarasa wajan Dr Zulfa zatai magana yaja hannunta da sauri zuwa room ɗin, tun daga bakin ƙofa zuciyar Zulfa ke bugawa bin Dr Haris take kawai, zuwa tai wani irin zare ido waje tace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Abeddeen.." da wani irin sauri ta ƙara sawa ciki tare da cewa "Get ready Dr Haris zamu shiga theater yanzu" tana faɗa ta nufi wajan Abeddeen Sara tabi da kallo wacce take kuka tana faɗin "Uncle, Twin ka tashi.... Uncle nima zan bika ka buɗe idanunka..." Wani irin zabura da Abeed yyi ya sanya Anuty Zulfa zubewa kan kujerar kusa da bed ɗin Abeed lokacin kuma Numfashinsa yana 23 gaba ɗaya likitocin suka rufe Abeed har lokacin kuma Abeed yana rungome da Sara duk jinin dake fita a jikinsa ya wanke mata shi, Hawaye na fita a idanun Anuty Zulfa ta shiga faɗin "La'iha ilillah Muhammadur ya s.a.w" kamar jira ake Abeed ya shiga nanata "La'iha ilillah Muhammadur Rasulullah s.a.w" idanunsa na wani irin sama yana cikin faɗa suka ji shiru ya daina faɗa Na'urar cak ta tsaya da aiki, da sauri Anuty Zulfa ta duba jikin Computer taga 0... Miƙewa tayi ta kama hannun Abeed amma ina baya tayi zata faɗi Dr Haris yyi saurin tare ta, yace "Aikin za'ai masa?" Hawaye na gudu a fuskarta kuka na son kwance mata cikin wata iriyar Murya tace "He's gone... Abeed die Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Abeddeen ya mutu.....




😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭 Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un......


Zain Abeed isn't free contact to subscribe dan Allah 08119237616
[08-15 08:45] +234 703 831 1110: *24 Nimcyluv*
Ɗit! Ɗit! Ɗit! Na'urar ta dawo da ƙara da sauri jikin Dr Haris har rawa yake Wajan faɗin "he still alive.." Miƙewa Anuty Zulfa tayi wani irin Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da taga yatsun hannunsa na motsawa numfashi na sauka a ƙirjinsa, Sara tunda taji Anuty Zulfa ta ambaci mutuwa ta wani ja ajjiyar zuciya da ƙarfi tare da kwanciya kan Abeddeen ɗin a sume, a gurguje Anuty Zulfa ta shiga haɗa kayan theater tana kallon Dr Haris tace "Take her into another room....." Dr Haris da wata likata suka sauyawa Sara gado tare da tura ta zuwa wani room ɗin, likitan da wasu likitoci mata suka rufu a kanta, Anuty Zulfa na sanya riga jikinta tace "Follow zuwa Theater Room" gadon da Abeed yake kai suka tura tare da bin bayanta, Khabeer da yaci kuka ya ƙoshi ya nufi Mosque domin yiwa Abeed addu'a, Danish kuwa kaiwa da komowa yake yana faɗin "Oh, Jesus" likitoci wajan goma ne akan Abeddeen babu wanda yake magana cikin su, sai dai kawai aiki su, gefe guda na zuciyar Anuty Zulfa tana addu'ar Ubangiji ya sanya tayi aikin nan a Sa'a duk dauriyarta jikinta rawa yake, suna aikin wata likita mace na ɗan bubbuga bayan Anuty Zulfa alamar rarrashi...... Fitowa Amma tayi daga kitchen hannunta riƙe wani glass cup sai bottle water, tana zuwa tsakiyar Main Parlo taji jiri ya kwashe ta kafin taji Zuciyarta ta buga gaba ɗaya ruwan da glass ɗin suka zube a ƙasa hakan yyi daidai ta faɗuwar wani photon Abeed dake maƙale jikin bango shima a nan wajan ya tarwatse, hannu Amma ta sanya ta dafe kanta tare da cewa "Abeddeen? What happened to my son, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta faɗa tana zubewa a wajan tare da ɗaukan photon Zain da Abba dake shigowa daga sallar Asr suka kalleta kafin Zain yace "Amma lafiya?" Ya faɗa a sanyaye domin shima yau gaba ɗaya wani iri ya tashi, ga mafarkin Abeed da yake ga kuma faɗuwar gaba, Amma tace "Zain Biyuninka....Zain look?" Kasa Mgn tayi sai nuna masa photon Abeddeen da tayi wajanta ya ƙarasa yace "Mene Amma? Ya kira ki ne?" Amma na kuka tana faɗin "Wani Abu ya faru da Abeed ɗina, Zain wlh Abeed baya cikin kwanciyar hankali jikina ya daɗe da faɗin haka, kaje ka nemo Abeed ya dawo gareni ko wani abune zai faru dashi ya kasance yana kusa dani" Abba ya riƙe ta yace "Zain go and call Junaid for me.." Amma ta kalli Abba tace "Abeed ɗina wani abu ya faru dashi, jikina ya bani haka dan Allah ka dawo min dashi kace ka yafe masa i donno wanna lose him, i love my son" riƙeta Abba yyi sosai ganin da gaske bata hayyacinta kuka take sosai har lokacin Zain ya shigo yana gaba Junaid na binsa sanye da fararen kaya, Abba yace "Junaid ina injection ɗin da kke ma Saratu?" A hankali Junaid yace "gata Abba" Abba yace "Ok zo kayi mata" haɗa infection ɗin yyi Amma na jikin Abba yyi mata allurar, nan take idanunta ya fara rufewa tace "Abeed come back to me son...am where mother zan kula dakai please come back" A hankali Abba ya kwantar da ita kan Kujera yana jan numfashi kafin ya kalli Junaid da Zain yace "Wacce ƙasa kuke tunanin Abeed zashi?" Zain da zuciyarsa ke tsananin bugawa yace "Paris, Mascow" Junaid dai baice komai ba, Abba yace "New York fa?" Kafin Zain yyi mgn Junaid yace "I don't think zai je can sbd Anuty Zulfa" Abba yace "Extly......zan saka SPIDER ya duba min domin ya gware wajan bincike" shiru duk sukai kafin Zain yace "Abba" Abba ya kalli Zain alamar yana sauraran sa Zain yace "If something bad happing to my Biyuni..." Kasa Mgn kawai yyi sai ya juya zuwa part ɗin sa, Junaid ma fita yyi domin kwanaki kaɗan suka rage ya koma aikinsa, Abba kallon Amma yyi dake bacci tana sauke ajjiyar zuciya...Zain na shiga part ɗin sa ya samu Du'a zaune tana kallo ganin yanayinsa ya sauya tace "Mene ya taɓa ran mijina" zama yyi kan sofa ta zauna saman cinyarsa tace "Mene ya faru yanayinka ya sanya bana son naga kana shiga damuwa haka" Zain da idanunsa sukai ja yace "Du'a wani abu ya samu Abeed, idan na rasa Abeed I'll never forgive my father, ba zan ya fewa Abb..." Da sauri ta rufe bakinsa tace "Subuhanallahi, haba kasan me kke son cewa kuwa? Kasan darajar iyaye ka rufa min asiri karabu dasu Abba, duk abinda Abba zai maka har abada kada ka sake cewa komai, yana da iko da kai but kai baka da iko dashi, zai iya yanke ko wanne hukunci a kanka amma kai ba zaka iya ba, baka da abinda zaka saka musu duk duniya, hukuncin da Abba yyi nadan cikin fushi da ƙunar zuciya yyi, babu yadda za'ai ka haifi ɗa a cikinka amma kace yyi kaza yace ba zai ba, dole ransa ya ɓaci yana ganin ya isa da Abeed tunda shine ya haifesa,mu bar komai wajan Allah in sha Allah komai zai daidai in sha Allah, nasan dole amma yyi ladamar yanke hukunci cikin fushi come closer.." ta faɗa tana rungome Zain tare da ɗan bubbuga bayansa alamar yyi hqe everything I'll be fine, shiru yyi yana jin yadda take shafa ƙirjinsa zuwa fuskarsa duk dan ya mance da komai, Murya can ƙasa Dua tace "pray for him, idan kai ma ka shiga damuwa yaya Amma Zatai? Kai da take gani ta ɗauka shine, Kai Naila ke gani ta ɗauka Abeed ne please be strong my man" kansa ya ɗaga ya kalleta kafin yace "Thank you wify... thank you alot Allah yyi maki albarka" Murmushi tayi tana haɗe bakinsa da nata Duk yadda Zain ke kaucewa sai da Dua ta jashi janta yyi sosai ya shiga kissing ɗinta yana sakin numfashi, ganin yana ƙoƙarin shigarta a nan ya sanya ta shagwaɓe tace "No please muje bedroom" Murmushi yyi ya ɗauke ta zuwa cikin bedroom... Lokacin da Junaid ya isa part ɗin su a parlo ya samu Riya da Ummi suna ganinsa sukai shiru baice musu komai ba ya shige part ɗin sa, Ummi ta bisa da harara tace "Gulmamme, ai tunda Saratu ta rabani dakai wlh itama ta rabu da ɗan ta ke nan har abada" Riya tace "Ummi yaya kukai dashi?" Ummi tace "Uhm, Malamin nan ai ɗan iska ne, yace kafin aikin ya shiga jikin Abeed dole ne a samu damar da za'a shagalar tare dashi kona shekara ne, amma idan har yana kwana da Alwala aikin ba zai ba" Riya tace "With don't have any prblm with dat kawai yyi aikin" Ummi tace "Eh, amma ai da matsala" Riya tace "tame Ummi?" Ummi tace "Yace dole ne ya kwanta dake, kuma dole ne sai yyi rubutu jikin ki" shiru Riya tayi Ummi tace "Ni budurcin ki nake gudu" Riya a sanyaye tace "Ummi ai bana da budurcin" da wani irin mmki Ummi tace "What, Riya baki da budurcin fa, ashe ina can ma saki baki ina zagin ƴar ƴan Mutane wanda suke karuwanci bani da labarin tawa ta gama watse wa a waje" Riya tace "Am sorry Ummi, wlh wata game akai wani ban waye ba gashi bana harka da samari, nace ma friends ɗina a waye nake, shine sukace idan haka ne naje club aga tabbaci ina zuwa aka haɗani da wani ɗan class ɗin mu muka kwanta tare dashi, kuma ba Ummi ance ai yanzu ƙauyanci ne zuwa gidan miji da budurci" Naila dake shigowa tace "Hoooo! Jakar uba to wlh tun tuni kafin mala'ikunsa su rubuta maki zunubi ki tuba, wanne Algungumin ke yace maki haka? To Allah na tuba mu a zamanin mu wama yasan aure bare yyi ya faɗi wannan kalmar tsirara haka, a'a wlh babu ruwanmu shekarun baya kana gudu miji na gudu babu wanda ya damu da wani wlh, Allah na tuba wannan nono ba sai a gidan mijin yake ɗan huduwa ba Allah ya sauwaƙa amma dai wlh ba'a haka ki tuba" Zama Naila tayi tace "Yana ganku kamar dai wasu munafukai, to wannan dai ba siffar mutanan ƙwarai bace" Ummi tayi Murmushi tace "Zuwa kikai Naila" a fusace Naila tace "Kaga masifa sai akace nida gidan ɗana ba zan zo ba, to ai ba iya mai rawanin can bane ɗana, harda Audillahi ciki ni ba dangi iya balle na baba ina ruwanki ne da zuwa? Kawai dan kina matar Audil, banda Allah ya nufa nima na saka baki da tuni ɗan garuwa kikai aure fa? To ai abin munafurci bane yarinyar da aka ɗauko da ƙyar daga gidan karuwai?" Riya tace "To ke kika ɗauko ta ko?" Naila tace "A'a Wacece ke, nidai ban saka dake ba ki rufa min asiri wlh tsoron haɗa hanya nake dake wannan ramar taki abin bincika ne" shiru kawai Ummi tayi deep down na Zuciyarta tana tsinewa Naila.


Ana kiran magrib suna kashe wutar ɗakin theater, a hankali likitocin 1 by 1 suka shiga fitowa daga cikin room ɗin Anuty Zulfa itace ƙarshe wajan fitowa, hannunta ta sanya ta goge zufar dake yanko mata idanunta sunyi wani irin ja, numfashi kawai take ja, Khabeer dake tsaye yyi saurin nufarta yana faɗin "Ya jikin nasa?" Kallonta tayi tace can tace "Muna saka ran tashinsa" tana faɗin haka ta nufi room ɗin da Sara take tana kwance itama drip na shiga jikinta tai wani irin faɗawa, ruwan ta zare mata ta ɗauki wani daban ta saka mata tare da sanya mata wata yellow ɗin injection kana ta rufe ɗakin ta nufi office ɗin ta, tana zama Dr Haris ya shigo ya zauna fuskarta a kame domin sai yanzu ta tuna da riƙentan da yyi tace "how long ka kasance kana kula da Abeed?" Yace "Duk sanda yazo ƙasar nan nike kula dashi, duk wata ƙasa da Yake zuwa yana da likitan sa a hannu" shiru kawai Anuty Zulfa tayi tana tunani kafin taji Dr Haris yace "kaga kamar kin san shi" da ƙyar ta iya cewa "Yeah, he's my son....i mean my sister's son" Dr Haris yace Allah sarki, Allah ya bashi lafiya" yana faɗin haka kuma ya tashi yyi waje, Anuty Zulfa shiru tayi ta shiga juya kujerar da take kai ta daɗe a haka kafin ta miƙe ta nufi toilet tayi Alwala Zhur, Asar ga Magrib haka ta jera su tana istigifari tare da yiwa Abeed addu'ar samun lafiya, tana zaune har Issha, bayan ta idar da sallah taji wayarta na ringing ɗauka tayi ganin me kiran, Yusra tace "Mami naji ki shiru lafiya?" Muryar Anuty Zulfa a sake tace "Listen to me Yusra, ki kwanta tare da Auta kin san Abbanku baya nan" Yusra tace "To kefa?" Anuty Zulfa tace "Zan kwana a hospital ok, da safe ki haɗa breakfast mai ɗan ruwa ruwa ki saka driver ya kawo min please sweetheart kuyi addu'a ok" Yusra a sanyaye tace "Bye Mami" kashe wayar tayi gently ta miƙe ta nufi ɗakin hutawar da aka kaisa, yana kwance flat idanunsa rufe sai green riga dake jikinsa kumburin fuskar dana ƙafar ya saɓe, Numfashinsa ya daidaita amma har yanzu oxygen ɗin yana bakinsa, fita tayi ta nufi room ɗin Sara tana zuwa ta samu Dr Haris a wajanta daga inda take bata ƙarasa ba tace "Ya nata jikin?" Yace "Allahamdulillah, amma ta shiga duguwar suma anytime zata iya tashi" kai ta ɗaga masa da sauri tana barin wajan... Ranar Anuty Zulfa a wajan Abeed ta kwana cirr bata runtsa ba, wani irin so da ƙaunar sa take tun ba yanzu ba, balle yanzu data san meke damunsa, da Subhi tayi sallah a nan room ɗin kana ta ɗauki wayarta dake ƙara ta nufi waje tana faɗin "I want to talk to you Abban Yusra.... serious talking" yana daga can ƙasar da yake zai shiga airport yace "Am on my way yau zan dawo" tace "Ok luv Allah ya tsare ya kiyaye sai kazo" Yace "Ok My lady be strong, ko dan ciwon ɗan ki ne Shine zaki zama raguwa" tana ɗan Murmushi tace " Is not like that.... wlh he's critical condition Saratu ba zata jure ba nasan yadda take son Abeed fiye da komai na nan duniya, komai nasu ɗaya ne da Zain amma son da take ma a Zuciyarta special ne" Yace "Owk, ok My lady zan shiga jirgi bye luv u" kashe wayar tayi tasan idan plan ɗinta ya samu shiga har abada ba zatai ladama ba hakan kuma shine daidai ga duk su biyun.....Masarautar Zahel Sairah ce ta kalli Subash tace "Me yasa kuke dake sani ne?" Da mmki yace "Wanne sani? Akwai wanda ya sanar damu wani abu ne?" Kallonsa tayi tace "Baka san Littafin ku ba ke nan? Baibul ko a ciki ba'a faɗa muku cewa Allah ɗaya bane bashi da abokin tarayya bai haifa ba, ba'a haifa masa ba, Sannan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama shine Manzon Allah na gsky, wanda Allah ya turo sa da Littafin Alkur'an kafin kuma Isra'il da mi'iraji su bashi damar zuwa amsar sallah?" Shiru Subash yyi kafin yace "kina nufin Mu ɗin nan yinmu akai?" Was so surprised Sairah ke bin Subash da kallo kafin tace "To waye yyi ku?" Ya ɗaga mata kafaɗa tare da wargatsa hannunsa alamar waya sani, can kuma yace "kawai a haka na ganni, Mabus yace babu abin bautawa sai Abin bauta kabas da dodo, sune suke bamu abinci ruwa, iskar shaƙa da komai?" Miƙewa Sairah tayi tana hange hange tace "Akwai ƙwayar wake kota masara" shiru yyi can kuma yace "Ban sani ba" tace "Addinin Musulunci ya zo ne daga Allah ta hannun Annabi Muhammad(SAW) tsira

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads