Showing 60001 words to 63000 words out of 110552 words
Chapter 21 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
da ita ba din.
Sai da su ka yi nisa dan adaidaita sahu ya tuna mata cewar bata fada masa in da zasu je ba. Ta zabura ta dawo daga duniyar tunanin da ta tsunduma.
Ta ce "tashar Kano line za ka kai ni."
Ya ce " amma kudin drop za ki biya ni ko? Dan ba hanyar zan bi ba."
"Nawa ne kudin din?" Nihal ta tambaya .
"Naira dari da hamsim za ki biya, wallahi har dari biyu ake biya. Ke ce ma na yiwa ragi dan na ganki da gwanina Bash Auta."
Ta yi dariya ta ce "saboda Allah kuma saboda kaunarka da Bash naira dubu biyu ma zan baka maimakon naira dari biyu."
Sai ya zabura ya waiwayo ya kalle ta, bai santa a fim ba san haka sai ya zaci 'yar uwarsa ce mai son 'yan Fim ta kawowa Bash ziyara.
Ya hau kirari ya na godiya da jinjina. Ya ci gaba da cewa " lallai kin fi ni son Bash Auta tunda kika yi min kyauta domins."
Ya shiga ba ta labarun Finafinan Bash da suka fi burge shi, a ciki har da sabon Fim din Idris wanda ta taya Aisa samun daukaka. Ya yi ta koda bajintar Aisa da Bash a fim din nan.
Ta na ta dariya ta fada a zuciyarta " an gaida Nihal Niren Mubin."
Da ta tashi bashi kudin sai ya ga ta lunka akan kudin da ta yi masa alkawari kafin ya sake yi mata godiya ta bace ya neme ta ya rasa ta. Addu'a ya yi mata a bayyane ya ce "na dade ban ga mai kirki kamar ki ba. Allah Ya ba ki a aljanna Ya biya miki buqatun ki na alkhairi."
Nihal ta sami mota qarama a layin masu lodi ta ce ya kara mutane biyu za ta biya sauran kujerun su tafi. A zatonsa iyakacin kujerun da babu kowa ne za ta biya ashe tana nufin har da na wadannan mutane biyu. Mace da namiji ne Namiji ya shiga gidan gaba, macen ta zauna a baya tare da Nihal har za su biya sai direba ya nuna Nihal ya ce "ku yi mata godiya ta biya mu ku."
Kallon qurilla su ka yi ma ta su na mamakin wanda yake iya taimako a wannan marar. Sai su ka hada baki su ka yi mata godiya.
"Ni kamar na sanki a wani waje." In ji fasinjan da ya ke zaune a gaba.
Macen da take zaune kusa da Nihal ta ce " ka santa mana a fim din 'Tsumma' ya fito ita da 'yar kwalisa su ka yi."
Sai gaban Nihal ya yanke ya fadi bata ma san finafinan da ta yi har sun fara shiga gari ba.
Nihal ta yi murmushi ta sake rufe fuska ta ce " A a sai dai kama amma ba ni ba ce."
Matar ta ce " ke yar nan na san ki sosai, ga gidanki nan ma a bakin kwalta. Ke ce qawar Hashim dan gidan Inna Habi me surfe. Ai ki na zuwa gidan Marka mai dinki har kin taba kwana a gidan lokacin da su Mami harka su ka kore ki daga dakinsu."
Nihal ta zazzare ido ta cika da mamaki da tsantsan takaici yadda ta zama bata da sirri kowa ya san labarin halinda ta ke ciki ashe.
Direba ya ce " oho ko ke ce aka ce su Mami harka sun sa 'yan daba su dake ki asiri ya tonu dan kin zo daga baya kin fi su daukaka?"
Nihal ta fada a bayyane ta ce " shikenan ai kun gama magana."
Jero mata tambayoyi su ka ci gaba da yi, sunayen 'yan fim din da ba ta taba ji ba ma. Har da Bash Auta da Aisa abin mamaki su ma hirar Fim din nan na Darakta Idris su ke yi yadda Aisa ta yi bajinta.
Fasinjan da yake zaune a gefen direba ne yayi magana ya ce " Asiri ai ya tonu an ce duk abin nan da suka yi a fim ba su ba ne wata ce ta yi aka dora fuskokinsu."
Nihal ta ci gaba da saurensu ta na mamakin yadda rayuwar 'yan fim ta za ma ba su da sirri, kowanne labari sai da aka kwakwalo shi.
Direba ya ce " Haba no fa in ce yaushe muka samu wannan ci gaban haka gaskiya sun yi abin mamaki a fim din. To ita wacce ta yi acting din a fito da ita mana kowa ya santa. Me ya sa zaa boye fuskata a dauki jikinta?"
" Allah sarki sannu Nihal Nuren kina da kirki ashe akwai masu hankali da nutsuwa a cikin 'yan fim amma ake yi musu kudin goro ana cewa sun cika wulaqanci. Allah Ya sa ki fi haka kin ji. wallahi haka Marka ta ce min ki na da kirki da hankali. Ki ci gaba da addua dan tabbas su Mami harka ba sa qaunarki." In ji matar da take kusa da Nihal.
A qofar gidanta ta ce sauka su na yi mata godiya tana yi musu itama.
Gida ta shiga ta yi sallar la'asar ta na idarrwa ta ji ana buga gida, ta fita da sauri sai ta zaci Hashim zata gani ashe Shazali ne.Babta yi mamaki sosai ba, ganin ya na murmushi ya nuna komai ya adaidaita kenan. Bayan sun gaisa sai ya ba ta labarin komai, gami da yi mata albishir akan mai gida ya siyar mata da gida akan kudi Naira miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin, sai la'ada Naira dubu hamsin.
Ya zaci za ta ce yayi tsada sai kawai ya ji ta ce "ina za mu je mu biya kudin. Amma komai a yi shi a bisa ka'ida. Zaa yi a rubuce a saka lauya a ciki ayi takardu akan qa'ida."
Haka kuwa aka yi Nihal ta dauko jakarta wacce ta ke shaqe da kudi su ka dunguma wajen mai gida da mai unguwa. Kafin qarfe takwas na dare gida ya zama mallaki Hashim da sunansa aka siya.
Ita kadai ta ke murmushi ta na ta jin dadi a ranta, dan babu abinda ya fi faranta mata rai a rayuwa irin ta zama silar farantawa Musulmi rai kuma ta cire shi daga cikin ukuba da damuwa zuwa ga farin ciki. "Alhamdulullah." Kawai take ambato.
Washe gari da misalin qarfe goma na safe Hashim ya bayyana a qofar gidan da yake mallakarsa ne ba tare da ya sani ba. Ya yi ta bugu sai ga Nihal ta bayyana a gabansa ko tantama babu ta san irin bugun Hashim ne. Ya na ganinta sai ya fara murna domin jiya ya wuni shi kadai bai ji dadi ba.
"Darakta Abbas ya kira ni daga jiya da daddare zuwa yau ya kai sau goma ya na son yin magana da ke, ya ce kin je Kano jiya. Shine amma baki fada min ba?"
Nihal ta dade tana tunani kafin ta san amsar da za ta bashi, ta gyada kai ta ce " eh na shiga kano na je kasuwa."
"Me ki ka siyo?" Ya sake tambaya.
Wannan karon sai ta cika da mamaki amma da ta tuna da cewa da dan karkara take magana ba da turawa ba sai ta ga normal ne ai.
" Malam Abbas ya ce in mun hadu da ke in yi masa flashing." In ji Hashim.
Bai rufe bakinsa ba sai ga Abbas ya sake kira Hashim ya miqa mata wayar da sauri. Nihal ta karba ta na magana cikin ladabi. Bayan sun gaisa sai ya qara ba ta haquri game da abinda ya faru jiya.
Nihal ta yi murmushi ta ce " haba Darakta da kai ne ka fadi wannan kalma a kaina zan ji haushi amma kai qaryatawa ka ke yi, tabbas na shaide ka ka na qaunar ci gabana kuna da gaske neruda gashi har a bayan idona kana kare ni."
Ya ji dadi da jin kalamanta ya tabbatar ta gama jin duk abinda ya faru, ya sake yin godiya ga mai sama da ya matse bakinsa Ya hane shi da aikata mugun lafazi akanta, lallai da anji kunya.
Ya ci gaba da ce " mun tattauna da Bash Auta ya ce " a baki roll din qawar Jaruma za ki firfito a wurare kamar guda goma. Ki yi hakuri takardun nan da na baki ba ma fim ba ne ki taho min da su, ranar na rikice ne."
" ba damuwa, na gode kwarai Darakta zan dawo.maka.da su. Yaushe ne zaa tafi aiki? "
"Jibi ne, da wuri za ki fito." Abbas ya fada cikin fara'a.
"Zan iya zuwa da abokina Hashim? Da shi kadai na saba, dan yake taya ni hira."
Hashim ya daga hannu sama ya na addua Allah Ya sa Abbas ya amsa. Sai aka ci sa'a ya ce su zo tare babu damuwa.
Bayan sun kashe waya sai murna ta kama su biyun suvka shiga tunanin siyo akwatuna qanana wadanda za su zuba kayansu a ciki. Wannan ne karo na farko da za su yi fim a nesa da gida kuma wanda za su kwana a location.
*** *** ***
Ranar da zaa tafi, qarfe bakwai na safe a qofar gidan Nihal ta yiwa Hashim, ya na ta azalzalar ta, ta zo su tafi. Ko karyawa basu yi ba suka dunguma. Qarfe tara a bakin ofishin Abbas ta yi musu babu ma wanda ya qaraso, har shi kansa Abbas din dan haka sai su ka sami waje su ka zauna zaman jira. Ba su dade ba Abbas ya iso, ya ji dadi da ganinsu. Daga nan aka fara taruwa, motoci su ka cika farfajiyar wajen damqam dukkansu na tafiyar ne. Yawancin kowa motarsa ce kowa da abokan tafiyarsa.amma Nihal da Hashim ba su san kowa ba basu san a in da zaa raba su ba. Abin mamaki sai ga Bash Auta ko kallon Nihal bai yi ba da alama ya ji haushin abinda ta yi masa shekaranjiya.
A wata doguwar bus aka dura su Nihal daga ita sai tarkacen 'yan bayan fage da kuma 'yan kan ta waye. Nihal ta juya ta dubi maka-makan motoci masu sanyin Ac, ranta ya dinga biyawa dan ba ta san nisan tafiyar ba, kuma ba ta san irin jigatar da za ta yi ba kasancewar ba ta saba yin doguwar tafiya a cikin kwarababbun motoci ba. Halima Jabir ta hango tare da Bilal sun kame a wata babbar jeep baqa sai nishi motar take saboda tsabagen kyawun inji da sabunta. Su biyu ne kawai a cikin motar kujerun bayan babu kowa, sai dai babu damar ta je ta roqe su cewar su tafi tare.
An kama hanya sai Nihal da Hashim su ka yi addua su ka shafa aka ci gaba da tafiya. A cikin motar ne Nihal ta yi qawa me suna Duduwa indiyana. Da ta fadawa Nihal sunanta sai Nihal ta rasa inda aka dauko sunan india aka hada anan, da alama dai ba'a ce ake yi ma ta domin babu abu daya na suffar Indiyawa da ya bayyana a jikinta. Ga ta dai baqa qirin ga rashin gashi, ga rashin aji. Ga ta da yawan magana, har ta fara isar Nihal tun ta na amsa mata har ta daina. Amma da Duduwa ta gangaro kan labarin Nihal Nuren Mubin sai Nihal da Hashim su ka fara marmarin jin kanun labaran.
Nihal ba ta san har an santa haka da yawa ba haka an san labaru da yawa akanta.
Duduwa indiyana ta shaida ma ta cewar "an ce Bash Auta ya na sonki, kuma Aisa ta na kishi da ke dan babu wanda ta tsana a duniya kamar ke. Aka ce da ke ce za ki zama Jaruma a wannan fim din, amma Halima Jabir ta kwace miki dan Bilal ma ya ce ba zai iya yin fim da ke ba kin yi masa local. An tabbatar da cewa wannan daukaka da Aisa ta samu a sabon fim din da ta yi ta dalilinki ta samu amma ta na yi miki butulci."
Nihal ta kalli Hashim shima ya kalle ta suka juya gaba daya su ka kalli Duduwa Indiyana cike da mamaki.
TALLA ! TALLA!! TALLA!!!
Me talla shi ke da riba.
Note:
Kada a manta ba JUT ba ce me kaya, talla kawai aka ba ta馃グ馃グ
鉂も潳鉂も潳鉂も潳鉂も潳
Duk wacce ba tayi anfani da sabulun nan ba an barta a baya a can karshen baya ma kuwa. Duk Mai tantama akan sabulai na gyaran jiki cewa basa aiki toh ya cire mg's domin kankat neInsha Allah. Babu Wanda ya yi anfani da sabulunmu ya ce baiyi ba ko yaushe mg's sai san barka.
Amare da uwargidaye harda ma 'yanmata ku hanzarta ku samu naku, ba karya domin bama cika baki ku gwada ku bada labari da bakunanku. Sabulu daya tamkar da dubu wadanda ma basa san using cream sabulun 'mg's herbal whitening black soap' ya wadace ku, jikinku zai yi kyau koda yaushe ku kasance clean cikin kamshi Ku na glowing koda bakusa turare ba馃.
Kayanmu ba na bleaching ba ne organic ne su na gyara jiki fiye da tsammaninku. Zai fiddobmuku da ainihin 'natural beauty dinki ne Wanda ya gwada shi zai tabbar. Amare ku yi kokari ku mallaki mg's domin ba ruwanku da zuwa andirje muku jiki, za kuga yanda fatarku za ta dinga walwali.
Ina masu pimples
Tabo(spot),
Sun burn dama duk wani matsalar fata?. ku yi kokari ku nemi soap din nan before 2weeks zai share muku hawaye, ku zama abun kwatance. Sisters ma su nankarwa kuma ku nemi soap dinnan Ya na rage nankarwa sosai馃馃徎鈥嶁檧锔廳uk me shakku tanyi kokari ta gwada mg's insha Allah ba za ki so rabuwa dashi ba.
Akwai mai saka haske Amma kayanmu na fada ba na bleaching ba ne zai fiddo miki da ainihin halittarki ne ya goge dukkan dattin jiki.
Akwai Kuma Wanda zai miki maintaining skin dinki ya saka ki fresh, fatar ki ta zama kalar hutu
Sannan mu na da beauty kit馃duk me bukatan (flawless skin/perfect glow) toh yy kokari ya mallaki set dinnan wannan zncn baa mgn馃馃徎鈥嶁檧锔廲uz duk inda kayi se an kalleka馃榾 Buh gsky wnd be son yy haske karyayi using set din cuz gsky yana sa haske buh ba na bleaching ne zai dai murje fata ne nd bring out that hidden beauty in you馃槏
Pls bama cika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted
Beauty kit: 11k
Soap price: 3k
Location: kaduna but muna turawa ko Ina Amma delivery is not free
Masu so kindly message 08062991549
Call 08064532391
Note:
Babu in da zaku sami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bai riga ya kai market ba in yakai we will let you know but as for now wnn number ne kawai馃檹
Maiso ya hanzarta before ya ji sold out akwai su available now in sunkare you HV to wait a kawo, so mai so ya hanzarta馃檹adade anayi sai gsky馃き馃
Mg's skincare
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 鉂�
GABA GADI
NA
JAMILA UMAR TANKO
(JUT)
"Yanzu kenan dan ina yin fim ba ni da sirri ko kadan? Su waye su ke fitar da maganarmu? Ba kowa ba ne a junanmu ne, tabbas mu na da farin jini dan haka kowa ya na son ya san yadda mu ke rayuwa a zahiri abin burgewa ce ace an ji labarin rayuwar dan fim a bakinka dan haka ta ko ina farautar labarin ake yi. Makusantanmu su suke yadawa musamman ma idan abin ba mai kyau ba ne . Mutane sun fi zumudin su yayata sharri fiye da alkhairi. Wacce irin rayuwa muke yi a qasar nan ne? A qasashen da su ka ci gaba abin ba haka hake ba. Tabbas su na da wannan dabi'ar su ma na neman labari a kan celebraties amma da yake acan celebrateties su na da tsaro da kudi baa ganinsu barkatai a fili, ba kamar mu ba." Nihal ce ke tunani yayin da maganar Duduwa indiyana ta katse tunaninta.