Header Ads
Showing 69001 words to 72000 words out of 110552 words

Chapter 24 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ajiye wuqa suka dauki cokali mai fadi su na kaiwa baka yayin da dadi ya gauraye bakunansu har zuwa kunne. Da abu ya gagara sai su ka kai hannu su ka yagi kaza. Abincin da su Bilal su ka siya bai kai rabin-rabin na su Nihal ba ma amma bill din sai da ya tsorata su.
Tabbas su Aisa sun sami abinda ake so, qaryar Nihal ta qare daga yau, za su ga yadda za ta saki jiki ta koyar da tsalle da fadan canis.
Fuskar Bilal za ka kalla ta cika taf da murmushi ya na cin abinci cikin nishadi yana kallon kauyawa a birni.
"Wato lemo ma ya kai kala goma, tabbas da sun san kudin lemo daya ma da ba su dauki guda goma ba." Halima ce ta fada tana dariya.
Su ma ma'aitan maganar su ke yi? su na ta qus-qus-qus a junansu. Su na sake tambayar ma'aikaciyar da ta rubuta order, anya ta nuna musu kudin abincin nan kuwa kuma sun fahimta?
Abincinsu kawai su ke ci ba tare da sun damu da kowa ba. Bilal Ya qurawa Nihal ido ta wannan ne karo na farko da ya taba kallon fuskarta a cikin haske tar, tabbas ta yi kama da matar na da suka gani dazu Bash ya dage ya ce ta yi kama da Nihal. Haka a lokaci guda ya ga kamar ta da princess last born.
"Rigiji-gafji me ya ke shirin faruwa ne anan?" Bilal ne ya fada a bayyane yayin da ya zabura kamar zai miqe tsaye sai ya fasa.
Kansa ya daure sosai ya daina ganin laifin Bash da ya dage ya ce ta na kama da Nihal. Ya ci gaba da kallon sarautar Allah.
Aisa ce ta dora hoton su Nihal a Instagram ta rubuta a qasan "some thing big is going to happens."
Halima ma ta dora, kalamai daya su ka rubuta.
Ashe Bilal ma hakan take ya rubutawa miliyoyin abokansa cewa ga su a qasar Nijer a jihar Maradi, nan da 'yan mintuna za su ji wani labari mai dadin saurara. Ya saka alamar dariya, ya saka alamar gwalo.馃槂馃槂馃槢馃槢.
Kafin ka ce kwabo ananta ruwan comments da likes ana ta dokin a ji. Tabbas wannan babban al'amari ne, tunda Jarumai ukun suka saka hoto iri daya suka fadi kalamai iri daya.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 鉂ゐ煡�


GABA GADI
Na
Jamila Umar Tanko


Su na gamawa ma'aikaciyar ta qaraso dauke da zungureriyar takardar bill ta miqawa Nihal. Nihal ta karba ta duba yayin da ta tuna da cewa ashe da bata iya karatu ba sai ta wayance ta fara jujjuyawa. Ta tashi ta nufi wajen da ake biyan kudi. Ta fara magana da sauran ma'aikatan ba tare da kowa ya ji abinda suke tattaunawa ba. Ta na ta magana an rasa me take cewa.
Su Aisa dariya suke ta sheqawa.
"Halima ta ce "ta tafi ta roqe su ayi mata ragi, ta dauka a Wudil ne. Yau kam zaa yi ta kenan."
Ba su ga sanda ta miqa musu kudi ba saboda ta juya baya, sai dai su ka ga Nihal ta dawo kan tebur dinsu ta yiwa Hashim da Najaatu magana su ka tashi suka bi ta su ka fice. Sai kan su Bilal ya daure matuqa.
Mata mai bada bill ce ta qaraso ta miqawa Bilal resit ta ce " Wacce ta fita yanzu ce ta biya muku dukka."
Kamar a mafarki, kamar almara, su ka ji tamkar tatsuniya. Aisa ta nuna teburin da su Nihal su ka tashi ta sake tambaya,aka tabbatar masu da cewa ita ce.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai masanin gaibu."
Wayar Bilal ce ta ke ta ruri lambobi barkatai ne su ke kiransa. Ya amsawa mutum na farko, na biyu, da na uku dukka abu daya su ke fada cewar su nan su na jira su ji wannan al'amari da yake daf da faruwa fa. Baya bada amsa sai ya katse wayar, saboda bai san me zai ce musu ba, kiran dai ake ta yi ya qi amsawa. Gumi ne yake ta tsatsafowa daga goshinsu su dukka.
Bilal ya ji kansa ya fara juyawa ya zabura ya ce " ku tashi mu fita waje. "
Su ka fito suka tsaya a waje su na shaqar sanyayyar iska an rasa wanda zai fara magana a cikinsu.
Wayar sa ce ta sake yin qara Bash Auta ne ya kira shi ya na fada " wai wannan wanne irin wulakanci ne ku ke yiwa Nihal? Me yasa ku ke so ku tozarta ta ne?"
Bilal ya fusata ya yi tsaki ya katse wayar.
Wayar Abbas ce ta shigo " ka na ina ?" Tambayar da yayi kenan.
Bilal ya kwatanta masa, babu dadewa sai ga Abbas da Bash sun tsaya a cikin mota,su ka firfito suka same su.
"Abbas ya ce " mene haka? Wanne irin post ku ka yi? Me yasa zaka biyewa mata ku taru ku tozarta bayin Allah? kawai dan a wulakanta yarinyar nan za ku dauke ta a hoto ku yada? Meye dan sun hau kan teburin cin abinci, su ba mutane ba ne? Dan haka ku gaggauta goge wannan post din dan a zauna lafiya bana son irin wannan.
Bash Auta da Bilal ne suka hautsine da fada yayin da Abbas ya shiga tsakiya yana rabiya. Kan ka ce kwabo waje ya cika da mutane musamman da aka gane 'yan fim ne babu abinda yan Nijer suka fi so a wajen'yan Nigeria irin su ga 'yan Hausa fim. Babban takaicin Nihal shine yadda suke da daraja bai kamata su zubar da qimarsu a gaban masoyansu ba wannan shine babbar illar 'yan fim.
Sai a lokacin Nihal da su Hashim su ka san an tura hotonsu a social media shine ya jawo fadan dan haka suka labe a lungu su na leqe su na kallo, fadan da babu ruwanka dadin kallo ne da shi.
Fada ya koma kan Aisa da Bash tabbas daman tana neman wannan rana da zata yiwa Bash tatas yadda ya ke raragefe akwai alamar yana son Nihal, bayan ya tabbatar da cewa ita ce take bala'in sonsa.
Abbas yayi iya kokarinsa wajen rabon fadan domin masu Restaurant sun ce zasu yiwa 'yan sanda waya. Qasarsu akwai doka yanzu nan zaa yi ram da su, 'yan jarida su sami abin bugawa kuwa.
Bash ne a fusace ya bar wajen ya koma gefe yana huci, yana waiga bayansa Hashim Najaatu da Nihal ya hango a labe su na shan kallo sai ya sake bude ido ya dube su sosai tabbas su din ne.
Abbas na can ya na bada hakuri sai da ya tabbatar Bilal da su Aisa sun shiga mota sun tafi sannan ya dawo ya cewa Bash su tafi. Bash ya shiga mota ya zauna yana huci. Ido su ka hada da Nihal tana kallonsa, wani mugun sonta ne ya ji ya sake sauka a qahon zuciyarsa mai tafe da tausayinta.
Abbas ya fisgi mota da gudu suka hau titi ya ce "maganar gaskiya ana caja min kai na gwammace ban gayyaci Bilal ba, ka ga yadda ya saka yarinyar nan a gaba bai kamata ba. Daman can Aisa ta tsane ta kowa ma ya san da haka. Wannan wacce irin rayuwa ce? ka ce wani ba zai daukaka ba sai ka durqushe shi?"
Bash ya ce "ka bar ni da su zan koya musu darasi kuma Nihal za ta dauka da babu yadda su ka iya."
Da misalin qarfe goma sha daya na dare ne Bilal na zaune a reception din Hotel yana waya ransa a bace yake magana tabbas Bash yake jin haushi kuma ya sha aradu zasu hadu a kano sai nuna masa shi ba sa'ansa ba ne.
Wayar da bai qarasa ba kenan princess last born ya hango su na tafe tare da turawa sun zo sun wuce shi, ita kadai ce baqar fata. Ya zabura ya miqe ya bi su a baya yana kasa kunne ya ji me suke cewa amma kash yaren faransanci ne.
Kujeru na musamman aka jera musu aka kuma saka jami'an tsaro su na gadinsu a kowacce kusurwa. Dan haka Bilal bai isa ya qaraso in da suke ba. Ta sha riga da wando ta daura dan sirin mayafi a kai, daman haka take yin shigar ta kullum. Gashi yau da ya qarewa Nihal kallo ya ga sun yi kama amma babu tantama wannan princess ce.
Ya na daga nesa ya na kallonta, takardu da yawa suka miqa mata ta sassaka hannu. Bilal ne ya kira lambar Bash yaqi amsawa, ba dan komai ba ne sai dan ya zo ya ceto shi daga cikin damuwar nan, domin shine ya san Nihal sosai, shi kuma princess ya sani.
Da ta gama saka hannu sai taro ya tashi kowa ya kama gabansa maimakon ta fita waje sai ta haye saman bene inda dakunan suke.
A kan matattakala ta ci karo da Bash Auta za ka iya ganin zaburar da yayi ya saki baki yana kallon ta har ta wuce yana.kallonta tana kallonsa babu wanda yayi magana a junansu. Ya bi ta da kallo har ta sha kwana.
Ta na shan kwana ta yi kicibus da Aisa da Halima su ma razana suka yi, gabansu ya fadi ko tantama babu wannan ta yi kama da Nihal. Ganin halinda su ka zunduma sai ta gaishe su da yaren faransanci.
Su ka bi bayanta da kallo tafiya take ta na rangwada sanye da wani takalmi mai dankaren tsini wanda ko kudi aka ba su ba za su iya tafiya da shi ba.
Su ka kalli juna cike da mamaki sai Aisa ta ce " ko dai gamo mu ka yi waccan ta yi kama da Nihal."
Da sauri suka sauka qasa suka iske Bash da Bilal su na magana akan abimda idanuwansa suka gani, hakan su Aisa su ka shaida masu abinda suka gani.
Waya Bash Auta ya dauko a gigice ya kira Fati dangerous. Ya ce " kina ina yanzu? ki koma gidanku dakinku ki dubo min Nihal tana nan kuwa?"
Fati dangerous ta ce "ina qofar gida ne shiyasa ka ji hayani amma ban dade da na na ganta ba ita da Hashim. Amma bari in dubo maka ita. Bayan wasu mintuna ya sake kiran Fati ta tabbatar masa gata ga Nihal tana bacci a daki. Tun kafin Bash ya fada musu abinda Fati ta ce sun ga yadda yanayinsa ya nuna. Ya sake sanar musu da cewa Nihal tana dakinsu.
In ba Nihal ba ce wannan toh wacece? " in ji Bash Auta.
Bilal ya ce "in ba Princess ba ce wannan toh wacece ita?"
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne馃グ


GABA GADI

NA




JAMILA UMAR TANKO
(JUT)


Da sassafe misalin qarfe bakwai Bash, Bilal, Aisa da Halima ne su ka dira a qofar dakin su Nihal domin sun kwana ba su rintsa ba, mamaki ya hana su sukuni.
Su ka buga qofa sai Duduwa ta bude idanuwanta cike da bacci. Ta zabura ta murtsike ido ta kalle su, gabanta ne ya yanke ya fadi ganin gidiga-gidigan jarumai a gabanta da sanyin safiyar nan.
"Ina Nihal Nuren?" Bash ya tambaya a zabure.
"Ga ta can ta na bacci.
Ke Nihal! Ki zo ana nemanki." In ji Duduwa indiyana.
Nihal Nuren ce ta bayyana a gabansu, dakyar take iya daga ido ta dube su saboda baccin da yake cike a idanuwanta. Sai dukkan su suka bude baki su na kallon junansu cike da mamaki marar musaltuwa.
" wannan wacce irin kama ce? kuma aca har da tambarin sallar na goshi iri daya? Kai wannan al'amari akwai rikitarwai." In ji Bash.
Nihal ta shafa goshinta ta taba tabon sallarta ta ce "me abin sallata yayi? Lafiya? Ku fada min me yake faruwa ne?"
Zuciyar Bilal ce ta hasko masa fuskar princess, babu banbanci har da tabon sallar itama.
Bilal ya sosa qasumba ya ce " babu amfanin yi ma ta bayani fa ba zata taba ganewa ba. Tunda bata da ilimin da zata gane ma. Ku zo mu tafi."
Su ka juya suka tafi suka bar Nihal da Najaatu da Duduwa a tsaye cike da fargaba da mamaki.
Najaatu ta ce " me suke nufi? Wani abu aka ce kin yi?"
Nihal ta girgiza kai ta ce "ni ma na kasa ganewa tun jiya Bash yake zuwa yana tambaya ta ko ina da 'yar uwa a Nijer? Na ce masa bani da 'yar uwa ."
Najaatu ta zabura ta ce "mai kama da ke suka gani kenan sun zaci ke ce. Ai a duniya masu kama daya an ce su bakwai ne ake yinsu haka dai aka ce."
Duduwa ta tabe baki ta ce "dama baa hada mu a daki daya ba wallahi, neman rigimarki Nihal ta yi yawa. Tun jiya an hana mu sakat sai a kira a ce ina Nihal ya fi a kirga. Wa ya san mugun abinda kike yi musu, kin hana kowa sakat. Har fada ki ka hada Bash da Bilal, ki ka raba abotar shekara da shekaru. Na rasa dalilin da ya sa ma manyan jarumai kamar su suke kula karamar Jarumar kauye irinki,saboda kawai kin iya fadan canis."
Najaatu ta zabura zata mayar da martani, Nihal ta damqe mata baki ta girgiza kai, alamar kada ta yi magana.
Duduwa ta warware murya, ta dunkule hannu, ta baje qafa sannan ta ruguzo asharai ta ce " bar ta ta zo mu d'ame, in nuna misali akanta zata tantance ko ni kanwar lasa ce."
Nihal ta ja hannun Najaaatu suka fita qofar gida, dan ba zasu koma cikin dakin ba ma balle a ci gaba da fadan, idan ta huce sa dawo.
Hashim ne ya hango fitarsu ta wundun dakinsu, sai ya fito ya zo ya same su su ka zauna akan wani dogon benci. Bayan sun gaisa Nihal ta fuskanci jikin Hashim yayi sanyi.
Hashim ya yi tsaki ya girgiza kai ya ce " akwai matsala fa, wato fadan Bash da Bilal jiya ya jawo miki zagi a social media, an ce akan ki wata kucaka irinki jarumai biyu sun yi fada. Ali goga ne ya nuna min a wayarsa, hotunanmu ne a wajen cin abinci su Bilal suka dora su na cewa ga wasu kauyawa sun shiga shagon cin abinci mai tsada ba su san yana da tsada ba, zaa ga yadda za su biya kudin himilin abincin da suka yi order. Har yanzu mutane su na jira su ji yadda aka qarke amma basu koma sun ce kin biya ba sun bar mutane a duhu. Sannan Fadan Bash da Bilal ya jawo miki zagi qaton hotonki aka saka dan wulakanci ma baa dauki hoton da kika saka kaya masu kyau ba, aka dauko yagaggiyar atamfa ce a jikinki, hotonki a lokacin da ake daukar shirin 'keke ko Babur' na kamfanin Tukur. A qasan hoton aka rubuta 'Manyan jarumai biyu sun bawa hamata iska a qasar Nijer a sanadiyar Nihal din qauye.' Tunda na ga hoton nan ban iya yin bacci ba wannan cin zarafi ne. Me kika yi mu su ne haka?" Yana gama fada sai wani zazzafan hawaye ya sirnano daga idanuwansa.
Najaatu ma ta fara kuka, Nihal ba tausayin kanta ta ke ji ba, ita haka ma ta fi so domin tabbas daukaka ta zo

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads