Showing 72001 words to 75000 words out of 110552 words
Chapter 25 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
tunda yanzu kowa zai santa. Tausayin qunar zucin da aka dasa akan zuciyar masoyanta sai itama ta fara hawaye. Aka rasa wanda zai lallashi wani a cikinsu.
Abbas ne ya dira a gabansu, gaba daya suka dago da jajayen idanuwansu cike da hawaye suka kalle shi. Nan da nan hankalinsa ya tashi tabbas ya san komai.
Hawaye ya cika masa ido shima amma sai ya daure ya hana shi zubowa.
Ya ce "Nihal sai kun yi haquri sosai wannan ita ce alamar nasara, babu wanda ya taba zama wani abu ba tare da ya sha wuya ba. Ina mai yi miki albishir da samun nasarar da daukaka a cikin wannan harka. Ku tashi mu shiga cikin gida, ku hado kayanku ku fadawa sauran kowa ya shirya nan da awa daya zaa kawo motoci zaa tafi garin da zaa yi shooting."
A sanyaye su ka tashi su ka shiga cikin gida, daman sun yi wankansu tun da asuba, kayansu ma a hade yake, suka sanarwa da sauran sakon Abbas. Sai suka fara yin gaba, su ka fito su na jira a qofar gida.
Hashim ya ce "yunwa nake ji, gashi basa karbar Naira."
Nihal ta bude jakarta ta dauko 'cefa' ta miqa masa ya karba ya tafi wajen me shayi ya hado musu indomi da kwai da shayi ya kawo su ka yi ta ci, har da wasu ma sun samu saboda ashe kudin da ta bayar me yawa ne. Ba su ma san yawan kudin ya kai haka ba sai bayab da suka ga himilin abincin sannan su ka tantance me yawa suka miqa.
Sai kowa ya cika da mamaki idan aka ce Nihal ce ta biya kudin abincin da mutane sama da goma suka ci su ka qoshi.
" Yanzu wannan bakauyiyar, talakan ce ta iya biyan wannan kudin?" Mutane ne a gefe suke gulma, kasancewar duk an firfito qofar gida.
Motocin ne suka iso, sai kowa ya d'uru a ciki, aka fara tafiya cikin qauyuku cikin sahara. Nihal ta waiga ko ina ba ta hango motocin manyan jarumai ba, ta san dai daga hotel dinsu zasu taho. Nihal ta na ta addu'a Allah Ya sa a ba ta roll din da za ta hau raqumi ta yi rawani ta yi tafiya a sahara. Irin wannan al'adu na gargajiya turawa su ka fi so. Tabbas in har ta Samu ta yi zata sami daukaka in har fim din ya fito su ka samu labarin itace.
Su ka iso wajen daukar shirin, lallai Abbas ya kashe kudi sosai, gini ya yi na gidajen sarauta. Ga buzaye nan 'yan qasar sun hallara da rakumansu da kaya irin nasu jaka-jaka. Abbas ya ba ta tausayi yadda ya kashe maqudan kudin nan, Allah Ya sa a yi ma sa abinda yake so. Dan ta lura da yadda wasunsu suke yi, ba sa mayar da hankali su yi acting yadda ya kamata kamar da gaske ba sai a tsaya ana ta wani jan aji. A qa'idar fim ana so idan kai mahaukaci ne ka nuna hauka tuburan, idan kai wawa ne ka yi wawancin sosai.
Aka ce su bar kayansu a cikin motoci duk su firfito, Nihal na fitowa da hararar basawan qauye ta ci karo wato Tukur da tawagarsa. Gaban Hashim ya yanke ya fadi sai ya zabura.
Nihal ta rada masa "ka ka sake ka nuna alamar ka ji tsoro sa, babu abinda ya isa yayi maka kuma kada ka gaishe su."
Su ka zo suka wuce ta gabansu ba tare da kowa ya ce da kowa uffan ba.
"Munafukan banza kawai." In ji Tukur.
Basu kula su ba suka wuce abinsu.
Mami harka ce ta ce "babu wacce ta fi bani mamaki ma irin Najaatun nan, a cikinmu fa take amma ta tashi ta koma cikin munafukan can dan kwadayi. Ta zaci wata tsiyar zasu bata su ma ta kansu suke, ana ta yawan neman dakin zama an kasa kama haya. An sami gida me kyau an rabe ance gidan 'yan uwa ne, ina jiran ranar da masu gidan zasu zo su koro su mu ga ta tsiya."
Amina 'yar kwalisa ta yi dariya ta ce " yau dai qarya zata qare sai mun wulakanta ta, mun gama magana da su Aisa da Halima Jabir wallahi sai ta raina kanta bata isa ta shiga fim din nan ba."
Mami ta ce " da gaske kike kun gama hada komai? Alhamdulullah Allah Ya ba mu saa, yadda ta zo haka zata koma kuwa,shegiya kamar mayya bata fushi kuma."
Duk abinda suke fada su Nihal su na ji dan a inda suka zauna babu nisa.
Nihal ta yi murmushi ta ce "bai kamata ku damu ba mu da mu ka ce min yarda da Allah ai mun gama samun komai."
Najaatu ta ce "haka ne " amma me ya sa kike bari su na zaginki su na hada miki tuggu ba kya ramawa bakya bari a rama miki? Shiyasa suke sake samun damar raina ki."
Nihal ta ce " idan mutum yana hali irin na dabbobi bai kamata kai a matsayinka na dan adam mai hankali da daraja ka biye shi ba, sai ku hadu ku zama dabbabin ai."
Sai karaf a kunnuwansu Tukur. Ashar Amina ta saki ta kalli Mami ta ce " kin ga yarinyar can 'yar qauye tana kiranmu da dabbobi?"
Tukur ya ce "ku ma banzaye ne, na ce ku bar ni da ita na san yadda zan yi da ita amma kuna bata bakunanku."
Shalele ya ce " oga da ya gama hada mata duk wani tuggu da ku ka sani tunda ya ce ku yi shiru kawai ku share."
Su ka yi shewa suka tafa su ka ce " tuba muke, sai babban Darakta.
Hashim ya zabura ya ce "kina ji ko ? Sun gama hada miki tuggu fa suke cewa, ba za ki yi fim din nan ba."
Nihal ta fusata ta dakawa Hashim tsawa sai da kowa ya zabura ya waiwayo ya dube su.
Ta ce "Hashim na ce ka yi shiru ka kyale duk wanda ya ke ganin zai ja da ikon Allah. Nihal ta dogara da Allah in har duk duniya zasu taru da niyyar su cutar da ni babu abinda zai same sai abinda Allah ya rubuta Ya qadarta zai same ni daman."
Aka yi shiru ana gasgata maganarta tabbas kowa ya san tsanar da aka yi mata ta isa. Aka ci gaba da yin qua-qus wasu na yabonta wasu na ci gaba da zaginta. Wannene ne karo na biyu da aka taba ganin bacin ranta Nihal a location, da lokacin da Amina ta mare ta sai kuma yau.
Kuma yau din ma Hashim ne ya tunzura ta. Hashim da Najaatu ne suka shiga bata hakuri, huci kawai take yi kamar wata kumurcin muciji ta tashi a fusace ta bar wajen ta tafi can nesa ta zauna ita kadai. Ta na sake zagin mahaifinta da jawo ma ta duk wadannan matsalolin.
Ta juya gefenta Abbas ta gani bayan katangar zana shi kadai a zaune a cikin yashi ya dafe kai yana jujjuyawa da alama ya na cikin masifa.
Gabanta ya fadi sai ta taso da sauri ta same shi. Sallamar da ta yi masa ne ya tsorata ya zabura ya dago da jajayen idanuwansa ya dube ta, duk iya kokarin da yayi wajen boye mata damuwarsa abu ya gagara ta kasa boyuwa.
" Darakta ka fada min damuwarka wataqila in zama silar gushewarta." In ji Nihal.
Ya dube ta har takaici ya so ya saukar masa domin maganarta kamar sab'o ce, dan bata san girman damuwar ba ne har take tunanin za ta zama silar warware ta. Abbas ya kasa fada domin ko ya fada mata wannan baqauyiyar babu abinda zata qara masa sai takaici.
Da ta dame shi da magiya kuma ya na jin nauyinta ba zai iya korar ta ba sai ya ce " Nihal na kashe kudi mai yawa akan fim din nan sai da na biya manyan jarumai rabin kudaden aikinsu sannan suka yarda suka taho. Ina iyakacin qoqarin ganin kada a sami matsala, tun jiya nake rabon fada tsakanin Bash da Bilal amma yau ma sun sake barkewa da fada. Bash ya yi post akan Bilal da su Halima cewa sun ji kunya sun kasa fitowa su qaryata kansu akan hotunanki da aka saka cewa kun shiga Restaurant kun ci abincin da baki da kudin biya. Aka yi ta zagin su Bilal a social media shine Bilal ya gani ya sami Bash suka yi fada a hotel dazu kafin su fito. Yanzu ni ina ruwana a maganar nan da zai shafe ni? Bilal ya dauke Halima Jabir sun juya kano ya ce a fada min in har da Bash da Nihal a Fim din ba za su yi ba. Dan Allah in shi ba zai yi ba ya kamata ya dauke Halima Jabir? Ita ce fa Jaruma gaba daya a fim din nan, gara roll dinsa zan iya saka Bash in ya so roll din Bash Musbahu ya hau. Yanzu yaya zan yi? Ina ta kiransa a waya yana katsewa ya qi ya amsa min. Da aka jima kuma Bash ya kira ni ya ce Bilal da Halima sun yi hatsari sun ji ciwo sosai, an kira shi a waya an ce ya je ya same su a asibitin Maradi."
"Subhanallah! Innalilahi wa inna ilaihi rajuun." Nihal ta fada yayin da ta dafe qirji.
Abbas ya ci gaba da magana hawaye ne ya fara zuba daga idanuwansa a wannan karon ya ce "Yanzu maganar a roqi Bilal ma ba ta taso ba dan har na fadawa wadanda suka isa da shi su roqe shi ace ya dawo, sun amince zasu kira shi su yi masa magana kafin su kai ga kira zasu ji mummunan labari. Bash har ya kamo hanya ya nufo nan aka kira shi da wayar Bilal aka ce ya zo waje kaza ga 'yan uwansa sun yi hadari. Ina ga shine wanda su ka yi magana ta qarshe shiyasa suka kira shi. Na ce Bash ya ranta ya biya komai ba zan iya tafiya in bar ku a dokar dajin nan ba. Ga masu raquma na dauko haya babu ruwansu daga yamma ta yi zasu tafi kuma sun ci kudinsu."
Nihal ta yi a jiyar zuciya ta sami waje ta zauna tana magana cikin sanyin murya "Allah Ya bawa Bilal da Halima sauqi, Allah Ya sa komai ya zo musu da sauki. Darakta Abbas tabbas ka na cikin damuwa kuma insha Allah babu asara a tare da kai saboda kyakykywar niyyarsa. Ka yarda da Allah ka yarda da ni. In har ka yarda zan iya ni kuwa zan yi maka abinda Halima da Bilal ba za su iya ba. Ka bani wuqa da nama ka yiwa jama'arka nasiha akan su bi duk abinda na ce su yi. Idan an yi haka komai zai tafi daidai, za ka sha mamaki. "
Abbas ya tsaya ya na kallonta cike da rashin fahimta da kokonto. "Me Nihal ta iya bare ta koyar? Ina ma zaa hada, yaushe zata iya maye gurbin Halima? Ita da ba ta iya karatu ba ta ina za ta san abinda ya kamata a ce? Ni da zan koya mata a yau bani da qarfin da zan iya kwakwazo, gaba daya ma shirin fim din ya fita a raina." Abbas ne yake tunani.
Nihal ce ta katse shi ta ci gaba da cewa " dole kokonto zai addabi zuciyarka saboda kana ganin Nihal 'yar qauye ba za ta iya ba, ba ta iya karatu ba ma balle ta gane. Ina so ka sakar min komai ni ce Darakta ni ce me jan ragama. An karance min tsaf roll din Halima in ba ka manta ba ka bani takardun kafin a canja ni a bawa Halima amma in baka yarda ba, shikenan mu koma Kano in sun ji sauqi sai mu dawo mu yi."
Abbas ya zabura ya jingina da jikin katangar zana ya ce " haba yaushe za mu jira su, har sai sun warke? Wannan filin ma hayarsa aka ba ni na sati guda, ginin kuwa na kashe miliyoyin kudi kuma ba ruwansu wa'adina na cika za su rushe. Dan ba ruwan qasar nan da na goro doka kawai suke bi. Nihal.ba ni da wata mafita ki je na ba ki wuqa da nama."
Nihal ta ji dadin amsar nan matuqa sai ta miqe tsaye ta karkade baqar abayarta da ta yi fututu da yashi. Ta ce "mu je a fara shooting amma kada ka damu da duk wani canji da zan yi daga masu yin fim din har labarin dan akwai yiwuwar a farke shi tas sannan a dinke. "
Wannan karon dubanta ya yi cikin rashin fahimta. Sai kawai aka ga Nihal Nuren da Abbas sun bullo ba tare da an ga sanda su ka tafi ba.
" Wai awannan Nihal ce can take tafiya kafada da kafada da babban Darakta, tana masa labari kamar wani sa'anta?" In ji Mami.
Amina ta ce " zuwa ta yi ta roqe shi ya saka ta a fim ai ta ji abinda Darakta Tukur ya ce ya gama hada komai ba zaa saka ta ba. Kin san fa makira ce sim-sim-sim da ita kamar wata mumina."
Tukur ya juya ya kalli su Nihal sai ya yi qwafa ya ce "ku bar ta duk ta yi ta gama kamun qafarta. Yau dai Abbas ma bai isa ba sai yadda na yi da shi, dan kayan da na kawo masa dole sai da su shirin zai tafi daidai, kome na fada masa zai yarda in ba haka ba, ba zan bashi ba zan juya da su in ya ji haka dole yayi min abinda nake so." Su dukka su ka kwashe da dariya.
Talla!! Talla!! Talla!!!
Katafaren wajen cin abinci mai suna a qasa:
'JAYROUQ CAFE'
Ana daf da bude shi.
Akan titin Court Road opp kotun Nafi'u.
Abincin zamani irin su:
Chinese fried Rice
Fried rice
Coconut rice
Jellop rice.
Source:
Chiken in sweet and sour source.
Stewed Fish
Chicken soup
Salad:
Macaroni salad
Chicken Salad
Les vagas barbecue chicken salad.
Potato salad.
Pastries:
Shawarma.
Burger.
Cakes:
Birthday cakes
Chocolate cake
Vanilla cup cakes
Red valvet cake
Mocktail:
Virgin mojito
Melonade
Lemonade
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne馃グ
GABA GADI
Jamila umar tanko
(JUT)
Su na qarasowa Abbas ya daga hannu ya ce "dan Allah a marmatso ku bani aron hankulanku nan, na zo mu ku da babban saqo."
Ma su kyamara sun fara hada kyamarori, masu kula da kayan sakawa sun fara warware, masu yin kwalliya su na ta warewa dan haka kowa ya ajiye ya taho. Abbas ya sanar musu da baqin labari cewa Bilal da Halima sun yi hatsari dan haka akwai gagarumar matsala. Sai aka dauki salati wasu na dafe qirji wasu sun dora hannaye akai.
"meye abin yi yanzu?" Tukur ya tambaya.
Nan dai kowa ya dinga kawo shawarwarin da yake ganin sun dace. Wasu su ka ce a koma Kano kawai a bari ayi wani lokaci, wasu kuma su ka ce a yi fim din kawai wasu su maye gurbinsu. Hayaniya dai ta barke har baa jin maganar wani. Sunaye barkatai ake ta kira cewar sun dace su maye gurbin Bilal da Halima amma babu wanda ya ambaci sunan Nihal ma a ciki.Tukur ya dage Amina 'yar kwalisa ce ta cancanta, da yawa su ka ce Aisa Buzuwa ce ta dace duk da bata qaraso wajen ba amma an ce ba ta cikin motar da aka yi hatsarin.
Duduwa ta baje murya ta yi gatsine ta yi fari da ido ta ce "mu kuma kashi muka yi muku a jiki da baa ambaton sunayenmu? Ko mu ba mata ba ne?"
Aka kwashe da dariya gaba daya wajen. Hankalin Abbas