Header Ads
Showing 66001 words to 69000 words out of 193443 words

Chapter 23 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

tafe yana cire jacket ɗin jikinsa, yabar singlet ɗin ciki, idanunsa jajurr yana jan wani irin numfashi a haka ya ƙarasa wani Paul’s Casablanca, lokacin daya isa wajan 11 saura, a entrance ɗin club ɗin yaga wasu zafafan motoci duk haɗuwar su bata kai tasa ba, ko a kuɗi kashe motar yyi shi kansa bai san meke damunsa bai san wanne kalar abu ke jan ragamar rayuwarsa ba, wani lokacin ji yake kamar yyi kuka sbd ƙunci da baƙin cikin yadda rayuwa ta juya masa salon ƙaddararsa, fesar da numfashi yyi mai zafi kafin gently ya buɗe murfin motar ya zura da ƙyakkyawar farar ƙafarsa zuwa waje, ƙarasa fitowa yyi yana kame fuska key ɗin motar ya sanya cikin Aljihu tare da ɗaukan Wayarsa walking slowly yake nufar cikin hotel ɗin, wanda gaba ɗaya sautin kiɗa ya sanya ba'a jin Mgnar Mutane, iya haɗuwa ya haɗu matane kala kala masu ajin gske yawancin su da skirt iya gwiwa, sai wata riga wacce bata shige half vest ba, rabin ƙirjinsu duk a waje, yana shiga gaba ɗaya maza ta matan wajan suka miƙe suna Kallonsa tare da nunasa da mmki, domin babu wanda ya tsammaci ganinsa a yanzu, kansa a ƙasa tunda yyi musu kallon farko ya ɗauke kai, can ciki ya shige waje mai kyau mara hayaniya yana zuwa ya zauna saman Kujera idanunsa a lumshe kafin ya buɗe ya shiga danna Wayarsa ringing wayar ya fara yaga sunan Dr Adyan kamar ba zai picking ba sai kuma ya ɗaga yana saita bluetooth ɗin kunansa, daga can ɓangaren Dr Adyan yace "Akan na faɗa maka Gsky kaji haushi ko? Nasan ba kai tunanin ganina a Cairo ba, wlh Abeed idan wani yace min kai ne kake abinda kake yanzu sai na kaishi ƙara" shiru Abeed yyi yana ɗagawa wani ma'aikacin wajan hannu tare da yi masa alama ya kawo masa abin sha, Dr Adyan yace "Tunda baza kaji ba, zan kira Zain na faɗa masa komai tare da inda kke zaune" Calmly cikin kamewa fuska Abeed yace "idan kayi hk babu ni bbu kai har abada Adyan..." Yana faɗin hakan ya kashe wayar, ma'aikacin yana cikin shiryawa Abeed abin sha Nusy ta ƙarasa wajansa tace "Hi" Ma'aikacin yace "Hi Ms Nusy" da hannunta wanda yasha farce tace "Me yace ka kawo masa?" Yace "Galaxy Mini Wine Rack" Murmushi tayi tace "ka kai masa Whiskey" da mmki Ma'aikacin yace "sorry Maaah, i can't do it.." jakarta ta buɗe ta ɗauko kuɗi mai yawa ta ajjiye masa, cikin sauri ya ɗauke kuɗin yana sauya abin shan Abeed zuwa Whiskey (Alcohol). Wajanta ta koma cikin friends ɗinta, Abeed na zaune Ma'aikacin ya kawo masa Whiskey ɗin wacce bai tunanin ita bace, ya jima kafin ya ɗauka yana ƙare mata kallo yana juyata a hannunsa, a hankali ya nufi bakinsa da ita nan take ya ajjiye sbd warinta daya daki hancinsa, runtse idanunsa yyi sosai da sauri kuma ya kifa kansa yana jan numfashi, a hankali daga samansa akace "Hy Singer" shiru bai ɗago ba Nusy ta zauna kusa dashi tana ɗura hannunta akan cinyarsa Abeed da wani kalar sauri ya ɗaga kasa sbd wani masifaffan abu daya ratsa masa zuciya abinda bai taɓa jinsa ba ke nan iya kacin rayuwarsa, ya jima yana kallon Nusy frm head to toe kafin ya wani kalar sanya hannunsa ya ɗauke ta mari yana huci kuma ya tashi kamar walkiya yabar cikin wajan bayan ya ajjiye kuɗi mai yawa, gaba ɗaya guys ɗin suka fara mata dry baƙin cikin duniya ya kamata itane ne gayan nan zai mata haka? Wlh idan har tana raye sai ta rama abinda yyi mata. Abeed na fita ya shiga motarsa tare da barin wajan kamar zai tashi sama, sam bai ba lura da wata mota dake bin bayansa ba har ya shiga cikin gidansa, da ɗan sauri yake tafiya yana zuwa ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa sai numfashi yake fitarwa ga wata azaba daya keji a mararsa ya rasa mene yake so mene kuma yake buƙata, baya iya bacci sai ya haɗa da maganin bacci, kwanciya yyi abin tausayi tare da yin lamo saman bed, jin mararsa ta ƙara murɗawa har Abeed ɗinsa na ƙoƙarin Miƙewa ya sanya ta sauri ya miƙe ya nufi bathroom ya ƙara sakarwa kansa shower, ga Asthma bata son sanyi data takura abin duniya duk ya damesa sai wajan 3 bacci ya ɗauke sa, yana ji ana sallar Subhi amma bai iya tashi ba...


Zain ya kalli wani ɗaya ɗaya daga cikin state Cid ɗin da suke tsaye a ƙofar shiga Masarautar Zahel, yace "Sau uku ke nan muna zuwa prvt investigator ɗin mu na shaida mana Sarkin baya nan" Jabir yace "Ba zamu saki mu shiga ba" Zain a hankali cikin nutsuwa yace "But Why?" Jabir yace "Mutanan Masarautar Zahel basu da imani suna iya yanka mutum ba, kafin shiga dole mu tabbatar Sarki Mabus yana nan idan sunga shi muka kama da kansa babu abinda suka isa suyi mn" Zain yana ware idanunsa sosai yace "You're right.." har zai juya sai kuma tsaya domin kamar daga sama yake ganin wata kamar Sara, Subash ya kalli Sairah yace "Ba zaki iya aure na ba?" Girgiza kai Sairah tayi tace "Ba zan iya rayuwa a nan ba, ina buƙatar barin Masarautar nan" shiru yyi mata kafin can yace "Ok yanzu Sarki baya nan zamu fita ai" tace "Har kai?" Yace "Zan biki, domin rabauta kince idan har sbd ina son na aureki na keson musulunta Gwamma ban musulunta ba, idan na biki kuma zanta ganin yadda kike wannan dunguran har Abin ya zauna a Zuciyata" Cikin nutsuwa Sairah ta kalli Subash tace "Salla ake cewa" yace "Ohh, afuwa" tace "Never mind" ɗago kan da zatai idanunta ya sauka Zain wanda take tunanin Abeed ne, da wani irin sauri tayi bayan subash hankali tashe a Zuciyarta tana tunanin ko Sara ce ta gudu yazo zai kamata? Ko ita tace masa ba ita ta caka masa wuƙar ba?" A karo na farko Subash da yaji mace ta riƙe masa jiki da kansa ba shine ya nemi hakan ba,sai hakan ya haifar masa da wani irin sabon yanayi a jikinsa, sakinsa tayi yace "Menene?" Girgiza kai tayi tana ƙara kallon ƙofar ga mmkinta bbu kowa, to ko gizo yake mata ne? Subash yace "Na rantse da abin bauta kabas babu wanda ya isa ya cutar dake" Sairah tace "Abin bauta kabas ɗin banza? Dukkan wata kariya tana wajan Ubangiji, shine yake da ikon bani kariya a lokacin da yaso, iko,isa, mulki ta ƙama duk tana wajan Ubangijin talikai Ubangijin daya hallici mutum da aljan, yayi duniya da abin ƙawa haka kuma ya halicce lahira da abin ƙi" da mmki Subash yace "Kamar ya duniya da abin ƙawa lahira da abin ƙi?" Murmushi tayi tace "Akwai lokaci zan faɗa maka" tana faɗin hakan tayi gaba da sauri zuwa sashin da take, Subash kuma ya fita da kallo so dana ƙauna... A rikice Zain yace "Bana ko tantanma Sara ce wannan, ke nan aljanun nan suka dawo da ita? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yaya zanyi yanzu, Wlh ba zan iya barinta a nan ba" Jabir yace "Look Zain, zamanka a nan hatsari ne ka bari muyi shiri baki ɗaya sai muzo kawai" shiru kawai Zain yay can kuma yace "Ok" mota suka shiga tare da barin Zahel baki ɗaya....... Kasancewar yau weekend ne babu shcl yasa duk suna gida, Sara na zaune bedroom ɗin ta daga ita sai vest da wanda 3Qauter hannunta riƙe da ice cream tana sha, sai kuma game ɗin da take jikin system, Mami ce ta Turo ƙofar bedroom ɗin ta shigo Sara ta ɗaga fararan idanunta ta kalli Anuty Zulfa, Anuty Zulfa tace "Sara ba zaki shopping ɗin ba?" Kai kawai Sara ta ɗaga tare da yin Murmushi alamar Eh ba zata ba, Anuty Zulfa tace "Ok ki fito Parlo,kafin mu dawo zuwa anjima" A hankali cikin nutsuwar ta Sara tace "A dawo lfy Mami" Murmushi Anuty Zulfa tayi tace "A tawo maki da chocolate da kuma Ice cream?" Sara ta miƙe tsaye Anuty Zulfa tana mmkin yadda kullum jikin Sara ƙara buɗewa yake, Tace "You're right Mami..." Juyawa Anuty Zulfa tayi ta fita tana faɗin "Ok dear Kada ki zauna da yunwa" kai ta ɗaga bayan Anuty ta fita Sara ta shige bathroom shower tayi har lokacin kuma bata sallah, da Anyi mata Maganar ranar babu wanda zata kula har dare, wanka tayi daman ta safe sukaje wajan Saloon aka maita wata sabuwar kalbar manya masu kyau aka saka bit, fitowa tayi tana Ƙamshin shower gel, wani Body oil ta shafa kafin ta ɗauki Teyana wide-leg trousers da Silk short robe wacce ta kama ta, amma tana da faɗin wuya da siririyin hannu, jikinta na Ƙamshin Valentino, slippers ta saka kanta babu komai ta nufi Main Parlo, jikinta na wani irin motsawa, tana zuwa parlon taji ƙamshin Bois elite yana shiga cikin hancinta babu wanda yake amfani da perfume ɗin a gidan hakan yasa ta shiga ware idanunta, a zaune ta gansa kan kujera sanye da Paisley tank top, da Tracksuit trousers ya ɗura ƙafa ɗaya kan table idanunsa akan Wayarsa dake dannawa, Jikin Sara ne ya ɗauki rawa domin duk ƙarfin zuciyar mutum taga Abeed sai Zuciyarta ta buga, da ƙyar ta haɗiye wani abu, kafin a fili kuma ta ɗan taɓe baki ta juya zuwa wajan Deep frizeer sai a lokacin ya ɗaga idanunsa ya bita da kallon mmki, na sauyin da yaga tayi bakinsa ya taɓe har lokacin idanunsa a kanta Apple ta ɗauka da inibi sai bottle water, zata shige ke nan taji yace "Saaaaa" ya faɗa a taushashe cikin wata kalar golden voice mai ratsa zuciya, sbd bugawar da Zuciyarta keyi kasa tsayawa tayi ta nufi part ɗin su, ganin hakan yasa gently Abeed ya miƙe tsaye tare da bin bayanta tana ƙoƙarin rufe ƙofa taji ya Turo sakin ƙofar tayi ta juya da sauri zata shige bathroom yyi saurin sanya hannunsa duk biyun ya riƙe faffaɗan waist ɗinta.........




Zain Abeed isn't free contact to subscribe....08119237616 kiji tsoran Allah......ki biya kafin karantawa.
[08-15 08:45] +234 703 831 1110: *28 Nimcyluv*
Zuciyar Sara na wani kalar bugawa tayi saurin ɗaga fararen idanunta zuwa fuskar Abeed dake tsaye kusa da ita, kallo ɗaya kuma tayi masa ta ɗauke kanta, baki Abeed ya taɓe tare da zame hannunsu daga riƙon da yyi mata, wani irin kallo yake ma Sara frm head to toe kafin Murya can ƙasa kamar mai raɗa yana kame fuskarsa yace "Kawo min ruwa" yana faɗin hakan ya juya tare da fita daga cikin bedroom, da idanu ta bisa ganin yadda yake tafiya kamar wani sarki, ajjiyar zuciya ta sauke kafin a hankali ta nemi waje akan bed ta zauna ta shiga shan Apple ɗin data ɗauka tana rufe idanunta har lokacin kuma ƙamshin Abeed bai bar shiga cikin hancinta ba, bata wani sha Apple ɗin da yawa ba ta ajjiye tare da Miƙewa ta nufi bathroom brush tayi ta dawo cikin bedroom ɗin tare da yin kwanciyarta akan bed tana rufe idanunta domin tuni ta mance da abinda yace tayi ɗin, Abeed tsaye yyi a gaban deep frizeer ɗin kafin a hankali ya ɗauki bottle water mai ɗan sanyi ya koma kan kujera tare da zama yana jan numfashi, idanunsa kuma akan ƙofar bedroom ɗin da Sara ta shiga, daman baiyi tunanin zatai abinda yace ba, shima kuma koda ta kawo baya buƙata he just wanted be free with her, He wanted talk to her yana son yyi mata some questions haka, yana ta zaune zuciyarsa cike da tunani kafin yaji motsin fitowa a hankali take fitowa daga cikin bedroom ɗin zuwa Main Parlo a tunaninta Abeed ya jima da barin gidan saboda shirun da taji, kanta a ƙasa ko'ina na jikinta juyawa yake bata lura dashi ba, ƙamshin Hugo boss data keji ma ta ɗauka tun na ɗazo ne, tana zuwa inda yake zata shige yyi saurin sanya mata ƙafa ƙara ta saki tare da yin baya zata faɗa kansa yyi saurin Zamewa ta faɗa saman Kujera kanta ta daki Armchair, ba wani zafi taji ba amma hakan bai hana ta sakin kuka ta yarfe hannu ba, abinda bai taɓa gani tayi ba ke nan, sai lokacin da ciwonsa yyi zafi sai dai kawai hawaye ya taro idanunta, gyara zama yyi tare da ɗaukan ƙafarsa ɗaya ya ɗura kan ɗaya, narkakkun idanunsa ya zuba mata daga kan long gashinta wanda kai mata kalba aka sanya mata bit zuwa kan siririyar necklace ɗin dake wuyanta, a hankali kuma ya dawo da idanunsa kam fararan yatsun ƙafar ta wanda suke dugwaye a jere gwanin sha'awa, taɓe bakinsa yyi tare da saurin kawai da kansa zuwa kan t.v ganin zata kamasa, Sara na wani irin shagwaɓe fuska tana jan Numfashinsa tace "what have I done to thee?" Banza yyi mata ba zaka taɓa cewa yasan da zamanta ba idanunsa akan t.v yama ɗan ƙure sounds, Miƙewa tsaye tayi tana murguɗa masa baki tace "this is evil" tana faɗin hakan tayi gaba zuwa kitchen sai a lokacin ya ɗaga idanunsa yabi bayanta da kallo, yana zaune duk abinsa take yana jin ƙamshin girki bai motsa ba, babu alamun zai bar gidan ma, Yana zaune yaji shigowar su Anuty Zulfa, Auta ce farko sai Anuty Zulfa sai kuma mai gadi daya kwaso musu kaya daga Boot, ganin Abeed zaune fuska kame babu walwala yasa Auta tace "Laa, Yaa Abeed yaushe ka dawo" shiru dai bai Mgn ba har Anuty Zulfa ta shigo ta zauna tana faɗin "Sannu Isa" yace "Ba komai Hajiya" kallo ɗaya Anuty Zulfa tayiwa Abeed ta ɗauke kai, ita Mmkin yadda ya tara uwar suma take, but sumar yyi masa wani masifar kyau kamar wani ɗan India, amma ta lura da faɗawar da yyi, Abeed ya kalli Anuty Zulfa Calmy yace "Wlcm Mami..." Tana danna waya tace "A'a barshi, ai ban kai darajar da za'a gaida ni ba" kallonta kawai yyi kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace "Sorry Mami.." harara ta wurga masa tace "Wato Abeddeen saboda na hanaka tafiya da Saraa shine ka kullaceni ko? Shine ka tattara gaba ɗaya ma kabar ƙasar ni zaka nunawa ban isa dakai ba ke nan?" Baki ya buɗe zai magana ganin Sara ta fito daga kitchen idanunta akan Anuty Zulfa yasa shi taɓe cikin wata kalar Murya yace "Who is Saraa Mami?" Hatta Sara sai da ta kalli Abeed jin rainin hankalin da yake,ko ita har abada ba zata taɓa cewa ta manta Abeed ba balle kuma shi, Anuty Zulfa tace "Uwar kace, Shasha nine zaka tambaya waye Sara Abeddeen?" Shiru kawai yyi yana ɗan shafa kwantaccen beard ɗinsa wanda yake ƙara haska fuskarsa, Sara ta jima tana kallon Abeed kafin a sanyaye ta ɗauke idanunta tace "Wlcm Mami" Anuty Zulfa tayi Murmushi tace "Yawwa Dear, me kike ne duk muke jin ƙamshi haka?" Sara na juyawa zuwa dining room tace "white rice and liver sauce" Anuty Zulfa tace "Eyeee ke kam babu mijinki da bin Restaurant wlh, ban san yaushe kika ƙware a girki ba" Cute smile kawai Sara tayi bayan ta gyara dining room ta nufi kitchen, idanun Abeed akan Auta yace "Level nawa?" Ware idanu tayi tace "Yaa Abeed yanzu zamu fara exam na first semester a level 1" taɓe baki kawai yyi baice komai ba, Anuty Zulfa ta tattara shi gefe guda ta zubar, ganin haka yasa ya miƙe tsaye hannunsa riƙe da key car ya fara tafiya a hankali zuwa barin parlon kallonsa Anuty Zulfa tayi tace "Ka tsaya kaci abinci" kai kawai ya girgiza nata alamar baya ci, cikin Murya ba wasa tace "To dani dakai aga wanda ya isa" tana faɗin hakan ta miƙe zuwa dinnig lokacin Sara ta gama haɗa komai, har Auta duk suna kan dining a hankali Sara ta shiga serving nasu, tana zuwa kan Abeed ya haɗe fuska ta mau yace "Kee banso" idanunta ta ɗaga suka haɗa idanu ya wani haɗe rai yana hurga mata harara, "Uhm" kawai tace ta zauna ta juya spoon bata san mene ya hanata cin abincin ba, kawai ta samu kanta da rashin sakewa duk wani ƙamshin turaren sa ya cika ko'ina na hancinta, ajjiye spoon ɗin hannunta Sara tayi tare da rufe idanunta ƙirjinta na ɗan bugawa kaɗan, ganin yanayinta yasa Anuty Zulfa cewa "Sara Are You Okay?" Idaniya ta buɗe kamar mai jin bacci gently kuma ta ɗagawa Anuty Zulfa kanta, taɓe baki Abeed yyi kafin ya kalli Auta yace "Idan na ƙara ganin this dress a jikinki sai na ɓallaki" Auta tace "Am sorry Yaa Abeed ban sake sawa" Anuty Zulfa dai na zaune ba tace komai ba sarai kuma ta gane zan can na Sara ne, ajjiye cup ɗin hannunta tayi ta kalli Sara tace "Na bawa Yarima Yashim iznin zuwajanki, be ready" da sauri Sara ta kalli Anuty Zulfa magana zatai amma ta kasa sbd tarin da yazo mata, kusan a tare Abeed da Sara suka miƙa hannu wajan ɗaukan ruwa, shine ya fara sauke hannunsa kan cup ɗin cikin rashin sani kuma Sara ta ɗura nata, Wani kalar abu Abeed yaji ya tsarga masa, tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafin ƙafarsa gargasar jikinsa suka shiga buɗewa alamar amsar sabon yanayin da sukaji, wata kalar wahalalliyar ajjiyar zuciya Abeed ya sauke a hankali kuma ya zame hannunsa tare da Miƙewa, babu wanda ya ƙara kallo yyi waje abinsa, ta gefen idanu Sara ta bisa da kallo tana ɗan taune bakinta, kafin a hankali baki na rawa tace "Ma... Mami ni?" Anuty Zulfa tace "A'a Ni..." Shiru kawai Sara tayi Anuty Zulfa tace "Anjima zai zo" tana faɗin hakan ta miƙe, Auta tace "To mene kuma Sara, guy ɗin yyi wlh kuma he's unique handsome Elegant...." Miƙewa Sara tayi ba tare data kula Auta ba, tana zuwa part ɗinsu ta nufi wajan window tare da rufe idanunta tana shaƙar fresh air, kamar ance ta buɗe idanunta ta kalli wajan parking space ta hangi Abeed jin gine da motarsa ya ɗan kifa kansa a bayan motar ga wata duguwar kwalba a hannunsa, wacce bata san

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads