Showing 21001 words to 24000 words out of 110552 words
Chapter 8 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
ya ji kansa ya fashe " eh a hannuna mahaifinta ya damqa min ita, ai training dina ce."
Darakta Idris dai ya kalle shi bai sake magana ba . A ransa ya ce " training dinka a ina? Finafinan naka ba mu na gani ba.Yaushe aka taba yin irin wannan bajintar?"
Darakta Idris ya rufe jarumai mata da fada yana fadin "kun ga yadda yarinya take acting da zuciya daya kamar da gaske, nan da nan ake kammala sin amma ku ayi ta fama .
Lambar wayarta Darakta Idris ya tambaya ta ce bata da waya. Tukur yayi sauri ya bashi ta sa ya ce shi zaa tuntuba idan ana nemanta.
Nihal da Hashim sun fito bakin titi su na neman mota zuwa wudil ko acaba da zai kai su tasha su hau motar Wudil sai gobe kuma in Allah Ya kai mu. Jaruma Aisa da Hasiya Carkwai ne suka biyo su a baya . Basu ankara ba suka ji an dira a gabansu, fuskokinsu a turbune babu annuri.
Aisa ta kama qugu tana girgiza ta ce " ke baqauyiya 'yar iskar qauye! kada ki sake ki shiga gonata yau dai kin yi nasara. Gobe zaa dawo location kada ki kuskure in ga qafarki anan idan kuwa kin qi tabbas duk abinda ya biyo baya ke ki ka sani."
Hasiya carkwai ta ce " ki fada mata kawai hukuncin da zamu dauka , 'yan daba zamu sa su kakkarya miki qafa na ga yadda za ki koyawa mutane fadan canis din ."
Hashim ya fara basu baki gami da lallashi yana fayyace musu Nihal ba da niyyar ta kwance musu waje ta zo ba alkhairi ne ya kawo ta .
Nihal bata ce komai ba ta tsayar da mai acaba za ta je ta hau. Hasiya carkwai ce ta figo ta sai ga hannun atamfar jikin Nihal ta yage tun daga sama Nihal qasan yana reto.
Aisa ta ce " banza qazama kalli tsummar atamfar da take sakawa wai a haka zata ce zata shiga huruminmu. Ke da kika samu ma har kika tsaya a kusa da mu muna magana, ba na'ima ba ne. Kin isa ki ganmu ma in a kano ne. "
Dan acaba ne ya shiga fadan ransa ya baci ya ce " Haba bayin Allah Yaya zaku dinga zaginta kuna wulaqanta dan kunga bata magana. Ni ma fa dan iskan gari ne kada ku zaci dan kuna yin fim kun fi kowa?"
Nihal ta haye babur ta ce su tafi . Hashim ya biyo su da gudu ya na tsayar da su. Nihal ta ce kada su tsaya su tafi kawai. A hanya kuka mai tsanani ya rikito mata ta yi ta kuka, dan acaba yana bata baki. Ta ce tasha zai kaita zata tafi Wudil ne , nan da nan ya ce shima can ya nufa dan haka su tafi kawai . Kura da iska duk sun cika mata ido haka ta daure tunda motocinta masu Ac sun yi mata nisa. Ta nuna masa inda zai kai ta, ba gidansu ba ne shagon Shazali ne in da take zuwa ta karbi abinci.
Nihal ta tambaye shi kudinsa sai ya ce ta bar shi saboda ya tausaya mata . Ta dauko naira dubu daya ta bashi da yaqi kaba sai ta tura masa a aljihu. Ya cika da mamaki a lokacin da ya zaro ya ga naira na dukan naira har dubu ce.
Ya kwalla mata kira ya ce " 'yan mata kin san kuwa nawa kika bani ?"
Ta juyo ta yi murmushi ta ce " na sani, na ka ne dukka ." Yayi dariya ya yi mata addua " Allah Ya sa ki zama super star ki fi su Aisa shahara. "
Ta ji dadin adduar nan sai ta amsa da amin ."
Hashim ne ya taho a sukwane ya sauka daga kan babur a qofar gidan Nihal , saurin da yake yi ma shine dan ya zo ya biya mata kudin babur ya san bata da ko sisi. Ya shiga ciki da sauri qofar dakin ma a rufe babu kowa sai ya cika da mamaki da fargaba a inda ta maqale. Gashi bata san gari ba ko dai sun bata ne ?
Daga baya ya fi zaton ko fushi tayi akan wulaqancin da su Aisa suka yi mata ta tafi wani waje ta zauna tana kuka ne . Ya dade a zaune a qofar gidan yana jira bata zo ba .
Ya dauko kwarababbiyar wayarsa ya kira Tukur Darakta ya ce " oga wata matsala ce ta taso min ta kudi, zan kai tsohuwa asibiti dan Allah Ka bani naira dubu biyar a cikin kudin aikina. "
Sai da Tukur ya gama cashe masa da fada da gori sannan ya ce ya zo gida ya same shi .
Hashim ya tafi da sauri gidan Tukur ya karbi kudin . Bai tsaya a ko ina ba sai a shagon Tanimu mai shagon atamfofi da leshina da mayafai. Atamfofi biyu ya siya masu arha naira dubu bibbiyu da dari bibbiyu sannan ya sayi mayafi naira dari takwas kalar da zata shiga da kowacce atamfa. Gidan Marka mai dinki ya wuce daman ta san Nihal tunda sun taba zuwa tare a lokacin da ta kawo yagaggun kayanta ta dinke mata. Sai ya biya ta dubu daya ya ce ta dinka masa zuwa gobe da safe . Ta Amince zata yi hakan tunda ya biya kudi da yawa .
Kofar gidan su Nihal ya dawo ya ci gaba da jira, bai jima ba sai ga ta, ta sauka daga kan acaba . Ta tsorata da ta ga mutum a tsaye a bayanta .
Ya yi dariya ya ce" ke matsoraciya ni ne fa. A ina kika shiga ne ? Na zaci ai bata ki ka yi ko me babur ya sace ki ."
Ta yi murmushin karfin hali ta ce " haba dai na san gari ai ."
Shi ya biya mata kudin acaba naira hamsin sannan suka qara kan dakalin qofar gida, Nihal tana ta boye yagaggen hannun rigarta da mayafi ta kasa sakewa. Hashim ya kula da haka sai ta qara bashi tausayi . Ba zai fada mata ya kai mata dinki ba, so yake ya bata mamaki gobe da safe .
Hashim ya ce " Nihal sai kin yi hakuri musamman da Allah Ya baki wata boyayyiyar baiwa, wacce za ta kai ki ga shahara duniya gaba daya zata sanki nan gaba . A tarihin Fim industry gaskiya baa taba samun macen da ta iya tsalle da fadan canis irinki ba daga bakin daraktoci nan na ji su na fada. Dole ki sami maqiya mahassada. Kin san wani abu ne dole fa mu dage da addua don baa shiga harkar Fim GABA GADI a shahara kuma a wanye lafiya kalau ba. Sai mun je wajen malamai sun yi mana addua an baki layu da guru kin daura saboda maqiya . Zan raka ki wajen malamina a wani qauye nan kusa . Me yasa kika ga kowacce rawa sai an saka ni ? Ai na tsare jikina na sha rubutun farin jini ne."
Dariya ta kama Nihal ta rufe baki dan kada ya gane ta ce " Allah ko ? To shikenan ."
Su ka yi sallama akan sai da safe zai zo da wuri su koma wajen shooting .
Nihal ta shiga daki ta iske su dukka suna nan. Babu wacce ta amsa sallamarta sai Najaatun Gujungu. Aka hau yasar mata da habaici.
Mami ta ce "Wallahi idan mutum ya na shishshigi a kauye ya kwana lafiya ya kiyayi shishshigewa 'yan birni . Daga ji sun zo aka yi carab aka tafi neman wajen zama . "
Ba ta kula su ba tana ajiye mahaifinta sai suka ga hannu a yage. Su ka kwashe da dariya suka tafa.
Iyantu ce ta ce " dan tsumman da ake ji dashi na fita unguwa shine ya yage? Allah sarki su super star manya. "
Naja'atu ce take ta qifta musu ido akan su daina amma suka qi.
Najaatu ta ce " Nihal gobe kiyi min magana idan zaki fita akwai wata atamfata da nake so in bayar, zan baki . "
Nihal ta kalle cike da farin ciki ta ce " na gode Allah ya kai mu."
Ta tafi ta yi wanka ta dawo daki, su ka cika da mamaki da suka ga ya farko sabuwar rigar bacci fil daga leda ta saka. Sai aka hau kallon-kallo a junansu.
Mami Harka ta ce "na fada mu ku yarinyar nan wai ita a dole 'yar gayu ce wato mu take kwaikwaya har rigar bacci aka siyo an daina kwanciya da tsumma. "
Iyantu ta ce " ba kya ganin wai ita a dole sai ta yi turanci rannan fa ce min ta yi please akwai micro wave a room din nan kuwa? Da na sake tambayar ta sai ta qi maimaitawa ta ce babu komai ."
Asabe ta ce " tana son yin turanci gashi kuma baa iya ba. Ni ma rannan wai tawul zata ce sai da tayi wata malkwada wai ita baturiya wai towel. "
Su ka kwashe da dariya suka tafa .
Najaatu ta ce "gaskiya bana jin dadin abinda ku ke ya bakuwar nan shiyasa ma ban cika kwana a dakin nan ba. Ita bata shiga harker kowa kun saka mata ido ."
Nihal ta ja fulo ta kwanta a kan tabarmarta ta juya musu baya , haka suka hana ta bacci su na ta shewa har sai da kanta ya fara ciwo.
Asuba ta gari Nihal Nuren Mubin!!!
Da safe misalin qarfe tara Hashim dauke da ledar kayan dinki ya iso gidan su Nihal, daman ta hana shi shigowa cikin gidan kai tsaye, a zaure ya tsaya ya baza murya ya kwala sallama. Ta gane muryarsa sai ta fito da sauri. A kofar gida suka tsaya, bayan sun gaisa sai ya miqa mata leda me dauke da sosai mai zafi sannan ya miqa mata babbar leda mai dauke da atamfofi da mayafi .
Ta karba cike da mamaki ta tambaya " mene wannan ? Na waye ?"
Yayi dariya ya ce " naki ne ki shiga ciki ki bude ki gani . Na baki awa guda ki shirya ki zo mu tafi yau a kusa da kano zaa yi a wani gari da ake kira Cinkilawa a qaramar hukumar Warawa yake. Zaa kawo motoci sai mu shiga mu tafi .
Ta shiga daki ta warware kaya, sai ta cika da mamaki da ta ga dinkakkun atamfofi guda biyu har da gyale. Ta ji dadin da bata taba ji ba sai ta sake cure Hashim tabbas mai kaunarta ne. Ta yi mamakin yadda aka yi ya san kalolin da ta fi so, katari kawai aka yi .
Ta wutsiyar ido ta hango su Mami suna kallonta ashe baccin qarya suke yi. Ta ci kosai guda biyu ta ji zai tayar mata da zuciya kasancewar da man kwanti aka soya. Sai ta ajiye a gefe ya shiga wanka.
Iyantu ce ta tashi da sauri ta hau daddaga kayan, su na kallo, sun yi niyyar su saka reza su tsatstsaga sai Najaatu ta kwashe ta hana su. Da Nihal ta shigo dakin ta kula kamar akwai wani abu da ya faru domin taga an baza mata kayan kuma sun yi carko-carko su na kallonta kamar basu da gaskiya.
Ta saka kayanta ta shirya tsaf da sauri, ta yafa gelenta wanda yayi marching da kayan. Bata kula su ba sai ta yiwa Najaatu sallama ta fice.
Mami ta ce " idan ba mu yi hankali ba da zarar kudi sun fara shigowa yarinyar nan zata waye ta yi can sama ta fi mu .
"Kun ga yadda ta yi bala'in kyau da ta saka sabuwar a atamfar nan, dan ma leda-leda ce. Toh ina ga idan ta fara saka super holland? Sai mun yi da gaske wallahi. Yaushe ta zo garin ne?" Iyantu ce ta fada .
Najaatu ta ce " ashe kina da aiki kuwa , yarinyar da ta dogara da Allah Shi kadai ba Zai taba bari wata hallitta ta cutar da ita ba wallahi. Duk in da qarfe ukun dare ta yi ta gama bacci . A tsaye take tana sallah har asuba sannan ku ce zaku iya hana ta daukaka, "
Nan dai Iyantu ta yi kan Najaatu su ka hau fada da zage-zage, wai don me zata fadi haka?
Da Nihal ta fito sai Hashim ya gagara gane ta sai da ta yi masa magana .
Ya dinga mamakin yadda ta canja ta yi kyau ashe tsumma ne ya ke zamar da ita kamar wata 'yar talla.
Su ka yi ta dariya Hashim yana yi mata tsiya. Ta masa godiya sosai bisa dawainiya da kulawar da yake yi mata. Ta yi masa addua Allah Ya sa ya zama babba Jarumi ya Bash Auta gwanin na sa.
Ya cika da mamaki da ya ji Nihal ta ce ba zata je wajen daukar shirin "yan birni ba . Ta ci gaba da yi masa bayani ta ce Akwai wani darakta Aliyu wanda Tukur ne ya hada su ya ce zata zo yau ta yi masa aiki. A cikin garin Wudil zaa yi can zata je .
Hankalin Hashim ya tashi yayi ta magiya ta qi yarda. Wayar Hashim ce ta fara qara Darakta Idris ne yake kira , daga Hashim din har Nihal ne suka zabura .
Darakta yana magana cikin rikicewa. "Ku na ina ne ? Ga motoci an kawo zaa tafi location ban ganku ba . Ina Nihal ?"
Hashim ya miqa mata waya da sauri, ta karba suka gaisa ya ce "ku taho da gaggawa zaa wuce." Ya kashe waya ba tare da ya jira amsarta ba.
Hashim ya yi tsalle yana murna ya ce "kin gani ko daman sai da na fada miki . Kin haye kawai tunda Darakta Idris ya san da zaman ki ."
Mami ce da Iyantu suka fito tsegumi suna so su ga in da Nihal za ta nufa, sun yi fakare sun tsaya sun gama sauraren abinda ake fada a waya .
Nihal ta zo ta zauna akan dakali ta ce " na fada maka ba na son in sake zuwa wajen daukar shirin Fim din 'yan birnin nan bana son rigima . Na ce maka ba zan je ba ."
Mami ta zabura ta ce " kai Hashim wai wanne irin shishshigi ne wannan? sai Cusa ta kake tana gwale ka, ka rabu da ita mana tunda bata san alkhairi ba .
Hashim ya tsaya yana ta yi musu bayanin irin muhimmancin Nihal a Fim din birni. Ba tare da ya san kamar wuta yake hura musu a qagon zuci ba .
Darakta ya sake kiran Hashim ya ce " ku na ina yanzu ? Ga mu nan zuwa kawai mu dauke ku akwai waje a motar ta mu duk an yi gaba."
Hashim ya kwatanta masa, babu jimawa sai ga wata dankarareriya Mota qirar jeep baqa, mai baqin gilashi ta tsaya a in da suke . Aka zuge gilashin windon gaba Jarumi Bash Auta ne ya bayyana. Sai a yau su Mami suka taba ganinsa ido da ido. Da aka zuge gilashin baya Darakta-daraktoci ne Idris ganinsa sai an cike form shine ya bayyana.
Sai ga su Mami su na durquso su na kwasar gaisuwa suna gabatar da kansa a matsayin suma jarumai ne a wannan masana'anta. Asabe da Najaatu ne suka fallo da gudu suka fito gaba daya su ka yanyame jikin motar su na ta soki burutsu a dole a fim suke so saka su.
"Ke Nihal ta so mu wuce mana, kina zaune kina mallon mutane. " Darakta ya fada a lokacin da suka hada ido da Nihal tana zaune akan dakali.
Bash Auta ya ce " ah daman ita ce waccan ? Kai! yaya naga ta canja ba kamar jiya ba ...."
Bai gama fada ba Darakta ya ce " ka yi shiru Malam kada ka tunzura dan na ga kamar bata son zuwa. In babu ita kuwa yau akwai matsala. "
Nihal ce ta qaraso in da suke ta gaishe su cikin ladabi sai. Aka ce ita da Hashim su ghiga baya su zauna tare da Darakta .
Nihal ta ce" mazan ne ya kamata su hadu a baya ni a bani gaba ."
Haushi da mamaki ya kama Bash Auta tayaya zaa ce wannan kucakar da ya kamata ta yi biyayya dan a saka ta a fim amma ita take bada direction. Ransa bai so ba Darakta Idris ya roke shi ya dawo baya, bayan ya tabbatar masa da cewa yarinyar ta fi su gaskiya bai dace ta gwamutsa da maza ba.
Nihal Nuren ce ta haye gaban mota yayin da mazan suka shiga baya.
Zo ka ga bude baki dan mamaki da hassana kiri-kiri sun bayyana akan fuskokin su Mami.
Nihal ta kalle su ta yi murmushi ta ce " sai anjimanku." Ta ja galas sama ta rufe aka ja mota aka tafi .
Asharai kala-kala suka dinga saki.
Mami ta ce " shikenan muna zaune ta zo ta fi mu. Ai Hashim da Tukur ne munafukai su suka kaita suka hada ta da manyan daraktoci."
" Wallahi ba zai yiwu ba ko da asiri yarinyar nan sai ta koma garinsu ." Asabe ta fada.
Iyantu ta ce " daga gani da asiri ta shigo in ba haka ba yaushe ta zo? Watanta guda kenan da zuwa fa ."
Mami ta ce "mu je mu yi mata wurgi da kayanta a tsakar gida daman ai wata ya qare bata biya ba kudin haya ba."
Asabe ta ce "mu je mu yi mata Watsin da kaya ta dawo ta tsinci kayanta a tsakar gida ."
Najaatu ta ce " kada ku yi haka, ku bari ta dawo ta kwashi kayanta da hannunta ta tafi ."
Ba su saurare ta ba cikin gida suka shiga da sauri suka fara yi mata watsi da buhun kayanta da filo a tsakar gida daman tabarmar ba ta