Header Ads
Showing 69001 words to 72000 words out of 193443 words

Chapter 24 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ko ta mece ba, tana kallon sanda ya gaji da tsaiwa kafin ya shiga motarsa ya jata da wani irin gudu yyi waje, a wahalar ce ta sauke numfashi kana ta juya tare da kwanciya kan gado tana jin wani iri a Zuciyarta,ita mene ba za tace da wani Yarima Yashim? Mutum zai shegen surutu kamar yaci naman aku.. Abeddeen gudu kawai yake saman titi idanunsa a rufe sbd wani irin mugun ja da sukai wanda kai tsaye ba zaka iya gane jan mene yyi ba, furzar da iska yyi kafin ya ware idanunsa sosai akan motar dake bin bayansa ta cikin mudubi, taɓe baki yyi yaci gaba da gudu har ya ƙarasa gidansa yana kallon motar ta tsaya daga can baya, gatekeeper ya buɗe masa gate ya shiga. Wata magidanciyar mata dake cikin motar taja numfashi tana sanye da baƙaƙen kaya gaba ɗaya ta rufe fuskarta, Sarki Mabus dake zaune yace "Shegen mutum...., Ni labarin dukiyarsa kawai na keji amma ban taɓa ganinsa ba" Ayyana dai ba tace komai ba sai kanta kawai da take girgiza wa alamar waƙa take a Zuciyarta, Sarki Mabus yace "Juya Ayyana, kafin mu samu nasara akan wannan zamu sha wahala, shigar dare za muyi masa" key tayiwa Motar ta juya zuwa hotel ɗin da suka kama, ita ce ta fara fita zuwa reception kafin Sarki Mabus ya biyo bayanta, yyi shiga ta kamala ya ɓoye a salin waye shi, yana zuwa reception ɗin ya kalli Ayyana kana ya kalli mutanan wajan yace "Ashe kema nan kika yo, da Kinyi Mgn na rage maki hanya" ya faɗa yana amsar key, kai kawai ta girgiza tace "A'a, nama ƙarasu" Sarki Mabus yace "Sai haɗuwa muke ba tare da sanin juna ba" kallonsa kawai tayi tace "Daman hk ne" ta faɗa tana nufar wani hanya daban shi kuma ya nufi wata daban, sukai pretending babu wanda ya san da wani a rayuwa... Parking Abeed yyi ya jima cikin motar kafin gently ya buɗe ya fito, walking slowly kamar wani gwamna ko shugaban ƙasa ko kuma sarki haka Abeed ke tafiya, har ya shiga ƙayataccen part ɗinsa, Zama yyi saman kujera yana zama Wayarsa ya hau ƙara ganin number Danish daman ya buƙatarsa, answering yyi idanunsa rufe cikin wata Murya bata fita yace "ka sanya a gyara min ɗaya gidan zuwa dare..." Bai tsaya jin Abinda Danish zai faɗa ba, ya kashe wayar tare da Miƙewa tsaye jirin ɗaya ɗauke sa ne ya sanya yyi saurin kama hannunsa a tunaninsa bango ne, sbd wani irin juyawa da idanunsa sukai baya gane komai baya kuma fahimta, Bai san kuma meke faruwa ba, girgiza kai yyi cikin Muryar ƙaraji da tsawa yace "How dare you, ehhhh" ya faɗa yana tura hannunsa cikin sumar kansa kafin da sauri ya ɗaga kwalbar hannunsu ya shiga shan abinda yake cikinta, sai da ya shanye tass kafin yyi cilli da kwalbar ta dagi jikin bango gaba ɗaya ta fashe a wajan, surutai ya shiga yi kafin a hankali ya yanke jiki ya faɗi saman Kujera wani irin bacci yyi gaba dashi daidai lokacin da ake kiran sallar Asr, gashi ko sallar Zhur bai ba. Ana kiran sallar Magrib yana buɗe idanunsa kansa da yyi masa wani irin nauyi ya dafe, kafin ya miƙe a hankali kamar mai lura da yadda yake tafiya haka ya nufi bathroom, shower ya sakarwa kansa hannunsa duk biyun dafe da bango sai yanzu yake jin zuciyarsa sawai ba kamar ɗazo ba, bathrube ya saka tare da yin brush ya fito a Abeed ɗinsa mai cikakkiyar nutsuwa yana wani irin fidda ƙamshin Gatsby Leather Body Shower Gel, fatar jikinsa na zubar da ruwa, mirror ya nufa ya gyara samar kansa sosai kafin ya shafa body oil, wata Arabian jallabiya ya saka kafin ya shimfiɗa pra mat ya jera salloli Zhur, Asar, Magrib yana idarwa ya zauna har akai Issha kana ya gabatar, jallabiyar ya cire ya ɗauki Shawl Lapel Suit Nevy blue ya saka a jikinsa wani irin kyansa ya fito kana ganinsa kaga singer kuma Rockstar, Derby Shoes ya saka a farar ƙafarsa kafin ya ɗauki duk abinda yake buƙata ya nufi waje yana baza ƙamshi, wata Ford F-Series ya nufa tare da shiga bai tsaya jiran Khabeer ba, key yyiwa Motar mai Gadi ya buɗe, har zai shige sai kuma ya tsaya yana ƙarewa gatekeeper ɗin kallo kamar wanda akai forcing nashi wajan mgn haka ya buɗe baki fuska a kame yace "kada ka kwana a nan" yana faɗin haka yyi gaba, meeting ne dashi akan wasu da suke buƙatar waƙa daga wajan meeting ɗin kuma ya nufi gidan Anuty Zulfa, kusan a tare motarsa data Yarima Yashim sukai parking, Yarima Yashim ne ya fara fitowa cikin wata farar shadda mai ɗaukan idanu, nutsuwarsa duk ta bayyana, ba ƙaramin kyau yyi ba, jingina yyi da jikin motar yana kiran number Auta tana ɗauka yace "Assalamu alaiki sisten mu" Auta tana dry idanunta akan Sara dake zaune gaban mirror tayi shiru tace "Wlsm bro" Murmushi Yarima Yashim yyi yace "Ykk sis, gani dai na cika al'ƙawari hope ban takura ku ba?" Auta tace "Haba dai, bari na fito" tana faɗin haka ta kashe wayar ta miƙe tana kallon Sara tace "Yazo fa" Shiru Sara tayi tana kallon Auta harta fita, ita dai bata baƙin ciki da zuwansa infact tana ganinsa a shcl taji ya kwanta mata, amma ta rasa faɗuwar gaban me take, Tana nan zaune har Auta ta dawo tace "Gashi can a Parlo" shiru Sara tayi Auta tace "Wlh zan faɗawa Mami Allah" harararta tayi tace "To gulma" Miƙewa tayi ta shirya cikin Nidha Abaya dark brown wacce ta haska fatarta, tayi rolling kanta da Vail fararan idanunta sukai wani kalar haske, wani Haute Curry shoe ta saka, har zata fita sai ta tsaya ta saka perfume mai daɗi ta ɗauki wani peach ɗin Lip balm ta shafa akan lip's ɗinta, a hankali ta shiga tafiya zuwa Main Parlo babu kowa sai ƙamshi Air-con dake tashi, Yarima Yashim na zaune yana danna waya Ƙamshin Valentino ɗin jikinta ya sanya ya ɗaga idanunsa da wani irin sauri ya miƙe yana ƙara Kallonta wata ajjiyar zuciya ya sauke kafin gently ya ƙarasa inda take cikin wata kasalalliyar Murya yace "My princess" ya faɗa a nutse, Murmushi kawai tayi masa yana kashe mata idanu ɗaya yace "You're my princess, kina da kyau Saraa U look like takeaway" kanta dai a ƙasa ba tace komai ba, Yarima Yashim yace "Shall we....?" Kai ta ɗaga masa suka nufi kan kujera ta zauna saman 3Seater shi kuma kan 1Seater a hankali tace "Ina yini?" Idanunsa ya lumshe yace "Allahamdulilla, ya weekend naji kamar na shekara ban ganki ba, dana ƙara kwana ɗaya sai dai kizo kiga" ya faɗa yana langwaɓar da kansa gefe tare da fito da harshen sa waje ya zare ido kamar ya zama gawa, wata kalar haɗaɗɗiyar dry Sara tayi a karo na farko ganin Yadda Yarima Yashim ke da abin dry, shira suka shiga yi tun bata sakewa harta fara murya ya gyara yace "Serious Saraa, i love You ina Sonki ina son auren ki" baki ta buɗe zatai magana ƙamshin Bois elite da taji ya sanya tayi saurin ɗaga kanta tsaye taga Abeed gaban frizeer ya ɗaukan bottle water, jikinta ne ya ɗan fara rawa sai kawai ta maze ta kalli Yarima Yashim tace "Uhm" Yarima Yashim yace "Will you marry me Sara...zaki auren?" Ƙarar faɗuwar Bottle water ɗin da sukaji ya Sanya gaba ɗaya suka kalli inda Abeed yake, fuska ɗauke ya goge hannunsa sbd ruwan daya zubu masa yake ƙoƙarin tafiya hanci, kafin gently kuma walking slowly ya nufi kujerar da Sara take kai, yyi kamar bai san dasu ba, zama yyi kusa da ita ta ɗan ja baya Zuciyarta na bugawa sbd ƙamshin Bois elite da take shaƙa, Yarima Yashim daya kalli Abeed da mmki yana son yasan inda yasan fuskarsa amma ya manta can dai yace "Sannu da zuwa" Ba tare da Abeed ya kallesa ba idanunsa akan t.v. da yake kunnawa yace "Kana lafiya?" Yarima Yashim yace "Allahamdulilla" Sara ta saci kallonsa sbd wani irin kyau da yyi ga wata jelar sumarsa dake lilo a gefen fuskarsa, Yarima Yashim yace "Uhm Ina Mgn Sara ke nake saurare Will you marry me?" Sara na ƙoƙarin magana Abeddeen ya ƙaro Sounds ɗin t.v ganin haka yasa Yarima Yashim yana ja ƙwafa kafin ya miƙe yace "Bari naje sai munyi Anjima" miƙewa Sara tayi da niyyar Raka Yarima Yashim Abeed yace "jeki kawo min ruwa" kallonsa tayi da mmki ita kam mene ta tare masa banza tayi dashi ta raka Yashim tana tsaye har ya shiga mota, tana ƙoƙarin juyawa zuwa gida taci karo da Abeed dake tsaye a bayanta, fuskarsa tayi jajur zatai Mgn ya kama hannunta tare da buɗe mota ya cillata ciki da wani irin sauri yaja motar yyi waje, Sara tace "Malam waye kai? Mene ruwanka dani ne, ban sanka ba amma kabi ka wani takura ni?" Bai kulata ba yaci gaba da gudu yaji tana faɗa masa Mgn yyi mata banza daga ƙarshe ta fashe da kuka tace "Wannan zalunci ne, ɗai shaye-shaye kawai" wani irin burki yaja wanda ya sanya kan Sara ya daki jikin motar idanunsa har wani ruwa suke sbd masifa, a karo na farko ya kalleta sosai ba tare da yace komai ba ya buɗe mota ya fita, a hankali yake tafiya akan titin yaje ya dawo yaje ya dawo trying to control his temper, da sauri kuma ya dawo wajan motar tare da buɗe ƙofar da Sara dake ya sanya hannunsa ya fisgota waje, kana ya buɗe bayan motar ya saka ta shima ya shiga ya zauna tare da rufe ƙofar, wani irin tsoro ya kama Sara amma ta dake, Calmy Abeed yace "Did i heard you correctly????" Shiru tayi masa cikin zafin nama ya fisgota tare da kama duka shoulder ɗinya ya matse yace "Speak again...." Cikin dauriya da da kuma taurin zuciya Sara tace "Nace ɗan shaye shay....." Bai bari ta ƙarasa faɗa ba ya wani irin fisgota jikinsa tare da....




Zain Abeed isn't free contact to subscribe.....08119237616 kuji tsoran Allah👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻.


Allah ya bamu alkairin dake wannan rana....Ai weekend lafiya.i.*page29****Idanunsa da sukai jajir ya buɗe akan Sara yana binta da wani irin kallo, ita kanta sai da yanayinsa ya bata tsoro, with a very low tune daidai kunnanta Abeed yace "I am not a drunkard....Saaaaa" ya matse shoulder ɗinta ganin yadda ta sunkuyar da kanta ƙasa, kafin cikin daga Murya yace "Who gave you permission to look after this stupid person?Ke har kin isa kula wani ke nan?" Ya faɗa yana wuci kafin cikin saurin ya saketa yana daka mata yace "Out of my car..." Sai lokacin Sara ta ɗaga kanta tare da kallonsa kaɗan, wani irin abu wanda bata taɓa gani a tattare da kowa ba shine take kallo a wajan Abeed, gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun fito, fuskarsa tayi wani kalar jaa sai hannunsa da yake bugawa a iska, ganin bata da niyyar fitowa yace "Kada na sake mki Mgn..." Kallonsa tayi sama da kasa kafin a hankali jikin muryarta mai sanyi da ɗaukan hankali tace "Ka mai dani gida, idan kuma kai ba mashayi bane mene?" A hargitse ya juya gaba ɗayansa tare da sunya hannunsa ya wani fisgota waje, bai tsaya jiran komai ba ya shige motarsa ya jata da wani kalar azababban gudu kamar zai tashi sama, da idanu tabi bayansa Zuciyarta na bugawa, ƙilan wani shaye-shayen zai sake yi, wrist ɗin hannunta ta duba daga tuni 10 na dare ya shige, a hankali take kallon wajan da take bata taɓa zuwa nan wajan ba, gashi unguwar manyan mutane ne, Shiru babu kowa kan hanyar, a hankali take tafiya idan tayi nisa sai kuma taga hanyar ya mayar da ita wani wajan, tayi tafiya mai nisa ta nemi waje ta zauna a hankali tana dafe kanta tace "Na shiga uku ni Sara" daga samanta taji ance "Baki shiga uku ba" da sauri taga ɗaga kanta wata dattijon mutum ne tamkar buzo ya rufe fuskarsa, hannunsa riƙe da gorar ruwa, ya kalleta a hankali yace "What are you doing here? Baki duba time bane?" Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, ruwan hannunsu ya miƙa mata yace "Drink...u feel better" babu musu Sara ta amshi ruwan bashi da wani sanyi amma haka ta buɗe murfin gorar ta shiga sha tana sauke ajjiyar zuciya, wani irin zafi Zuciyarta ke mata, Dattijon mai cike da kamala yace "Ya kamata ki tashi, akwai dog's da yawa a nan area ɗin" miƙewa tayi tsaye a hankali tana ɗan Murmushi tace "Thank you" tana faɗin hakan ta fara tafiya, tayi nisa sosai lokacin maganar 12:15 ake na dare, wata motace tasha gabanta da ƙarfi, hakan yasa tayi baya tare zaro idanunta waje, Ta cikin motar ya ƙare mata kallo, kafin yaja wani breathing a hankali kana ya buɗe motar ya fito, bai tai tunanin ganinsa ba hakan yasa taja da baya taci gaba da tafiya a hankali, wannan karan ya sauya kaya wandon dake cikinsa trousers ne iya karsa qwiwa sai white kaftan, ƙafarsa cikin Scuff faux-shearling slippers sai ƙamshi yake ba kamar ɗazo ba sbd abinda ya sha, ganin yadda tayi masa nisa yasa walking slowly ya fara bin bayanta, yanayin tafiyar da take yasa ya cimmata yana zuwa fuska a haɗe yace "Keeee" banza Sara tayi masa Calmy yace "Muje ki shiga mota" Still ignored him bata kulasa gabanta yasha fuska a kame yace "magana nake?" Cak ta tsaya ba tare data kallesa ba tace "Ka bani hanya, ko duniya zan shiga Meye naka?" Ka faɗa ya ɗaga yace "Owk, bari na mai daki, sai ki shiga duniyar i don't have any prblm with dat.." idanunta ta ɗaga a hankali ta kallesa suka haɗa idanu da sauri ta janye nata idanun, ta gefensa ta shige har zai mata mgn sai ya hango wani ƙaton American dog yana zuwa wajan, baya yyi yana watsa mata hannunsa alamar taje, shi kuma ya juya zuwa wajan motarsa, haushin karan da Sara taji shine ya hanata ƙarasa tafiyar da take, zaro ido tayi ganin gaba ɗaya karan wajanta yayo, juyawa tayi da saurin Abeed na tsaye gaban motarsa yana ƙoƙarin shiga, Sara ta wani kwasa da gudu tabi bayansa nan take kuma karan ya mara mata baya, wani kalan ihu tayi tana faɗin "Uncle....Twin zai cije ni" ta faɗa ita bama ta san ta kira sunansa ba, wani irin abu Abeed yaji yadda ta kira sunan nasa, kafin yyi magana ta ƙarasa wajansa da ƙarfi ta wani irin faɗawa jikinsa ta ƙanƙamesa, tsoro duk ya kamata daidai lokacin kuma mai karan ya shiga kiran karan nasa, da gudu ya juya zuwa wajansa, Ajjiyar zuciya Abeed ya sauke domin kusan mutuwar tsaye yyi, jikinsa Sara rawa kawai yake still holding onto him, gani take tana buɗe idanunta karan zai kamata, Abeed a sanyaye murya can ƙasa yace "Sake ni" idanunta ta buɗe ganin yadda ta ƙanƙamesa fuskarta a ƙirjinsa yasa da sauri ta sakesa tana komawa baya tare da tura bakinta gaba, sai kuma shaaaa hawaye ya shiga sakko mata, bai ce mata komai ba ya buɗe matarsa ya shiga, baya ta buɗe ta shiga tana tura baki bai kulata ba yyiwa motar key yabar wajan, bata san mene ya sameta ba ita dai kawai taji kuka yazo mata, da sauri ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka kamar wacce aka daka, driving kawai yake sai da yyi nisa kafin ya gangara gefen titi a hankali yyi parking, kashe motar yyi baki ɗaya kafin gently ya fito daga cikin motar kai tsaye kuma bayan motar ya nufa tarw da buɗewa ya shiga kana ya rufe motar, har lokacin Sara kuma take ya jima yana kallonta kafin, kafin cikin ƙasa da Murya yace "Keee...." Ƙin ɗago tayi ta kallesa, ya matsa kusa da ita tare da sanya hannunsu ya ɗago fuskarta da sauri ta rufe idanunta, Abeed yace "Open your eyes.....Saaaaa" shiru tayi masa tana ƙara sautin kukanta, cikin wani irin ɓacin rai ya sanya hannunsa tare da jawota gaba ɗaya ta faɗa jikinsa tana sakin wani kukan, ƙanƙame ta yyi a jikinsa idanunsa yyi wani jaaa, kukanta ya keji har tsakiyar kansa,kamar neman mafaka haka Sara ta rufe fuskarta a ƙirjinsa tana rusa masa kuka da iya ƙarfinta, shiru Abeed yyi yana sauraran yadda take kuka a hankali yake ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, yana ƙara Rungome ta a jikinsa, tun tana kuka har ta dawo shassheƙa ta dawo sauke ajjiyar zuciya. almost 10 minute kafin ya saketa yana ɗago fuskarta da hannayensa, idaniya ta rufe taƙi yarda ta kallesa, Murya can ƙasa yace "Uhm...U called me ɗan shaye-shaye, i didn't do anything, ban maki komai ba, na tsani kuka shine za kizo kina min ihu akai, why baki je wajan wancan banzan ba?" Da sauri ta buɗe Idanunta tana zame jikinta can gefe guda tace "Zaka iya komai, but don't ever trying to call him with that name again" kallon ta kawai Abeed yake da mmki, har zai Mgna sai kuma ya buɗe murfin motar ya fita zuciyarsa na wani irin zafi da ciwo, key yyiwa motar tare da fara tafiya, ganin direction ɗin daya ɗauka yasa Sara faɗin "Ina zaka kaini?" Banza yyi mata a babban wani haɗaɗɗan gida ya shiga Horn gatekeeper ya buɗe masa gate, da gudu ya shigar da motar cikin entrance na gidan, buɗe ƙofar yyi ya fito, wajan side ɗinta yaje yace "Get down.." kallonsa tayi ta ɗauke kai tace "Zaka iya aramin key car ɗin?" Wani kallon sama da ƙasa yyi mata yace "Ok fito" fitowa tayi fuska a kame tana miƙa masa hannunta ya bata key ɗin, durƙosawa yyi kamar zai wani abu ya ɗauke ta Cak, tsoran da Sara taji yasa tayi saurin riƙe masa gaban riƙa tace "Meye haka?" Banza yyi mata tace "Ni ka sauke ni,ni ba ruwana da kai mene haɗina dakai?" Riƙe da ita ya shiga Main Parlo ɗin part ɗin da yake zaune, Bai tsaya ko'ina ba sai bedroom ya sauke ta akan bed not looking up yace

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads