Showing 87001 words to 90000 words out of 110552 words
Chapter 30 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
Nihal da Anas suka yiwa juna murmushi suka gaisa haka Hashim ma ya gaishe su.
Nihal ta koma kusa da Anas dan taga irin kwarewarsa, tabbas yana qoqari amma akwai kurakurai. Ta tambaya kai ne kake rubuta translation na turanci.
Ya girgiza kai ya ce "Bilal ne amma ya tafi dauko dictionary. "
Sai ta ji ta raina shi ma ashe turanci na sa kadan ne. Ta jawo kwamfuyuta ta fara dubawa tashin farko ta hango kurakurai a waje uku mabanbanta. Ta gyara su sannannta ci gaba da yi kan kace kwabo ta kusa kammalawa. Har yanzu ya na can ya je ya nemo dictionary dan Nihal ta kusa gamawa. Abbas ya koma gefe yana kallonta cike da mamaki wacce aka ce bata iya karatun Hausa ba ma.
Nihal ta dago ta dubi Abbas ta ce " ai bai kamata a yi editing ayi translation ba na kusa ba tunda na yi amfani da wani yare wanda ni kadai na san ma'anar. In ba za ka damu ba idan su Bilal suka gama ka bani in sake bibiya."
Abbas ya gyada kai ya ce " ah ai an baki dama ki tafi da shi a yanzu ma."
Nihal ta girgiza kai ta ce "bari su gama dai wajen jibi zan zo in karba."
Ta tashi ta bar wajen ya koma kan kujerarta ta zauna kenan sai ga Bilal.
Bilal ne ya shigo dauke da qaramin dictionary, ya na ganinsu sai ya yi turus da alamar ya razana da ya gansu amma sai ya dake. Ya yi sallama a ciki ciki ya shigo, haka itama ta amsa a ciki-ciki ya wuce yana taqama ya zauna a kusa da Anas.
Ya ce " sorry na dan jima ban dawo ba ko? Na hadu da jarumin nan ne na kaduna Iliyas muka dan bata lokacin a studio Silicon. Ina muka tsaya ma?"
Anas yayi dariya ya ce "ai mun yi nisa sosai ma."
Bilal ya dubi Anas duba na rashin fahimta.
Anas ya bude ya nuna masa ce "ka ga in da ya bamu wahalar nan ta yi shi ba tare da ya duba dictionary ba."
Bilal ya tambaya cike da fargaba " wacece ?"
Anas ya nuna Nihal. Wannan karon zaburar da ya yi sai da ta nuna a zahiri. Ya cire kokonto wannan princess last born ce babu wata tantama. Sai ya qura mata ido kallo na takaici da dana sani da kuma nadama.
Ta kawar da kai gefe bata kalle shi ba. Tun daga nan ya ji ba shi da wani qarfin da zai ci gaba. Gumi ne ya dinga tsatstsafo masa domin ya ga samu ya ga rashi. Princess ta yi masa Albishir da alkawura masu yawa tana daf da zata cika masa sai ya neme ta ya rasa. Yanzu gata har gida cikin rashin sani ya wulaqanta ta.
Abbas ya ce " Nihal akwai wani sabon fim nawa ko za ki sake taimakawa ki yi min?"
Ta gyada kai ta ce " Sai dai ba zan iya ce maka A a ba Darakta."
Ya yi murmushi ya ce " amma na gode sosai. Fim din yawanci a Abuja da kaduna zaa yi shi kuma zan so ki karanta labarin na san akwai gyara idan ma zaki farke shi ki wargaza ki dinke irin wancan na baki gari."
Su ka yi dariya su dukka. Hashim yayi carafe ya ce " Darakta namu ai kawai ka sakarwa Nihal wuqa da nama. Allah Ya sa in sake samun matsayi in fito a ciki."
Nihal ce ta harare shi sai ya yi shiru.
Nihal ta gyara zama ta ce " waye Jarumi a fim din?"
Abbas ya nuna Bilal ya yi dariya ya ce " a baya kuskure ne, ya yarda za ku yi fim tare yanzu."
Hashim ya zabura ya ce "Alhamdulullah fim din zai yi matuqar qayatarwa ga Nihal ga Bilal, wai zaa yi wuta."
Allah Ya sani Hashim ya na disga ta kwarai.
Ta yi magana a cikin takaici " ah ina kuwa wannan hadi yayi daidai ai bai yi daidai ba, tunda zaa hada Jarumar qauye da Jarumin birni ai sai ta zubar masa da aji. Yayana Abbas ka yi hakuri ba zan iya yin fim da Bilal ba saboda ba matsayinmu daya ba."
Bilal ya ji kalamanta tamkar a mafarki, ya ji takaicin furucinta a kansa. Yanzu da ya gane princess ce babu abinda ya fi begets irin yayi fim da ita, tabbas fitowa a fim tare da ita nasara ce babba.
Abbas ya shiga bata baki. Kalma daya ta fada ta tashi ta fice shine babu yadda zaa yi ita da Bilal su hadu su yi fim, sai dai Darakta ya zabi daya ko ita ko shi.
Hankalin Abbas ya tashi amma na Bilal ya fi nasa tashi. A ka rasa wanda ya iya magana a cikinsu. Hashim ya tashi da sauri ya bi bayanta. A bakin titi ya hango ta, ta na jiran adaidaita ashe Bash ma ya ga wucewarta a fusace, shima ya biyo bayanta. A gabanta ta gansu ba zato ba tsammani, ta daga ido ta kalle su sai ta shaida ashe Bash ne.
Ya fada cikin lallashi " ke da ba kya fushi me aka yi miki haka kika wuce a fusace?"
Hashim ya ce "ita da mutumin ne Abbas ya ce zai hada su fim da Bilal shine ta ce ba zata taba haduwa da Bilal su yi fim ba, tunda ya ce ba zai yi fim da ita ba a baya."
Bash ya gyada kai ya ce "wannan gaskiya ne ta yi min daidai."
Nihal ta ji dadin kalaman Bash sai ta saki fuskarta, ya ci gaba da lallashinta akan ta dawo afis din Abbas a zauna a yi magana. Dakyar ta yarda ta juyo, su na tafe Bash yana ta tsokano ta da labari.
Aisa ce ta dira gabansu ta kama qugu ta na girgiza ta ce "nan ma location ne da aka fake ana soyayya aka ce a fim ne?"
Nihal ba ta kula ta ba dan bata so ya aikata wani abu da zaa buga a jarida. Aisa ta sake tarar gaban Nihal alamar fada ta ke so su yi.
Bash ne ya daka mata tsawa " Aisa ki matsa ki bata hanya ta wuce kada ki ja abinda zan wanka miki mari anan."
Aisa da Bash suka kaure da Cacar baki, Nihal ta gaggauta barin wajen. Hashim dan shishshigi shine mai rabiya, abin alfahari ne yau a wajensa yana tsakiyar super stars yana raba su fada.
Nihal ta isa bakin kofar ofishin Abbas sai ta yi kasaqe tana sauraron abinda suke cewa.
Abbas ya ce "ka yi kuskure Bilal, ba kyau wulaqanta dan adam ashe Nihal din da ka tsana ka raina ita ce princess din da ta ce zata taimake ka har kake cewa kana bala'in sonta. Shawara ta da kai shine ka dinga yin komai dan Allah sai Allah ya taimake ka. Ga irinta nan duk wani wulaqanci ka gama yiwa yarinyar nan a niger da Nigeria. Maganar gaskiya ta fi mu gaskiya, ba ni da ta cewa kuma dole in zabi daya a cikinku."
Bilal ne yake magana cikin sanyin murya " ni dai a roqe ta ta yi haquri ta yi fim dani wallahi Darakta burina ba zai taba cika ba idan ban yi fim da Nihal ba. Mafarkina kenan a rayuwa, ina son princess fatana in yi fim da ita. Na san ban kyauta mata ba amma rashin sani ne ai. Princess ta so ta taimake ni a rayuwa amma ni ban taimake ta ba, tabbas na yi nadama."
Abbas ya cewa Anas ciro min original copy na fim din nan in bata ta gyara, ai yanzu da na san ko ita wacece ba zan yi wasa da damata ba, editin din ta ma na san zai zama special
Na gode Allah da na taimake ta lokacin da take neman taimako, ga shi nima tana taimakona."
Anas ya ciro ya miqawa Abbas, sai ya fito da sauri sai kuwa suka yi kicibus da Nihal a bakin qofa.
Abbas zai yi magana Nihal ta daga masa hannunta ce "kada ka damu. A shirye nake in yi maka komai. "
Ya miqa mata CD ta karba ta saka a jaka.
Ta ce " jibi zan dawo maka da shi insha Allah idan na kammala."
Abbas godiya yake har yana duqawa, Nihal ta zo ta wuce Bash da Aisa da Hashim har da qarin wasu masu sasantawa, ba tare da sun ganta ba ta hau adaidaita ta wuce gida. Ta na isa ta jawo laptop dinta ta fara aikinta a falo. Sai can da jimawa sannan Hashim ya dawo.
Har da fada yake yi mata yaya zaa yi ta tafi ta barshi a can yana ta wahalar nemanta?
Ta fada cikin gadara "ai in har kai juninka shishshigi wallahi haka kullum zan yi maka."
Hashim ya kwalla kiran Ngozi ta zo da sauri ya ce "give me juice and water and chicken."
Nihal ta yi dariya ta ce "a kawo musu abinci ma tunda an gama. Akan dining table aka jere musu abinci kala kala, ga farfesun kajin ga shikafa a ga miya.
Nihal ta aika a ka kira tsohuwa Baba Balaraba suka gaisa da Hashim sanan suka hau kan tebur suka ci abinci tare.
Da yamma Hashim ya ce zai koma gida sai ya zabura ya dauko wata waya mai kyau ya ce in ji Bash ya ce in baki , waya ce da sim dinta. Ya ce ki yi wa Allah dan darajar Annabi ki kunna ku yi magana, ya na son yin magana da ke.
Ta harare shi ta harari wayar, Hashim ajiye a kan tebur ya fice ba tare da ya jira abinda zai biyo bayan qarshen hararar ba.
Nihal ta fada a bayyane "tabbas Hashim ne silar tona min asiri har sai an san in da nake. Wanna yaron ya qi wayewa."
Ta jawo wayar ta kunna tana kunnawa ta samu sakonnin Bash da yawa ta cika da mamaki da ta ji kalaman tsantsar qauna mai hana bacci da ta ginu a cikin zuciyarsa. Ta yi murmushi kawai ta ajiye wayar a gefe.
Kira ta ji yana yi data duba sunansa ne ya fito. shine ya yi saving da kansa.
Ta yi kamar ba zata dauka ba sai ta tuna cewa ya hada ta da darajar masoyinta shugaba S.A.W, tabbas babu abinda ba za ta iya yi ba in dai ba haramun ba ne muddin aka hada ta da Annabi.
Sai ta amsa ta yi masa sallama ta gaishe shi cikin biyayya. Bash ya lumshe ido tabbas ya ji tamkar an yi masa Albishir da aljanna saboda farin ciki.
Gaisuwa ce dai kawai suke ta yi su na maimaitawa ya kasa qara furta wata kalma mai kama da soyayya sai yayi mata godiya data kunna wayar ya na fatan ta ci gaba da amsa masa ba dan shi ba sai dan darajar Manson Allah S.A.W. Ta rasa yadda aka yi ya san abinda ta fi so duniya da lahira shine manzon Allah. Ta yi amsa alqawarin zata yi masa hakan saboda darajar ma'aiki.
Bash ya kashe waya ya juya ya kalli Bilal ya ce " ka taya ni murna yau Gimbya Nihal ta kula ni."
Zuciyar Bilal ta cika da kishi ya ce " ba na tantama Nihal ita ce princess bana ta kokonto yanzu. Saboda yadda na ga turancinta a wajen editing yayi min kama da na princess. Yanzu yaya zaa yi? Bash ka ga kuskuren da na tafka ko? Please ka gyaro tsakaninmu na ga kamar kuna shiri."
Bash ya harare shi ya ce "ai ba kama ba ne ba ma, tabbas ina shiri da Nihal kuma har mun kulla soyayya ma."
Bilal ya saddaqar ya san ya rasa Nihal kuma ya yi wa kansa. Yayi ajiyar zuciya ya ce " Allah Ya sa ta kula ka, kai din ma. Wai ka san matsayin yarinyar kuwa ?"
Bash ya ce "babu ruwana da matsayinta, abinda na sani shine Nihal 'yar qauye ce daga Wudil kuma a haka take burge ni tun ban san ko ita wacece ba."
Bilal ya gyada kai ya ce "haka ne. Wai yau ni Bilal har in ce zan yi fim da yarinya ta ce ba zata yi fim da ni ba. Lallai Nihal kin hadu."
Bash ya ce " ai bata yi laifi ba idan har zaka iya tuna ranar da na dinga rokqarka da ka daina wulaqanta ta haka, har fada ka yi da ni."
Bilal ya gyada kai ya ce "an yi haka sai dai Nihal ta tafka babban kuskure bata san Bilal ba wallahi ko ta halin yaya sai an hada mu a fim.
Bash ya fusata da jin kalamansa sai ya diro daga kan mota ya miqa masa hannu ya ce " zan tafi gida umma ta na nemana."
"Ok sai anjima" in ji Bilal.
Bash ya shiga motarsa ya fara tafiya. Hashim ya kira a waya ya na tambayarsa yadda su ka yi da Nihal.
Hashim ya ce " ba ta karbi wayar ba sai kawai na ajiye mata a kan tebur haka bata ce komai ba dai."
Bash ya tabbatar yana da babban aiki nan gaba kafin ya samu ya shawo kan zuciyar Nihal.
Nihal ta wuni ta sake wuni tana aikin editing da translation zuwa turanci a fim din Abbas.
Editing din da baa taba yin irinsa a Hausa industry ba. Ta taso da kanta ta kaiwa Abbas. Ya karba yana godiya itama tana godiya suka tsaya akan sai ranar da zaa nuna fim din a cinema zata je.
Dr. Hamza ne ya fito daga bangarensa a gigice ya sami Asp Umar a nasa falon ya miqa masa wayarsa shima kuma a an turo masa a lokaci guda. Hotunan Nihal Nuren ce ya basu ko ina.
Wayar Miawiyya ce ta shigowa Hamza ya amsa da sauri.
Mu'awiyya ya ce " Hamza shegiyar yarinyar nan fa ta fara wuta a fim."
Hamza ya ce "Nihal ko? Ga hotunan ta nan an turo min yanzu muke maganar da ASP Umar. Ance labarinta ke trending a social media."
General Nuren ya tara yaransa kakaf a babban falo ya fara magana cikin sanyin jiki ya ce " haqiqa na batawa kowannenku rai ba dan ina so ba sai dan shine kadai hukuncin da ya dace da Nihal. Na fi ku shiga fargaba da tashin hankali a lokacin da na kaita qauye na ajiye ta bata da kowa bata da komai sai Allah.
Ta na kuka na juyo na bar ta, na dade bana ci bana sha bana bacci. Kun fi ni kwanciyar hankali dan ba ku san yadda na baro ta ba kuma ban fadawa kowa inda take ba.
A lokacin da Ambassador Abba Muse ya kai qarata wajen yayana da sauran abokanmu sun yi min fada sosai sun yi Allah wadai da