Showing 45001 words to 48000 words out of 110552 words
Chapter 16 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
ga haske a cikin auren."
Hashim ya ce " har yanzu ina nazarin maganar da kika fada min. Gaskiya ne daga lokacin da kakannina su ka ce sun amince da yawun bakinsu in yi fim daga sannan na fara ganin haske da kudi hankalina ya kwanta na daina fargaba, haka da kika ce in dinga kula da cinsu wallahi tun daga lokacin na ke ganin albarka. Gaskiya mun gode da zama da ke, muna qaru sosai."
Hashim na rufe bakinsa sai su ka ji hayaniya a qofar gida muryar mata da maza da qarar tsayuwar motoci. A guje Hashim da Najaatu su ka fita amma Nihal ta qi fita, sun dade a waje su na kallo.
Hashim ya shigo a gigice ya ce "Nihal ki taso ana rigima a kanki har da 'yan sanda."
Ta dube shi sororo kallo na rshin fahimta. Ya ci gaba da cewa su Mami harka ne su ka biya wasu 'yan daba su dake ki, ban san yaya aka yi ba 'yan sanda su ka ji labari su ka damqe samarin su kuma su ka tonawa su Mami asiri."
Nihal ta yi shiru ta na tunani tabbas Shagali ya fada mata cewar Babanta ya biya 'yan sanda su na bibiyarta su na gadinta.
"Allah gatana. Ya Allah Ka ci gaba da kare ni.Ka dubi kyakykyawar zuciyata." Nihal ta fada a lokacin da ta miqe tsaye ta shige falonta.
Hashim ya zabura ya ce "ina za ki je kuma? Ki zo mu je waje ki ga ganewa idanuwanki."
Ta bashi amsa ba tare da ta juyo ba "me zan je in gani. Abinda na sani shine ina addu'a kuma ina da kyakykywar niyya akan kowa. Ko an neme ni ka ce ba na nan kawai."
Sai washegari da safe Nihal ta amsa kiran 'yan sanda ta je ofishinsu a inda aka garkame Mami, Amina 'yar kwalisa da Iyantu bisa zarginsu da biyan 'yan daba da su zo gida su dake ta. Daya daga cikinsu ne ya tuna da cewa Nihal ce ta taimake shi da kudi a lokacin da ciwo ya kusa kashe mahaifinsa shine ya kai qara wajen 'yansanda asiri ya tonu. Bayan da aka yiwa Nihal bayani aka tabbatar mata zaa kai maganar kotu sai ta ce ta yafe kada a kai su kotu sai dai a rubuta statement a tsakaninsu duk abinda ya same ta nan gaba su ne. Su Mami ne aka fito da su daga bayan kanta sun galabaita Kumar Nihal suke ji babu wacce ta iya hada ido da ita. Dole 'yan sanda suka sa suka durkusa suka bawa Nihal hakuri haka su ma 'yan dabar da suka so yin aika aika suka yi nadama gami da alkawarin ba zasu sake yi ba.
Bayan sun fito ne Najaatu ta yiwa su Mami tatas ta tuna musu cewar ta sha fada musu akan Nihal zasu ji kunya dan ita bata da mummunar niyya akan kowa. Hashim ma ya cashe musu yayi musu tatas.
Babu wacce ta iya tsayawa ta basu amsa dan kada jamaa su taru aji aika aika da suka tafka amma tuni magana ta cika gari kowa ma ya ji kuma ana ta Allah wadai da su.
Tukur da sauran abokansa daraktoci sun ji labarin abinda aka so a yiwa Nihal sun yi Allah wadai da su kuma sun kudiri niyyar ba zasu sake saka su a fim dinsu ba sai kowa ya ji shaawar Nihal ta yi masa fim , wannan al'amari ya sa mutanen gari da masu shirya fim sun qara kaunarta. Allah kenan.
Aiki ta ko ina kullum Nihal Hashim da Najaatu su na kan aiki daga sun gama wannan sai su Shiga wancan. Nihal ce kuma tauraruwa a kowanne fim. A jajjere sai da tmsuka Finafinai biyar babu qaqqautawa kuma sun sami kudi sosai hakan kamar darajarta da tsadarta ne ya karu.
Kudin yana hannun Hashim Nihal ta kalle shi ta ce nawa ne kudinmu gaba daya ya ce ce kudina dubu ashirin na Najaatu dubu sha takwas na ki dubu hamsin da biyar."
Ta yi shiru zuwa wani lokaci ta ce " gaba daya idan aka hada ya kama dubu Casa'in da uku kenan."
Hashim da Najaatu suka hau murna.
Najaatu ta ce "sai kawai mu kama gidan haya tunda nan aro aka ba mu ko da yaushe zasu iya zuwa su tashe mu. Hashim ya ce ai idan Zaa kama gida sukutum rabin kudin ya tafi gara dai ku kama daki daya dubu ashirin ko sha biyar."
Nihal ta ce " Hashim ka ware dubu ashirin ka kaiwa Inna da Baba su yi cefane. Ka ware dubu ashirin Zaa kaiwa iyayen Najaatu. Dubu goma zamu yi kudin mota mu kai Najaatu garinsu. A ware dubu ashirin a siyo kayan abinci da su omo da sabulai. Ka dauki dubu goma ka bawa Najaatu dubu goma."
Najaatu da Hashim suma sororo kansu ya daure gaba daya amma tana gama fada ta shige daki ta datse ta ce kanta yana ciwo zata dab yi bacci rana.
Najaatu ta kalli Hashim shima ya kalle ta, mamaki a cike a fuskarsu. Najaatu ta ce " wannan wacce irin mutum ce? Ta fara bani tsoro fa kamar ba mutum ba ce normal irin mutane ba. Na kasa gane halinta. Aljanu ne fa aka ce basa kashe kudi ko dai ba mutum ba ce aljana ce ta shigo cikinmu?"
Hashim ya yi dariya ya ce "wallahi haka take na rasa me yasa bata son kudi kuma ga talaucin da iyayenta ke ciki ta qi ta tuna da Babanta ta yi masa aike ko ta je ta kai musu kawai sai ta rabar da duk abinda ta samu. Ya zu haka dan Tukur baya nan aka biya ta kudin nan da shi zata bawa ko ta ci karo da almajirai kawai sai ta miqa musu dukka.
Mu yinyadda ta ce kawai in ba haka ba wallahi kwashewa zata yi ta rabar idan muka qi."
Najaatu ta ce " ina tsoron in koma garinmu a hana ni dawowa da na fara jin dadin rayuwar Fim haduwa da Nihal da kai."
Hashim ya ce "ki yi abinda ta fada miki kawai na yarda da kaifin tunaninta kuma tana da ilimin addini sosai."
Jikin Najaaatu a Sanyaye ta tashi ta raja Hashim gidansu ya kaiwa Inna naira na dukan Naira jar dubu ashirin ya so ya rage ya basu dubu goma Najaatu ta ce ya basu dukka idan Nihal ta bincika ta ji bai basu dukka ba ranta zai baci. Inna ta fara tsuma hannunta na rawa ta karbi wadannan makudan Kudi kamata a mafarki. Tambayar da ta yi shine " Nihal ce ta ce a kawo min ko ?"
Su ka masa mata da "Eh ita ce sai ta rusa kukan dadi ta dinga kwararo mata addu'a da fatan alkhairi marar adadi. Haka tsoho ma ya taya ta yana gefe yana addua har da hawayen dadi.
*** *** ***
Bayan kwana biyu ne su Nihal su ka shirya tafiya garin Darazo gidan su Najaatu wajen iyayenta domin neman yafiyarsu da kuma yardarsu akan wannan sana'a.Hashim dai an yi masa dole ne kawai ya shirya binsu amma ba don son ransa ba. Ya na ganin kamar wannan shishshigi ne abinda bai shafe su ba ne ta shiga ta yi kene-kene.
Da sassafe su ka shirya su ka fito zuwa tasha, sun ci saa kuwa su ka sami mota har garin. Sun isa kafin azabar kwatsam 'yan unguwar su ka ga Najaatu kafin su qarasa gida labari ya kaiwa iyayen Najaatu sai kowa ya tanadi taryarta.
Tsoro Najaatu take ji a bayan Nihal take ta maqale yayin da Nihal take bata qarfin zuciya tana tunano mata addu'oin da zata yi ta fada a lokacin da masifa da fargaba ta tunkarowa bawa.Nihal ma Addu'ar take yi Hashim yana ta ya su. Ya ja ya tsaya a qofar gida yayin da Nihal ta fara saka kai a ciki gidan ta yi sallama ta shiga. Aka amsa mata sallama a shelaqe. Gidan yawa ne iyaye da kakanni da facaloli waje-waje sai firfiryowa suke yi ana so a ga yadda Mahaifin Najaatu zai yi da ita.
Babu wanda ya basu wajen zama sai kallo sama da qasa ake yi musu.
Najaatu ta radawa Nihal ta ce kin ga abinda nake gudu ko? Shikenan yau na mutu dakyar in basu kashe ni ba dan duka."
Babu mai dukanki ki kwantar da hankalinki." Nihal ta fada cikin qarfin zuciya.
Nihal ta tambaya " ina iyayen Najaaatu? Wajenki na zo ko zaku bawa bakuwarku tabarma ta zauna ku saurari saqon da na zo mu ku da shi?"
Ba ki da wajen zama a gidan nan kun je kun gama watsewarku acan me zaku ce mana? Ai mun ganku a fim." In ji ganin mahaifinta Najaatu Najaatu su na Sa'idu.
Nihal ta yi murmushi ta ce " Alhamdulullah da Allah Ya sa har kun san inda 'yar ku take. Najaatu ta yi kuskure bata kyauta ba ko daya. Hakan ya sa na kawo ta da hannuna don ku hukunta. Tun daga ranar da ta shaida min ta zo ba da yawun iyayenta ba na kudiri niyyar sai na dawo da ita gida kun hukunta ta."
Nihal ta jawo Najaatu ta turo ta gaban iyayenta sai Najaatu ta durkusa ta fashe da kuka.
Nihal ta ci gaba da magana cikin sanyin murya zafafan hawaye na kwaranya daga idanuwanta. Ta ce "ku dake ta ku kakkaryata idan ta ji ciwo ku zaku kaita a asibiti idan kuma ku ka kashe ta ku ne dai zaku dauke ta ku binne ta bata da kowa a duniya kamar ku. Idan ta zama ta gari da sunanku Zaa kira ta idan ta lalace da sunanku Zaa kira ta. Jini ba wasa ba ne. Kullum dan adam me laifi ne a wajen mahaliccinsa amma kullum Ya na yafe mana. Ya kamata ku yi farin ciki da ganinta ta dawo kuma duk wani qasqanci da yake samun bawa daga makusancinsa ne. Najaatu ba karuwa ba ce bata ma taba yin saurayi ba tun tafiyarta tana can Kardashian kulawar masanaantar fim. Idan aka ce 'yan fim ba ana nufin sai karuwai ba irin wannan kallo ake yiwa duk wata 'yar fim wannan ba daidai ba ne. Idan ku ka zargi yar ku da cewa ta Shiga fim ta iskance haka jamaar gari zasu dauka kuma idan magana ta fita babu yadda zaku taro ta sunanku ku dukka ya baci. Ku ti mata uzuri dalilinku ta fita aka rasa ta . Me yasa ba Zaa bar yarinya ta zabi mijin da take so ba me yasa Zaa yi yunkurin yi mata auren dole? Iyayen da su ke tilastawa yaransu aka sai sun aikata abinda basa so sukan jefa yaran a cikin matsala. Na kawo muku Najaaatu 'yar ku ko ku karbe ko ku sake nemanta ku rasa kada ku ga laifinta idan ta sake guduwa saboda ukuba. "
Nihal ta turawa Najaatu akwatin kayanta ta ce " ki zauna da su ki basu hakuri ki bi wancan shawarar da na baki . Ni zan tafi na barki lafiya ."
Najaatu ta zabura ta kama hannu Nihal ta ce "jada ki tafi ki bar ni ba ki tsaya kinga yadda za su yi da ni ba."
Mahaifin Najaatu ne a fusace ya yi magana " Najaatu dauki akwatin kayanki ki bi ta ku je can ku karanta na sallama ki."
Mahaifiyar Najaatu ta yi carab ya kama hannun 'yarta ta ce " mun Sami ta dawo babu in da zan bari ta sake tafiya sai dai ka kore mu tare ." Ta ja hannunyar ta suka shige daki. Dadi ya kama zuciyar Nihal ta share hawaye ta yi murmushi ta ce Alhamdulullah ta fice ta bar su a tsaye sororo. Sai a lokacin su ka fara magana kowa yana fadar albarkacin bakinsu. Wasu fada su ke yi me yasa Zaa karbi Najaaatu wasu kuma su na fadin maganar Nihal gaskiya ne hannunka ba ya rufewa ka yanke ka zubar.
Ta fito ita da Hashim suka dunguma zuwa tasha domin komawa garin Wudil. Hashim yana ta jero mata tambayo Alan abinda ya faru da alama bata son yin magana abinda yake damunsa shi yake damunta. Ta ce masa ya bari zata bashi labari daga baya.
Su na zaune a mota sai wayar Hashim ta yi qara yana dubawa sunan Darakta Abbas ne ya bayyana nan da nan ya amsa cikin garin ciki. Bayan sun gaisa tambayar da yayi shine ina Nihal?
Hashim ya miqa mata waya da sauri gami da fada mata suna mai kira.
Nihal ta yi sallama ta gaishe shi amma tana cike da mamaki da zumudi son jin dalilin kiran. I.sha Allah ta san alkhairi ne.
Abbas yana mai farin cikin sanar mata zai fara daukar wani babban fim kuma yana yi mata Albishir da cewa zata fito a matsayin Tauraruwar shirin gaba daya."
Sai ta yi hamdala ta yi godiya. Ya ce in da hali ta shigo kano yanzu don su tattauna.
Ta sanar2a da Hashim abinda ya fada sai suka bawa masu mota hakuri suka fita suka canja mota mai zuwa Kano.
Hashim da Nihal su ka cika da murna sai dai Hashim yana tsoron yadda zata kaya tsakaninNihal da Adnan gaba jaruman birni su Aisa Buzuwa. Amma ya lura Nihal ko aikinta bata kawo wannan a ranta.
Ya kalle ta cikin sanyin jiki ya ce " tsorona daya su Aisa buzuwa ba sa kaunarki. "
Ta kalle shi ta yi dariya ta ce " baba fargabar hakan karka damu na shirya musu."
Kan Hashim ya sake daurewa sai ya bi ta da kallo kawai a ransa yana fadin na yarda da basirarki da jarumtarki Nihal Nuren Mubin.
Sun isa kano unguwar zoo road lafiya. A bakin ofishin Abbas idanuwanta su ka yi mata kicibus da a abinda ya firgita ta ya yamutsa tunaninta. Ta yi turismo ta tsaya gami da ja da baya da sauri ya dafe kirji.
Kalmar innalilahi wa inna ilaihi rajuun ta ambato yayin da tsakar jikinta ta tashi jikinta ya dauki karkarwa. Hashim zo mi juya Wudil na fasa shiga." Tambayar ta yake " Nihal wai meye? Me yake faruwa ? Me kika Hango? Amsa daya ta gagari fita daga bakinta. Tabbas razana ta kai kololuwar razana gaba daya ya fita hayyacinta.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI
Na
Jamila Umar Tanko
(JUT)
Da su ka isa unguwar zoo road sai Hashim ya kira Darakta Abbas a waya sai ya fada masa inda za su tsaya, zaa zo da mota a dauke su.
Ba jimawa wata mota qirar Honda civic ta zo ta dauke su, direban bai tsaya a ko ina ba sai Tiga kwanar dawaki.
Sun isa wajen sun iske dandazon mutane ana tsaka da daukar shirin.Nihal na dosar wajen abinda kunnuwanta su ka fara jiyo ma ta shine.
"yau ma tsinanniyar 'yar qauyen nan su ka sake kwaso mana." Aisa buzuwa ce ta fada.
Yayin da dukka 'yan matan da su ke zaune da ita su ka juyo su ka kalli Nihal.
Tafiya su ke yi cikin sanyin jiki kasancewar sun shigo cikin wata duniya da baa qaunar ganinsu.
" wannan ce wannan me tsallen?Jin ta ya fi gabinta."
Wasu samari ne su ke gulma, maganarsu ta gangaro ta fado cikin kunnuwan su Nihal.
Har yanzu dai tafiya su ke su na kutsawa cikin jamaa, fatansu su isa wajen Darakta Abbas wanda su ka zo dominsa.
Su ka ci karo da Bash Auta da su ka gaishe shi sai ya amsa dakyar cikin rashin sakin fuska, ya wuce abinsa kamar bai taba saninsu ba.
Nihal ta isa in da Darakta ya ke zaune, ya na ganinta ya zabura ya miqe cike da murna.
"Yauwa zo nan Nihal." Abbas ya fada .
Su ka koma gefe ya na yi mata bayanin abubuwan da ake so ta yi.