Showing 102001 words to 105000 words out of 110552 words
Chapter 35 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
Asiri ba zai kama ni ba tunda ina yin Azkar safe da yamma kuma ban taba cutar wani ba. Me yasa 'yan fim wasu ba sa qaunar junasu? Daukaka ta Allah ce. Me yasa ba zasu saka a ransu cewar kowa iya rabonsa zai ci ya tafi? Da baa matsawa a bawa wasu fili su zasu zo su yi na su tashen ne? Wannan ita ce babbar matsalar 'yan fim. Da gaske dole a zage mu a duniya, kwata kwata wannan ba tarbiyya mai kyau ba ce."
Bash ya gyada kai ya ce " tabbas maganarki gaskiya ce gara da kika zo da kanki ki ka gani. Ko na yunkuro zan kula Aisa sai in ga wani mummunan hali a gare ta. Na taba kamata ta na cewa idan ta aure ni sai ta gyarawa ummata zama dan ta fuskanci bini-bini sai ta kira ni a waya ta ce in dawo gida kamar wani yato qarami. Kin ga kenan bukaye za ta bi ta halakar da ni in guji uwata. Nihal ina neman alfarma kada ki tilasta min ki ce sai na auri Aisa na san manufarki. Ni ke nake so kuma ina addua ki amince ki aure ni."
Ta zura masa ido tana kallo ta na tunani mai nauyin gaske. Ko me take tunawa? oho.
Ta tayar da mota suka tafi, a qofar gidansu ta ajiye shi ba tare da ta sake cewa komai ba, ya fita ita kuma ta qara gaba. Tabbas ta bar shi a cikin dimuwa da fargaba. Maganarsa ba ta da amsa kenan.
Nihal ce ta saka ma'aikata suka zo da mota daga asibitin mahaukata aka dauki Aisa da Hasiya carkwai da qarfin tsiya a kai su asibitin mahaukata. Bayan Nihal ta gana da dangin kowaccensu. Ta tabbatar musu bayan maganin asibiti ma su na buqatar addu'oi na warware tsubbace-tsubbace dan shi suka yi ya koma kansu. Ta ji dadi da Allah Ya sa dukka danginsu sun san komai. Ta ba su kudi mai yawa ta ce su tara malamai a taya su da addua. Sun yi mamaki yadda aka yi wacce suka yi niyyar su cutar Allah ya tsare ta yanzu ita take nemo musu hanyar waraka. Sun yiwa Nihal addua da fatan Allah Ya saka ma ta da gidan aljanna tabbas ita 'yar halal ce.
Labari ya cika kafafen sadarwa da jaridu da gidajen radiyo cewa Aisa da Hasiya carkwai sun haukace a sanadiyyar su haukarta da Nihal ya koma kansu. Nihal ta dauki nauyin kaisu asibitin mahaukata da kuma biyan malamai su tayi musu addua.
Duk yadda 'yan jarida su ka so jin ta bakin Nihal abu ya ci tura ta qi yin magana har da Mu'awiyya yayanta ta qi ta amsa masa. Amma Bash ya tabbatar musu da gaskiyar faruwar wannan al'amari.
Sai kowa ya ji Nihal ta sake burge shi,wadanda ma basa sonta a da yanzu sun ji su na sonta haka wadanda ke sonta sun sake sonta.
*** **** ***
Fim din labarin rayuwar Nihal a duniyar fim mai suna ' A wata duniyar' ya fito kasuwa. Sabuwar Jaruma Fatima Maikudi ce ta fito a matsayin Nihal, Atika a matsayin Najaatu, Tanimu a matsayin Hashim. An sami wadanda suka fito a matsayin su Tukur da su Mami harka. Babu abinda labarin ya rage duk abinda ya faru da ita daga farkon shigarta fim har zuwa yadda take yanzu ta rubuta.Hatta qasar London sai da ta kai Fatima maikuudi aka nuna John da Williams a farkon fim din kenan.
Wadanda ba su sani ba yanzu sun san abubuwan da aka yi mata da wahalar da ta sha. An yi kuka a fim din dan tausayi. Sunayen kawai ta canja da kuma sunayen garuruwa.
Su Tukur an ji kunya haka ma su Mami harka. A qarshen fim din an nuna sun yi nadama sun sami qarshe mai kyau Fatima Maikudi ta saka musu da alkhairi.
An kalli fim din sosai kuma an tabbatar musu labarin gaskiya ne daga baya aka gane labarin ita kanta Producer kuma Director fim din ne wato Nihal. Bayan nan an yi hira da Nihal ta tabbatar da duniya cewa Hashim da Najaatu su ne kadai suka taimake ta sai daga baya Bash, Idris da Abbas sun taimake ta.
An sake jin qaunar Hashim da Najaatu a duniyar 'yan kallo kuma ana son kallon finafinansu a yanzu dau babu masu tashe a wannan zamanin irin Hashim da Najaatu. Sun waye sun goge fiye da Bash auta da Bilal da Aisa da Halima Jabir.
Motocinsu na farko Nihal ce ta siya musu kafin daga baya suka sake siya da kudadensu. Najaatu ta na yawan zuwa garinsu Darazo, ta bude wajen koyawa mata sana'oin hannu da fadakar da su. Ma su buqatar shiga fim ta hanya mai tsafta da yardar iyayensu take kawo su bayan sun sami horo a makarantar Nihal. Waqa da rawa a fim ya zama sai jifa jifa domin da yawa su na kwaikwayon tsarin Nihal.
An sami yawaitar masu rubutun script sosai an yaye su daga makarantar Nihal dan haka an sami labarai masu ma'ana a finafinai haka a wajen editing an sami ci gaba.
Nihal ta saye wannan gidan da ta kama haya har da maqwabtansu ma ta mayar da gidan wajen sauke baqi 'yan fim ko wadanda suka zo daga wasu garuwan yin karatu Daya gidan mata daya na maza.
Nihal ce da Bash a zaune cikin wani katafaren lambu da yake cikin gidajenta.
Ta kalle shi ta ce " ka sha yi min tambayoyi game da aurena da kake so ka yi sorry ba wulaqanci ba ne na kan rasa amsar da zan baka ne. Ina da jin nauyin mai kaunata kuma ina daraja shi, ina girmama shi. Bash na yarda da salon yadda kake sona na yarda ka na sona saboda Allah. Ba dan abinda nake da shi ba ko dan nasaba ta ba. Ka kaunace ni lokacin da ni ba kowa ba ce kuma bani da komai. Ka tsaya min a lokacin da kowa yake kyara ta yana kora ta.
Ka hadu da ni a lokacin ina da baikon Muqaddas a kaina."
Bash ya zabura ya gwale idanuwa yana fargabar jin sauran kalaman da zasu biyo baya.
Nihal ta ci gaba da cewa "kamar yadda ka gani a fim dina a labarin rayuwa ta saura watanni uku bikina mahaifina ya yanke wannan hukuncin kuma aka bata alakata da Muqaddas. Bai daina sona ba ban daina sonsa ba. Amma kalmar da mahaifinsa ya fada ta cewa 'yayansa ba zasu auri 'yar fim ba ita ta tsaya min a rai ina ganin ko sun dawo da maganar aure ba zan amince ba kuma na San mahaifina da wuya ya amince shima, gaskiya zai yi wuya aya amince dan na san halinsa. Idan ba Muqaddas na aura ba tabbas Bash Auta zan aura duk duniya ba ni da kamar ka."
Bash ya ji sanyi ya ji dadin da bai taba ji ba. Ya sha ganin alamar kamar Nihal tana sonsa bata so ya gane ne. Yau wannan hira ta burge shi matuka sai ya washe baki yana magana cikin marainiyar murya. Fata yake yana addua Muqaddas ya hakura ya bar masa.
Bilal ne ya dira a gabansu ya yi sallama ya ja kujera ya zauna aka hau kallon-kallo. Ya miqawa Nihal da Bash katin daurin aurensa ne shi da Halima Jabir.
Su ka karanta sai Nihal ta dago ta dube shi cike da farin ciki ta ce " amma fa na ji dadin wannan al'amari haka ya kamata 'yan fim su dinga auren junansu sai a daina raina sana'arsu ana tsine musu."
Bash ya miqawa Bulal hannu su ka gaisa ya ce "congratulations abokina ka ci saa, nima ka yi min addua nawa burin ya cika."
Bilal ya yi dariya ya dubi Nihal ya ce " ina yi muku fatan alkhairi a duba maganar abokina Bash kuma a kanku ku manya ya kamata a nuna misali kamar yadda na burge ki dan zan auri 'yar fim ya kamata ki burge kowa ki auri dan fim."
Su ka kwashe da dariya su dukka.
Nihal na shiga farfajiyar gidansu sai ta iske taron motoci maza ne damqar da ta tambaya sai aka shaida mata cewar kudin aurenta aka kawo daga gidan su Muqaddas basu fada mata ba ne dan ana so a yi mata bazata. Muqaddas ne ya ce a boye mata.
Wannan karon gabanta ne ya yanke ya fadi ba kowa ya fado mata a rai ba sai Bash, dazunnan su ka gama maganar nan. Ta san ya na sonta da yawa zai shiga damuwa mai yawa. Ta shiga yi masa adduar samun dangana da canji mace ta gari.
Bayan kwana biyu kuma aka kai kudin auren Abubakar gidan su Siyama. Tuwon girma miyar nama bigi sai bigi komai mai yawa aka kai. Kudin aure da kayan sa rana.
Bash ya gigice a lokacin da ya sami wannan labari yayi ta kuka Nihal ma kuka take ba tare da ta san abinda za ta ce masa ba, daman can ba ta boye masa ba.
Hashim da Najaatu ne ke lallashinsu. Su ma basu ankara ba suka ji sun fara zubar da hawaye. An dade a cikin wannan hali kowa ya kasa lallashin kowa.
Nihal ta goge hawaye ta dago ta dubi Bash ta ce " ina so ka auri Najaatu. "
Wannan kalma ta firgita dukkansu a wajen.Bash bai ce komai ba ya tashi a da sauri yana share hawaye ya shiga motarsa ya tafi.
Najaatu ta dora hannu aka ta ce " shikenan Nihal kin kashe ni, gaisawar da mu ke yi da Bash mun daina."
Nihal ta yi dariya ta ce "ki bari ya je ya huce ya dawo zai amsa min ni na sani. Amma ka da ki dauka ban gane kina sonsa ba."
Sai Najaatu ta yi wuqi-wuqi da ido Hashim ya hau dariya domin ya san komai.
Najaatu ta sha fada musu cewar tana so ta yi fim da Bash ko sau daya ne a rayuwarta a hada su a matsayin mata da miji. Me wannan yake nunawa kenan?
Nan dai ta hau musawa su na qwale ta. An dauki watanni sannan aka fara ganin Najaatu da Bash a wasu wurare su na hira hakan ya nuna an fara kulluwa. Najaatu ta waye tana da kyau ashe rashin gyara ne ada fara ce sol ga dogon hanci ga idanuwa gazargazar. Ga ilimi ga gayu ga ta 'yar soyayya. Duk sai yanzu Bash ya lura da hakan a rashin Nihal. Bash ya ziyarci garinsu su Najaatu ya gaisa da iyayenta. 'Yan Darazo sun ga Bash Auta, gari ya dauka ana ta dandazon zuwa ganinsa.
Hashim kuwa sun dinke da sabuwar yarinyar nan mai tashe Fatima maikudi tana matuqar qaunarsa kuma har an je gaisuwa a gidansu bayan da aminiyarsa Nihal ta yi amanna da ita. Nihal ce ta cika masa kudi ya sayi katafaren gida a unguwar sharada ana zai tare bayan biki.
Bash daman dan gidan masu kudi ne ba laifi gida guda qato a cikin Nassarawa GRA mahaifinsa ya gina masa anan zaa kawo 'yar Darazo.
Yayin da Amina 'yar kwalisa ta auri mai trader a Wudil, Mami ta auri mai gurasa da nama a bakin tashar Wudil, Asabe ta auri mai siyar da takalma a qauyen Wudil, Iyantu ta auri Tukur Darakta su na can su na dambe da Sadiya matarsa dambe har qofar gida ake fitowa. Fim yayi gardama an hakura da shi babu kudin babu sunan. Dan inda ake samu a soka su ma kowa ya daina.Rayuwa kenan duk abinda ka shuka shi za ka girba.
An sha biki a layi-layi in an gama wannan sai a shiga na wancan. Bilal ne ya fara yi sai na Hashim sai na Nihal sai na Bash da Najaatu. Aure bai hana su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba, matan sun daina yin fim amma daga cikin gida su na rubutawa mazan su fim su na kuma yi musu editing su na daukar nauyin fim dinsu da kansu su siyar su sami riba.
Bash ya budewa Naja'atu gidan kwalliya da dinki. Hashim ya budewa matarsa wajen gyaran jikin amare da kunshi. Daman sun yi suna a fim dan haka aka dinga tururruwar zuwa wajen dan a gansu ma.
Nihal da Muqaddas kuwa sun sha shawaqi (honey moon) a qarshen duniya. Haka Siyama da Abubakar su ma sun kama hanyar su daban kowa da qasashen da yake so. 'Yayan gwamna kenan maganar kudi ma baa magana.
Allah Ya bada zaman lafiya Amin.
11/14/21, 7:20 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 鉂�
GABA GADI
NA
JAMILA UMAR TANKO
(JUT)
Gwamna muse ya cikawa 'yan fim alqawuran da ya dauka, duk abinda ya ce zai yi musu yayi har ma ya qara wasu akansu.Ya bawa Nihal kwamishiniyar mata da qananan yara duk da ma da farko ta qi karba amma an matsa mata sai da ta karba dole. Dalili kuwa kowa ya tabbatar ita ce ta fi kowa tausayin mata da qananan yara da kudinta da jikinta ma yi musu take yi balle kuma ta zama hukuma. Ta na yaqi da mata masu shaye-shaye tun daga cikin gida wato 'yan fim har zuwa ga 'yan waje.
Amare da angwaye su na zaman lafiya cikin jin dadi da nishadi, arziqi da soyayya.
Cikin ikon Allah matar Hashim ta haifi 'ya mace aka saka mata suna Nihal. Watan da ya zagayo Najaatu ta haifi 'ya mace aka saka mata suna Nihal. Major Abubakar da Siyama sun haifi 'ya mace sun saka mata suna Nihal dole su saka sunanta mana dan ita ta hada wannan qaqqarfar soyayyar.
Nihal ta yi farin ciki matuqa kuma ta yi wa takwarorinta tara ta arziki. Ita ce dai ba ta sami haihuwa da wuri ba sai a yanzu ta sami ciki qaramin kuma an tabbatar mu su 'yan biyu ne. Ita da mijinta sun yi shiru tukunna basu fadawa kowa ba. Su na a addu'a kada a gane sai ya girma sannan kowa zai sani. Wannan babban abin farin ciki ne a wajensu.
*** *** ***
Yau ne daren karrama gwanaye(Award Night). Wanda wani babban kamfani da hadin guiwar gwamnati suka hada domin karrama wadanda suka yi wata bajinta a fim da wadanda suka kokari wajen taimaka ci gaban harkar.
Daren wata asabar a wani babban dakin taro in ka Shiga sai ka rantse a Amerika kake baa kano ba. Nihal kenan ta kwaikwayo wancan dan haka ta debo turawan ne suka zo suka tsara. Baa taba samun wajen da ya yi kyau kamarsa ba daman ta karantawa 'yan fim yadda ake yin taron da irin kwalliyar da ake yi. Dan haka kowa da kowa ya fito tsaf gwanin kyau. Ta basu shawara mata da maza da su yi Shiga irin ta al'ada wannan shine zai banbance taron Hausa fim da taron igbo fim da taron turawa. Manyan baqi daga turai Hausawa mazauna can da Turawan da 'yan fim din Lagos da Abuja na yarbawa da na inyamurai.
Shigar Nihal ta yi kyau sosai dinkin atamfa ne amma fa a turai aka dinka yankan da yadda aka kwalmada zaka zaci English wears ne. Ita da Muqaddas sun yi shiga matching color shima da shadda aka yi masa nasa dinkin aka rasa gane ko menene su ka saka.
Nihal ce ta dinkawa iyayenta na su sun fito gwanin shaawa haka Yayyanta guda bakwai gaba daya sun hallara cikin shiga mai kyau kuma su na cikin garin ciki daman don a ranar aka saka musu ranar aure su dukka sun sami matan da zasu aura.
Su Hashim da Najaatu da iyalansu ma baa cewa komai, ha