Header Ads
Showing 99001 words to 102000 words out of 110552 words

Chapter 34 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

shawarwarin yadda zaa shagon kan mahaifinta ya yarda ta yi. Dan sun san ba zata taba yin abinda Daddy bai bata umarni ba.
Sun so su dawo da ita Nigeria sai ta zauna a wani babban hotel a ci gaba da magana da Daddy ba tare da ya san tana qasar ba yana amimcewa sai kawai ta fara kamfen. Nihal bata yarda da shawararki ba saboda ta san halinsa zai gane. Su ka taho suka bar ta amma ta yi musu alqawari zata shawo kansa.
Ta fara yi masa nasiha a waya "Daddy baa saka tsiya da tsiya kai ka saka masa da alkhairi mana. Abokinka ne, ka yi masa uzuri ka tuna halacci da ka dinga fada yayi maka a lokacin yana Ambassador. Ya hadaka da shugaban qasa an qara maka girma a lokacin ana mulkin soja har sunanka ya bayar aka zabe ka aka nada ka gwamnan Lagos. Jaba Daddy mu na yiwa Allah laifi ma ya yafe mana ka bari in yi masa kamfen in ya so ba sai mun auri 'yayansa ba."
Yadda maganarta take shiga haka take fita bai Amince ba. Washegari irin wannan nasiha ta yi masa amma a banza. Sannu a hankali dai ya fara saukuwa, ya yarda ta yi masa kanfen amma ta social media ba ta zahiri ba.
Ta ji dadi da hakan ma, ta na fara yi sai ga dandazon comments da likes.
"Nihal kema kina yin Abba Muse daman saboda ke mu ma zamu yi shi kuwa." In ji masoyanta.
Hashim da ya ga haka sai ya buga hoton Nihal a gefe na Abba Muse ne ya dinga liqawa a ciki da wajen Wudil yana cewa "ku zabi Muse mahaifin Nihal ne."
Nihal ta ji labari sai ta bawa Hashim da Najaatu kudi masu yawa suka ci gaba. Sun daukar mata da maza dauke da fastoci aka shiga gari yin kamfen.
Zabe ya rage watan biyu Abba Muse ne a waya yana magana da Nihal da alama ma hawaye yake zubarwa. Yana cewa "Surukata ki taimake ni duk wanda zai bani shawara sai ya ce in neme ki, ke ce kadai za ki iya ki taimaka min. Na san halin mahaifinki shine ya hana ki amma ki roke shi ya na sonki ke ce kadai mace yarsa. Zan iya tunawa ya taba fadamin wata magana a lokacin kina yarinya. Ya ce duk duniya babu abinda na fi so irin Nihal gata bata da lafiya babu abinda na qi jini a rayuwarta in ganta a kwance. Ciwonki ya na tayar masa hankali. Kin yi wani ciwo da kike suma. Sai da aka yi miki aiki kika warke. Ina so ki nuna masa bacin rai ya sa ciwonki ya tashi kin suma sai a asibiti kika tsinci kanki. Dan haka ya bari ki dawo gida ki yi min kamfen."
Nihal ta sake shiga tsaka mai wuya. Ta yaya zata tayarwa da mahaifinta hankali haka?
Ta kira mahaifiyarta ta fada mata yadda suka yi da Ambassador abin mamaki sai ta ji Mummy ta yi amanna. Saboda wannan shawara ita ce kadai mafita. Idan ya ji damuwa ta tayar da ciwo zai saduda dole ya bari.
11/14/21, 7:20 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 鉂�


GABA GADI


NA JAMILA UMAR TANKO
(JUT)


General da abin qaunarsa Shatu ne ke zaune a falo su na kallon labaran qarfe tara, su na yi su na shan kayan marmari inibi da tofa. Da alama yau General yana cikin nishadi sai hira yake yana zolayarta. Shatu ce farin cikinsa ita kadai take gani yaji sanyi daga ita sai 'yayanta.
Major Abubakar ne ya shigo ya gaishe su sai ya fita ya sake shigowa ya fita,ya dawo zai sake fita alamu sun nuna yana cikin damuwa.
Prof Shatu ta tambaye shi "Abubakar lafiya kuwa? Wani abu ne ya faru?"
General ya ci gaba da kallon talabijin dinsa, ya nuna halin ko in kula daman haka take yi musu.
Abubakar ya zo ya zauna a sanyaye ya daga ido da kyar ya kalli mahaifansa ya ce " mummy ba na so in katse muku nishadinku in tayar muku da hankali ne amma ya zama dole in fada muku. Nihal ce ba lafiya tana asibiti ta shide ta sume, likita ya ce damuwar da ta shiga a cikin kwanaki nan ce ta jawo...."
Remote din da ke hannun General ce ta fadi qasa dan gigita.
Ya zabura ya dubi Abubakar ya fada cikin tsawa " Nihal din ta wa? Wacce damuwa ce kuma?"
Abubakar ya jawo wayarsa ya kira lambar waya, baturiya ta dauka wato likita mai da kula da Nihal. Ya saka ta a speaker kowa ya na iya jiyo bayananta.
Ta ce sun binciko file din Nihal sun ga tarihin ciwon nan na ta ashe tun tana qarama ta warke bai sake tashi ba sai wannan lokaci, ya kamata a daina takura mata akan wasu abubuwa damuwa da fargaba na damunta.
General ya fisgi wayar ya fara magana cikin gigita
"Ina Nihal din? Ta farfido ko tana sume? A bani ita mu yi magana."
Nihal ce ta karbi waya tana magana cikin galabaita.
Ya tambaya "meye danuwarki? Ki fada min ko meye shi zan yi miki."
Ta fara kuka sai ya tashi ya tafi can nesa da su yana lallashinta ya na tambaya. Dakyar dai ta ce ba ta da wata damuwa illa ta abubuwan da suke faruwa a kwanan nan, maganar kamfen din Ambassador. Ta shiga tsaka mai wuya tana jin kunya Siyama da Muqaddas za su ga kamar ba ta kyauta ba."
Sai ya ji sanyi a ransa da ba wata damuwa ba ce mai yawa. Ya yi tsaki ya ce "wannan ce kadai damuwarki, har kike qoqarin jefa kanki a cikin matsala? Na amince ki dawo gida ki yi masa kamfen. Amma ki bari ki sake jin sauqi nan da sati daya."
Murna ta rufe Nihal ya ce ta bawa likita waya ya na magiya akan ta tsaya ta kula da Nijal ita kadai ce 'yarsa mace a duniya. Ya na sonta matuqa. Likita ta yi masa alqawari za ta yi masa hakan. Yayi godiya suka kashe waya.
Nijal da ketrine suka yi tsalle suka rungume juna daman ba wata likita ba ce, qawarta ce suka hada baki.
General ya dawo wajen da su Abubakar suke zaune ya na fada " akan wani dan qaramin abu shirmen banza zata kashe kanta. Wai damuwarta akan bata yiwa Ambassador kamfen ba ne tana jin kunya su Siyama. ji shirme fa."
Su ka dauki salati kamar da gaske nan kuwa su dukka hudun bakinsu daya.
"Yanzu yaya zaa yi? Shatu ta tambaya.
General ya ce " na bar ta ta zo ta yi in dai dan kamfen ne."
Abubakar ya dauki bambamin fadan qarya " ai da ma baka bar ta ba ta je ta kashe kan nata. Meye hadinta da su?"
" ka ji shashasha a bar ta ta mutu dan kai ba asararka ba ce? Ciwon nan da ya kusa kashe ta tun tana yarinya shine yake so ya dawo." Inji General ya fada a fusace har da kaiwa Abubakar duka da bayan hannu.
Abubakar ya fita da fushi wai shi a dole bai so aka amince ba, nan kuwa dariya ce a kunshe a bakinsa.
Shatu ma da kyar ta daure dariya ce ta ke cinta.
Zufa kawai General ke yi tabbas ya gigice. Ya jawo wayarsa ya kira Ambassador Abba bayan sun gaisa ya yi masa albishir da cewa Nihal zata yi masa Kamfen. Sai murna ya ke yana godiya.
Babu tantama ya san abinda ya shirya mata ne ta bi, ba dan haka ba ya tabbatar in duniya zata hade General ba zai taba amincewa ba, don akwai shi da taurin kai da taurin zuciya.
Su na kashe waya ya kira 'yayansa su Muqaddas ya shaida musu, sai aka hau murna.
Wayar Muqaddas ce ta shigo wayar Nihal amma number busy dan su na ta waya da Abubakar su na ta tuntsira dariya. Sai bayan da ta gama da Abubakar ne ta kira Muqaddas ya na so ya ji kanun labarai shima.
Ta shirya tsaf nan da kwanaki biyu zata iso, kafin kwanaki biyun nan ta shirya komai ita da masu taya ta 'yan uwanta 'yan fim.
Ta cika da mamaki duk lokacin da ta dora sabon hoton Gwamna Muse sai ta ga Billal ya yi reposting yayi sharing shima kamfen yake taya ta tun qarfi. Ita kuma sai ta danna masa likes ta yi comment da Thanx. A hakan ma dadi yake ji ya samu ta Kula shi har ta san abinda yake yi.
Nihal Nuren ta iso da qarfinta da kuma kayan aikinta wato kudi. An bazama babu dare babu rana, wataran tare da Ambassador da tawagarsa wataran ita da 'yan fim kadai. Sun shiga lungu-lungu, kusurwa-kusurwa ta cikin kauyuka da burane su na ta kamfen.
Hankalin 'yan adawa ya tashi tabbas Muse ya biyo ta hannun da zai ci nasara tunda ya hada da su Nihal. Farin jinin 'yan fim shine gaba da kowa saboda hotunansu da bidiyoyin shirye-shiryensu ya kai kowanne lungu so ake kawai a gansu a zahiri kuma kome suka ce zaa yi amfani da shi. Da maqudan kudi su ka so su siye Nihal akan ta juya akalar kamfen din dinta daga kan Muse ta dawo kan dan adawarsa. Tabbas kudin ya na da dinbun yawa in har za ta karba to fa sai dai a saka ta a sahun masu kudin afrika.
Allah sarki Nihal ta kau da kai babu ma maganar cewa a bata lokaci ta yi tunani gaba gadi ta ce bata so.
Ranar zabe babu ko kokonto kowa Muse ya dangwalawa. Masha Allah Muqaddas da Siyama sun zama 'yayan Gwamna. Muse ya ci zabe. Gari gaba daya ya dinke da murna sai celebration ake yi. 'Yan fim sun fi kowa murna saboda alqawuran da yayi musu in har ya zama gwamna zai tu musu. Saboda ya sun 'yan fim sun yi masa karamci su ma. Ya yi musu alqawarin zai inganta sana'arsu da masana'antarsu. Zai gina musu Fim village wato gari guda zaa dauka a yi fasalin komai kamar na gaske, idan aka yi fim sai a dauka turai ne. Yayi alqawari zai mayar da makarantar Nihal jamiar mai lasisi. Zaa dinga fita da shaidar digiri kamar na kowacce jami'a. Zaa bawa manyan producers da Directors jari na yadda zasu samu su inganta sana'oinsu.
Nihal kuwa zai duba Muqami mai girma a gwamnati a bata daga kwamishinan mata zuwa sama.
Madalla da wannan gwamnati. Fatan Nihal kawai a taimaki talakawa musamman na qauye tana da littafi guda data rubuta jerin matsalolin da suke addabar suda idanuwanta ta gani ba labari aka bata ba.


*** **** ***
Bayan zabe kowa ya sami nutsuwa an gama baccin gajiya. Nihal ta sami labarin Aisa Buzuwa ta haukace a sanadiyyar shaye-shaye ba komai ba ne saboda Bash ya qi aurenta.
Hankalin Nihal ya tashi matuqa ta nemi adireshin da zata iya samunta. Bash Auta ya cika da mamaki da ya ga kiran Nihal da sassafe.
Ya na amsawa ta ce " ka fito qofar gida gani a bakin get din gidanku."
"Qofar gidanmu kuma?" Bash ya tambaya cike da mamaki.
Ya fito a gigice ya na adduar Allah Ya sa lafiya. Ta yi masa nuni da hannu alamar ya shigo cikin mota ya na shigowa ya zauna baki a bude yana so ya fara tambaya sai ya ga ta fisgi mota ta tafi da shi.
Gabansa ya fadi a zatonsa ko wajen sojoji zata kai shi a casa shi a dalilin ya ce yana sonta, ko kuma wasu ne suka hada su aka yi masa sharri. Magiya yake yi mata ta tsaya ta yi masa bayanin abinda yake faruwa bata ce masa komai ba har yanzu.
Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ga ta tsaya a qofar wani gida kuma ya san gidan. Yanzu ya gane maganar dai akan Aisa ce.
Ya yi tsaki ya girgiza kai ya ce " ban da ke babu wanda zai yi min haka in kyale shi. Meye hadina da Aisa yanzu? Daman can fim ne ya hada mu kuma take haukarta."
Nihal ta ce "na sani amma tana buqatar taimakonka. Bash daga yau ina so ka saka a ranka kada ka yi wasa da zuciyar duk wanda ya furta kuma ya nuna yana sonka domin kuwa ba ka san iya gejin da ya kai a qaunarka ba. Za ta iya rasa rayuwarta a dalilin sonka kai kuma ka dauki abin da wasa. Haka kada ka dauki qiyayyar wanda ya ce yana qinka da wasa dan baka san zurfin qiyayyar da yake yi maka ba wataran zai iya halaka ka. Mu je ciki wajenta kawai."
Nihal na gaba yana biye da ita a baya a zauren gidan su ka ganta a zaune ta na shan wiwi bayan ta gama da kwalaben kayan maye.
"Wa'iyazu billah. Aisa me nake gani? Ki yi haquri ki ajiye ki daina wannan ba ita ce mafitar matsalarki ba. Ga ni ga Bash mun zo wajenki ne don mu yi magana."
" Dalla can munafuka ba ke ki ka raba ni da Bash din ba. Yar rainin wayo kawai wallahi sai na kashe ki na kashe Bashir Auta sannan in kashe kai na." Cikin muryar 'yan maye Aisa ta fada.
" Subhanallah mai yayi zafi haka? Na zo a sulhunta ne, tashi mu shiga ciki mu yi magana." In ji Nihal yayin da ta kama hannun Aisa zata tashe ta a tsaye.
Hasiya carkwai ce ta danno da gudu da tabarya hannunta, ashe har gara haukar Aisa ma sau dubu. Hasiya tunbele take jikinta babu suturar kirki ta kusa yin tsirara. Tabarya ta daga ta kai bugu saura kadan ta sami Nihal a goshi, Nihal ta daka tsalle ita da Bash suka yi waje da gudu.
Manyan asaharai Hasiya carkwai ke yi a cikin bayaninta sun take cewa sun yiwa Nihal asiri ne ya dawo kansu.
Hankalin Nihal ya yi mummunan tashi daman har qiyayyar da suke yi mata ta kai haka abin har da bokaye? Ta yi mamaki ta yi Allah wadai da wannan halin na su, ba ta taba kawowa a ranta cewar har akwai ranar da kunnuwanta zasu ji irin wadannan kalamau ba amma duk da haka ta sha alwashin sai ta taimake su.
Ita da Bash ne a zaune a mota bayan sun yi nisa da gidan Hasiya sai dai su na hango ta daga nesa, ta fito tana jifansu da duwatsu tana tonawa kanta asiri.
Waje ya cika da mutane masu wayoyin hannu har sun dauka sun watsa a duniyar social media. An rubuta Aisa da Hasiya carkwai sun haukace a sandiyyar zasu yiwa Nihal asiri ya koma kansu.
Nihal ta matse hawaye ta dubi Bash ta ce " sai yaushe zamu ci gaba ne a qasar nan ? Sai yaushe za mu waye? Sai yaushe za mu san da cewa mun shiga sabon cetuary? Wannan abubuwan da suke yi fa tun a zamanin jahiliyya aka yi su.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads