Header Ads
Showing 81001 words to 84000 words out of 110552 words

Chapter 28 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

qafafuwansu aka zuba su a bayan mota, aka tafi da su.
Ashe Aisa ta yi niyyar bin su ta fasa yin fim din, bayan jiya an fara yi da ita. Bash ne ya yi mata gargadi ya ce muddin ta tafi, ba shi ba ita. Ga shi ita take son sa dole ta tsaya, amma ta cika fom kamar za ta fashe. Ta tafi a fusace ta bude gaban motar Bash ta shiga ta zauna, ta na huci kamar kumurci. Bash ma a fusacen yake ya ja mota suka tafi, shima fushin yake yi tun jiya ba tare da kowa ya san dalili ba dan haka babu mai yiwa wani hira a cikinsu.
Abbas da Hashim ne a gidan gaba, Nihal da Najaatu ne a kujerun baya suka tafi. Suka isa location su ka iske wajem ya cika tab da mutane dan har motoci sun iso tun dazu? har da qarin wasu motocin daga Kano. Yau ne ranar da zaa ragargaza fim dan na jiya wasa ne.
Abbas ya gaisa da kowa a ka shiga ware kayayyaki, masu neman batir na kyamara da sauran abubuwa duk Abbas ya siyo musu ya rarraba musu. Ya bude script ya na karanto in da aka tsaya da kuma ta in da zaa gara yau.
Sai su ka hango qura daga nesa, raquma ke tafe himili guda da masu shudayen kaya akai. Su ka juya baya su ka hango wasu tawagar raquman masu jajayen kaya ne akai. Sai kowa ya mimmiqe tsaye ana kallo tun baa ganewa har suka fara matsowa aka fuskanci raquma ne tuli.
Sai hankalin Abbas ya tashi ya zabura ya ce "me zan gani? Me yasa raquma suka dawo, bayan na sallame su jiya da kudi mai yawa?"
Najaatu ta ce "Nihal ce ta ce su dawo yau ma."
Abbas ya daka tsalle ya gigice har sai da wandonsa Jeans ya sulmiyo ya kusa faduwa saboda tashin hankali, Allah Ya sa akwai gajeren wando (boxes) a ciki da an yi tsirara.
Abbas a cikin fushi ya ce" ubanta ne zai biya su da ta ce su dawo? Ina Nihal din? Sai ta ci ubanta yau. Wannan yarinya ta cika rawar kai."
Aka waiga ko ina babu Nijal babu alamarta Najaatu ta ga Darakta yayi kanta kamar zai sakar mata mari sai ta gudu gefe ta tsaya.
Hashim kuwa ya dade da artawa da gudu sai da ya kai wani geji da ya tabbatar ya haye sannan ya tsaya yana leqensu daga nesa.
Nan fa maqiya suka samu su na ta caccaka "ah toh ai an fada maka ka qi ji, Nihal sai ta kashe ka tukunna ka ga yanzu ta sa har wandonka ya na shirin fadowa, toh nan gaba ma sai ka yi tunbur? rigar ma sai ta fado." In ji Tukur.
Aisa yi take, su Duduwa yi suke, da sauran mata da mazan wajen kowa na zagin Nihal.
Amina ta ce "wai ina armurar take ne ko ta gudu?"
Daman Nihal sun hada baki da masu kyamara, kawai sai ya fara dauka. raquma su na matsowa hotuna su na sake bayyana.
Nihal Nuren Mubin ce a tsakiyar raquma guda hamsin tana cikin masu shudin kaya duk da bata shudin an banbanta shi da na sauran kowannensu takubba manya ne a hannunsu. Su na tafe su na jujjuyawa, ga ganga ga kida, ga busa ga kirari ana yi ta yi ma ta.
Daman a sin din yau zaa tashi ne a inda zasu fito yaqi amma a qasa zasu fito ba a kan raquma aka ce su fito ba dan ba zai iya daukar hayar su ba.
Da Jamaa suka ga haka sai kowa ya arta da gudu ya zubar da kayan da yake hannunsa suka tafi can nesa suka tsattsaya su na kallon ikon Allah.
Buzaye tawa biyu suka hade a tsakiya, sai su ka hau yaqi a junansu. Ana ta karo da tokubba kamar yaqin gaske waje ya kidime da qura.
Nihal ma yaqin take yi, gumurzu yayi gumurzu. A can ka hango su Abbas sun sake cillawa da gudu kowa yayi ta kansa. Masu kyamara ne kadai su ka rage a filin daga ashe Nihal ta sake yin hayar wasu masu kyamar Darren fata guda biyu, suma su na cikinsu su na daukar bidiyon.
Abbas ya na tsaye kusa da Bash Auta ya ce " Bash na shiga uku, ban taba shiga masifa irin ta wannan fim din ba. Yanzu wadannan su waye? Da ta hayo su kuma sai ta gudu, ko bata nan su dai sun yi aikinsu dole a biya su. Da me zan biya su duk an gama tatike ni. Ashe yarinyar nan haka take har nake goyon bayanta? Nihal ta kashe ni." Ya dora hannu akai kamar mai shirin fasa ihu?"
Bash ya ce " kada ka yanke hukunci, bari su gama karon nasu su sauko sai mu ji daga inda suke."
An dauki lokaci mai tsayi ana dauki ba dadi da masu Jan rawani da masu Shudi. Ga gawawki nan burjik a qasa amma masu jajayen aka fi kashewa. Su Nihal ne masu shudin kaya dan haka sun ci gari. Sai masu jajayen su ka rage sauran dan haka sai suka ruga da gudu suka yi can nesa. Masu shudaye suka tattare raqumansu suka yi gaba suka bar gawawwaki a zube a qasa. Sai kida da busa suka canja, wannan busar ta alamar an yi nasara ne su ka juyo gida.
"Cut." in ji Nihal. Sai masu dauka su ka tsaya.
Ta sauko daga kan raqumi ta cire rawani sai ga fuskarta ta bayyana. Ta dagowa su Abbas hannu alamar su taho.
Sai a yanzu suka gane ta, kowa ya sake cika da mamaki gami tsananin takaici.
Abbas ne a gaba a sukwane ya tunkaro ta ya na fada yana baza hannuwa. Meye hakan? Me kika yi kenan? Kin saka ni a masifa Nihal? Da yawun wa kika aro rakuma, da me zan biya su?"
"Ai an biya mu ranka ya dade." daya daga cikin buzayen ya bawa Abbas amsa."
Sai ya sankare a tsaye ya na mamaki.
" waye ya biya ku?" Bash ya tambaya cike da gigita.
Buzu ya daga yatsa zai nuna Nihal sai ta zabura ta ce " Gwanantin Niger ce ta biya har ta bamu turawan faransa masu kyamara guda biyu." Ta nuna turawan.
Sai kan kowa ya kulle musamman Abbas ya san dai babu wata gwamnati da take tallafawa 'yan fim.
Shi dai koma menene tunda bashi zai biya ba komai ta fancama facan. Sai Abbas ya ji wani sanyi a ransa ya fara washe baki ya na tafi yana yabon yadda sin din ya qayatar.
Kwakwalwar Bash ce ta tunano masa maganar Bilal cewar ya ga Nihal da Buzu da Bature sun yi meeting tabbas wannan ne dalilin yin meeting din, ita ta biya babu wata gwamnati.
Wannan karon maqiya ne suka fusata su na ta suka cewar "ta yaya zaa bashi gudunmawa amma bata nuna masa bata sanar da shi ba kawai ta yi gaban kanta. Ta shirya komai ba tare da sanin Darakta ba? "
Abbas ne mai basu hakuri yana cewa ba ta yi laifi ba a bar zancen kawai."
Maqiya sun rasa yadda zasu shiga tsakani Nihal da Abbas duk ta in da sika bi sai a gyaro ta.
Mai daukar hoton tsegumi ya tura hotunan Abbas lokacin da wando ya sulmiyo qasa. A ka rubuta Nihal ta cazawa Darakta Abbas kai har wandonsa ya fado qasa. A sake rubutawa Darakta Abbas ya zagi Nihal a lokacin da ta yi gaba gadi ta hayo hayar raquma masu yawa ba tare da saninsa ba. Amma yadda suka kai wancan rahoton haka suka koma suka warware da aka ji cewa an biya kudin raquma tuntuni, Abbas ya na washe baki yana yabon Nihal. Aka dauko hotunan Nihal a yayin da ake gumurzun yaqi a filin daga.
Abbas ya tambaya "yanzu Nihal me zaa yi nan gaba?"
Ta ce " borori ne zasu saka kayansu su fito a layi dauke da kwaryayyaki mai dauke da alkaki sai su jeru su na jiran isowar Gimbiya daga yaqi. Sarki ma zai shirya ya zauna a fada, Gimbiya za ta wuce ana yi mata jinjina da busa har ta shiga."
"Cab ana wani abu wai shi juyin mulli a nan wajen" in ji Aisa.
Tukur ya fusata ya ce "na zaci kai ne Darakta ita kuma akta daman akta ce za ta fadawaDarakta abinda zaa yi ko Darakta ne zai fadi abinda zaa yi?"
Abbas ya kwashe da dariya ya basu amsa daidai da tambayar su ya ce " Nihal ita ce Actress ita ce Actor ita ce Darakta ita ce mai kyamara."
An wuni ana ta daukar fim, sinasinai masu ban sha'awa da abin mamaki. Nihal ta na ta yi musu ba zata musamman yadda suka ji tana furta wasu kalamai cikin yaren Buzaye, ita da Najaatu. Yaya aka yi ta koya? A ina ta koya? Wa ya koya mata? itace tambayar da suke ta yiwa zuqatansu
Hashim ya bawa jamaa mamaki yadda shima ya zage ya na acting kai ka ce kwarare ne. Toh ai zama da Nihal ne ya jawo masa haka.
Bash Auta da Nihal yau an gwabza yaqi bayan an qare sai aka sauko aka kamu da soyayya mai qarfi a inda iyayensu kuma suka ce basu san zance ba.
Sai ga Nihal da Bash su na zubar da hawayen gaske su na ban kwana a biyayya, sai da kukkansu ya taba zuciyar kowa tamkar soyayya gaske.
Aisa ta gasgata wannan kallo da kalamai da hawaye ya wuce wasa. Kishi ya tokare ta ta fusata sosai sai da kowa ya gane ta.
Tabbas Abbas ya na da tabbacin nasa ba irin na su ba ne, abokan gaba sai su mutu.
Idris ya yi saranda ya yarda Nihal ta zama tsanin kai Abbas ga samun nasara, domin ya na ta samun hotuna da labarai kai tsaye daga mahallata wajen shooting.
Alhamdulullah an yi wuni guda ana tafka fasaha a wannan waje, haka Nihal ba ta fadawa cewar da kudinta ta hayo hayar rakuma har aka gama, ta ce gwamnati ce ta ba ta kowa bai yarda ba amma an tafi a hakan.
Su Mami sun yi saranda cewar Nihal ta girme su a komai sun ba ta girman ma kawai. Fasaharta da wayewarta sun yarda ba za su iya ja da ita ba. Aisa ma fa ta miqa wuya ta yarda Nihal ta gyara mata sinasinanta ko Allah zai sai ta daina kwafsawa. Sai ga Tukur yana shiga harkar Nihal, bata bashi amsa dan shine babban maci amana, ya wulakanta a lokacin bata da tamkarsa.
An yi mako guda ana zarya saga Maradi zuwa cikin sahara haka raquma basu daina zuwa ba.
Bayan an gama da cikin sahara sai a ka dungumo aka dawo kano a birni zaa qarasa.
Nihal da tawagarta su na motar Abbas sun girmi motar su Duduwa Indiyana.
Su Nihal basu koma Wudil ba a wani gida qarami Abbas ya sauke ta ita da Najaatu a daki guda Hashim a daki guda.
Su dai sun ga in an gama shooting tana fita ta dawo, ba zato ba tsammani sai suka ji ta ce su zo su raka ta wani waje, cikin wani katafaren gida a cikin Nasarawa GRA ta kai su ashe hayar gidan ta kama wanda kudin hayar ya kai a sayi gidan sumunti a qauye, komai akwai a ciki.
An yi sati guda ana ci gaba da daukar fim din a cikin garin Kano. Nihal su na zuwa su na dawowa ba tare da an san daga ina suke zuwa ba.
Da aka kammala sai Abbas ya sallami kowa ya biya su har Najaatu da Hashim. Sun yi bazata sun sami kudin da basu taba zato ba su na ta murna.
Abbas ya shiga jin nauyin Nijal dan ya rasa ma nawa zai biya ta kudin wahalar ta, tabbas ya kamata kudinta ya fi na kowa dan ita ce ma Fim din gaba daya.
Nihal ta lura da haka sai ta yi murmushi ta dube shi ta ce " Darakta ni ce da godiya domin ka yi min komai. A lokacin da na buqaci da ka yarda da ni ka damqa min komai, ka amince da hakan ka bani dama. Damar da na jima ina nema baa ba ni ba sai kai. Ka dade ka na cewa ka ji a jikinka zan iya ka na so ka gwada ni. Idan ka yunkuro sai maqiya su danne ka har zuwa lokacin da Allah Ya ce ayi kuma aka yi. Ka gama biya na ba na buqatar naira dayarka ta hada mu. Dan haka kada ka damu kanka a kaina. Bata jira ya bata amsa ba sai ta fice sai dai su Hashim suka same ta a wajen ofis din suka wuce. Hashim dai ya kasa yin shiru sai da yayi magana.
Ya ce " yanzu duk wahalar nan da kika sha kin yafe masa komai ya tafi a banza?"
Da ya ga babu amsa sai harara, ya ja bakinsa yayi shiru tabbas shi da Najaatu su na tattaunawa sun kasa gane ko ita wacece.
Nihal Nuren ve zaune a katafaren falonta da remote Ac a hannunta tana qarawa tana ragewa da safiyar jumaa. Hashim da Najaatu ne zaune akan luntsum-luntsuman kujerun falon, su na zuqar na'ura mai sanyi su na kallon talabijin.
Nihal ta jawo jakarta ta dauko mukullin gidanta na Wudil sai ta damqa a hannun Hashim.
Ta gyara zama ta ce " ina so Najaatu ta ci gaba da zama a dakinta, ina so ka dauko Inna da Baba su zauna a daya dakin kai kuma ka zauna a dakina."
Hashim ya karbi mukulli cike da mamaki musamman da ya ji ta ambaci sunan Inna da Baba. Haka ma ta ga irin wannan mamakin akan fuskar Najaatu.
Nihal ta sake bude jaka ta dauko wasu takardu ta miqawa Hashim ta ce "ka karanta da qarfi kowa ya ji ka san ni ban iya karatu ba."
Hashim ya fara karantawa ni Alhaji mansur isa Wudil na siyarwa da Hashim Ibrahim wudil gidana da ke unguwar kalau by pass, akan kudi naira miliyan daya da dubu dari biyu, ya biya baa binsa bashi."
Hashim ya zabura ya daka tsalle ya dafe qirji ya ce "ni Hashim din ko wani ne? Gidan waye? waye mansur?"
Najaatu ta gane sai ta ce "Mansur sunan wanda ya siyarwa da Nihal gida ita kuma ta siya da sunanka, idan na fahimta Nihal Nuren ta siyawa Hashim Inrahim gida sukutum. Haka ne ko Nihal ?"
Nihal ta yi dariya ta gyada kai ta ce " Eh an yi haka."
Sai Hashim ya barke da kukan dadi ya durqusa a gaban Nihal ya na hawaye ya kasa godiya.
Ya ce "daman Nihal ke me kudi ce ki ka shiga cikinmu kika saje da mu talakwa? Ni kuwa wanne irin hallaci na yi miki da har na cancanci ki

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads