Header Ads
Showing 120001 words to 123000 words out of 193443 words

Chapter 41 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

zaki aura Sarah? Why why?" Wani kallo take binsa dashi kafin tace "Shine komai nawa, idan nayi farin ciki a yanzu shine, idan nayi kuka a yanzu shine sbd dashi na samu kasancewa a haka harka ganni he's my father, mother, sister, brother, friends, No need ka sake magana akan shi na sake faɗa babu soyayya tsakanin mu, kuma ni a yanzu sai na schl gaba ɗaya nke burin yin aure" with so much shock Yarima Yisham ke kallon Sarah, ya jima a haka kafin yace "Ki saka a ranki koma yaushe ne,nine Mijinki daga nan duniya har lahira, I can't stop loving you till the end of my life" yana faɗin hakan ya miƙe tsaye yana gyara zaman Alkyabbar jikinsa, da idanu ta bisa har ya fita daga cikin gidan yana fita kuma dogarawa suka rufa masa baya, kanta ta ɗura saman ƙaramin table ɗin da take kai, Zuciyarta ce ke mata zafi na rashin sanin mene mafita game da rayuwarta,yana da kyau ta san waye zaɓin Zuciyarta waye kuma wanda take jin tausayi, Dafa kafaɗarta akai tayi saurin ɗaga kanta suka haɗa idanu da Beeba, Murmushi da ƙaƙalo zatai Beeba tace "No need" ta faɗa tana zama a nutse take kallon Sarah kafin tace "Stop pretending Sarah" da rashin fahimta Sarah ta kalli Beeba ba tare da tace komai ba, Beeba tai Murmushi tace "Mene yasa kike ƙarya? Baki son Yarima Yashim just tell zai kasheki ne, matsalarsa ce ba, ita Soyayya ana bata haƙƙin ta ne komai a sanya shi cikin muhallinsa" ɗauke kai Sarah tayi a hankali tace "I luv him, stop talking noises Beeba" Beeba ta watsa hannu tace "Ko a ƙafata fa, darajar soyayya tasa nke maki wannan mgnar,domin ni bana zuba idanu ana cin amanar soyayya ko aƙi bata muhimmanci, kallo ɗaya nama idanunki babu son Yarima Yashim a cikinsu abinda idanunki ke nunawa tausayi ne" Sarah ta harari Beeba tace "So ke kawo tausayi" Beeba tayi shewa tace "Jama'ar Nigeria har yanzu basu da waye akan soyayya, tun zuwana U.s na fahimci no need ka tsaya ɓata lokacin ka akan wanda baka so, muhimmanci tausayi daban Sarah, soyayya daban babu kewar tafiyar Yarima Yashim idanunki, U have to think bana son a tauye maki haƙƙin ki, tell me idan baki son sa ni kuma zan faɗawa Umma sai ta faɗawa Mami mene a rayuwar ne, daga Kano sai Abuja fa" Sarah dake kallon wani waje nada ban tace "Mami ta gama min komai a rayuwa, yadda take kula da Auta haka take kula dani, kuma ita ta bawa Yaa Yashim dama mene yasa zan bijire zaɓinta koda bana so dole so balle ina so..." Beeba taja tsaki tare da faɗin "Kutumar uba can, gsky ke middle class ce Sarah, soyayya fa soyayya kike wulaƙanta wa haka, to ni kuma idan ina raye sai kinbi zaɓin zuciyarki, ki saurara daga yanzu zuwa wayewar gari waye kike buƙatar gani ko jin muryarsa koda ace zai zagi uwarki da Ubanki, waye kike son ki kwanta jikinsa kiyi kuka, waye kike son ko zai kasheki zaki iya faɗa masa damuwarki? Waye kike jin ko zai kaiki ya siyar zaki iya binsa duk inda zashi, duk wanda zuciyarki ta faɗi sunansa shine asalin wanda kike so, love ur lover Sarah, ki soshi da zuciya ɗaya, ki saka a ranki duk abinda zaki masa baki faɗi ba, idan kin tabbatar wanda kike so shine zaki aura ki saki dashi ko kwashi soyayya bance sex ba, but Zaki iya masa komai ya zamana duk inda ya juya tunaninki ne a rasa ki hana Zuciyarsa sakat Sarah, ki nutsu yadda kike jin baki da kowa da komai yanzu ya dace ki samawa kanki namiji wanda zai zama garkuwar ki a ko'ina, namijin da zai ɓoye ciwonsa sbd damuwarki, namijin da zai nuna maki hanyar Gsky namijin da ba zai tsaya gabanki yana maki complain akan wasu mazan ba, sai dai yaje ya tari mazan ya shata masu layi... Think think" tana faɗin hakan ta miƙe tsaye tare da barin wajan hankalinta kwance, da idanu Sarah ta bita Zuciyarta cike fal da tunanin maganganun da Beeba ta faɗa mata... Masarautar Zahel.
Sarki Mabus ne ke tafiya da sauri kamar zai tashi sama, jama'arsa na take masa baya hannunsa riƙe da wata zangegiyar takobi, a haka ya Ƙarasa kurkukun masarautar Zahel can ɗakin ƙarshe, Buɗe masa ƙofar akai Sarki Mabus ya tura kansa ciki yana huci takobin hannunsa na ɗigar da jini yace "Kana nan akan bakar ka?" Subash dake durƙushe yyi wani kalar baƙi ya rame sosai da ƙyar yake buɗe idanunsa, ji yake inama ya mutu ya huta, bai damu da azabar da mahaifina ke gana masa ba, burinsa ya sanya Sairah a idanunsa ya tambaye ta mene yasa ta yaudaresa? Mene yasa ta gudu ta barshi bayan ya faɗa mata zai bita duk inda zata, mene yasa sai daya amince ya amshi addinin musulunci sannan zata tafi da barsa da tunanin anya Musluncin babu yaudara cikinsa, saukar takobin da yaji a gadon bayansa ya sanya yyi saurin faɗin "Muhammadur Rasulullah S.a.w" ya faɗa ya runtse idanunsa sbd jinin dake zuba a jikinsa gashi Sarki Mabus wani kalar sara ya sauke masa wanda ya sanya naman jikinsa zabtaruwa, A tsawace yace "Zaka koma addinin Zahel ko har yanzu kana kan bakan ka akan wannan gurɓataccen Addinin musulunci mara gsky da tushe, eh? Ko kuma su kake kamar yadda na yankan sauran wanda suka amshi Musuluncin kai ma yanka ka?" Cikin tsananin azaba Subash yace "Allahussamad, Babu abin bautawa da gaskiya face Allah, kuma na yarda Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama Shine Manzon Allah shine Manzon ƙarshen zamani" cikin fushi Sarki Mabus ya ƙara sarawa Subash takobin a ƙafarsa nan take ƙaramin yatsarsa ya cire gaba ɗaya, ƙara da ihu Subash yyi yace "La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah S.a.w, Allahussamad! Lallai Sarki Mabus zaka taɓe kamar yadda taɓewa ta samu fir'auna matarsa Asiyya ta samu rabauta, Lallai Sarki Mabus zaka halaka kamar yadda Annabi Luɗ ya halaka, rabauta ta samu ɗan sa, Lallai zaka halaka kamar yadda jama'ar Annabi Isa Alaihissalam suka halaka, ka zama ruɓaɓɓe ka zama sallamme taɓewa da hasara su tabbata a gare ka ya akai azzalumi" Subash ya faɗa idanunsa na lumshewa sbd ɗauresa da igiya da Sarki Mabus yyi, a fusace yabar cikin kurkukun SUBASH yaja numfashi a hankali yace "Sairah, Sairah kinci amanata" sai Numfashinsa ya ɗaure baki ɗaya..... Da gudu gudu Sarki Mabus yake takawa har zuwa wajan boka,boka na ganinsa ya miƙe tsaye yace "Na faɗa maka cewa, ɗan daka haifa shine zai zama ajalinka, na faɗa maka haka lallai ka shirya tunkarar masifar dake shirin zuwa Zahel" iska Sarki Mabus ya fesar yace "Gimbiya Noro tace amanata, duk inda ta ɓoya sai na nemuta, a yanzu yarinyar can bana buƙatar zama da ita bana buƙatar saduwa da ita, rayuwarta nake son ɗauka kamar yadda ta tarwatsa min Masarauta da addinin su, Na rantse da abin bauta kabas sai naga bayan rayuwarta" Boka yyi dry yace "Masu cin amanar taka suna da yawa, na faɗa zuwan yarinyar nan tsararre ne, kuma shirin su ya kusa tabbata, Zahel zata halaka haske zai mamaye ta, taɓa yarinyar nan da kake shirin yi shine babban kuskuren ka,ka rabu da ita ka barta" ɗauke boka Sarki Mabus yyi da mari bai jira cewar sa ba, ya miƙe tare da tattara manyan mayaƙansa masu shiga daji ya fasallata musu kamannin Sarah matsayin Sairah, domin bashi da labarin Sairah har yanzu Sarah kawai ya sani "Duk inda take a faɗin Nigeria akawo min ita" yana faɗin hakan yyi gaba, Ayyana dai na can shashinta tana sabgar gabanta.... Naila ce ta fito da sauri tana faɗin "Yawwa Junaidu, maza kiramin hisba, tunda sun mayar dani gantalalliyar tsohuwa, zan nuna musu na fisu iya bariki da kuma tijara, wlh hisba zan kai mai rawani nima fa fitsararriya ce na iya masifa kallon kowa nake, to mene haɗina dasu ba dangi iya balle na baba wlh zasu gane nima ƴar bariki ce." Junaid dai Kallonta kawai yake ba tare da yace komai ba, kallon Tsaf tayi masa tace "Ji banza, ƙila yarinyar ma ta mutu kake hauka zaka kashe kanka sbd ita, tirrrrrrrrrrrrr wlh a Zamanin mu ba'ai wa soyayya mugun sabo, ƙilan kai da ita sai dai ka ganta da rundumemen ciki ko ƴaƴa" banza yyi mata ya shige part ɗin su, yana dafe yana riƙe kai, Naila ta washe baki tace "Yawwa Zaunaid, maza kiramin hisba ɗan mutum ƙatoto ba wasa ba" ta faɗa tana fashewa da kuka, Murmushi Zain yyi yace "Idan na kira miki Shalale kinyi al'ƙawarin ba wanda zaki faɗawa?" Da sauri Naila ta runtse idanunta tace "To ƴar Iska ce ni akace maka?" Hannunta ya kama suka shige part ɗin sa, Ummi ta bisu da idanu tace "Kai da samun ɗan kanka sai a lahira, kamar yadda Riya tabi duniya a yanzu Wlh Abeed ma sai ya lalace yabi duniya, ba naga sai saukar Alkur'ani Mai martaba yasa ake ba ko ta mece Ohhu!" Ta buga cinya tana faɗin "Mu zuba mu gani shege ka fasa"..... Wani irin shaƙuwa ce mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin Jaan da Pinky, haka zatai tai masa kuka ita son ganinsa take, Jaan ko baya ƙauna zai parking a gate ɗin gidan Yaya Rooma Sarah ta fito suna haɗa idanu zai sakar mata kiss ta iska yana langwaɓar da kai da Idanu kawai suke kallon juna kana yaja motarsa yyi gaba, Sarah takai matakin da bata iya yiwa Abeed musu, bata mene yasa ba amma ko tana ɗaki taji ance Yaa Abeed sai ta leƙa ta window Just to see him yaya yake, bayan hakan babu abinda ke haɗa su, tunda ya bata waya bai taɓa kira ba sai dai Jaan ya kira, tsana wajan Raudah ba'a magana zaki baƙar magana amma bata kulata, Abeed ya janye daga jikin Sarah ne sbd wani masifaffan feelings dake damunsa baya iya bacci, baya iya cin abinci kullum cikin tunanin mace yake, wani time ɗin har ƙoƙarin zuwa hotel yake amma sai ya kulle kansa ya tsiri azumin da bai niyya ba, gefe guda kuma ya tarkata harkan Companies ya barwa Danish hatta waƙoƙi ya ajjiye a gefe, jama'a Kullum cikin posting suke a I.G, Twwiter ZAIN ABEED babu latest song's ne?..... Yau friday sati biyu ciff da zuwan su Sarah Katsina yau ne kuma sanya Safna a lalle, tun safe Sarahh take kumbure kumbure ita bata ƙaunar shiga cikin Masarautar wlh, shiryawa sukai cikin fararen lace fitted gown, wacce tai kyau sosai, bag da shoe da veil duk black colour, sun sha makeup kamar me, suna zaune a Main Parlo na Yaya Rooma Beeba ta tictok tana hawa sabuwar waƙar, ABIN YA MOTSA, YANA DUKAN RAI, YA BAKIN GANGA, SOYAYYA CE... Dry Auta tayi tace "Beeba Allah ya shiryaki, yanzu sai ayi tai maki comments da like ko?" Murmushi Beeba tayi tana ajjiye wayar tace "Wa muke jira ne? Yanzu fa duk abokan ango sunzo da angon kansa wlh, nawa mijin nake son samu a cikin su" Raudah tace "Ni kam na tafi gsky" Auta tace "Sarah ake ɗaurawa ɗan kwali fa" kafin su yi magana Sarah ta fito ihu Beeba tayi tace "Gsky Sarah banai maki fatan auren talaka, to wlh ko Safna da take jinin sarauta, batai kyan da kikai ba, Oh My God u look like takeaway, ko ɗan sarki sai yyi faɗa da tarin jama'a kafin ya sameki, idan ba shugaban ƙasa ba gsky mun yafe" Auta tace "She's more beautiful, kamar ruwa biyu take wlh,haka kyan Yaa Abeed ke ban mmkin Anya Mai martaba ba Balarabe bane? Yanzu ance Sarah matar Yaa Abeed Subuhanallahi zu kuga zuƙa zuƙan yara" Raudah taja tsaki tace "Balle ma har abada ba zata zama matarsa ba" Auta tace "Just imagine ace matar tasa ce ai" Beeba tace "Bura'uba da nafi kowa murna, wlh za'a buga soyayya a wajan nan, girman kai da girman kai" kwaɓe fuska Sarah tayi tace "Please ban so.." Miƙewa duk sukai, mota ɗaya suka shiga Beeba ke driving Raudah a gaba Sarah da Auta a baya, tunda Aka buɗe musu ƙofar shiga Masarautar idanun Beeba ya sauka akan abokan ango cikin dakakkiyar shaddar su, manyan yara ne sosai kuɗi ya zauna musu, parking tayi tare da fitowa suma duk suka fito banda Sarah dake cikin Motar, kai tsaye wajan kamon suka nufa Safna na zaune tasha Alkyabba ana jiran ango ya siyi Fuskar Amayar, kuɗi ya zaro 500k ya ajjiye akan cinyar Auta, Beeba ta saki ihu tace "Yeeee Yaa Malik wlh made it subuhanallahi 500k" Beeba ta faɗa tana yaye fuskar Safna, Murmushi Yaa Malik yyi a hankali ya sanya hannunsa ya ɗaga Safna tare da bata side hug yace "Beautiful wife, Buddy see my wife" Yaa Malik ya faɗa yana bugo hannun babban abokinsa, Gently Junaid dake tsaye yana danna Wayarsa yasha farar shadda ya ɗago idanunsa, tare da kallon Malik ba tare da yace komai ba, Beeba tace "Wow, bawan Allah gsky kai ƙyakƙyawa ne i lyk ur style ina chocolate handsome" taɓe baki Junaid yyi a hankali yace "Oh! Thank you, shall we?" Ya faɗa yana kallon Malik daya kama hannun Safna, kai kawai Malik ya ɗaga, Juyawa Junaid yyi yana son answering call ɗin da ake masa, kai tsaye motar da Sarah ke ciki ya nufa yana zuwa ya jingina, Sarah dake cikin mota zafi ya dameta ta sanya hannunta tare buɗe motar zata fito, kafin ta fito wayarta ta shiga ƙara ganin sunan Jaan yasa tayi Murmushi tare da picking call tana kwaɓe fuska a hankali ta narke murya tace "Uhm Uhm ni bun ɓata" gyara zama Abeed yyi wanda yake cikin motarsa daga can ƙofar Masarauta ba tare daya fito ba, but all abinda ake yana ganin komai tuni idanunsa ya sauka akan Junaid, murya kaushashe babu alamun wasa cike da izza da kamewa yaja numfashi yace "Pinky,stay where you are, don't come out" turo baki tayi tace "Ina mota, zafi kuma" a tsawace yace "Sarahh.." a hankali gabanta na faɗuwa tace "Am sorry Jaan,zan zauna ciki" bai ce komai ba amma tana iya jiyo sanda ya sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya kana ya kashe wayar, Junaid ji yyi kamar motsi ya keji a motar hakan yasa ya ɗan leƙa ta cikin glass ɗin motar, bai iya ganin komai ba sai bayanta kawai, tsaki yaja ya matsa daka wajan tare da yin wajan su Malik, buɗe ƙofar motar Sarah tayi maƙale da yawa cikin wata kalar Murya tace "Na gani" tana faɗin hakan ta kashe wayar, tunda ta fito daga motar Abeed yake binta da kallo haka Yarima Yashim dake tsaye kusa motarsa ya ɗauka wajansa za tazo sai kawai yaga ta buɗe mota ta shiga, tana shiga motar Abeed ya ɗauke kansa, yana yiwa motar key, Murmushi tayi gently ta matsa kusa dashi hannunta ta sanya ta shafi sajansa zuwa gemunsa tace "Sorry Jaan" banza yyi mata ya shiga driving tare da ficewa da sauri Yarima Yashim ya shiga motarsa ya mara musu baya, ganin yadda ya ɓata fuska ko Kallonta ya ƙiyi yasa Sarah ta miƙe kujerar da take ƙiris ya rage Abeed ya daki wata motar, lokacin da Sairah ta zauna zaman cinyarsa babu shiri yyi parking, dry tayi tana ƙanƙamesa tare da kissing lips ɗinsa tace "Uhm Am sorry Jaan" juyawa yyi ya kalleta ba tare da yace komai ba, ganin yana ƙoƙarin ɗauke fuskarsa yasa Sarah tayi saurin kama fuskarsa tare da haɗe bakinsu waje guda wani kalar fitanan nan kiss Sarah kewa bakin Abeed wanda ya Sanya yyi saurin rungometa, idanunsa buɗe yana kallon cikin idanunta kamar yadda take kallonsa a hankali ya kama tongue ɗinta ya shiga yi masa wani kalar tsotsa hannunsa kuma na shafa bayanta, yana ƙoƙarin zuge zip ɗin rigarta yaji ana knocking ƙofa, da sauri Sarah ta matsa daga jikinsa tana gyara zaman rigar ta, kusan 5mnts kafin Abeed yyi ƙasa da glass ɗin motar, idanu biyu sukai da Yarima Yashim wanda idanunsa yyi jajur, kallon Abeed dake sanye da wata sakaki black shadda sai ɗaukan Idanu take, idanunsa ya mayar kan Sarah yace "Come out" Kallonsa Sarah tayi ta juya ta kalli Jaan taka ko inda take bai kalla ba, Yarima Yashim yace "I said come out Sarah" haɗe fuska tayi tace "Nifa ba zan koma wajan bikin ba" fuuuuu Yarima Yashim ya nufa wajan side ɗin da take yana zuwa ya buɗe motar kafin yasa hannunsa akan Sarah Abeed yyi saurin sanya hannunsa ya fisgota zuwa jikinsa, murfin motar ya buɗe ya fito tare da kulle Sarah ciki, kamar zaki yana huci ya nufi inda Yarima Yashim yake, da sauri shima Yarima Yashim ya nufo kan Abeed, cikin ɓacin rai Yaa Yashim yace "Itace yarinyar da nake so, ita kuma zan aura" watsa hannu Abeed yyi yace "And so? Na hana ka aureta ne, bance ina sonta ba buhhh she's my life,kana iya cinnawa motar wuta amma ka sake hannunka yana sauka akanta.... Uhm" ya jinjina kai tare da sanya hannunsa ya daki motar irin bai ma san me zai ba, Yaa Yashim yace "Na fika iko da ita, naga alama kai babu mai faɗa maka gsky gantali kawai kake a gari, idan baka da labari yanzu ka samu labari na kai kuɗi an bani Sarah,Kuma ko a yau zan iya kai sadakin Sarah idan yaso na jira lokacin aure, ko zaka jaa na dake ka na daki banza" shafa sajansa Abeed yyi walking slowly ya Ƙara️sa kunnansa yace "Kasa a yau zan aikata abinda banyi niyya ba, idan ka isa ɗan halak ne ka hanani, zan tabbatar maka a yau na fika iko da ita" yana faɗin hakan ya juya kamar walkiya ya shiga motarsa Sarah da tsoro ya kamata tace "Jaan please, i need to talk to him" fisgota yyi tare da matseta a jikinsa yace "As from today, zan tabbatar dake a...." Shiru yyi yana fesar da huci tare da matseta a jikinsa ya shiga sharara gudu akan titi lokacin anata kiran sallah, kai tsaye haɗaɗɗan gidansa ya nufa da ita...




Zain Abeed isn't free

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads