Showing 9001 words to 12000 words out of 110552 words
Chapter 4 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
Hausa ne . Babu wani karatu da bashi da amfani kuma ya kamata ta amfani al'umma abinda ta karanta."
Ambassador Abba ya yi magana cikin daga murya da gigita " General ! Ka kuwa san abinda kake cewa ? Ka yarda ka tura zuriaarka zuwa wajen watsewa? 'Yan Hausa fim me suke koyarwa banda raye-raye da lalata dabi'un yara ."
General ya Girgiza kai ya ce " daidai kenan ita da ta yi digiri ta yi masters akan abin zata kawo musu gyara mai yawa su na bukatarta sosai."
Ambassador ya zabura ya miqe tsaye a fusace ya ce " ka manta an saka ranar aurenta da Muqaddas? Ta yaya zan bari d'ana ya auri 'yar Hausa fim ?"
General ya ce " ai daman bai kamata ta auri bare ba, sai ta auri dan uwanta dan Hausa fim."
Nihal ta kwala ihu ta durkusa a gaban mahaifinta ta na neman gafara akan ya bar ta kada ya kai ta Hausa fim bata so.
Muqaddas ma a gigice ya zo ya durkusa har da Siyama su na rokonsa.
Justic. Hassana sai yanzu ta yi magana ta kalli Mahaifiyar Nihal ta ce " Professor kina ganin wannan danyen aikin Zaa aikatawa yarki kin yi shiru."
Professor ta matse hawaye ta ce "da ma ku daina bata bakinku ku na rokarsa don kamar zuga shi ku ke yi. Na yi imanin duk duniya babu wanda ya isa ya hana shi aikata wannan danyen aiki . Ku yiwa Nihal addua kamar yadda nake yi mata Allah Ya sa hakan ne ya fi alkhairi a rayuwarta. "
Nihal ta zo ta kankame mahaifiyarta ta na kuka " Mummy yanzu sai ki bari a kai ni in yi Hauaa fim. Shikenan rayuwata ta salwanta."
Mummy ta turo ta itama hawaye take yi " ta ce lokacin da zaki canja course ba ki nnemi shawarata ba ai ."
Abubakar ya fada " me nake gani ne kamar almara ? Daddy zaka rugaza martabar ka da ta iyalinka gaba daya."
Hamza ya ce " daddy yin haka kuskure ne ka dai kara yin tunani ."
Muhammad ya ce " Daddy pls ka yi hakuri ka rufa mana asiri . In har dole ne sai ta yi fim ka Mayar da ita can London ta yi anan ne zasu iya biyanta kudi mai yawa kuma duniya ta kalle ta . Amma me zata samu a Hausa fim. Iyakacinta a santa a kasar Hausa kawai."
Hamza ya ce " idan ma Hausa fim kake so ta yi ka bata kudi me yawa ta shigo da kyamarori masu kyau ta zama excecutive producer kuma director ba wai ka kaskantar da ita haka ba. Me zata samu ? "
Umar zai yi magana " tsawa General ya sakar musu ya zabura ya miqe tsaye a fusace " zan fasawa duk wanda ya kara yi min magana baki . Na gama magana yau Nihal ba zata kwana a gidana ba . A industry zata kwana .
"Ambassador ya tashi a fusace ya ja hannun 'yarsa Siyama ya ja hannun Muqaddas ya juya ya dubi General ya ce " 'D'ana ba zai auri 'yar Hausa fim ba haka 'yata ba zata auri yayan 'yar Hausa fim ba ." Ya fice yayin da Justis. Hassana ta bi bayansa a fusace itama .
Ko kallonsu bai yi ba haka bai damu ba dan an fasa auren 'yayansa, shi dai fatansa ya cika burin da ya kudina.
Abubakar ya dafe kai ya ce " shikenan ai an raba ni da Siyama . Daddy ka gani ko ? An dinga yi mana gori kenan."
General ya miqe tsaye ya damko hannun Nihal ya fice .
"Daddy Daddy ka yi hakuri dan Allah." Haka suka Dunguma suka bi su a baya. Nihal na rusa kuka sai da ta bawa kowa tausayi had da masu zubar da hawaye a cikinsu. Ko kallonsu bai yi ba . Ashe duk wannan abinda ake yi me adaidaita sahu ya sa aka nemo masa, yana wajen get yana jiransu, ya tura ta ciki shima ya Shiga suka tafi.
Haka suka bi adaidaita sahu da kallo ba tare da sun san yadda zasu hana shi ba .
Mu'awiyya ya ce "ai shikenan mun zama dangin 'yan Hausa fim, duk wata fosta idan aka Kafe ta irin fuskarmu Zaa gani dan mu dukka kanwarmu daya. "
" kai ba zai yiwu ba wallahi." Muhammad ya fada yayin da ya juya cikin gida da sauri .
Abubakar ya ce "kawai gara mutum ya koma kudu da zama wallahi Zaa dade baa ganni ba ."
Dr Hamza ya ce "Daman zan tafi karatun Phd dina Daddy ya hana ni tafiya wai sai na koyarwa jamia an amfana da ni gaskiya gara in tafi . "
Kowa ya koma cikin gida yana tunanin yadda zai bar kasar Hausa, gara su bar garin da a aikata wannan danyen aikin abin kunya ne a wajensu .
Mummy bata falo har ta koma cikin daki ta kulle tana kuka . Yau ne ranar data sake yin nadamar auren Nuren, har an daura mata aure da dan uwanta ta ki yarda sai da aka warware.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI
Ep 5
General da Nihal su na tafe a adaidaita sahu yayin da kowannesu yana tunanin abinda ya ishe shi . Ya juya ya kalle ta itama ta kalle shi cike da damuwa .
Ya ce " kar ki zaci zan kai ki wani katafaren kamfani ne don ki je ki fara yin Fim , A a ina so ki faro daga farko kwarewarki ta sa ki sami Karin girma ki shigo birni. Shine abinda ake nufi da 'kan ta waye' , dan haka kiyi biyayya kada ki sake ki nuna musu kin fi su iyawa ko ma kin san wani abu da ya shafi fim idan kina so ki yi nasara."
Ta gyada kai yayin da zuviyarta ta harba don fargaba .
General ya nemi da dan adaidaita sahu ya kai shi shagon nan da zasu karbi sako .A bakin wani shago suka tsaya shi kadai ya Shiga ba jimawa ya fito a lokacin da Nihal ta runtse ido ta yi kuka harte ishe ta . Sai bayan sa ta ji ya zauna a kusa da ita ne ta yi sauri ta bude fuskarta. Kanta a sunkuye bata so ya ga jajayen idanuwanta.
A cikin tashar Kano line suka sauka yayin da General ya biya mai adaidaita sahu kudi na ban mamaki. Yayi ta godiya ya tafi su kuma suka tunkari wajen motoci masu yin lodi.
Sai suka tambayi motar Wudil aka ce masa ko ya hau me zuwa Dutse ko ya hau me zuwa Wudil kai tsaye amma tana da tsaye-tsaye akan hanya .
Ya yanke shawara gara su hau marar tsayawa a hanya har Wudil. Aka nuna musu motar Dutse wata sharon. Ya zauna a kujerun tsakiya, Nihal da bugun kayanta a hamata ta zauna a kusa da shi .
" Alhajji sai kun harhada jikinku mutane hudu zaa saka anan fa." In ji kwandasta.
Ta zaci zai saye kujerun dukka don su baje sosai sai ta ga ya matsa jikin wundo, wata mata ce me goyo ta shigo daga ita har jaririn karni da zarni suke yi.
Nihal ta dube shi sai ya dauke kai yana kallon taga, warin kayan jikinta ma kawai ya isheta balle an kara mata da wadansu kala-kala .
Yunkurin amai ne ya yunkuro mata General ya dube ta ya ce "ki bude buhun kayan kiyi a ciki daman kayan masu datti ne sai ku je rafi ki wanke a kauye."
Ta ji kanta yana juyawa kamar ba a duniya take ba kuma kamar ba da Mahaifinta take tare ba . Ko dai ta yi gamo ne, aljanu ne suka sace ta suka yi shigar mahaifinta suka kawo ta duniyarsu? Domin ko a mafarki bata taba zaton zata hadu da rana irin wannan ba .
" Ni ce kuwa ? Wannan Daddy na ne kuwa ? A ina muke ? Ina zamu je? Wudil dai na san hanyar garinsu ne Gaya. Can zai Mayar da ni da zama ?"
Kwandasta ne ya katse tunanin da ta tsunduma tana yi ya ce " ke 'yar Baba matsa sosai, ga mutum daya fa zai shigo. "
Nihal ta cika da mamakin yadda zaa yi wannan zaman mutane 4 manya a kujerun nan . Wani mahauci ne me tsire har da qaton daronsa a kan cinyarsa. Su ka matsu, suka takure kamar kayan cikinta zai zubo.
Ta fashe da kuka ta ce "Daddy ka biya kudin seat din dukka, bana numfashi ."
Ya harareta ya ce " ina na ga kudin biyan naira dari 700 har sau 4? "
Matar da take kusa da Nihal ce ta kyalkyale da dariya ta ce " yaro man kaza, ta zaci sassako kudin kake yi Alhaji. Bata san yadda ake wahala ba ne a qasar nan. Su na kwance ake nemo musu komai, amma mu sai mun yi surfa sannan muke samu mu ci ."
General ya ce " fada mata dai Hajiya gara ta san rayuwa , don bata san halin da talaka ya ke ciki ba ne."
Bai rufe bakinsa ba jaririn ya daddage ya kutso koren kashi, ashe ko dan diras bata saka masa ba, sai ga kashi har kumfa yake bayan mugun kara kai kace babur ake tashi.
Ba Nihal ba har General ya kusa ambulo amai.
Matar nan kuwa ko a jikinta sai ta dauki murna da hamdala.
"Alhamdulillah ya samu yin kashi ai maganin shawara da sabara na bashi ita take damunsa. "
Ta daga shi sama sai ga kashi mai yauqi yana disa, ta saka zanin ta share masa sannan ta miqawa Nihal.
Ta ce " baiwar Allah riqe min shi in kalmasa inda babu kashin in kwantar dashi ."
Nihal ta zabura ta ce " bana iya daukar jariri ai."
General ya harare ta ya ce "karbar mata shi ki rungume. Da kin zama likitar haka zaki cewa patients dinki?"
Nihal ta fada a zuciyarta " na Shiga uku yau .Allah Ka yafe min, na san laifin da na yi ne yake bibiyata. "
Nihal ta yi sauri ta karba sai ya kwaro mata tunbudi har kirjinta.
Matar nan ta sake yin hamdala gami da cewa " cikinsa ya saki kenan tunda har yayi tunbudi, ai in fada miki kwana uku babu kashi aka kwatanta min wajen masu maganin gargajiya kin ga ikon Allah ko gida bamu je ba ya warware."
General ya tura kansa ta windo yana shaqar iska domin hancinsa ya gauraye da karni kamar zai yi amai daurewa kawai yake yi.
Matar nan zabura zata saka zanin nan mai kashi ta goge jikin Nihal.
Nihal ta zabura ta ce " ki bar shi zan goge da kaina. Karbi baby ki ."
General ya juyo ya dubi Nihal ya ce " karbi jaririn za ki ce.Ina ta san kalmar wani Baby ? Ke malama dole ne fa ki koyi yaransu, kada ki je kina yi musu ingausa Hausa da Turanci. "
Ta sirnano da hawayen takaici ta bude buhun kayanta ta zaro wani zani, ta goge tunbudin sai wari biyu ya hadu. Yawu ya cika bakinta ta bude zanin ta zuba ta sake kunshewa ta mayar cikin buhu.
General ya gyada kai ya ce " yauwa haka ake yi, kinga ko baki wanke ba in kika shanya sai ki saka kayanki ba wani abu ba ne. Baki ga matar nan yadda ta yi ba , da ta lunkube kashin sai kawai ta dora yaron a kai."
Tun daga nan Nihal ta tabbatar zata shiga aljanna saboda azabar da ta tunkaro ta babu tantama kankarar zunubi ne. Ta tunano rayuwarta ta dazu da safe ma a cikin dakinta a kan gadonta ko ina kamshi, baa ma kai da nisa ba maana bata ma hango rayuwarta a London ba a wuraren shakatawa masu daraja ba .
"Astagfirullahi waatubu ilaihi". take fada tana nanatawa.
Mota ta cika tab da bil adama da kaya kamar zata fashe . Sai dai kash! babu batir me kyau dan haka sai da qartai su ka daddage su ka tura su .
Bayan batir ma motar tana bukatar abubuwa da yawa dan wani kara take da hayaqi, sai daga baya Nihal ta gane cewa motar ma ba da mukulli ake kunna ta ba waya da waya ake hadawa sannan ta tashi . Bata taba sanin ana yin haka ba sai yau .
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun kawai take kira a zuci domin tunda aka haifeta bata taba hawa motar haya ba sai yau , motar ma ta hanyar qauye.
General ma addua kawai yake yi ba zai nuna ba ne amma fa hankalinsa ya tashi yadda ya ga over load da aka yiwa motar ga rashin lafiyar inji da tayoyi.
Suka yi addua aka shafa aka kama hanyar Wudil. General ne ya dauko wata kwarababbiyar waya wacce ko masu gadi da masu wanke-wanken gidan bata taba ganin mai irinta ba . Ya kira wata lamba.
" salamu alaikum Malam Tukur! Malam Nuren ne da Habu ya hada mu, wanda ya ce maka zan kawo yarinya. Yauwa ka shaida ni ko to ga mu nan mun taso daga kano . A Wudil a ina zamu sauka ? Toh daga mun tsallako gada wajen ruwan nan ko ? Alhamdulullah ashe ma yanzu ku na cikin aiki kenan, haka ake so. Sai mun zo ."
Nihal ta zazzare ido tana kallonsa tana kuma kallon wayar. Ya harare ta ya mayar da wayarsa aljihu. Mamaki bayyananne zaka gani a fuskarta.
Tafiya yankin azaba kowa a matse ga wannan me goyo da jaririnta sun hana Nihal sukuni sai mutsu-mutsu suke suna buge ta, ga kayan kazanta kala-kala su na fitarwa bayan kashin yaron matar ma tari da kaki take tana tofowa duk akan wannan zanin, ta ci goro kakin jajawur.
Allah ne kadai ya san me take ji yau a cikin zuciyarta domin abin baya fasaltuwa.
Daf da garin Wudil Mota ta fara gardama a dole direba ya gangara gefe ya tsaya aka ce kowa ya fito sai an daga inji an gani .
Suka firfito gaba dayansu sai yanzu Nihal ta lura kayan da yake jikin mahaifinta ba na sa ba ne , kodaddu ne har hamata ta yage. Da yake yana da tsawo da kiba sun yi masa kadan har ma sun dage masa. Takalmin qafarsa ya sude har ya huje, wata tsohuwar hula ya ciro daga aljihunsa ya saka a kansa . Ashe shagon da suka tsaya dazu kayan ya Shiga ya canja.
Da General ya ga kallon da take yi yayi yawa sai ya ce " meye kike kallona ne ? Talaka ai shi yake haifar talaka ko ? Ta ina Zaa ga Babanki fes ke kuma da tsumma? Ba zamu iya jira har sai sun gama gyaran nan ba zo mu hau babur ya karasa da mu kada su tashi ."
" Babur ? Nihal ta maimaita.
Bai tsaya bata amsa ba ya kara gaba. Bata ankara ba ta ganshi ya haye bayan wani babur, ya nuna mata na kusa da shi ya ce ta hau . Dakyar da sudin Goshi ta hau, ya umarce ta da ta rike sosai dan a babban titi suke .
" kwandasta da direba fadi suka "Alhaji yaya zaku tafi? Yanzu fa zaa gyara ."
Ko kallo basu ishe shi ba suka kara gaba . Ana tafe tana salati har suka isa inda aka ce su je. Ba tare da ya yi tambaya ba ya hango dandazon mutane masu shirin Fim da 'yan kallo ana ta daukar shiri. Tana sauka daga kan babur sai ta koma gefe ta tsugunna ta kwaro amai, sai da ta amayar da duk abinda ta ci.
Nihal ta cika da mamaki da taga yarda mahaifinta yake acting irin na 'yan kauyen da basu taba zuwa makaranta ba .
Shi da masu babur ma sun dade ana magiya akan su yi masa ragi tamanin tamanin zai biya, su kuma sun ce sai naira dari, karshe dai director Tukur ne ya zo ya cika hamsin din . General ya dage shi a dole kudin hannunasa kenan.
Wannan al'amari ya fi karfin kuka dan haka Nihal kallo kawai take yi tana jinjina iko da irada na Ubangiji mai jujjuya lamuranSa a duk lokacin da Ya so .
Suka qarasa wajen da ake daukar shirin a baki ruwa . Dandazo almajirai ne da 'yan gari yara da manya kowa da kalar warin jikinsa. Ta kalli masu hada shirin da masu acting din sai ta tabbatar ta shigo wata duniyar da ta daban ba duniyar da ta saba gani ba . Ta tuno yadda ake daukar shiri a qasar England ta jera ta dora akan sikeli ta tabbas bai kamata a kira su da suna daya ba . Babu ma hadi bata san ma sunan da zata kira wannan abin ba dan bai yi mata kama da Fim ba .
Mahaifinta ne ya katse tunaninta a lokacin da ta juyo yana zubar mata da daraja a gaban mutane .
Ya ce " wannan diyata ce mace guda daya tal da nake da ita. Daga kauyen Dan ciyau muke can kusa da Bosuwa ta karamar hukumar Gumel."
Tukur ya gyada kai ya ce " na san Gumel amma Baba kun yi zagaye, dama baku biyo ta kano ba, da ta Gujungu ku ka biyo ta Gagarawa. "
General ya ce " ai babu kudin motar ne sai da zo kano dan uwana ya ranta min ."
Tukur ya yi dariya ya ce " Allah sarki ai haka rayuwar take, daga ta karbu a wajen masu kallo watarana Mota zata siya maka Baba."
General ya face majina ya saka gefen hannunsa ya goge sannan ya goge a jikin rigarsa, babu mahalukin da zai gan shi ya ce ya taba shiga aji, ko yana da naira dubu daya tasa ta kansa ba .
Nihal tana kallonsu ta