Header Ads
Showing 75001 words to 78000 words out of 110552 words

Chapter 26 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

a tashe yake ya saka tsawa ya ce " wannan fa ba abin wasa ba ne masu raquman nan hayar su na dauko na yini guda,idan ma ba su yi ba su dai kudinsu zan basu. Na yanke shawara Nihal da Bash zasu maye gurbin Bilal da Halima."
Shima da ya fada sai da gabansa ya fadi balle ita Nihal din daman tuntuni ta sami lungu ta zauna.
"Eh-Eh Darakta ba mu ji sosai ba kamar Nihal na ji ka ambata." Tukur ne ya tambaya.
Abbas bashi da tabbacin Nihal za ta iya dan bashi da tabbacin da zai daki qirji ya shaide ta. Ya fada cikin rashin confidence "eh a gwada ta a gani ina ga za ta iya."
"Cab lallai akwai matsala." Mami harka ta fada.
Hayaniya ta kaure 80% ba sa goyon baya a dora Nihal, irin su Hashim ne kadai ke goyon bayanta. Murna ta kama Hashim da Najaatu har tsalle suke yi sannan arnan gaba su ka hango su su ka fara zagi.
Babu wanda ya san Nihal da Najaatu sun sulale sun zagaye baya wajen masu raquma akwai masu jin Hausa kadan-kadan, ta shaida musu zaa fara fim su yi mata shigar 'yayan sarakuna irin na qabilarsu, daman ta iya hawan raqumi a irin qasashe kamar su Dubai da Egypt idan sun je yawon shaqatawa.
Amma duk da haka ta ce su koya ma su yadda za su hau, da yadda za ta riqe. Cikin mintuna talatin komai ya kammala.
Labari ya kai social media babu tantama akwai wakilin 'yan jarida a cikinsu. Kafin ka ce kwabo duk abinda aka tattauna ya isa ga dinbun jamaa.
Idris ne ya kira Abbas a waya, Abbas ya koma gefe ya na amsa waya.
Idris ya ce " Abbas ka yi hakuri, ka nutsu domin na san ka na cikin jarabawa. An ce babu Bilal babu Halima sun yi hatsari kana can ka dimauce za ka tafka asara. An ce ka ce za ka saka Nihal a matsayin Halima. Abbas da wata asarar gara wata da ka saka Nihal ka yi asarar Fim dinka gaba daya, gara ka yi asarar wannan rana kafin ayi tunanin wacce zaa saka a madadin ta. Abokan gabarka kamfanin AZ da kamfanin Zubebe su na ta murna wai fim din da kake so ka tsorata su da shi yayi wanwar ya baje. A social media aka dora hotonka a wajen nan da kake yanzu ka yi wujiga wujiga. Ba na bada goyon baya ka saka yarinyar nan ta qauye gaskiyar magana zaa yi ma ka dariya, ni zan taho maka da Salma disco gobe sannan ga Aisa buzuwa a ciki ka zaba...."
Iyakacin maganar da Abbas ya fahimta kenan hankalinsa ya koma ga kallon Nihal Nuren Mubin tare da tawagar buzaye akan raquma su na yi mata busa , kida gami da waqoqin sarauta na al'ada. Kidan gwanin dadi haka shigarta ta qayatar a matsayin 'yar sarki ta dawo daga yaqi, gefenta kuwa babbar aminiyarta ce a fim kuma a zahiri Najaatu 'yar mutanen Darazo.
Darakta Idris ya ce " yaya na ji alamar ganga ana kida an fara shooting din ne?"
Abbas ya ce "Idris katse wayar ina zuwa."
Da gudu Abbas ya rintimo ya hadu da dandazo mutanen da kowa ya bude baki yana kallo ba tare da an gane ko su waye ba.
Abbas ya cewa masu kyamara ku hasko su daga nesa har su qaraso wannan yana cikin sinasinanmu.
"Kamar yaya su dauka? alhali ba ka san ko su waye ba." Tukur ne ya fada a fusace.
Abbas bai bashi amsa ba masu kyamara su ka fara aikinsu. Tawagar raquma ta qaraso yayin da gaba daya fadawa su ka fara yiwa gimbiya kirari cikin yaransu na Buzaye. Cikin taqama Gimbiya ta ke jinjina da takofi a hannunta, kasancewar ta sha rawani babu wanda ya gane su. Da gudu aka shinfida mata
dardumai abin mamaki sai raqumi ya tsugunna gimbya ta sauko tana tafe tana taqama, qawarta na bayanta itama an koya mata abinda za ta dinga fada cikin yaransu na buzaye.
Abin shaawa kowa ya sauko daga kan raquma. raquma guda arba'in ne Abbas ya hayo da buzaye arba'in, sai suka bi layi a saitin qofar shiga gidan sarki.Takofi ta zaro tana yi musu jinjina suna yi mata da tasu takofin har ta shige ciki.
"Sin 1 ya kamamala Alhamdulullah."
Abbas ya kalli buzaye cike da mamaki ya tambaya "ban koya mu ku abinda za ku yi ba, yaya aka yi ku ka yi tunanin yin hakan?"
Nihal Nuren ce tare da Najaatu suka fito daga cikin gidan su ka yaye rawaninsu.
Nihal ta ce " Darakta na fada maka ka kwantar da hankalinka ka cire kokonto.
Nan da nan yayi amanna ya gasgata za ta iya.
Abbas ya zabura ya washe baki ya ce " Ina Baba Shuaibu kai ne sarki marmaza ka zo Buzayen nan su yi maka shigar sarkinsu a ci gaba da dauka. Alhamdulullah komai zai tafi daidai."
Tukur da tawagarsa sulale su ka yi su ka zauna, wasu sun dafe kai wasu sun yi tagumi saboda maqaqin hassada da ya mamaye zuqatansu. Ta ina? Ta yaya Nihal za ta ja ragamar wannan babban fim din, su na zaune su na gani.
Labari ya canja a social media an dora hoton Nihal da Najaatu akan rakuma a matsayin gimbiya da aminiyarta. Rigijigafji tabbas labarin Nihal ne ke tashe(trending) a wannan satin a Twitter, bloggers su na maganar a youtube, Instagram su na ta reposting, haka ma a Facebook.
Sarki ya kame ya zauna fadawa sun yi da'ira 'yarsa Nihal ce a durqushe a gabansa ta na jinjina. Ya daga takofi sama yayi rantsuwa ya ce "na rantse da wanda raina yake hannunsa babu wanda ya isa ya ci mu da yaqi in har Rima 'yata tana raye."
Abbas ya dakatar da su ya ce "a cire sunan Rima a saka sunan Nihal kawai. Daman sunan fim din Gimbiya Rima dan haka sai ya koma gimbiya Nihal.
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun Amina 'yar kwalisa ta fada yayin da ta yi wuf ta fice waje ta na kuka. Mami ce ta biyo ta a baya anan suka iske Duduwa da Fati dangerous su ma su na tattaunawa, baqin ciki ya wanzu a zuqatansu. Haka Tukur ya dinga gani kamar al'mara kamar mafarki.
Labari ya kai social media an shaida musu cewa sunan fim ya canja daga Gimbiya Rima zuwa Gimbiya Nihal. Sai masoyan Nihal su ka hau murna. Baa santa ba sai jiya aka fara ganinta aka ji sunanta a lokacin da su Bilal su ke da niyyar wulaqanta ta ba su san tallata su ka yi ba, a kwana daya kacal Nihal Nuren ta yi suna. Hotonta akan rakumi ta yi shigar sarauta ta daga takobi shine akan status da dp dinbun mutane.
Idris ya na ta kiran Abbas amma ina Abbas bai ji ba aiki yayi aiki, fargaba da baqin ciki sun gushe.
Ya na karanto abinda zasu ce Nihal na gyarawa,a haka aka kammala Sinasianai masu yawa. Sai ga Najaatu Darazo a tashin farko ta sami daukaka. Basu ji tashin hankali ba ma sai da Nihal ta ce a saka Hashim a matsayin yayanta uwa daya uba daya mai suna Dan sarki Ishaq. Roll din Bash Auta kenan, da Aqilu zaa saka toh bai qaraso ba.
Duk abinda Nihal ta nuna masa da shi yake amfani, ya zamanto kawai sai ta zaba ma yayin da kowa ransa ya baci. Mami Harka da Amina da fati da Duduwa dukka a matsayin bororinta su ka fito, daman can ma a haka tsara musu amma yanzu da yake gimbiyar wacce basa qauna ce sai ransu ya baci.
Nihal ta dakawa Amina 'yar kwalisa tsawa ta ce " zo nan makira, ban yarda da ke ba. Ke muguwa ce mai mugun hali kina nan aka kashe baiwata fawaza."
"qarya kike 'yar talawa Gimbiya Nihal tafi qarfinki." Najaatu Darazo ce ta fada.
Amina ta daga hannu ta ce "cut."
Ma'ana a tsaya, aka tsayar da dauka. Ya miqe tsaye daga durquson da ta yi a gaban Nihal da Najaatu ta yi magana cikin fusata "gaskiya Darakta ba zan iya fitowa a matsayin baiwar wadannan banzayen ba? ka na jin zagin da suke yi min? Baya cikin abinda aka ce su fada ba."
Mami harka ta daka tsalle ta shigo fili ta fara hayani. Abbas ya dakatar da su ya ce maganar su Nihal ta yi daidai? in ba zasu yi ba su tube kayan su kama gabansu, ga dinbun masu so nan."
Tukur ya zabura ya miqe tsaye ya fara fada yana fadin gaskiya babu adalci a cikin shirin nan. Kenan an kawo su dan a wulaqanta su ne. Kowa ya shiga tunanin ta in da wulaqanci ya shigo ciki a daukar fim din nan.
Jamaa da dama musamman 'yan bayan fage su na son Nihal musamman masu kyamara ta nuna musu makamar aiki sosai, yanzu ba sa shan wahala dauka ba tare da an tsaya ana ta gyare'gyare ba.
Buzaye ma su na jin dadin aiki da Nihal tana da faraa gata da mutunta mutane, ga saurin fahimta nan da nan aka yi sinasinai masu yawa.
Sin din Bilal, Bash Auta zai hau shi ake ta jira amma hakan bai sa an tsaya ba, an ci gaba da dauka daman Hashim ya riga ya haye matsayinsa.
Lokacin sallar azabar yayi kuma an kawo musu abinci da abin sha a cikin manyan Kuloli. Matar da Abbas ya bawa kwangila ce ta kawo daga Maradi ita da ma'aikatanta daman kowa yunwa yake ji an jigata.
Hashim ya karbo musu abinci su uku, ruwa da lemo su ka koma gefe cikin wata inuwa su na ci.
Hashim ya kalli Nihal ya ce "na gaishe ki 'yar baiwa a she ke ce tsanin da zan taka in hau sama. Na gode da Allah Ya da Ya sa na sanki na hadu da ke domin ke alkhairi ce a rayuwarmu."
" Eh dole ka ce haka mana munafuki, in kere na yawo zabo na yawo zaa hadu wataran, sai dai in ba zaku koma Wudil ba." In ji Tukur.
Nihal ta giftawa Hashim ido alamar yayi shiru.
Najaatu ta fada cikin gadara dan ta basu haushi ta ce "kai daman Hashim sai yanzu ka san muhimmancin Nihal a rayuwarmu? Ai na dade da sanin Nihal alkairi ce, muna godiya 'Gimbiya Nihal."
Idanuwan Amina da Mami ta hango, saboda harara kamar zasu fado qasa.
Sai ga Bash da Aisa Buzuwa a sukwane wujiga wujiga da su.
" A bamu abinci da ruwa mai sanyi." Su ka hada baki suka fada.
Aka zubo musu suka zauna su na ci tare a faranti daya.
Munafukin da yake yada labari ne ya turawa 'yan Nigeria hotonsu. Nan da nan aka watsa. :Bash Auta da Aisa Buzuwa soyayya ta yi qarfi Allah Ya ida nufi." Abinda aka rubuta kenan.
Sai bayan da Bash ya Farfido ya fara gane mutanen da ke gifgiftawa. Ya bawa Abbas labari me dadi cewar an yiwa su Bilal dressing a jikin ciwon da suka ji har an sallame su ma, ya mayar da su hotel anan Maradi da yake babu karaya.
" Aisa ta ce " sai dai ayi hakuri a basu kamar sati biyu tabon ya kame sai a fara daukar shirin, har gara ma Billal hannuna da qafa ne ciwon amma Halima a fuska ne duk ta guggurje ko ina duk bandeji. "
Abbas ya ce " ah ba zai yiwu mu dakata da daukar shiri dan ba sa nan ba mu tuni ma har mun yi nisa. Yanzu ma break aka tafi zaa ci gaba."
" Su waye su ka maye gurbinsu?" Aisa ta tamabaya cike da kidimewa.
Abbas ya ce "ku je ku yi sallar ku zo a ci gaba, kada dare ya yi.
Da misalin qarfe biyu da Rabi aka dawo bakin aiki sai Aisa ta zabura da ta ga Nijal a matsayin Gimbiya Wajenta kuma har Najaatu ta haye. Wajen Bash kuma Hashim ya haye.
"Me yake faruwa ne?" Aisa ce ta tambaya.
Yayin da maqiya Nihal suka matso kusa da 'yar uwarsu Aisa maqiyar Nihal su ka bata labari tsaf.
Sai ta girgiza kai ta ce "ba da ni ba, wallahi ba zan yi fim da kucakai ba abin ma ya zama shirme."
Abbas ya ce "qofa a bude take duk wanda ya ga ba zai iya ba, ya qara gaba."
Aisa ta ce " au haka ma ka ce? Ai kuwa zaka san ni 'yar halal ce."
Bash ne ya daka ma ta tsawa ya ce ta rufe musu baki. Fim din na ta ne? Ina ruwanta da duk wanda me fim ya saka? Ita ba aiki aka dauke ta ba ta yi abinda ya kawo ta ta wuce kawai.
Son sa take yi bata so su sake batawa, sai ta koma gefe tana girgiza kamar wata 'yar tauri.
Bash na zaune a inuwa ya na hango yadda Nihal take acting.
" kai babu yadda zaa yi a ce yarinyar nan jahila ce, ta san abinda take yi kuma cike da ilimi."
Ya na mamakin yadda ta farke fim din nan ta canja masa salo kuma ya tafi daidai.
Sai yanzu aka zo kan sin din Nihal da Bash. Bash yayi kyau cikin kayan sarauta amma sarautar Hausawa.
Ya taho akan doki ta taho akan raqumi suka hadu a bayan gari daga ita sai shi. Kowannensu na riqe da qatuwar takofi, mai tsanani kyalkyali. Su dukka su ka sauko daga kan abin hawansu su ka hadu a tsakiya kowannensu cike da bacin rai.
" ke Nihal! Ke din wacece ne? Ki fada mana asalinki. Qarya kike kin boye asalinki."
Baya cikin abinda aka karanto masa aka ce ya fada.
Abbas ya tsayar da shirin ya ce "Haba Bash yaya haka? cewa aka yi ka ce ke 'yar sarki ce yadda kike taqama haka nake taqama nima dan sarki ne."
Nihal ta ce " Darakta ka bar shi a haka yayi, bari ka ji amsar da zan bashi."
Ta dubi bash cikin fushi ta ce "a lokacin da mutum ya shiga cikin abokan gaba ya kamata ya boye kansa. Wanda ya san abinda yake baya nuna asalinsa fa martabarsu domin a lokacin zai gane maqiyansa na asali da masoyansa na asali. Ni Nihal 'yar sarki ce kuma 'yar asali, attajira 'yar gidan altajirai gaba da baya, ni 'yar dangi ce wacce saboda gatana ko quda baa so ya taba ni. Kada ka ga mutum a hanya cikin tsumma ka yi zaton almajira ce qasqantacciya wataqila basaja ta yi."
Sai kowa ya fara tsarguwa tabbas a maganarta a kwai alamar tambaya.
Bash ya sake fusata fusatar gaske ya dora takofi a saitin wuyanta ya ce "tunda ki ka fito a wannan sigar tabbas ki na da wata miguwar manufa ba abinda ki ke yi ne ya kawo ki ba. Ki fada min me ya kawo ki cikinmu?"
"Na shigo duniyarku ne don in san menene rayuwa? In san haqiqanin halin dan adam. Mutum mugu ne kuma butulu ne. Talaka bashi da wani tasiri, dan uwansa talaka shi yake fara kyamarsa, ya tsane shi, ya yi masa sharri. Hakan ya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads