Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 110552 words

Chapter 10 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ka bi su da dukka .


Al'amarin Nihal kuwa daga gidan Marka wajen daukar Fim din Darakta Aliyu ta wuce acan suka wuni, wannan ne karo na farko da ta fara jan ragamar fim a matsayin cikakkiyar Jarumar fim din .


Ta wargaza gaba daya labarin ta sauya shi amma a cikin siyasa, Aliyu ya fahimta sosai tsarinta ya fi nasa yin maana. Ya ji dadin hakan kuma nan da nan aka yi sinasinai masu yawa a ka gama. Hashim ya samu shiga amma a matsayinta babban abokin actor. Tunda labari ya canja daga salon soyayyar da aka gina shi ya koma kan zamantakewa dan haka babu ma muhallin yin rawa da waqa. Duk da haka Aliyu ya dage sai an yi rawa da waqar amma akan qawar jaruma waqar ta sauya aka mayar da ita tunani qawar Nihal take yi a zuci dan tana son saurayin qawarta.


"A je a haka tunda baragadar dai sai sun yi amma ba da ni ba." Nihal ta fada a ranta a lokacin da take zaune akan kujera tana kallonsu su na ta tiqar rawa . Hashim kawai take kallo da wani qaton baqin takalmi kambas da yellow Jeans da ya siyo a gwanjo wai shi a dole sai ya zama super star. Takaici ya ishe ta dan ba yadda za ta yi ta hana su ne.


Sai daf da magriba aka tashi da zummar gobe zaa karkare. Naira dubu biyu Aliyu ya miqawa Nihal gami da bata haquri gobe zai qara mata dan wani abu. Ashe gara ita naira dubu guda aka bawa Hashim kuma murna yake. Dariya ce ta subuce mata ba tare da ta shirya ba, ta yi godiya suka fito hanya. A tunaninsu dariyar murna ce nan kuwa yawan kudin ne ya bata dariya ta tuna yawan maqudan kudin da ake biyanta a turai a wuni daya kacal.


Hashim yana ta yi mata kasafi yadda zasu samo daki me arha ta zauna ga dubu biyunta ga dubu dayarsa daman yana da wata dubu biyu a boye, ya zama dubu biyar kenan. Nihal ta miqar da dubu biyun nan tana tisa su tabbas guda biyu ne kudin aikinta na farko da aka fara biyanta a hannunta.


Ta fada a bayyane "Allah na tuba Ka yafe min." Dan ta tuna sanda ake yi mata kyauta miliyan daya ta raina. Tabbas wannan wani darasi ne da aka aiko ta ta koya a rayuwa. Yau gashi sai da ta wuni tana aiki ga yunwa da qishirwa duk akan naira dubu biyu .


Ta miqawa Hashim kudin ta ce " ungo hada dukka na baka."


Ya cika da mamaki ya ce " a hada da na wajena a kama dakin? Kina da naira dubu ashirin a hannun Tukur fa ."


Ta ce " kada ka damu ."


Yayi mata duba na rashin fahimta su ka ci gaba da tafiya .


Hashim ya ce " me zaki ci yanzu? A ina zaki kwana? Dole yau ma sai dai ki kwana a gidan Marka me dinki, zan sake roqarta."


Ta girgiza kai ta ce " A'a ba zan kwana a can ba na gano gidan wasu 'yan uwanmu can zan dinga kwana. Ka da ka damu can zan je. Zan hau acaba in tafi gobe mu hadu a location kawai ."


Kafin ya ce wani abu ta hau babur ya wuce. Ofishin Shazali ta nufa kamar tare suka iso ko fitowa daga mota bai yi ba ya dawo daga kano . Bayan sun gaisa sai ya miqa mata leda mai dauke da abinci mai zafi, daya ledar kuwa ruwa da lemo ne da ice cream masu sanyi .


Ta ji dadin hakan saboda tsananin jin yunwar da take addabarta amma jikinta yayi sanyi da ta tuno irin baqar yunwa da Hashim yake ji amma bata san yadda zata dinga bashi ba. Ko me zai samu ya ci yanzu? Ba zai wuce tuwon baqar dawa miyar kuka ba . Kullum maganarsa kakarsa ta surfa dawa ya kai niqa. "Allah sarki Hashim babu yadda zan yi ne domin bana so ka gane ko ni wacece. "


A cikin ofishin Shazali ta baje akan tabarma ta ci ta qoshi amma duk cinta bai wuce ta ci rabi ba, rabin anan take barinsa ko ta yi yunkurin zata fita da shi ta bawa almajirai sai Shazali ya ce ta bari yana da almajiri. Bata sani ba ko 'yayan hajinsa ne almajiran.


Da ya ga ta nutsu ta dawo hayyacinta sai ya yi mata albishir da cewa tun da yamma komai na sabon gidanta ya kammala. Sai ta ji dadi a ranta dan haka motarsa ta shiga ya kaita. Ba haka ta zata ba domin gidan yayi kyau har da get karami. Sannan daga ciki flat ne me falo da dakuna 3. Lallai Shazali yana da test ya san abinda ya dace da ita . Ya zuba kujeru a falon guda biyu, sai cikin dakuna kowanne da katifu manya da filo. Ga karamin jannareto sabo, ga bokitai a bandakuna sababbi. Sabon gida ne, ya tabbatar mata ya biya kudin shekara guda amma da ya fadi kudin hayar gidan sai ta ji arhar ta baci .


"Daman gida a kauye baya tsada? Kenan in siyan gidan ma zaa yi ba zai yi tsada ba ." Nihal ta tambaya .


Shazali ya ce " ai kuwa siyarwar su ka fi so ma dan dai ya dade a haka ne baa siya ba suka bayar haya. Ana so a siya ne ?"


Ta girgiza kai ta ce " ba yanzu ba a bari ayi shekarar a gani. "


Ta sake zayyano masa abubuwan da take buqata gobe ya siyo mata. Ta bashi umarni ya dinga aiko mata da abincinta gida tunda yanzu ita kadai ce a gidan ba sai ta dinga zuwa ofishinsa ba.


Ta yi bacci mai dadi yau wanda bata taba yin irinsa ba tunda ta bayyana a garin nan, babu sauro babu zafi babu taurin tabarma. Ta sha wanka a shaya kasancewar akwai ruwan famfo a gidan . Talabijin ce ta rage mata kawai.


" Allah abin godiya .Nihal ta fada a lokacin da ta tashi yin sallar tsakar dare a cikin sujjada.


Asuba ta gari Nihal Nuren Mubin.


Da misalin karfe 10:45am Nihal ta fito daga gate din gidanta ta datse sannan ta tari acaba ta hau, bata tsaya a ko ina ba sai a wajen daukar shirin. Ta iske su Hashim an dade da hallara.


An sha aiki tun qarfi amma a yau aka qarqare kafin magaruba. Naira dubu uku Darakta Aliyu ya qara mata , Hashim kuwa dubu daya da dari biyar ya samu ko dubu biyun bai kai ba.


Su na fitowa kan hanya sai ya ga Nihal ta miqawa wani makaho naira dubu daya, za ta kara masa wata dubun sai Hashim ya zabura ya fisge kudin.


Ya ce " kina da hankali kuwa? Rabarwa zaki yi alhali ko dakin zama baki da shi."


Ta yi murmushi ta ce " ya kamata in sadakar da kudin aikina na farko dan neman albarka. "


Ya kasa bata amsa dan ya rasa ma a yadda zai fassara wannan al'amari. Shin tabin hankali zai kira ta da shi ko rashin tunani?


Nihal ta rasa da yaren da zata yi masa bayani ya fahimta don ya tafi gida ya daina bin ta. Ya dage sai ya raka ta ya ga gidan yan uwanta. Su ka hau acaba suka isa qofar gidan a wajen gari gidan yake amma tabbas gidan 'yan gayu ne dan ya qeru. Akan dakalin qofar gidan su ka zauna yayin da Hashim ya lura an datse gidan da qaton kwado.


Ya zabura ya ce " ai gidan a rufe yake. Basa nan ne ? Yaya za ki yi toh? "


Ta yi dariya ta ce " sun fada min za su je Kano biki amma komin dare za su dawo. Zan jira su babu damuwa, ka tafi gida kawai sai gobe amma gobe bani da aiki ba zan fito da wuri ba sai da yamma zan zo in same ka, mu hadu a daidai gidan Marka ."


Ya amsa da " Ba damuwa amma yanzu me za ki ci? Wuni guda baki ci komai ba, ko gurasar da Darakta ya siyo baki ci ba. Ko in karbo miki biredi da tsire?"


Ta girgiza kai ta ce " ka tafi kawai kada ka damu ."


Ya tashi ya tafi da alama ba zai hau acaba ba dan kada ya taba kudin hanyar dakin da zai kama mata, cancana kudin nan yake.


Ta ji tausayinsa ya kamata ta fada a bayyane " dama zan iya taimakonka a yanzu, ka rabu da talauci kamar yadda kake daman tashi-fadi har sai ka inganta rayuwa."


Sai ta fashe da kuka sannan ta tashi ta dauko mukulli ta bude qofar get din ta shiga ta datse. Addua kawai take ta tottofawa a kowacce kusurwa ta gidan domin gidan yana bata tsoro zama ita kadai. A bakin kofar falo ta iske ledojin abinci Shazali ya kawo mata domin yana da mukullin get guda daya .


Ta bude qofa ta shiga da ledojinta. Abinci ta fara ci sannan ta yi sallah ta yi wanka ta kwanta .


** ** **
Ita da ta cewa Hashim su hadu da yamma sai gashi a bakin get din gidan da misalin qarfe tara na safe . Idonta biyu wannan karon rubutu take tana zayyano abubuwan da ShaAli zai siyo mata, ta gaji da daura zani dogayen rigima abaya take so guda uku da takalma.


Ta ji ana buga get bata yi mamaki ba ta dauka Shazali ne, ta na fita sai ta ga Hashim cike da murnarsa.


Ko gaisawa basu yi ba ya ce " ki zo da sauri. ta samu fa. An zo nemanki, akwai aiki har guda biyu daya na Tukur daya na abokin Aliyu ne, wato Darakta Musa. Domin Aliyu ya bashi labari kin iya acting. Zo mu tafi da sauri ana can location ana jira ance in kira ki ne."


Ta ji kamar ta kwala ihu domin ta gaji. Sai ta tuna abinda ya kawo ta kenan kuma dole ta yi.


Awa daya ya yi yana jiranta ta shiga ciki ta shirya sannan ta fito, ta datse get suka tafi .


Ya tambaye ta cike da mamaki "ba kowa a gidan ne na ga kin datse ta baya ."


Sai da ta yi inda-inda sannan ta hado kan amsar " eh basu kwana a gida ba ashe sun bar min mukulli a maqwabta sai da suka leqo suka ganni ina jira sannan suka kawo min, amma yau zasu dawo ."


Lallai kin caba kin huta da wulaqancin su Mami Allah Ya musanya miki da mafi alkhairi. Au na manta ban fada miki ba a fim din nan dukka biyu akwai Amina 'yarkwalisa, akwai Mami da Asabe dan Allah kada ki kula su ku yi fada, kuma kada ki ce ba zaki yi ba saboda su sai su ji dadi su zata tsoronsu kike ji."


Ta ji dadi a ranta da aka ce har da su, ai kuwa saboda su din ne ma za ta yi Fim din zasu gane akwai banbanci tsakaninsu da ita mai tsumma.


Ofishin Darakta Tukur suka fara zuwa, yayi murna da ganinta sai ya kwatanta musu wajen daukar shirin ya ce su hau acaba zai same su acan.


Sun isa wajen sun iske kowa ya hallara nan fa ransu Mami ya baci da suka ga har da Nihal. Ta yi sallama basu amsa ba sai harara da murguda baki suke yi mata .


Sun zaci za ta hau rabe-rabe saboda tsoronsu amma sai suka ga GABA GADI ta kutsa tsakiyarsu ta zauna fuskarta cike da fara'a.


Nihal ta dubi Hashim wanda ya sankare a tsaye yana fargaba ta ce " Hashim ka tafi wajen maza ka zauna zan zauna tare da 'yan uwana mata abokan sana'ata. "


Hashim yana tafe yana waiwaye sai bai ji wata ta sake yin magana ba dai. Addua Ya ke Allah Ya kiyaye tsautsayi da asarar qashi da tsoka, yana gudun kada a casu ka fasa baki ayi karaya .


" Amina 'yar kwalisa yaya jikinki?" Nihal ce ta tambaya gami da dafa kafadar Amina .


Hohoho zo ka ga takaici da baqin cikin da ya dirsu a zuqatansu.


Naja'atu ta yi dariya ta ce " Nihal baki da dama ashe, daman kina magana haka?"


Tsaki Mami harka ta ja ta ce da su " dalla ku taso mu bar wajen nan ."


Ta na tafe a gaba su na biye da ita kamar wata kaza da 'yayanta amma banda Najaatu bata bi su ba ita ta zauna tare da Nihal.


Hira suke ta yi Najaatu tana ta son dukan cikin Nihal ta ji tarihinta. Ita wacece? Me ya sa ta zo ta shiga Fim? Amsa guda bata samu ba sai ma dai ita ce ta ke ta bawa Nihal tarihin rayuwarta.


Najaatu ta ce ita 'yar garin Bauchi ce ta gudo ne a sanadiyyar zaa yi mata auren dole, har yau iyayenta ma basu san in da take ba .


"Subhanalllahi me yasa kika yi haka? Kuma ana saka ki a fim din? Finafinai nawa ki ka yi kawo yanzu ?"


Najaatu ta tabe baki ta ce " ina fa, kullum sai dai in yi musu rakiya, dakyar ma ake saka ni a cikin 'yan rawa ko 'yar aike."


" Ai ba zaki taba ganin daidai ba saboda babu albarkar iyaye." Nihal ta fada GABA GADI babu kokonto.


Naja'atu ta yi shiru can ta ce "ke ai babanki ne ya kawo ki da izininsa kika shigo shiyasa ki ka fara ganin hasken abin."


Nihal ta yi murmushi ta ce " haka ne ."


Tukur ne ya qaraso da sauri sai kowa ya taso ya zo wajensa ya tsaya cike da ladabi, ya fara rarraba aiki sai ga Nihal da Amina 'yar kwalisa an hada su a matsayin kawaye a cikin Fim din. Nihal ta dage ita bata iya karatun script ba sai dai a fada mata da baki. A yi ta fada mata ana maimaitawa daga qarshe ma Hashim aka saka ya zauna da ita ya dinga karanta mata kafin a zo kanta .


Nihal ce ta dafa kafadar Amina 'yar kwalisa a yayin da ake daukar shirin ta yi murmushi ta ce " qawata ki na da ji da kai amma ki sani ki daina wulaqanta mutane don baki san daraja da martabar da Allah Ya yiwa wanda kike wulakantawa ba. Zai yiwu ya fi ki asali , arziki , ilimi , Lima da martaba."


Wannan ba ya cikin script amma yayi daidai da sakon da ake so a isar a cikin fim din.


Amina ta zabura ta hada da ashar ta ce " gaskiya darakta ka raba ni da wannan yarinyar. Yaushe aka rubuta haka a script din in ba so take ta fada min magana ba?"


Tukur ya ce " banda abinki Nihal fa bata iya karatu ba dole ki yi mata uzuri. Abinda ta ga ya dace take fada idan ta fada kuma sai ya fi hawa."


Haka dai aka gama daukar Fim din nan kamar zaa yi fada amma Nihal bata kula su ba .


Tukur yayi qirmisisi bai bawa Nihal ko sisi ba haka bai yi mata zancen kudinta na wajensa ba ita kuma bata tambaya ba.


A cikin satin nan gaba daya Nihal bata zauna ta huta ba, aiki take ta yi daga safe har dare amma kudin data samu bai kai naira dubu goma ba. Ta raba gida biyu ta bawa Naja'atu rabi Hashim rabi ba tare da dayansu ya san an bawa dayan ba . Shi dai Hashim tara mata kudinta yake yana jira su cika a kama hanmyar daki .


Nihal ta takura sai Hashim ya kaita gidansu ta ga iyayensa tana ta yi mata hanya-hanya yana gudun kada ta je ta ga tsantsar talaucin da suke ciki. Yau da safe ta ce qafarsa-qafarta sannan ya amince suka tafi yana fargaba kada ta raina shi ta daina kula shi. Hashim ya yarda ya kai ta gidansu, ya kasancewar maraya a hannun Kakansa da kakarsa ya girma. Tsohon ya dade a zaune komai sai an yi masa a sanadiyyar ya sami shanyewar barin jiki. Tsohuwar ce me kwari sai ta yi surfe an biya ta su ke cin abinci, sannan tana saqar tabarmar kaba.


Nihal na shiga gidan sai ta ji hawaye ya cika mata ido don tausayi, gidan kasa ne duk yawancin dakunan sun rushe an saka zana an zagaye. Hashim yayi dibi-dibi ya rasa kujera me kyau da zata zauna akai, da kyar aka samu wani buhu aka shinfida mata a inuwa a tsakar gida. Ko ina shanyar dusa ce da qanzo.


Bayan sun gaisa da tsofaffi sai Inna ta ce mata tana da labarinta a wajen Hashim. Kan ka ce kwabo hira ta barke a tsakanin Inna da Nihal kamar sun saba . Hashim yana ta tsoron kada Inna ta baro masa, dan ya ga ta shiga bata wani dogon tarihin da baa tambaye ta ba.


Hashim yayi-yayi Nihal ta taso su tafi ta qi tafiya ta ce ya tafi ya barta. Bai san Ilimi ta ke kwasa ba, tarihin da-da-da ta ji wanda bata taba ji daga bakin iyayenta ba. Ta na ta nade sunayen abubuwa da yadda asalin aladar Hausa da masarautarsu take.


" Hashim ina wannan kudin yake?" Nihal ta tambaya


Yayi sororo yana kallonta ya na ta qifta mata ido akan tayi shiru kada ta yi maganar kudi a gaban tsofaffi .


Ta kawar da kai gefe kamar bata gane abinda yake nufi ba ta ce " kawo dukka."


Ya miqa mata nasa da nata ya kai dubu goma sha hudu bai ankara ba sai ya ga ta damqawa Inna gaba daya. Ta ce " Inna na ki ne dukka ku ci abinci ."


Inna ta fashe da kukan dadi ta shige daki tana rusa kuka ta bayan da ta damqe maqudan kudinta a hannunta. Ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads