Header Ads
Showing 42001 words to 45000 words out of 110552 words

Chapter 15 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

mota zuwa Kano, Nihal ce ta biya musu kudin motar su dukka ukun.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Jamila Umar Tanko
(JUT)


GABA GADI


A farfajiyar get su ka tsaya kowannensu zuciyarsa tafasa take huci kawai suke yi ji suke kamar qasa ba Zara iya daukarsu ba. Ji suke dama ace Nihal tana gabansu su yi ta duka, harbin iska kawai suke yi su na ta kai kawo a tsakar gidan daman kowa gwani ne wajen zafin zuciya. babban abinda ya fi damunsu shine rashin sanin takamaiman abinda ya ke faruwa. Tun kafin ma su ji abinda ta aikata, sun qudiri niyyar sai sun casa Nihal, sai ta gwammace ba ta fito a tsatsansu ba .


Abubakar ya juya ya dube su ya ce " me ku ke tunani ta aikata haka da har ya tunzura Daddy, ya firgita Siyama ta kasa fada? Ku duba ku ka biyayyar da Siyama ta ke yi min, ta san ba na son karya da boye- boye amma ta kasa fada min har ta gwammace in rabu da ita in fasa auren, har ta gwammace ta gudu ta bar iyayenta akan ta fadi abinda yake faruwa. Ba kwa ganin abin nan ba qarami abu ba ne ? "


Usman ya ce " na kasa tunano me Nihal za ta aika da har ya rikita su haka . Kalli yadda Daddy yake magana a waya har yana tuntube saura kadan ya kifa."


Mu'awiya ya ce " kalmar a kawo masa Nihal a raye ko mace ta gigita ni ."


Muhammad ya dago da jajayen idanuwansa ya dube su ya ce " kowa ya fada min me yake tunanin Nihal zata aikata da zai jawo London da Kano gaba daya ta hargitse haka? "


Aliyu ya ce " ko kirista ta zama zata auri kirista. In ba haka ba me zai sa Daddy da Mummy su shiga irin wannan damuwa haka? "


Gaba daya suka hada baki "wa'iyyazu billah. Allah Ya kiyaye ."


Hamza ya ce " ko wani ta kashe acan ? "


Su ka hada baki " A'uzubillahi Allah ma ya kiyaye."


Umar ya ce " Allah Ya sa ba cikin shege ta kunso ba . Kun san fa karatun 'ya mace a turai babu muharrami."


Muhammad ya cije baki ya daki kansa ya ce " kai haba . Muna raye kanwarmu ta aikata daya daga cikin wadannan abubuwa wallahi wallahi da kuwa da hannuna zan kashe ta kuma na kashe banza ."


Abubakar ya ce " abin dai da baa so a fada ne amma na san an yi daya daga cikin abubuwan nan da muka yi harsashe. In ba haka ba me zai tayar da hankalin Daddy da Mummy haka ?"


"Mummy fa ta san komai boye mana take yi kawai don girman laifin ba zai fadu ba." Hamza ya fada yayin da kwalla ta cika masa ido .


Muhammad ya buga qafa ya ce " daya daga cikinku ya shirya, London din zamu je mu taho da ita. Kamar yadda Daddy ya fada ko a mace ko a raye. Daga ita har kawarta Siyama zasu gwammace dama ba su taba sanin ire-irenmu ba. "


Gaba daya su ka hada baki "da ni zaa je, da ni zaa je."


Shigowar Motar mahaifinsu su ka hango, yana tsayawa ya fito sai ya gansu sun zagaye shi .


"Sannu da dawowa Dad. " Su ka hada baki a lokaci guda.


Bai amsa musu ba sai ma guzurin harara da su ka samu. Qoqari ya ke ya keta ta tsakiyarsu ya wuce.


Muhammad ya ce " Daddy muna cikin damuwa, muna so mu ji abinda yake faruwa."


Daddy ya ce " idan ta yi tsami za ku ji ." Ya wuce abinsa.


Abubakar ya zabura ya ce " Daddy mu na da haqqin mu sani don 'yar uwarmu ce ."


Daddy ya fada cikin fushi a lokacin da ya bude qofar falo ya na qoqarin shiga ya ce "babu ruwana da dangantakarku da ita." ya barsu a tsaye.


Umar ya fusata ya ce " wannan tsohon fa ya manta da cewa yanzu mun girma ne? Mun zama magidanta, mun wuce yara. Yadda yake mana hukunci da horo irin na da kamar a bariki, irin yadda sojoji su ke idan sun kama masu laifi yanzun ma haka yake so ya ci gaba da yi mana."


Muhammad a fusace ya ce " ku jira anan bari in je wajensa." ya wuce ya shiga cikin gida


Babu jimawa sai gashi ya fito a guje, su ka tare shi cikin dimuwa suka tambaya ko lafiya?


Ya na sheshsheqa ya ce " could u imagine da bindiga ya biyo ni."


Aliyu ya kwashe da dariya, gaba dayansu su ka yi kansa da tsawa " meye abin dariyar?"


Ya ce " hukuncin Daddy ne ya fara ba ni dariya ma."


Wannan karon Abubakar ne ya juya da sauri ya shiga cikin motarsa ya fice.


Muhammad ya dubi sauran ya ce "kowa ya tafi, mu hadu gobe da sassafe a babban falo."


Ya na gama magana ya shiga motarsa ya fice .


Mu'awiya ya bi bayansa shima a cikin motarsa. Yayin da sauran su ka nufi bangarensu domin kowannesu ya na da ginin gida a cikin gidan .


Toh fa! Kwamacala kenan . Tabbas Nihal ta yi gaskiya da ta ce gara ta shiga kasashen masu qananan idanuwa ta bace, gara kada a cikin ruwa ta cinye ta akan ta tunkari hukuncin da wadannan za su yi mata.


Major Abubakar ya kira Engr Muqaddas a waya, Muqaddas ya shaida masa su na filin jirgi har yanzu su na jiran isowar Siyama. Domin sun saka wasu ma'aikatan immigration na Airport din Abuja su hana ta shigewa. Har ma an yankar mata tikitin juyowa kano.


Abubakar ya shaida musu gashi nan zuwa Airport din shima zai jira isowarta.


Asuba ta gari Siyama Abba Muse !!!


Sun hallara da sassafe kamar yadda yaya Babba ya umarce su. Kafin su fara magana fitowar mahaifisu janye da akwatin kayansa ne ya katse musu hazari. Kowa ya bude baki ya na mamaki.


" Daddy ina kwana." su dukka su ka hada baki. Gami da tasowa da sauri kowa yana so ya karbi akwatin da yake ja.


" ku matsa ku bar min akwatina." Ya fada yayin da yake qoqarin ficewa daga falon .


A baya su ka biyo shi ba tare da kowa ya iya qara furta wata magana ba. Habibu direba ne ya iso da sauri ya karbi akwatin ya saka a but gami da bude masa gidan bayan motar, ya shiga ya zauna .


Muhammad ya qaraso da sauri ya riqe qofar motar ya dukar da kai ya ce "Daddy mun yanke shawara mutane biyu daga cikinmu zamu je London mu dubo halinda Nihal ke ciki . "


"Ka da a kuskura a ayi wannan tafiyar, ban saka ku ba. "


"Daddy yanzu ina za ka je? Ko London din za ka bi ta? " Hamza ya tambaya.


Harara ya wurga musu ya ja murfin motar ya rufe ya ce da Habibi " Ja motar mu tafi please , suna bata min lokaci."


Kowa ya sanqare a tsaye ya bi bayan motar da kallo . Ransu ya sake baci tabbas, a zuciye Conel Muhammad ya juya ya nufi cikin gida sai su ma suka bi bayansa kai kace kaza ce da 'yayanta. Bai tsaya a ko ina ba sai a bakin qofar dakin Mummy .


Ya fara bugawa har wasu daga cikinsu su ka taya shi bugun amma bata bude ba.


" Mummy ki na da labarin Daddy ya yi tafiya yanzu? Ya fada miki kuwa? " Abubakar ya tambaya.


Sun cika da mamaki da su ka ji ta basu amsa. " Eh na sani ."


Suka hada ido cike da mamaki .


"Ina ya ce miki zai je?" Umar ya tambaya.


Mummy ta ce " ban sani ba ."


Muhammad ya cije baki ya sunkuyar da kai qasa kamar mai tunani. Sannan ya dago da jajayen idanuwansa ya dubi 'yan uwansa.


Ya ce " ku bar ta kawai . Da alama fushi su ke yi da junansu."


Mu'awiya ya ce " kin ci abinci kuwa? Ko In kawo miki tea?"


Wannan karon bata amsa ba, kuma bata sake amsa musu ba ma, har suka gaji su ka tafi .


"Me na ke gani ? Me yake shirin faruwa da rayuwar Nihal 'yar auta 'ya ta guda daya da na fi qauna daga cikin 'ya'yana?" Zuciyar Mummy da Daddy ce ta fada a lokacin da kowannensu ya shiga tunani.


BAYAN KWANAKI BIYU
Da misalin qarfe hudu na yamma, motar General Nuren Mubin ce ta kutso cikin farfajiyar gidan.
Bar.Usman da Dr.Hamza ne kowannensu ya daga labulen wundo yana leqe daga bangarensa. Bayan General ya fito, sun cika da matukar mamaki a lokacin da suka hangi Nihal Nuren na biye da shi a baya, cikin matsanancin firgici ta na tafe ta na sanda. Su ka yi wuf da sauri su ka fito.


"Daddy sannu da dawowa." Su ka fada a tare.


Ya waiwayo da sauri ya ce " yauwa Hamza ku ce da 'yan uwanku ina neman kowa da kowa gobe da safe a falona. Wadanda basa gari ayi musu waya su dawo. A cewa Muqaddas ya kawo Siyama, domin zuwansu ya na da matuqar amfani. "


Cikin damuwa su ka amsa masa, yayin da harararsu ta dira akan Nihal sai ta zabura ta qara sauri a tafiyar da take. Kallo daya zaka yi mata ka san a firgice take kuma a wahale. Ba ka iya hango kwayar idanuwanta saboda kumburin fuska.


Habibu direba ne ya zo giftawa ya na janye da manyan akwatunan Nihal har guda uku. Daga nan su ka tabbatar ta qauro gaba daya.


Usman ya tambayi Habibu direba daga "London ku ke?"


Habibu ya ce " A' a a Abuja mu ka jira isowar Nihal Autan Daddy."


Usman ya kalli Hamza, Hamza ma ya dube shi su na cikin damuwa.


Usman ya ce " ban ga alamar ciki a jikinta ba fa."


Hamza ya ce "daman waye ya ce lallai-lallai ciki ta yi? Mu jira goben mu gani. Zo mu je mu kikkira su a waya, domin Conel yana Lagos, Major ya na Kaduna , Asp Aliyu ya tafi Abuja. A ce duk su juyo su dawo gida kenan."
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 馃グ馃グ


GABA GADI


NA


JAMILA UMAR TANKO
(JuT)


Idris ya ce tunda ka na tausayinta ka na so ta daukaka kada ka qara mata kudi, kawai ka sami wani Fim da zaa haska ta sosai ta fito a santa kaga ai ka bata tukuici da shi."
Abbas ya yi shiru na dan lokaci ya ce "kuma haka ne fa, idan kudi ne za ta kashe lokaci daya amma wannan taimako ne na har abada. Akwai Fim din da zan fara shooting kwanan nan kawai zan saka ta a ciki ta zama Jarumar fim din."
Idris ya girgiza kai ya ce "ka cika gaggawa kada ta zama Jaruma gaba daya ma dau bata roll din da zata taka a ganta sosai ko da a qawar Jaruma ma zata iya fitowa kaga zaa hasko ta sosai nan gaba sai ta haye kujerar Jaruma."
Abbas ya ce " me yasa ka ke jin tsoro akan Nijal? Ni kuwa sai zuciyata take bani cewar yarinyar nan fa zata karbu, alamaunta na gani. Ta na da wayo, ga nutsuwa ga, iya magana."
Idris ya ce "ka dakata dai ka bi abin a nutse step by step. Zaa zo wajen a hankali."
Abbbas ya yi ajiyar zuciya ya ce "haka ne, Allah Ya kai mu."


*** *** ***
Nihal da Hashim da Najaatu ne ke zaune akan kujerun roba a farfajiyar gidanta da yamma su na shan rake. labari suke su na ta tuntsira dariya.Hashim ya dauko labarin su Mami Harka da yadda yanzu baqin ciki ya ishe su akan Nihal ta zo ta fi su yin suna da farin jini a fim.Najaatu ta na taya shi su ka dinga maganar. Sai yanzu ma Nihal ta ji cewar Amina 'yar kwalisa ta yi rantsuwa in har ta na raye Nihal ba za ta taba zama super star ba.
Abin mamaki ko uffan Nihal ba ta tanka musu ba, ta ci gaba da shan rakenta. Su Hashim su ka cika da mamakin game da wannan al'amari.
Najaatu ta kalle ta ta yi dariya ta ce " wai! wa ya ga ban san ana yi ba kin ja bakinki kin yi shiru kin bar mu mu kadai mu na babatu."
Nihal ta yi murmushi ta ce "wannan shine cin naman mutum ayi maganarsa a bayan idanuwansa bam saba ba kuma ba na yi. Na fi gane in tari mutum gar da gar in fada masa laifin da yayi min."
Cikin sanyin jiki Najaatu ta gyada kai ta ce " haka ne wallahi kin fi mu gaskiya."
Nihal ta ci gaba da cewa "da sun gane ma da sun daina gasa da ni dan ba abinda ya kawo ni ba kenan. Na yi biyayyar mahaifi na zo in cika aikina in tafi ne kawai."
Najaatu da Hashim dai basu fahimce ta ba kuma basu tambaye ta qarin bayani ba.
Ta kalli Hashim ta juya ta kalli Najaatu ta ce " abinda ya sa ku ke ganin kamar ba kwa samun nasara a harkar nan saboda kawai ba ku nemi albarkar iyaye ba ne. Ba ku fito da yardarsu ba dan haka ba ku sami addu'arsu ba. Da kun gane da kun je kun nemi izininsu idan sun qi amince ku hakura kawai. Hashim! Inna ta ce a boye ka shiga fim ka na yi mata karya kullum har sai da fim dinka ya fito a gari aka ganka a ka fada mata.Inna ba ta fara yin farin ciki da sana'arka ba har sai bayan da na hadu da kai ta ce min in har haka 'yan fim su ke da sanin darajar dan adam da taimako ta amince Hashim ya yi fim. A gabanka ta fada ko? Alhamdulullah yanzu za ka fara ganin hasken abin. Gyara daya da na ke so ka sake gyarawa shine ka yi amfani da damar da ka samu ko min yaya dai ana biyanka, idan ka yi fim to ka kula da tsofaffin nan sosai.
Najaatu! ke gaba daya ma ba ki shigo da yardarsu ba, babban tashin hankalin ma da kika ce gudowa kika yi baa san in da kike ba ma yanzu. Su na can su na kukan zuci da kukan sarari. Wannan bala'in kadai da kika jefa su ya isa ki dinga ganin takaici da wulaqanci. Babban abinda ya bata masana'antar fim kenan ake ganinmu watsatstsu shine na farko, a ta sigar da muke shigowa harkar. Yawanci za ka ga a sanadiyyar auren dole shikenan sai yarinya ta gudo a matsayin ta shiga duniya ta lalace sai ta fado fim ma'ana fim shine qarshen lallacewa alhali ba hakaba ne. Idan mijinki ya sake ki sai ki fado fim shine qarshen cewa kin girmi aure."
Najaatu da Hashim su ka zurawa ma ta ido, kansu ya daure ganin yadda take bayani kai kace karantar abin ta yi. Sannan ta manta itama talauci ne ya ishe su ta fito yin fim din.
Sai can Nihal ta tuna ashe fa ita baqauyiya ce marar ilimi, sai ta ja bakinta ta tsaya.
Najaatu ta yi ajiyar zuciya ya ce "duk abinda kika fada gaskiya ne. Ni yanzu ki bani shawara menene abin yi? Yadda mahaifinna ya tsani fim ba zai taba bani izini in yi fim ba, haka mahaifiyata ba za ta yarda ba. In sun ji labari ma na fara fim watakila su hadiyi zuciya su mutu dan baqin ciki. Ga babban laifin da na aikata sun bani miji na qi yarda, babban laifi da na yi musu shine da na gudo na shiga duniya. Duk duniya babu wanda zai yarda da cewa ba karuwanci make yi ba." Sai ta fashe da kuka.
Nihal ta shafa bayanta kamar yadda ake lallashi yaro ta ce " kada ki yi kuka, har yanzu ba ki makara ba . Zan baki shawara mai bullewa insha Allah."
Najaatu na jin haka sai ta tsagaita da kukan ta dago da sauri ta kalli Nihal ta ce " ta ina zan fara?"
Nihal ta ce ki shirya ki zo mu je garinku ni zan yi musu kalaman da za su yafe miki kuma su janye maganar yi miki auren dole."
Najaatu ta ce " amma ko sun yafe min ba zasu taba bari na in dawo fim ba, ni kuwa a rayuwata babu abinda na fi so irin in yi fim."
"Sai me in sun hana ki kiyi fim? Sai ki yi zamanki a gida tare da su har sai sun fahimce ki a hankali. Idan su ka qi daman kin yi karatun sakandire, ki koma makaranta kawai ko NCE ki yi. Laifinsu daya auren dolen da su ka yi yunkurin yi miki domin baya cikin tsarin addini da al'ada duk da na san ba zasu zabar miki abinda zai cutar da ke ba. Kuma da kin yi biyayya kin bi zabinsu sai ki

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads