Showing 6001 words to 9000 words out of 110552 words
Chapter 3 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
suka nufi bangarensu domin kowannesu ya na da ginin gida a cikin gidan .
Toh fa! Kwamacala kenan . Tabbas Nihal ta yi gaskiya da ta ce gara ta shiga kasashen masu kananan idanuwa ta bace, gara kada ta cinye ta akan ta tunkari hukuncin da wadannan zasu yi mata.
Major Abubakar ya kira Engr Muqaddas a waya, Muqaddas ya shaida masa su na filin jirgi har yanzu su na jiran isowar Siyama. Domin sun saka wasu ma'aikatan immigration na Airport din Abuja su hana ta shigewa. Har ma an yankar mata tikitin juyowa kano.
Abubakar ya shaida musu gashi nan zuwa Airport din shima zai jira isowarta.
Asuba ta gari Siyama Abba Muse !!!
Sun hallara da sassafe kamar yadda yaya Babba ya umarce su . Kafin su fara magana Fitowar mahaifisu janye da akwatin kayansa ne ya katse musu hatsari. Kowa ya bude baki yana mamaki.
" Daddy ina kwana." su dukka suka hada baki . Gami da tasowa da sauri kowa yana so ya karbi akwatin da yake ja.
" ku matsa ku bar min akwatina." Ya fada yayin da yake qoqarin ficewa daga falon .
A baya suka bashi ba tare da kowa ya iya kara yin wata magana ba . Habibu direba ne ya iso da sauri ya karbi akwatin ya saka a but gami da bude masa bayan mota ya Shiga ya zauna .
Muhammad ya karaso da sauri ya rike kofar motar ya dukar da kai ya ce Daddy mun yanke shawara mutane biyu daga cikinmu zamu je London mu dubo Halinda Nihal ke ciki . "
" Kada a kuskura a ayi wannan tafiyar ban saka ku ba . "
Daddy yanzu ina za ka je ? Ko London din da za bi ta ? " Hamza ya tambaya
Harara ya wurga musu ya ja murfin motar ya rufe ya ce da Habibi " Ja motar mu tafi pls , suna bata min lokaci ."
Kowa ya sankare a tsaye ya bi bayan motar da kallo . Ransu ya sake baci tabbas . A zuciye Conel Muhammad ya juya ya nufi cikin gida sai su ma suka bi bayansa kai kace kaza ce da 'yayanta. Bai tsaya a kunna ba sai a bakin qofar dakin Mummy .
Ya fara bugawa har wasu daga cikinsu suka taya shi bugun amma bata bude ba.
" Mummy kina da labarin Daddy ya yi tafiya yanzu ? Ya fada miki kuwa ? " Abubakar ya tambaya
Sun cika da mamaki da su ka ji ta basu amsa. " Eh na sani ."
Suka hada ido cike da mamaki .
"Ina ya ce miki zai je?" Umar ya tambaya
Mummy ta ce " ban sani ba ."
Muhammad ya cije baki ya sunkuyar da kai kasa kama mai tunani . Sannan ya dago da jajayen idanuwansa ya dube su.
Ya ce " ku bar ta kawai . Da alama fushi su ke yi da junansu ."
Mu'awiya ya ce " kin ci abinci kuwa ? Ko In kawo miki tea?"
Wannan karon bata amsa ba, kuma bata sake amsa musu ba ma, har suka gaji su ka tafi .
"Me na ke gani ? Me yake shirin faruwa da rayuwar Nihal 'yar auta 'yata guda daya da na fi kauna daga cikin 'yayana?" Zuciyar Mummy da Daddy ce ta fada a lokacin da kowannensu ya shiga tunani.
BAYAN KWANAKI BIYU
Da misalin qarfe hudu na yamma. Motar General Nuren Mubin ce ta kutso cikin farfajiyar gidan.
Bar Usman da Dr.Hamza ne kowannensu ya daga labulen wundo yana leqe daga bangarensa. Bayan General ya fito, sun cika da matukar mamaki a lokacin da suka hangi Nihal Nuren na biye da shi a baya, cikin matsanancin firgici tana tafe tana sanda.
Suka yi wuf da sauri suka fito.
"Daddy sannu da dawowa." Su ka fada a tare.
Ya waiwayo da sauri ya ce " yauwa Hamza ku ce da 'yan uwanku ina neman kowa da kowa gobe da safe a falona. Wadanda basa gari ayi musu waya su dawo . A cewa Muqaddas ya kawo Siyama zuwansu yana da matukar amfani. "
Cikin damuwa su ka amsa masa, yayin da harararsu ta dira akan Nihal sai ta zabura ta kara sauri a tafiyar da take. Kallo daya zaka yi mata ka san a firgice take kuma a wahale . Baka iya hangi kwayar idanuwanta saboda kuburin fuska.
Habibu direba ne ya zo giftawa yana janye da manyan akwatunan Nihal har guda uku. Daga nan suka tabbatar ta kauro gaba daya .
Usman ya tambayi Habibu daga "London ku ke?"
Habibu ya ce " A' a a Abuja muka jira isowar Nihal ."
Usman ya kalli Hamza, Hamza ma ya dube shi su na cikin damuwa .
Usman ya ce " ban ga alamar ciki a jikinta ba ."
Hamza ya ce "daman waye ya ce lallai-lallai ciki ta yi ? mu jira goben mu gani. Zo mu je mu kikkira su, Conel yana Lagos, Major yana Kaduna , Asp Aliyu ya tafi Abuja, Kenan ace duk su juyo. "
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI
NA
JAMILA UMAR TANKO
EP 4
Baa samu hallara taron ba sai bayan sati guda hakan ya faru ne daga General Nuren shine ya daga, domin yana so sai ya gama bincike akan gejin laifuffukan da ta aikata da kuma tunanin hukuncin da ya kamata a yanke mata.
Da misalin qarfe goma sha biyu na ranar asabar. General Nuren na zaune a bisa babbar kujerar falon, matarsa Professor Shatu a kusa da shi. Daya kujerar kuma Ambassador Abba Muse ne da matar Justis Hassana Abba Muse, wato iyayen Siyama. Sauran kujerun zuwa kujerun dining table Yayyan Nihal ne su bakwai da yayan Siyama Engr Muqaddas daman su biyu aka haifa a gidansu.
Siyama da Nihal suna tsugunne a tsakiyarsu an yi musu da'ira, tun ma baa saka su ba, da kansa suka yi kneel down suka daga hannu sama su na makerketa. Kwakwalwarsu tuni ta hango musu gadon asibitin da zaa kaisu nan da 'yan mintuna talatin. Wani lokacin kuwa cikin kabari kawai suke hangowa domin da alama zasu yi kwanan farko a labari yau. Gafara kawai zuciyoyinsu suke nema a wajen Ubangijinsu. Musamman idan sun kalli gaftara gaftara takalman da su ke kafar sojojin nan da 'yan sanda . Mu'awiyya dan jarida har ya fara daukarsu a hotuna yana jotting din muhimman bayanai . Wani sharbeben belt suka hango a hannun Conel Muhammad .
" Daman mutum yana sanin ranar mutuwarsa?" Siyama ta radawa Nihal .
Nihal ta gyada kai ta ce " gashi kuwa mu mun Sani. "
Zafafan hawaye ya fara kwaranya daga idanuwansu.
Kowa na zaune an yi carko-carko, shin da addua zaa bude taron nan ko da ashar? Oho.
General yayi gyaran murya sai Nijal da Siyama suka dauki kuka suka rungume juna.
Major Abubakar ya daka musu tsawa ya ce "ku saki juna ku wawware, ku matsa." Jikinsu na kakkarwa, su ka marmatsa.
Geberal ya kira sunan Siyama cikin tsawa da furgici "Siyama Abba! Tashi tsaye ki bamu labarin abinda ya faru bayan mun kaiku London karatu mun juyo da ni da iyayenki?
Siyama ta miqe tsaye jikinta na rawa ta fara magana cikin karkarwar murya ba tare da an gane yaren Hausa ko na turanci take yi ba ."
Asp Aliyu ne ya taso a fusace " Ya fisgo ta ya dire ta a tsakiya gami da yi mata tsawa " yar rainin hankali kin fi kowa Zakin murya idan kika sami gulma. Za ki yi yaren da zamu gane ko sai na harbe ko?"
Ta dora hannu aka ta kwalla ihu da kuka, kira take "Wayyo Ummata ki taimake ni ."
Zafafan hawaye ne ya fita daga idanuwan mahaifiyarta don tausayin 'yarta mace kwaya daya tal kuma 'yar auta, amma a yau ba zata iya taimakonta da komai ba sai addua .
Siyama ta ce " Na cewa Nihal kada ta yi amma ta yi, kuma zan fada ta bani amana ta ce kada in fada."
Su Muhammad su dukka su ka hada baki " me Nihal din ta yi ?"
Muryarta na rawa ta ce " a tambayi Nihal sai da na hana ta wallahi ."
Major Muhammad Ya zabura ya taho da sauri da belt a hannunsa zai taya ta amsa tambayar da ta kasa bayarwa, kai tsaye Siyama da Nihal suka makale juna su na ihu. "
Professor Shatu ta fusata " ta dakatar da Major ta ce " kada ka taba su, ku na tsorata su, ku bari su amsa tambayar da ake yi musu mana kafin ku hukunta su ."
General ya ce Siyama ta zauna Nihal ta tashi .
Nihal ta hau makerketa ta miqe tsaye.
General ya harare ta ya ce "fadi da bakinki abinda kika aikata a London. Ina so duk jumla daya ki saka kalmar GABA GADI a ciki ."
Sai aka hau kallon-kallo a junansu. Saboda rashin fahimta kalmar.
General ya gyara zama ya ce "Nihal Nuren wanne course Daddy da Mummy su ka ce ki je London ki karanta.?"
Cikin rawar murya ta ce " GABA GADI Medicine suka ce in karanta. "
General ya gyada kai ya ce "sai aka yi yaya? Ki bamu labari ."
Nihal ta kalli fuskokinsu har tsuma suke kowannensu yana so ya ji karshen labari.
Nihal ta sunkuyar da kai ta ce " GABA GADI sai na canja course. "
Wasu mugayen tambayoyi ta ji su na jeho mata
"Ke! Har kin isa ma ki yi abu GABA GADI ? Da izinin wa ? Wanne course kika koma ?"
Nihal ta ce " GABA GADI na koma karatun Fim. "
Hohoho sai suka ji kamar zaki mai tsananin jin yunwa ya hango nama. Ji Duke kamar su jawo ta su yi ta duka.
Kan ka ce kwabo falon ya hargitse da hayaniya.General ya ce su bari ta kai qarshen labarin.
Nihal ta matse hawaye cikin firgici ta ci gaba da cewa "na gama digiri GABA GADI na wuce masters."
Ta yi shiru General ya harare ta sai ta ci gaba da cewa "GABA GADI har na fara acting din Fim, na fito a finafinai guda biyu a can."
Gaba daya aka dauki salati dukka falon domin bayan ita da Daddy sai Siyama babu wanda ya san abinda ta aikata sai yanzu kowa ya ji. Da gaske Mummy ma bata sani ba ."
Nihal ta zame ta zauna ta rusa kuka " ku hukunta ni daidai da laifina ko ku kashe ni ."
Siyama ta rusa kuka " wallahi sai da na hana ta, ban taba raka ta wajen daukar fim (location) ba . Daddy ba ruwana wallahi ."
Muqaddas ya zabura ya ce da Siyama " rufe mana baki munafuka .Tun farko da zata canja course kiyi waya ki fada mana . Ke ba kin zama pharmacist ba."
Kowannensu saga cikinsu jikinsu tsima yake, jira suke a ce kule, su ce cas su kadddamar mata .
General ya bada umarni a yi shiru sannan ya umarci Nihal ta sake tashi tsaye ta ci gaba da amsa tambayoyi.
Nihal ta miqe ta ci gaba da karkarwa . Za ta iya hango hawayen da yake rugugin kwaranya daga idanuwan mahaifiyarta . Tabbas wannan shi ya fi tayar mata da hankali. Ta yi nadama da da-na-sani dama bata yi ba.
General ne ya katse tunanin da take yi, ya ce " wanne hukunci ya dace da ke? Kin qi jin maganar iyayenki? Kin qi jin maganar 'yan uwanki. Kin qi jin maganar kasarki .
Nihal ta fada cikin sanyin murya " a yi min hukuncin da ya dace na yi laifi ."
" Ni kike so in hukunta ki ko yayyanki?."
Ta ji gabanta ya fadi ta yi sauri ta daga ido ta dube su , kowa ya dunkule hannu umarni yake jira kawai .
Ta ce " na fi son su hukunta ni , bana son hukuncinka Daddy ."
Sai mamaki ya kama gaba daya bil adaman da suke cikin falon .
" Shin me Nihal take nufi da ta ce gara kartai su dake ta, su daure ta, tsallen kwado, aikin gida, tsangwama. Kenan gara duk wadannan azabar akan hukuncin mahaifinta shi da babu duka babu zagi.
General ya maimaita " gara hukuncinsu akan nawa hukuncin kenan ?
Ta gyada kai ta share hawaye ta ce " dukana zasu yi watakila su karya ni a kai ni asibiti amma hukuncinka"....sai ta rushe da kuka .
General ya fada a shelake " kuma hukuncina ne ya fi dacewa da ke har kuma na shirya miki komai . Babu duka, babu zagi. Yayyanki ba zasu hukunta ki ba ni ne da hannuna zan hukunta ki. "
Mamaki ya cikawa kowa ciki, su ka gyara zama, ana kallonta.
General ya ce a kira masa kaka talatu, tsohuwa mai aikin wanke-wanke a gidan tun suna yara .
Ta zo ta durkusa tana karkarwa .
General ya ce da ita " Hajiya Talatu ina so ki kawo min kayan sakawarki riga da zani kala biyar ki hado har da na jikinki wannan da General daura, daman hakan na fi so ba sai an wanke ba . "
Ta fahimta amma ta kasa gane abin da yin hakan yake nufi .Haka ma 'yan wajen . Ba dadewa sai ga Talatu dauke da tsummakarai ko linki babu . Tana karkarwa ta zo ta zuba a gaban General.
Ta ce " a yafe ni dukka kayan sun yi dauda ban wanke ba "
General ya ce " na ji dadin hakan Talatu a je a samo min buhu na shikafar da ta kare."
Ya juya ya kalli Nihal ya ce ta je daki cikin kayanta sababbi leshina da shaddoji da atamfofi ta dauko kala biyar amma ya zama dogayen riguna ko riga da zani .
Ta zabura ta tafi daki da sauri jikinta na rawa . Ba jimawa Nihal da talatu suka bayyana .
General ya ce Nijal ta bawa Talatu kayan nan kamar yadda ta bata nata an yi musanya kenan ."
Nihal tana rawar jiki ta miqawa talatu. Talatu zata yi magana General ya yi tsawa ya ce ta karba kawai na ta ne ta bar cikin falon. Sai ta hau godiya ta tafi da murna . Leshina ne babu na kasa da dubo dari da hamsin sai atamfofi super Holland da shadda gezna. Lallai wannan shine gaba ta kai ni gobarar titi a Jos.
Kowa dai kansa ya daure
General ya kalli Nihal ya ce "ga sabbabin kayan da zaki dinga sakawa, ki dauki sauri daya ki ajiye a gefe, sauran ki zuba a buhu. Ki Shiga daki ki cire kayan jikinki ki saka ki fito. "
Nihal ta bude baki don mamaki da tashin hankali tana tafe tana sanda.
Kalmar nnalilahi wa inna ilaihi rajuun ta ke ambato. Ta kwasa ta hada da buhu ta Shiga daki .
Babban tashin hankalin da ya same ta ma shine yadda zata saka kayan da suke wari, sun kode hamata a yage. Duk da girman jikinsu daya da Kaka Talatu ina zata kai katuwar riga mai katan wuya? Ta ina zata iya daura zani ita da bata saba dinki mai zani ba?
"Me yake shirin faruwa ne General?" mahaifin Siyama ne ya tambaya a gigice.
Hannu General ya daga masa alamar ya dakata.
Yayin da kwakwalwar mahaifiyar Nihal ta tabbatar mata da muguntar tasa ce ta tashi . Da wani hukuncin da zai yi maka ka gwammace gara a yi ta dukan mutum har ya mutu.
Abubakar ya ce " Daddy ka bari mu casa maka ita mu daure ta kamar shekara guda ko in kaita bariki sojoji ta yi ta tsallen kwado tana noma ."
General ya Girgiza kai ya ce " ai qasusuwan Nihal ba zai dauki wahala da yawa ba ai zai gutsire. Ku zuba ido kawai ."
Nihal ce ta fito sanye da qatuwar riga da zani ga dankwali da mayafi duk da atamfa daya aka dinka. Bata iya daura zanin ba balle daura dankwali, ga buhu a hamata. General ya ce ta je bandaki ta dauko silifas kada ta saka takalmi mai tsada .
Hankalin kowa ya tashi daga ta gifta sai warin dusa da hayaki.
Ta zo ta tsaya yayin da Aliyu ya kwashe da dariya, Abubakar ya dungure masa kai ya harare shi. Hamza ma dariya ce ta kusa subuce masa shima ya toshe baki.
General ya dubi kowannesu ya ce " na kai Nihal karatu don ta zama cikakkiyar gynaecologists ta karanci bangaren mata. Mata masu mutuwa wajen haihuwa kamar yadda gyatumata ta rasu a wajen haihuwar kanwata Baraatu. Abin nan a raina na ce duk sanda Allah Ya bani 'ya mace sai ta zama likitar mata ta zo ta taimaki 'yan uwanta mata musamman ma masu ciki da masu nakuda. Na sha zaman jira sai daga karshe Allah Ya bani mace murna biyu nake yi na sami mace wacce zan saka mata sunan Mahaifiyarta zulaihat sannan zata karanci likita ta taimakawa mata musamman na karkara masu ciki. Domin a rashin kulawar likita yayi sanadin mahaifiyarta ta rasu. Nihal ta tafi da zummar cika min burina sai kawai GABA GADI ta canja course. Dan haka nima GABA GADI zan hukunta ki."
General ya yi shiru kamar mai tunani ya ce " kin karanci fim don haka babu a inda ya dace ki yi aiki sai a acting industry. Ba kiyi laifi ba da kika fara Fim a turai domin abinda kika karanta kenan . Anan ma muna matukar bukatar irinki a industry , dan haka ki zo mu je kiyi Fim din hausa don ki taimaki al'ummar kasarki da yarenki da al'adarki. "
Gaba daya kowa ya zabura yana magana yayin da Mummy ta dafe kirji ta zazzare ido.
kowa ya maimaita "Hausa Fim???"
General ya gyada kai ya ce " tabbas wasan kwaikwayo na Hausa.Dalili kuwa mu