Showing 84001 words to 87000 words out of 110552 words
Chapter 29 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
siya min gida? Duk wahalar da ki ke yi da kakanni bai isa ba sai da kika siya mana gida. Allah ya saka miki da gidan aljanna mun gode."
Najaatu ma hawayen dadi ne ya dinga kwaranya ta na ta ta ya Hashim godiya.
Nihal ta tabbatar musu ba za ta sake koma Wudil ba, ta dawo kano gaba daya. Daman aiki ne ya kai ta Wudil yanzu kuma ta cika aikinta. Sai jikinsu yayi sanyi su ka ji ba dadi, ta sake tabbatar musu da cewa ta bar musu dukka kayan da suke cikin gidan gaba daya. Laptop dinta ce kadai zasu dauko mata, har kayan sakawa Najaatu ta dauka ta dinga sakawa.
Jerin tambayoyi su ka sha jero mata akan su na so su san ko ita wacece amma ta gagara basu amsa ko daya. Sai dariya kawai take yi, Nihal Nuren kenan.
Baa son ransu suka bar gida me Ac ba, su ka kama hanyar Wudil da yake kowannensu ya samu zunzurutun kudin da aka biya shi na aikinsa Nihal ba ta qara musu kudin mota ba.
Sun isa garin Wudil cike da murna, an kaiwa su Inna albishir mai dadi. Dangi gaba daya sai da su ka ji wannan labarin haka maqwabta. Nihal ta sha addua domin ta dasa murmushi akan kumatun talakawa, kamar yadda ta ke da buri yi a koda yaushe.
Bayan kwana biyu su Hashim su ka tare a gidan sumunti tabbas akwai banbanci tsakanin gidan qasa da na sumunti. Ina ma zaa hada.
"Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci Nihal. Wannan baiwa mai daraja ce kuma alkhairi ce. Ku kai ni Kano in ga Nihal in yi mata godiya." In ji Inna yayin da ta sake barkewa da kuka, a lokacin da ta ji fanka ta na fifita ta akan katifa mai laushi.
Hashim da Najaatu sun zaba celebraties sai Daraktocin wudil ne ke kawo musu hari, su na so su yi musu fim. Hashim ya fara tantama an ya zai sake yin fim a qauye kuwa?
Najaatu ta harare shi ta ce " wannan fim din maqiyinmu ne Tukur ka zo mu je kawai mu basu mamaki."
Hassada ga mai rabo taki ce sai ga Hashim da Najaatu sun yi wasai sun sake wayewa, kaya masu kyau, wayoyin hannu masu kyau. Su Mami su na ta harare-harare da tsaki,Tukur sai rawar qafa yake yana ambaton sunan Najaatu da Hashim.
"Wai ina Nihal take?" Tukur ya tambaya.
Amina ta ce "kai ma da bata baki kake. Ai Nihal ta girme ka, yanzu sai su Abbas. Ka na ganin ma an ce ta bar Wudil gaba daya."
Ta na rufe bakinta sai su ka ga motocin sojoji da wasu tare da wasu tsala-tsalan jifajifai sun tsaya a gabansu. Sojoji da bindigogi ne suka firfito su ka tunkaro su sai kowa ya gigice suka miqe a tsorace.
"Ku dakata kada ku gudu." wani soja ya fada yayin da ya daga hannu ya dakatar da su. Ya taho gabansu ya na magana cikin salama, abin mamakin sojan kamarsu daya Nihal sai kowa ya sake cika da mamaki.
Soja daya ya bude daya babbar baqar jeep din sai ga General Nuren ya fito tare da Prop. Shatu mahaifiyar Nihal. Shatu farar fata ce balarabiya sai dai babu wanda yayi kama da ita a cikin 'yayanta su da mahaifansu su ka to kama, sai Nihal ta dauko yanayin jikinta tsab ba su da qiba kuma basu da tsayi sosai kuma ta dauko tsayin hashinta da laushi.
" Malam Tukur ni ne Nuren Mubin mahaifin Nihal ka tuna ni ko?"
Tukur ya bude baki ya na kallonsa. Tabbas shine wannan talakan da ya zo har bashi da cikon kudin acaba. Yana ku ka yana face majina
General ya nuna mahaifiyar Nihal ya nuna Conel Muhammad da Major Abubakar ya sake nuna 'yan sanda biyu Aliyu da Umar ya ce " wadannan officers ne a aikin dammara dukka yayyan Nihal ne uwa daya uba daya. Nihal 'yar gata ce gaba da baya kuma mai ilimi ce, na yi mata haka ne dan ta zo ta ko yi darasin rayuwa kuma ta wayar da kan ku akan yadda za ku inganta sanaarku. Nihal ta yi digiri ta yi masters akan fim kuma ta fara yin fim da turawa ma, ita producer ce kuma director haka Nihal ta goge wajen daukar hoto komai na fim ta karanta. Yadda na kawo ta nan na yankwana ta yanzu na zo ne don in wanke ta da kaina. Na ga fim din Nihal tabbas ta fara kawo canji a masanaantar nan."
Kowa ya fara tuni mai zurfi, sai a yanzu suka dinga tunano wasu abubuwan da ta aikata tabbas na masu ilimi ne. Daman nutsuwarta ta isa haka bata damu da kudi ba a she ita a wajenta kudin fim ba kudi ba ne."
Tukur ya fara zuga karya ya na nuna yadda ya kula da ita, baya jin kunyar kowa.
" yanzu ina Nihal din?" mahaifiyarta ce ta tambaya domin ita burinta ta ga 'yarta.
Hashim ya zabura ya ce "nine babban amininta ni da Najaatu, duk garin nan ba ta da kamar mu. Nihal ta tafi Abuja an bata kwangila yin talla, turawa ne suka bata ta ce kada mu fadawa kowa amma ku iyayenta ne dole in fada muku."
"Ko kai ne Hashim?" General ya tambaya.
Dadi da mamaki ne ya rufe Hashim ya washe baki ya ce " kwarai nine babban amininta.
General ya gyada kai ya ce " tabbas haka ne Shazali ya na bani labarin cewa kullum ku na tare. Idan Nihal ta dawo ka ce ta dawo gida wa'adinta ya cika."
Kudi mai yawa General ya rarraba musu amma na Tukur da Hashim sun fi yawa. Sannan suka shiga motocinsu suka juya.
Su Mami sun yi saranda gami da nadama. Tunaninsu yanzu da wanne ido zasu kalli Nihal su yi qawance da ita dubi irin yadda suka wulaqanta ta. Sai suka fara yiwa Najaatu shishshigi ko Allah zai sa ta san yadda za ta yi ta gyaro musu. Domin sun ga in basu kama qafa da Nihal ba, ba zasu taba shahara ba.
Kallon sama da qasa kawai Najaatu ke yi musu babu kunya ba tsoron Allah har sun dawo su na sonta da suka ji asalinta.
Tunda Tukur ya zuba kudinsa a aljihu ya damqe, auna tudunsu yake yi yana harsashen za su kai naira dubu ashirin ko talatu. Sai ya ji kawai a dakata da daukar shirin nan sai gobe kuma.
Su ka hau yi masa tsiya Tukur da kudi sai Allah. Gaggawa yake ya isa gida ya bawa Sadiya matarsa wannan labarin, ita da ta tsani Nihal, ta wulaqanta ta toh yanzu za ta ji labarin ko wacece Nihal.
Su Hashim ma da su ka isa gida sai su ka bawa Inna labarin kowacce Nihal dinta.
" Na san zaa rina, saboda yarinyar nan daga gani ta gaji arziki gaba da baya.
Duka abin nan da ake yi Nihal ba ta sani ba ta na can Abuja tana ci gaba da aikinta. Bayan da aka gama tsara talla aka gama dauka sai ta dawo kano cikin katafaren gidanta ta yi luf tana hutawa, ta kulle kanta ta na baccin gajiya.
A Industry an gaji da nemanta kowa ya na so ta yi masa fim amma an neme ta an rasa don bata da waya.
Hashim ake ta damu da kira a waya ana neman Nihal. A dole ya shigo mota ya zo gidanta na Kano, kamar yadda ta ja kunnuwansu kada su bawa kowa kwatancen gidanta ba su fadawa kowa ba.
Ta sha mamaki da ta ji ana ta buga get, ta na budewa ta ga Hashim, ta cika da murna shi kuwa har hararar ta ya ke yi sabo ta na jawo musu asara. Akwai fim kala-kala da suke jiranta samunta shine samunsu shi kuma.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na Kudi ne
GABA GADI
NA
JAMILA UMAR TANKO
(JUT)
Ta yiwa Hashim iso zuwa ga babban falonta, abin mamaki sai ya ga ma'aikata inyamurai su na ta jera masa kayan dadi a gabansa.
Ya zabura ya ce Nihal "ina ki ka samo wadannan gidiga-gidagan Arnan?"
Ta harare shi ta ce "wai kai Hashim baka wayewa ne? Meye kuma gidiga gidagan arna kuma?"
Su ka kwashe da dariya su dukka.
Nihal ta ce "na dade ban ji wannan kalmar ba ma. Ngozi professional chef ce ma'ana mai dafa min abinci, stella kuma mai gyara min gida. Na dauko wata tsohuwa ma ta na taya ni hira ita ce ta raine ni lokacin mahaifiyata tana karatu kuma tana koyarwa a jamia."
Hashim ya zabura ya ce " au na manta mun ga mahaifiyarki ashe farar fata ce jajawur da ita, wayyo Allah na da kin yi farinta da mun sake yin tsada."
Sai Nihal ta ji gabanta ya fadi ta dafe kirji tabbas maganar Hashim ba qarya haka prof Shatu ta ke. Kafin ta farfido daga duniyar tunani Hashim ya ambaci sunan Prof. Shatu.
Sai Nihal Nihal ta zabura ta miqe tsaye ta tambaya " ka fada min mana a ina ka santa?"
Cinyar kaza ya kai bakinsa ya yaga ya kora da ruwan lemo ya lunshe ido ya ce " sun zo nemanki ita da General Nuren da Conel Muhammad da Major Abubakar kai har da yayyanki 'yan sanda biyu a garin Wudil."
Nihal ta dora hannu aka kamar mai shirin tsala ihu sai ta fasa.
Sai fada take tana nanatawa " Daddy ka kashe ni, ka bata min shirin da na kuaa cimma burina. Me ya sa ka yi min haka? Me ya sa ba ku bari duniya sun ci gaba da daukana a talaka wulaqantacciya ba?"
Hashim ya cika da mamakin yadda har yanzu bata so a san a asalinta alhali ga ta da asali mai kyau. Ko basu zo ba ai kowa ya fara zargin akwai abinda take boyewa.
Hashim ya sulalo ya sauko daga kan kujera ya ture tebur gefe ya jawo farantin kaji ya fara yaga domin zaman kan kujera da teburi ba zasu isar masa da sakon da yake turawa ciki yadda ya kamata ba.
Nihal ta taho da sauri ta dauke farantin ta mayar da shi kan tebur ta ce " wallahi ba ka isa ba, so kake masu aikina su raina baqona. Su ma fa masu digiri ne wayayyu, ka tashi ka hau kan kujera ka ci ga wuqa da cukali dole ka koyi gayu fa ina saka ran za ka zama super star na kwatance."
Hashim ya washe baki ya hau kujera ya zauna ya ce " kin katse min jin dadi, ni fa bani na kar zomon ba rataya aka bani. Dan iyayenki sun je Wudil an san kowacce ke sai ki huce a kaina."
Nihal ta tambaya " gidan Inna su ka je nemana?"
Hashim ya na ta faman dambe da kaza da wuqa da cokali ya girgiza kai ya ce " A location suka zo suka same mu, mutane sun kai guda dari a wajen suka tona. Dadday ya bada tarihin ki ya ce ya kawo ki ne dan ki koya mana sana'armu ta fim saboda shi kika karanta kenan."
Wannan karon qudindunewa ta yi akan kujera, dan ta fara jin zazzabin takaici.
Hashim ya bata labari daga farko har qarshen abinda ya faru sai Nihal ta yi saranda ta san yanzu kowa ya gama jin komai.
Sai da ya cika cikinsa taf sannan ya isar mata da sakonnin producers da Directors da suke damunsa da kira ana nemanta.
Nihal ta yi murmushi ta ce " na yi fim na farko nayi na qarshe. Mi Nihal Nuren Mubin sai dai in bada shawara ina gefe."
Da alama bai ji dadin wadannan kalamai na ta ba. Yayi juyin duniya akan ta zo su je wajen Abbas shima yana ta kira ta qi yarda. Bai rufe bakinsa ba Abbas ne ya kira, Hashim ya dauka Abbas ya tamabaya ko su na tare da Nihal? Nan da nan Hashim ya amsa " eh gata nan muna tare."
Babu yadda Nihal zata yi sai ta karba bayan sun gaisa da babban Darakta nata, mutumin kirki wanda ya qaunace a lokacin da kowa yake hana shi amma bai yarda ba sai da ya farfado da darajarta.
Abbas ya ji dadi da jin muryarta dan ya na tsananin nemanta.
Ya tambaya "Nihal ina kika shiga ne gari ya dauka ko ina hotunanki a social media da kuma manyan akan alluna na kan titi, ana ta tallar fim din Gimbiya Nihal. Ranar asabar mai zuwa zaa fara nuna shi a cinema a fadin qasar nan. Tabbas ana buqatarki a wajen saboda ke ma jama'a zasu biya su shiga don su ganki. Da fatan za ki yi min wannan alfarmar. Nihal kin yi min komai kin farke labarin kin tsara shi ya tafi daidai,kin qawata shirin da dukoyarki da jikinki dadin dadawa kin yi min duk wannan kyauta ba kya buqatar kudina. Nihal mun sami labarin ko ke wacece tabbas kin fito daga gidan arziki wacce ta gaji arziki."
Ta rasa abinda zata ce sai ta yi murmushi ta gyada kai ta ce " ga mu nan zuwa ofis dinka."
Murna ta kama Hashim, Nihal ta kira masu aikinta ta shaida musu zata fita, a cikin karshen turanci.
Hashim ya sake cika da mamaki ya ce " ka ji wacce aka ce bata iya karatu ba, bata taba shiga aji ba. Amma wallahi kin ba mu wahala."
Su ka kwashe da dariya su dukka. Wata lafiyayyiyar abaya ta dora akan riga da wandon da suke jikinta ta dauko jakarta suka tafi. Kallon qafarta yake ta yi saboda ya ga ta saka takalmi cambas fari. Ya na ta mamakin yadda mace zata saka cambas.
Bakinsa ya kasa yin shiru sai ya sake tambaya.
"Au daman mata su na saka cambass?"
Nihal ta yi dariya har sai da cikinta yayi ciwo ta ce " kwarai kuwa, lallai ina da aiki wajen wayar da kai."
Ba ta da mota har yanzu a adaidaita sahu suka tafi, sun isa bakin ofishin Abbas sai suka ga wata mota mai kyau an rubuta Bilali 4.
Hashim ya zabura ya nuna motar ya ce " wannan na daya daga cikin motocin Jarumi Bilal fa. Ya na ciki ma , amma mun ci saa."
Nihal ta harare shi ta ce "kai fa yanzu matsayinka daya da Bilal saboda kai ma super star ne, ina so ka nutsu ka ja ajinka kada ka sake a dinga ganinka kora ko dan maula."
Hashim ya gasgata maganarta sai ya nutsu suka shiga a tsanake.
Abbas ne kadai sai Editor Anas Bilya yaro mai tashe da ake ji da shi a wajen iya editing.
Abbas na ganinta sai ya miqe tsaye dan girmamawa da kansa ya gyara mata kujera suka zauna, bayan sun gaisa sai ya nuna mata Anas a matsayin wanda yake yi masa editing fim dinta.