Showing 75001 words to 78000 words out of 193443 words
Chapter 26 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt
zai wani ɗauke ki?" Ita dai Sara shiru kawai tayi ba tace komai ba har suka ƙarasa wajan cin abinci, waiter ta kawo musu abinci Sara Patatoes da meat shawarma aka kawo mata sai Green tea, Auta kuma Chips ne da Egg, suna cikin cin abinci su kaji zuwan mutum wajan ƙamshin turaren Jean paul Gaultier ya kama wajan, Cikin kasaita tasu irin ta masu mulki Yarima Yashim yyi sallama a taushashe, Auta ce ta kallesa tana Murmushi kafin ta miƙe yyi saurin cewa "No please zauna mana" ta ɗanyi dry yace "Zanyi wani abu, I'll be back" tana faɗin hakan tayi waje sai a lokacin Sara ta ajjiye spoon ɗin hannunta tare da ɗagowa ya kallesa Murmushi ya sakar mata a hankali tana ƙasa da kanta tace "Ina yine" Yana ta Kallonta jin baice komai ba yasa ta ɗaga kanta suka haɗa idanu idanu ɗaya ya kashe mata yace "Amin cin Allah ya tabbata ga ruhin Yashim Al'khasim Abubakar Wahab" Murmushi tayi yace "Kinyi kyau my princess" a hankali tace "Thank you" shiru yay can yace "Next week sai exam ko?" Kai ta ɗaga masa ya jinjina kai kafin yace "akwai bikin da Za'ai na kammala wani abu da ƴan low sukai ƴan level 3" tana wasa da yatsun hannunta tace "Naji an faɗa.." yace "Zadai kizo?" Tace "Not sure.." yace "U most come, nima ranar za'a ƙara min girma" ta juya idanunta kamar ba zatai mgn ba sai kuma tace "A nan makarantar kuma?" Ya girgiza mata kai idanunsa akan yana jin wata soyayyar ta a zuciyarsa yace "Wane yace maki ni University teacher ne?" Hannunta ta watsa masa tace "naga kana ɗaukan mu darasi ne" Murmushi yyi mai kyau yace "To ni ba Malami bane akwai dalili" kamar ta tambaye sa mene aikinsa sai kuma tayi shiru. Matsar da kujerarsa yyi sosai a hankali yace "Sarahh.." har ƙasan Zuciyarta taji kiran da yyi mata yace "Kalleni Sarahh" ƙin ɗago kanta tayi ya sanya ta tattausan farin hannunsa tare da tallafo haɓatar a hankali ya juyo da fuskarta suna fuskantar juna, Abeed dake tsaye yana kallon duk abinda Yarima Yashim keyi ya juya a hankali ya bar wajan, yana zuwa bakin motarsa yace da Auta "kice mata idan na shigo wajan zata gane bata da wayo" tsoro duk ya kama Auta ta juya da sauri zuwa cikin wajan, Calmy Yarima Yashim yace "Uhm, shy baby I love You Sarahh i am in love with you madly, Zaki auren?" Har lokacin fuskarta na hannunsa tace "Uhm, zan tambayi Uncle" Kallonta yyi tayi kafin ya zame hannunsa yace "Ok Promise me idan har ya amince zaki auren" a hankali tace "I promise in sha Allah" hancinta yaja yace "Thank Beb.." miƙewa tayi tsaye tace "Zan tafi" yace "ok sai munyi Mgn" tana fita Auta na zuwa tace "Sara kin shiga uku Yaa Abeed yazo" Idanunta ta juya ba dai tace komai ba tayi waje, Sara na zuwa ya kalli Auta tare da ciro kuɗi ya bata yace "Ki nemi abun hawa" Sara da kanta ke ƙasa sai ji tayi ya fisgi hannunta tare da cillata mota ya rufe da wani irin sauri yyiwa motar key tare da barin cikin makarantar......... Zain ya fito daga cikin Court hannunsa riƙe da briefcase yana tafe a hankali shi da wani suna Mgn mai muhimmaci, har Zain ya isa wajan motarsa baice komai ba sai da ya buɗe motar ya shiga ya kalli Mutumin yace "Ina da cases da yawa, amma zan duba naga" yana faɗin hakan ya yyiwa motar key tare da fita daga cikin Court ɗin, driving yake a hankali amma zuciyarsa na can Masarautar Zahel kullum a zalzalarsa take akan ya koma ya ɗauko Sara, a haka har ya iso gida bayi da Kuyangi nata gaishe sa, A Main Parlo ya samu Amma ita da Amintacciyar kuyangar ta zama yyi yace "Barka da yamma Amma" Murmushi tayi masa tace "Sannu ya hanya?" Yace "Allahamdulilla" tace "Naila nata rigima tana neman shalele" ya zaro ido yace "Bari na freshen up na leƙa" ta jinjina masa kai. Part ɗinsa ya shiga Du'a na ganinsa ta miƙe da murna tare da rungome sa tace "Oyoyo gwarzona" ta faɗa tana sakar masa kiss a wuyansa idanuna ya lumshe ya riƙe ququnta tare da ƙanƙame ta yace "Ya gida wify?" Tace "Babu daɗi baka nan" yana kissing ɗin gefen kunnanta yace "Uhm Ayyah" ya faɗa yana ɗago fuskarta a hankali ya wani haɗe bakinsu waje guda domin gani yake hakan shine zai iya mantar dashi tunanin Sairah dake damunsa a zuciya, ɗaukan ta yyi cak zuwa bedroom sai da komai ya lafa yyi wanka ya shirya cikin kayan shan iska yace "Bari naje wajan Naila" Murmushi tayi masa shi kuma ya fita zuwa sashen Naila, tana zaune ta saka furar data dama a gaba tace "Ita duniya a ba aljanna mace, daga Kano har duniya ɗai ɗaiku ne masu gsky Alkur'anin Ubangiji" Zain yyi sallama ya shigo da sauri ta ɗauki ƙwayar data dama furar ta ɓoye a bayanta tace "Ya..Ya..Ya haka kamar ana yaƙi za'a faɗo min kai ko yaƙin badar ai ba'ai wannan tijarar ba na rantse, kowa ya zama gantalalle wacce lukutar masifa ke son damun ƴan arewa ne?" Zain yace "Ke kin san yaƙin badar ke nan" ta riƙe haɓa tace "A'a ba zan kula ka wlh, ba sai dai kaci kanka ba? Kuma ka ƙaryata Uwarka Saratu" zama yyi yana faɗin "Naila ance kina kirana" ta marairaice tace "Ayya Alqur'anin Ubangiji na ɗauka wani can sallamamman ne, kayi hqr kaji kada ka kullaceni, yanzu daman na gama dama maka furar" sakkowa Zain yyi yana Murmushi yace "Ina shi yana zan wajan matarsa" Naila na basa furar tace "A to, ai kowa ta kai daman kana ganinsa kasan bashi da kunya idanunsa a tsakiyar ka yake fa? Baya ganin kowa da gashi kuma har yanzu matar taƙi yin ciki fa, Allah dai yasa basa maka gorin auren, tunda dai babu wanda kasan zuciyarsa sai dai ace li'ilafi qurash" Murmushi kawai Zain yyi har ya gama shan furar ta ɗauke ƙwaryar tana faɗin "A'a daman ai dan Allah nayi bance a gode min ba, amma dai duk ɗan halarci akai masa abu yace ya gode Allah ya sauwaƙa kamar dai mai rawanin can ne yaban kuɗin daka furar?" Shi dai Zain baice komai ba ya shiga danna Wayarsa kasancewar e-mail ɗinsa yana kan wayar yana shiga idanunsa ya sauka akan saƙon Abeed wani irin zabura yyi farin ciki a kama sa, bai taɓa tunanin zai ga wannan saƙon ba daman yasan ko mai daɗewa Abeed zai tuna dashi, da sauri ya fita daga sashen Naila tana zuwa tace "Kaga shasha tasono butulo kawai.." ta faɗa tana ajjiye Apple ɗin hannunta.....Har dare Anuty Zulfa na saka ran ganin Abeed ya dawo da Sara amma shiru ta kira Wayarsa babu adadin yaƙi ɗauka, Abeed kowa bai ma san meke damunsa ba shi kawai yaji baya so kuma baya ƙaunar Yarima Yashim idanma auren ne zai nema mata wani daban ba Yarima Yashim ba, Yana zuwa gida ya buɗe mota yace ta sauka ganin yanayinsa yasa ta shige ciki yana ganin shigarta ya rufe gidan ya fita har kusan 11 na dare bai shigo ba. Sara na zaune a parlo ta takure tsoron gidan ya kamata tayi wanka ta sauya kaya ta ɗan sha ice cream, 12 daidai taji motsin za'a shigo parlon da sauri ta miƙe tsaye Ƙafarsa ta fara shigowa cikin parlon sai kuma hannunsa dake riƙe da jacket ɗin Suit ɗinsa, kamar zai kifa haka yafe tafiya a hankali da sauri ta ja baya saboda warin abinda taji ga wata ƙatuwar kwalba a hannunsa, da ƙafa ya tura ƙofar parlon idanunsa da sukai jajur ya buɗe a kan Sara ya shiga Kallonta tun daga sama har ƙasa riga da wando ne a jikinta wando iya cinyoyinta ne, ko ɗan kwali babu a jikinsa, a hankali ya shiga takawa zuwa inda take tana ja baya yana binta juyawa tayi da gudu zata bar parlon ya sanya ƙafarsa tare da harɗe mata ƙafa gaba ɗaya tayo baya zata faɗi yyi saurin riƙe ta, bashi da wani ƙwari hakan ya sanya gaba ɗaya sukai baya tare da faɗawa saman Kujera itace a ƙasa shi kuma ya faɗa kanta tare da danne ta....**31***_Zain Abeed 31.... Complete book 1, 2 ku shiga Arewabooks domin samun update fiye da ɗaya_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62b1e5ccf0bafa279f2af05c
_Follow My Acct Habibaties🥰👇🏾_
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
Numfashi Sara ta shiga ja da ƙyar sbd yadda Abeed ya sakar mata dukkan nauyin jikinsa, ga yanayin yadda abin shaye-shayen nasa yake dukan hancinta kamar zata amayar da kayan cikinta haka ta keji, idanunta ta buɗe da ƙyar ta zuba akan ƙyakkyawar fuskarsa, idanu suka haɗa wani irin kallo yake binta dashi kallon da ba kowa zai iya gaya ma'anar sa ba, bakin Sara ya shiga rawa cikin tsoron yanayin Abeddeen tace "Uhm, bacci zan ka ɗaga ni" shiru yyi mata Banda Kallonta babu abinda yake, Sara da Idanunta tuni ya gama cika da hawaye tace "kayi min nauyi fa" sai a lokacin ya ɗan juya jajayen idanunsa wanda suka janye kafin a hankali kuma cikin mutuwar jiki ya zura hannayensa ta bayanta ya wani irin haɗa cikinta da fuskarsa yana lumshe idanunsa da sauri Sara tace "Ni ka sake ni, Allah zan faɗawa Mami" shi dai ko yana jin abinda take faɗa to ba sosai ba sbd gaba ɗaya jikinsa ya saki, a kasalance a kuma yanayi na son samawa zuciya da gangar jiki nutsuwa ya zaro hannunsa guda ɗaya tare da manna shi a shafaffan cikinta a hankali ya zame rigarta tare da ɗaga ta sama, rintse idanu Sara tayi sbd jin abinda Abeed keyi jikinta ya fara rawa na tsoro da kuma fargaba, domin gaba ɗaya taji tsigar jikinta na tashi, yunƙura tayi zata tashi ya ƙara sakar mata nauyin jikinsa, idanunsa da suke a lumshe ya buɗe kai tsaye kuma Kallonsa ya sauka a farar Cibiyarta mai kyau wacce take da ɗan zurfi ga ƙasan cibiyar wata baƙar tawadar Allah wacce ta ƙara haska fatar cikin nata, numfashi Abeed ya sauke tare da tsorawa wajan idanu kamar wanda yake neman wani abu, idanunsa yaja ya rufe ruf yana wani irin sauke ajjiyar zuciya, a hankali ya manna fuskarsa akan cikin nata bakinsa daidai wajan Cibiyarta ɗaya hannunsa kuma ya riƙe waist ɗinta ƙam! Wajan 2mnts suna haka kafin a hankali taji saukar tongue ɗinsa a cikin cibiyar nata wani ƙanƙamesa Sara tayi sbd jin abinda bata taɓa tunani ba, jikinta har rawa yake, Abeed jin riƙon da Sara tayi masa yasa shi ƙara zura tongue ɗin nasa yana ɗan juya shi tare da sakar mata wani irin numfashi mai zafi, a hankali kuma jikinsa ya ɗan fara rawa cikin wata kasalalliyar Murya mai tarin rauni damuwa baƙin ciki, buƙata, muradi ya buɗe bakinsa kaɗan daidai yadda Sara zata iya jinsa yace "Tashi a nan.." ya faɗa a kame kuma a wahalarce idanunsa yyi jajur sbd wahala da kuma abinda ya keji a gangar jikinsa, Sara ta yunƙura zata tashi taji ya ƙara ƙanƙame ta yana sakin numfashi yana ƙara manna fuskarsa a cikinta, kuka ta sanya masa tace "Dan Allah Uncle kayi hqr..." Ta faɗa tana turesa amma bai motsa ba, yana cewa ta tashi a wajan amma yana ƙara ƙanƙame ta, Sara ta shammace sa ta sakar masa cizo a gefen fuskarsa ya ɗan sassauta riƙon da yyi mata, da wani irin zafin nama ta sanya dukkan hannunta tare da turesa waje guda ta kwasa da gudu zuwa bedroom tana wani irin numfashi tare da dafe ƙirji, ƙofar ta rufe tare dayi mata key a hankali ta zube bakin ƙofar tare da saka kuka wanda ita kanta bata san dalili ba,amma har ƙasan Zuciyarta bata jin daɗin yadda take ganinsa yana shan kayan maye,ta jima a wajan kafin bacci ya ɗauke ta a wajan kuma a nan baƙin ƙofar. Abeed kuwa Sara na barin wajan yaji kamar ana zuba masa wuta a jikinsu domin har wani huci fatar jikinsa take, a hankali ya mirgina tare da jan pillown kujera ya ƙanƙamesa ko zai ji daidai, har aka kusan kiran Subhi idanunsa biyu kuma bai motsa ba, ana tsaka da kiran Assalatu bacci ya ɗauke sa.
Sara kamar a kunnanta aka kira Subhi jiki a matuƙar mace ta shiga buɗe Idanunta har ta kammala buɗewa Idanunta sun kumbura sosai gently ta miƙe tsaye har zata shige bathroom sai kuma ta ɗan buɗe ƙofar bedroom ɗin nata a hankali ta leƙa kanta zuwa waje, fararen tafin ƙafarsa ta fara hangowa kafin kuma ta hangi hannayensa da suke riƙe da pillow, fitowa ta ƙarasa yi zuwa parlon, cike da nutsuwa take tafiya tana son taga ya tashi yyi sallah amma tana tsoran abinda zai iya yi mata, fuskarsa ta leƙa taga fess ya wani ƙara haske da kwarjini duk da bacci yake, juyawa tayi ta rasa mene Zatai sai kawai ta ɗauki Wayarsa tare da yin connecting wayar da t.v jikinsa Sa'a kuma yyi Suratul Yaásin ta kunna gaba ɗaya ƙira'ar ta karaɗe duka Parlon da sauri ta ajjiye wayar ta juya zuwa bedroom ɗin ta, Abeddeen yana cikin bacci yaji saukar karatu a kunansa duk yadda yaso ya share kasawa yyi a hankali ya shiga buɗe idanunsa wanda suka dawo kamar yadda suke, da mmki yake min parlon da kallo da kuma inda ya kwanta ɗin bai san yaya akai ya kwanta a Parlo ba, ko wanka bai ba Miƙewa yyi sai a lokacin ya kula da kwalbar dake yashe a parlon kansa ya dafe lallai yau ransa ya ɓaci da yawa, walking slowly ya nufi bedroom ɗin sa yana zuwa ya shige bathroom tare da sakarwa kansa shower yana jin gajiyar jikinsa na warware wa brush yyi bayan ya gama ya fito ɗaure da towel, a nutse ya shiru cikin farar jallabiyar yana sabga ƙamshi Hugo boss yana gama shiryawa ana tayar da sallah, zama yyi kan bed yana runtse idanunsa kamar wanda aka tsikara kuma ya miƙe tare da ɗaukan pra mat ya nufi waje, Sara na ganin ficewarsa daga cikin gidan baki ɗaya ta sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, bathroom ta shige tayi wanka itama ta shirya cikin thobe jallabiya tana zaune dai a Zuciyarta tana istigifari Tunda Abeed yace babu dama tayi sallah dole sai ta sake amsar musulunci. Ƙarfe 7 ta miƙe daga kan bed ɗin a hankali take tafiya har ta ƙarasa cikin haɗaɗɗan kitchen ɗin gidan, ga mmkinta kaya ne da yawa a deep frizeer ɗin dake kitchen ɗin, ƙilan ba'a taɓa amfani dashi Bama, dankali ta kwasa ta shiga ferayewa tana gamawa ta haɗa kayan miya iya albasa da papper, kana ta ɗauki wani bushasshen kifi mai kyau ta gyara fatan dankali tayi yaji bushasshen kifi sai tea da kuma Chips, tana gamawa ta gyara wajan ƙamshi duk ya cika wajan, fitowa tayi daga kitchen ɗin zata bedroom ƙamshin turaren sa ya shiga hancinta, kasa kallon inda yake tayi ba tare da tace komai ba ya shige bedroom ɗin ta sauya kayan jikinta zuwa Abaya mai ɗan faɗi red and black. Abeed dake zaune a Parlo watching TV na labarai ya ɗan saci Kallonta lokacin da zata shige kitchen idanunsa ya mayar kan t.v yana zaune har ta fito ɗauke da plate da cup da kuma wata ƙaramar warmer, tana zuwa wajan ya miƙe tsaye ganin haka yasa Sara tace "Mrng.." bai amsa ba ya shige cikin bedroom abinsa yana zuwa ya kwanta kan bed yana lumshe idanunsa abu ne a zuciyarsa yake masa yawa dole ya nemi ma fita ta hanyar nisa daga inda take.
Tana zaune a Parlo bayan taci abinda zata iya ci ta gyara wajan kallon t.v. take amma hankalinta na wani wajan har bata san lokacin da aka buɗe ƙofar aka shigo ba, da sauri ta miƙe tsaye tana faɗin "Mami..." Wata harara Mami ta watsa mata kafin ta zaune saman Kujera hannunta riƙe da key car fuskarta a haɗe, Sara ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da tsugunawa tace "Ina kwana Mami.." ba tare da Mami ta kalleta ba tace "jeki kira min shi" shiru Sara tayi domin tana tsoran fushin Mami ba kaɗan ba, A fusace Mami tace "Ko ba zaki iya zuwa bane? Ki zuba min idanu Sara?" Girgiza kai Sara tayi Idanunta na cika da hawaye kafin ta miƙe tsaye tare da nufar bedroom ɗin sa, yana kwance har lokacin idanunsa a rufe jin Sallamar ta ya sanya ya juya a hankali tare da kafeta da fararen idanunsa, kanta a ƙasa tace "Mami na kira" idanuna ya ware kamar ba zai mgn ba sai kuma yace "Mami?" Kai ta ɗaga masa alamar eh, ya miƙe zaune ya zuro ƙafafuwan sa ƙasa fuskarsa a kame yace "Zo nan" ƙara sawa tayi wajansa ya haɗe fuska yace "Ba shige min nace kiyi ba" baya ta ja kaɗan yace "Ke kika kirata?" Ta girgiza masa kanta ta a haɗe fuska kamar yadda yyi yace "Ni kike haɗewa fuska?" Tai masa shiru calmly yace "Idan kika sake kika faɗawa Mami wani abu ko....uhm" ta buɗe Idanunta ta kallesa tana watsa hannunta tace "Kamarya" ya haɗe fuska yace "ban sani ba" juyawa tayi zata fita yyi saurin sanya hannunsa tare da kamo ta, kwaɓe fuska tayi cikin ƙasa da Murya tace "Ni ka sakeni mene haka wai" ƙin sakinta yyi sai ma matse hannunta da yyi tana shirin sakin kuka yyi saurin sakinta tare da Miƙewa ya shige bathroom, fita tayi zuwa Parlo Mami ta bita da kallo tana zuwa tace "Yana zuwa" harararta Mami tayi tace "Meya zaunar dake?" Kan Sara a ƙasa tace "Yana bathroom ne yanzu ya fito" Anuty Zulfa tace "Sai akace ki zauna kuma?" Shiru kawai Sara tayi kanta a ƙasa ta ɗan jima wajan, kafin ƙamshin Bois elite ya shiga karaɗe parlon, zuciyar Sara ta buga da ƙarfi yana sanye da Ralph Lauren Kaftan st, Zama yyi kan kujera idanunsa na can wani wajan yace "Mrng Mami" Anuty Zulfa tace "Bashi ya kawo ni wajanka ba Abeddeen kullum yaran dana haifa suna gaida ni riƙe taka na gode" a hankali yace "Uhm" shima