Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 110552 words

Chapter 5 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

kasa kwatanta tashin hankalin da take ciki ba , kunya ta kama ta ji take dama kasa ta bude ta afka. Sai gani-gani super star suke yi mata, matansu da mazansu. Su na yi su na toshe baki su na dariya su na nuna ta. Dariyar da suke yi kuwa ita ce yadda wannan burtuntunar Zata zo ta ce zata shiga Fim.


General ya dage wai ya fi so a saka ta a fim ta fara a gabansa. Su ka taru su na yi masa bayani ai baa shirya yi da ita ba kowa sai an bashi script ya karanta kafin a zo nan .


Abin mamaki sai Nihal ta ga ya kece da kukan karya wai a dole sai an saka 'yarsa a fim .


General ya ci gaba da cewa "tun tana karama take son ta Shiga fim , shine na ce sai na cika mata burinta kuwa. A taimake ni yaro, in wani abu ake biya a ranta min zan je in nemo bashi in biya."


" Ah babu wani kudi idan ta iya acting zaa ci gaba da daukarta. Kallonta suke yi sama da kasa kayan jikinta ma kadai ya isa abin tsantsani. Ta ina zasu saka ta a cikin wannan fim din ma banda abin tsoho .


" Cabdijam! Mutumin kauye ma sai dai a bar shi , kawai ka nuna masa zaka saka ta don ya tafi ya bar mu mu yi aikinmu." Haruna camara man ne ya radawa director Tukur.


" Shikenan Baba za mu duba mu gani . Amma kai da kuke nesa a ina zata zauna ? " Tukur ne yake magana .


General ya ce "akwai gidan kanwata amma a Gaya ne, idan akwai in da kuke sauke baki ku ajiye ta . Gata nan amana na dakata a hannun Allah a hannunka."


Nihal ta tsugunna da buhunta a hamata domin jiri take ji bayan tashin zuciyar warin kayan jikinta ya ishe ta .


General ya yi sallama da su Tukur akan ya bar ta anan zaa samo mata masauki, amma ya tabbatar masa zata jima bata sami shiga ba kasanceaar bata da wayewa kuma bata shafa mai ta yi fari ba irin na bleaching an fi daukar farare.


General ya kira Nihal gefe kamar su na ban kwana.
Ya ce mata " wannan shine ake kira da kan ta waye. Ki na yi a hankali daga kauye har Allah Ya sa ki shiga birni. Kada ki nuna kin taba sanin wani abu wai shi wayewa ko arziki .ki yi biyayya Allah Ya bada saa .kina da kudi a jikinki kuwa ? "


Ta Girgiza kai ta ce " bani da Naira sai dallar kuma ka ce kada in dauko komai nawa. "


Ya ce " gaskiya ne , ga dubu biyar ki dinga dan cin abincin da kika ga ana ci amma dai ki boye dan na nuna musu bamu da ko sisi. Kin tuna Lokacin da na kai ki karatu London sai da na kai ki wajen gyenea doctor ta auna ki aka tabbatar ke cikakkiyar budurwa ce ko ? Haka bayan kin dawo daga karatu shekaranjiya na kaiki asibiti an duba ki ko an ce babu matsala ko ? Alhamdulullah ba ki watsa rayuwarka ba haka yanzu duk ranar da kika cika aikinki na fim zan ce ki dawo gida, sai na kara kaiki asibiti an auna ki . Ki kiyaye kada ki watsa rayuwarki anan . In kika yi haka kin san abinda zan iya yi da wanda ba zan iya yi ba . Amma fa na yarda da tarbiyyar da na baki, ina so ki ci gaba da neman tsari daga sharrin shaidan da mutane, mu ma muna yi miki addua Allah Ya tsare ki Ya sa ki fara a saa ki fama a saa."


Ta amsa da " Amin na gode ." Sai ta zubo da hawaye zazzafa .


Ya ji kamar shima ya fashe da kuka sai ya daure. Ya kara yiwa 'yan waje sallama ya juya ya tafi . Tausayi ya hana shi ya waiwayo ya sake kallonta.


Tana kallonsa ya haye acaba ya kara gaba . Sai ta sulale ta zauna tana kuka kamar ranta zai fita .


Shewa ta ji 'yan matan nan sun yi gami da tafa hannu . Su ka kalle ta suka tabe baki suka ce " su fim manya , ko wanne tsami ma sai ya zo ya ce wai fim ya zo zai shiga. Ahayye yirit."


Director Tukur ya daka musu tsawa " ke Amina kwalisa! bana son haka fa, wannanai cin fuska ne . Yaya kuke yi mata dariya ne."


Amma fa shi ma dariyar yake yi yana zumde baya so dai Nihal ta gane .
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI


Ep 6


General Nuren bai iso gida ba sai da misalin karfe tara da rabi na dare. Masu gadi basu shaida shi ba da farko sai da yayi magana suka shaida muryar. Mamaki ya kama su da suka ga ya shigo da kafa da kodaddun kaya yana tafe yana dingishi kamar wani masaki. Bai amsa gaisuwarsu ba ya wuce cikin gida . Ya ci saa ya sami jerin abinci a kan teburin binci (dining table) . Idanuwansa sun rufe bai hango matarsa a zaune a daya falon ba, har sai bayan da ya cika cikinsa.


Ya zo ya wuce ta babu wanda ya yiwa wani magana a cikinsu dan kowa haushin kowa yake ji. Ta bi yagulallun kayan da yake jikinsa da dingishin da yake yi da kallo cike da takaici tabbas kallo daya zaka yi masa ka tabbatar ya sha wuya .


"Daman ai haka rayuwa take in ka ce sai wani ya sha wahala hakika kanka zai dawo, abinda ka shuka shi za ka girba." Shatu ta fada a zuciyarta.


Ta na da magana da shi ne shiyasa ma ta zauna zaman jiransa, maganar tana da amfani kuma a daren nan take so ta yi dan ba zata iya kwana da ita ba .


Ya na bude dakinsa ya shiga kafin ya rufe ya ga tayi zuruf ta fada. Ya kalle ta cike da mamaki, ko bata fada masa ba ya san ta tara shi ta zo don ta fesar. Ya tura kofa ya rufe ba tare da ya kalle ta ba . Bandaki ya wuce kai tsaye yayi wanka, ya dauro alwalla ya fito daure da tawul. Wani qaton ciwo ta hango a qafarsa har an daure da bandeji, gaban ya fadi hankalinta ya tashi amma bata nuna ba ta yi kamar bata gani ba.


Jallabiyya ya saka sannan ya dinga jero sallolin da ya rasa. Ya dade yana adduabayan idar da sallah amma rabin addu'ar Nihal yake yiwa domin ya tabbatar ya yanke hukunci ne me cike da garaje.


"Shin a matsayinta na mace wacce ta saba da jin dadi da kashe dallar da euro in bata da kudi wacce irin rayuwa zata fada ? A matsayinta na wacce bata saba da aikin wahala ba wanne ciwo ne zai same ta idan ta yi aikin wahala ? A matsayinta na wacce bata saba kwanciyar tabarma da cizon sauro ba wacce irin cutar rashin bacci da malaria ce zata same ta? Allah na baka amanar Nihal Ka kare ta ka bata juriya Ka bata mafita ." Sannan ya shafa.


Ya juya ya dubi matarsa wacce ke zaune har yanzu akan kujera, ta dora qafa daya akan daya tana girgiza kamar 'yar tauri, babu annuri a fuskarta har ma bata son kallon fuskarsa.


Ya yi gyaran murya ya ce "ina sauraronki. "


Ta fada cikin gadara gaba gadi ta ce " ina so ka sake ni."


Gabansa ya yanke ya fadi domin bai taba jin irin wannan kalmar ta fito daga bakinta ba, a tsawon shekaru arabian din da su ka yi tare.


Sai ya daure kamar bai damu ba ya fada a shelake " daman na daure ki ne ? "


Daman ta san zaa rina wai an zaci zanin mahaukaciya, tabbas yau zata hadu da bakaken maganganun da ya saba mayar da martani da su.


Ta ce " auren ne na daina domin na gaji da zama da mutumin da baya jin bari kuma kowa bashi da 'yanci, sai abinda ya ga dama yake yi kuma dole kowa ya bi."


Ya mike tsaye ya nade abin sallarsa ya ajiye a gefe, ya tafi jikin kofa ya sake murda mukulli ya tabbatar kofar ta kullu sai ya zare mukullin, ya kashe fitila ya hau gado ya kwanta.


Ta fusata ta kunna fitila ta ce " magana nake fa ka kwanta ka rabu da ni , na ga ka kulle daki ka dauke mukulli. Me hakan yake nufi ? "


Ya yi murmushin bada haushi ya ce " hakan yana nufin na kulle zuciyata babu wata sai ke haka ke ma kin kulle zuciyarki babu wani sai ni. Bari ma in fada miki kalmar da za ki fi ganewa babu yaji, babu saki a cikin auren soja haka muna anan a tare har mutuwa. Albishirinki! ko kin mutu ba za ki bar cikin gidan nan ba haka ko na mutu ba zan bar gidan nan ba . Haka a kiyama daman tare zaa hadamu domin baki taba sanin wani d'a namiji ba sai ni haka nima ke kadai na sani. Ke ce uwar gidana sai kishiyoyinki guda dubu saba'in. " Ya ja mayafi ya rufe fuskarsa.


Bakinta a bude ta kasa furta kalma daya dan takaici. Ta fara tunanin ko da zautacce take magana . Yaya zaa yi ya ce ko sun mutu ba zasu bar gidan nan ba? Gawar zaa ajiye ta dinga wari, ba zaa a binne ba?"


Ya tabbatar ta shiga rudani don haka sai ya taimaka mata, ya ye mayafin ya dube ta ya ce " na bar wasiyya idan na mutu a binne ni a cikin gidan nan haka ke ma zaa binne ki a kusa da ni .kin ga muna cikin gidan nan dai. Ki kashe min fitila ki zo bayana ki kwanta na gama wannan maganar ba na so a sake tayar da ita kuma ."


" Hmmm! Lallai ! A shekaruna da ilimina sai an zabar min abinda da zan yi kenan."


Bai amsa mata ba takaici ya sa ta kwana akan doguwar kujera, sai da asuba suka farka . Ya boye mukullin nufinsa shi da ita yau babu shiga babu fita sai dai su mutu tare a daki.


Nihal Nuren Mubin


Ta yi mawuyacin bacci marar dadi wanda bata taba yin irinsa ba tunda Allah ya halicce ta. A falon darakta Tukur aka kai ta, kan wata kwarababbiyar kujera marar tsoka sai qashin katako. Hakarkarinta ne ya sankare don haka sai ta sauka qasa kan ledar da babu shara ta kwanta, ta yi fulo da buhunta. Sauro da zafi suka addabe ta a sanadiyar rashin wuta, babu fanka balle Ac ga duhu. Ta tashi zaune cikin dare tana ta susa tana rusa kuka. Kukan da bata yi dazu ba sai yanzu ta yi shi. Ta fara kokonton anya iyayenta su ne iyayenta na gaske kuwa? Dan idan su suka haife ta ba zasu bari ta zo nan ta zauna ba. Laifin da ta aikata a ganinta bai yi girman da mahaifinta zai yanke mata wannan hukuncin ba.Ta na tunanin yadda rayuwarta zata kasance tare da 'yan matan fim din nan wadanda suka raina ta su na yi mata dariya da shewa su na tafawa, zumde da yafice baa tsaya anan kadai ba Amina 'yar kwalisa ma cewa ta yi ta dauko mata jakarta ta biyo ta a baya. Kenan 'yar aike za ta zama, sai ta yi bauta kafin a saka ta a fim? Amma da ta tuna disgi da qasqancin da mahaifinta ya jawo mata a bainal nasi bai kamata ta ga laifinsu don sun wulakanta ta ba .


Bayan duk wannan bala'i warin jikinta da tsantsanin makwancin, qishirwa da yunwa ne suka addabe ta . Kaikayin jikinta ya qara faskari , ashe borin jini ne ya hadu da raunin cizon sauro jikinta yayi burdun-burdun da ta tashi da safe ta gani. Fuska ta kumbura ido yayi luhu- luhu.


Muryar darakta Tukur ta jiyo a tsakar gida shi da matarsa mai suna Sadiya su na rigima, da ta kasa kunne tana saurare sai ta fahimci a kanta su ke yin fadan sai ta ji hankalinta yayi mummunan tashi. Kwana dayan da ya kawo ta tayi ne Sadiya bata amince ba, ta yi rantsuwa baquwar nan ba zata sake kwana a gidanta ba kuma daga kanta ba zata sake yarda ya kara kawo mata wata 'yar iska gida ba.


Shi kuma yana ta bayani yana bata labarin yadda mahaifin Nihal ya takura shi ya biyo ta wajen amininsa ya roke shi aka kawo ta ba tare da ya san yadda zai yi da ita ba.Ya tabbatar mata yau zata bar gidan zai kaita gidan haya dakin da su Usaina Danga da Mami Harka su ke, ta zauna tare da su.


Nihal ta yi wuf! ta fito sai ta durqusa har qasa ta gaishe su. Tukur ya amsa, amma matarsa bata amsa mata ba , ta dauke kai sai harara sama da kasa take yiwa mata.


Tukur yayi gyaran murya ya ce " yaya ma kika ce sunanki?"


Ta amsa cikin ladabi "Nihal Nuren Mubin. "


Sadiya ta tabe baki ta ce " lallai su Nihal manya. Daman dan zaa shiga fim har sai an sato sunan 'yan gayu an maqala?"


Tukur ya ci gaba da cewa " anjima zan aiko yaro ya zo ya raka ki gidan da muke sauke baqi mata 'yan Fim, a can za ki ci gaba da zama har mu ga yadda zai yi ."


Nihal ta gyada kai ta yi godiya.


Ya juya ya kalli dansa Isa ya ce ya dauki kofi ya je wajen me kosai ya siyowa bakuwa kosan naira dari, kokon ashirin a saka sukari na naira biyar.


Nihal ta kalli yawun baccin da yayi qawanya a kumatun isa, dattin jikinsa da Ruwan tsohuwar butar da aka dauraye kofin, sai ta zabura ta dakatar da su ta ce ba zata sha ba ta qoshi.


Tukur yayi shiru kamar mai tunani, domin ya ga tuwo da miyar kuka na dare da aka bata ma bata ci ba. Wannan dai ba zaa ce bata saba cin irin wannan abinci ba saboda qauyen da ta fito ma ya fi nan ragargajewa. Shin bata cin abinci ne kamar wata waliyyiya?


Sadiya ce ta katse tunanin da ya tsunduma yana yi. Tsintsiya ta dauko ta wurgawa Nihal.


Ta ce "a share falon da aka kwanta ki hada da tsakar gida. Ga wanke-wanke can ki yi min kafin a tafi in da aka ce zaa tafi. Yawon ta zubar, yawan rawa a titi aka fito. "


Tukur ya dakawa Sadiya tsawa " ke ! Mahaukaciya wacce bata san darajar dan adam ba . Da kudin fim din dai aka auro ki da shi kike ci kike sha."


Ya juya a fusace ya fice, yayin da Sadiya take tsalle tana direwa tana zazzaga masifa ta bi bayansa har zaure.


Zafafan hawaye ne ya sirnano daga idanuwan Nihal.Ba aikin da aka saka ta ne ya bata mata rai ba, baqaqen maganganun da wannan kucakar take fada mata ne. Dukka masu aikinta kakaf sun fi wannan wayewa da arziki. Sai ta tuna wanda ya jawo mata wannan qasqascin, shine Mahaifinta, dan haka bai kamata ta ga laifin kowa ba .


Cikin sanyin jiki Nihal ta dauki tsintsiya ta shiga falo ta fara shara, gashi bata saba ba a haka dai tana haki ta share ko ina. A bakin bandaki ake tsugunnawa a yi wanke-wanke, warin bandaki ne kawai yake busowa yana dukan hancinta. A guje ta fita qofar gida ta kwararo amai. Ta goge bakinta ta dawo ta ci gaba, ba tare da ta bari kowa ya gane ba.


Ta na gamawa ta ji sallama a qofar gida ana cewa "wai Nohel ta zo a kai ta gidan da zata zauna in ji darakta Tukur." Muryar wani saurayi ce .


Da farko bata gane da ita ake ba yadda yake kiran sunan kamar zai ce Hell fire .


Sannan ya sake maimaitawa "baquwar nan da ta kwana a nan an ce ta taho da kayanta a kaita inda zata zauna. "


Ta fada cikin sanyin murya "ganin nan zuwa."


Ta shiga falo ta dauko buhun kayanta, kafin ta fito Sadiya ce a tsaye a bakin kofa tana kallonta a yamutse .


Sadiya ta tabe baki ta ce " dauki buhun kayanki ki fito, kada a sibare min wani abu a jefa a buhu ."


Wannan karon wani murmushi na tsananin takaici ne ya bayyana a fuskar Nihal, saboda maganar ta yi mata zafi sosai a zuci.


Ta ce " Hajiya Sadiya ba kowanne talaka ne marar tsoron Allah ba, haka ba kowanne baqauye ba ne yake daukar wulakanci. Ki mutunta dan adam domin Ubangijin da ya halicce shi ma Ya daraja shi . Musamman mace 'yar uwarki da take neman yadda zata yi a rayuwa ya kamata ki tallafa mata, idan tana aikata wani hali marar kyau ki yi mata nasiha ta daina. Idan tana neman taimako ki bata daidai qarfinki, koda kuwa barin dabino ne. Allah Yana tare da masu taimako ."


Sadiya ta tabe baki ta ce " a qara gaba malama, a tafi gidan hadaka gidan camama. An sami falo da luntsumemiyar kujera an baje an dauka anan zaa zauna shine dai haushinki. "


Nihal ta yi murmushi ta gyada kai ta fice zuciyar cike da dariya yadda ta kira kujerar nan da sunan luntsumemiya. Tabbas Nihal ta tabbatar sai yanzu ta shiga makaranta don ada ba karatu ta yi ba .Yanzu ta shiga aji daya na furamare a karatun sanin rayuwa. Sai ta tsinci kanta tana farin ciki gami da murmushi. Murmushin ya kasa barin farfajiyar kumatunta, a sanadiyyar jin dadi don ta fara kwasar ilimi.


"Ashe talaka ya fi kowa qyamar

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads