Showing 105001 words to 108000 words out of 110552 words
Chapter 36 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
Bilal da Halima Jabir sun fito fa an kure adaka an yi matuqar yin kyau.
Tabbas babu wasu 'yan Hausa fim da su ka amsa sunansu da basu halacci wannan waje ba daga kowacce jiha.
Taro yayi taro kowa ya hallara waje ya cika maqil baka isa ka iya hango karshen hall din ba idan ka tsaya daga gaba.
Ayi Hausa ayi da turanci saboda baqi su ma su fahimta. Ga mai gayya mai aiki Gwamna Muse da Justis matarsa a kusa da shi. Qarshen magana kenan, qarshen haduwa, qarshen qarya dan babu abincin da babu da abin sha. Anya an taba yin taro a garin nan ko a ce a duniyar fim din Hausa irin wannan kuwa? Amsar ita ce "A'a baa taba yin kwatankwacinsa ba ma. Masha Allah! Tabarakallah! Alhamdulullah !
Nihal Nuren ce ta karbi kambun girmamawa. Ta daga shi sama ta yi godiya ga Allah, ta yi godiya ga iyayenta da mijinta ta sake yin godiya ga dinbun al'ummar da suke goyon bayanta su na qara zaburar da ita wajen qara qaimi.
Nihal ta sharce hawaye ta ce " ina kira ga iyaye su zama masu lura da inda yaransu suka fi karkata. Don da yawan yara tun su na qanana su kan nuna alamar abinda su ka fi so su zama a rayuwarsu.
Wasu yaran za ka ga sun fi raja'a a fannin zane- zane, wasu su na yawan nuna alamar su na son aikin labarai a talabijin, wasu su na nuna son gyare-gyare aikin injiniya. Wasu kuma su na nuna aikin likita su ke so. Wasu yanayinsu yana nuna za su iya aikin lauya.Amma sai ka ga iyaye basu kula ba ko kuma ko da sun kula sun rufe ido sun ture ra'ayin yaro sun qeqashe qasa sun zabarwa dansu abinda kwata-kwata ba layinsa ba ne. Daga nan ake fara samun gagarumar matsala, an tilastawa yaro ya je amma baya gane komai ko ya na yi baya murna.
Ni Nihal Nuren hakan ya taba faruwa da ni General ka yafe min zan bada misali ne."
Kowa dariya da tafi yake har da General, sai ya gyada kai alamar ya ba ta izini ta ci gaba da batunta.
Nihal cike da fara'a ta fara bayani ta ce "ya faru da ni ne a sandiyyar hakan ne ma na kawo ga wannan matsayi."
General ya kalli Shatu ita ma ta kalle shi, Muhammad ya kalli Abubakar shima ya kalle shi.
Abubakar ya ce " yarinyar nan da shegen surutu za ta jawo mana ruwa. "
Muhammad ya ce "ka bar ta ta yi misali da iyaye irin su General."
Nihal ta ci gaba da cewa "tun tasowa ta na kasance babu abinda na fi so a rayuwata irin in yi wasan 'yar tsana da 'yartsana nake tsara labari in yi kamar wasan kwaikwayo. Ta kai ta kawo ina zana gida da mace da goyo ina tara yara ina ba su labari kamar dirama. Iyayenta sun fuskanci hakan har su kan zauna su na kallona ina yi mu su wasan kwaikwayo a gabansu da ni da bango nake magana su na ta dariya.
Ko a makaranta babu club din da nake shiga sai na wasan kwaikwayo kuma idan na shiga drama kowa sai ya yi nishadi kuma ayi ta tafi don ina acting a cikin zuciyata kamar da gaske. Dalili kuwa shine dan ina son abin kuma bana tsayawa akan abinda director ya fada min sai na qara nawa kuma nawan da nake qarawar ya na zama daidai da sakon ake so a isar. Na yi suna a wannan fage da wuya a yi wani wasa baa saka ni ba tun daga furamarehar zuwa sakandire.
Ya kamata ace iyayena sun bi nawa ra'ayin ko baa bar ni na zama 'yar fim ba a bari in karanci mass com. Tunda ina shaawar labarai da duk abinda zaa haska ni a talabijin ko a saurare ni a radiyo.
Amma aka ce sai na karanci medicine, na fada musu abinda na fi so na karanta cewa ina so in karanci mass communication ina son in yi aikin jarida. Aka hana ni aka hada min da fada da gargadi aka tabbatar min ba shawara ake ba ni ba umarni ake bani.
Na tafi raina baya so kuma na tabbatar ba zan iya yi ba dan babu abinda na qi jini irin aikin asibiti. Na zauna da masana da dama a cikin malamanmu na jami'a ina tambayarsu akan maslaha akan wannan matsalar da nake ciki Cesar ga abinda iyayena suke so ga kuma abinda nake son in karanta. A cikin kashi dari kashi casa'in sun ce in bi ra'ayina, wadanda ma basu ba ni goyon baya ba sun ce in je in zauna da iyayena in fada musu zuciyata sun san zasu amince min. Haka suke gani a matsayin su na turawa wadanda suka san cikakken hakkin yaro. Ni kuma na san daga irin qabilar da na fito ba zan iya komawa in isar da buqatata ba, ko da na je ma ba zan sami abinda nake so ba.
Gaba gadi na bi ra'ayina na bi duk hanyar da zan bi aka bani course din da nake so, bayan an yi min jarabawa na ci, na ci da yawa ma har sai da suka yi mamaki, rabu da abinda yaro ya ke so.
Ina boyewa a gida har na gama digiri na yi masters na hada da wasu kwasa-kwasai domin karatun medicine ana dadewa na riga su gamawa. A wannan zaman da na yi ina jira lilitoci su gama sai mu koma gida tare da su sai aka dinga yi min tayi akan in fara amfani da karatun mana in fara acting a fim. Tsoro nake ji kada a ganni a fim amma a haka na daure na fara yi din. Ina tsoron kuma na yi na san zata fanjama kuma zata yi fanjam da ni. Kwakwalwata ta kasa hango min gejin masifar da zaa tafka. Na san ina cikin matsala sosai idan aka ji wannan labarin a gidanmu. Raina ne kadai ba zaa fitar min ba amma kowanne irin bala'i da ku ka sani na duniya na hango ni a cikinsa.
Iyayena sun zo wajen graduation dina na dinga ta kame-kame ba su san har na yi graduation dina tuntuni tare da 'yan ajinmu ba.
Sai da aka gama kiran likitoci kakaf amma babu sunana babu ni babu dalilina dan na gudu na buya.
Daddy na ya je ya sami malamai aka dubo masa a inda sunana ya fada su ka zauna su ka wayar masa da kai akan matsalata na san su na bata bakinsu ne yadda maganarsu take Shiga ta kunnen dama haka take fita ta kunnen hagu. Wannan shine labarina." Ta gyalgyale da dariya kowa ma dariyar yake yi a wajen. Har da General da matarsa. Gwamna ya yi ta tuntsira dariya dan ya san halin abokinsa, danger kenan.
Kowa ya qagu ya ji qarshen labarin nan daman in ta yi magana da Hausa tana maimaitawa da turanci saboda kowa ya fahimta. Nihal ta ci gaba da magana ta ce " Hukunci daya ya dauka akaina kuma wannan hukunci shine labarin da yake cikin fim dina da aka yi mai suna ' a wata duniyar' dukka abinda ya faru da Jarumar fim din shine ya faru da ni."
Sai aka kunna fim din aka haska kowa ya na kallo ga wadanda basu taba gani ba, an haska wasu daga cikin sinasinai masu muhimmanci, daman akwai fassara turanci a qasa wadanda ba sa jin Hausa ma sun karanta sun fahimta."
Nihal ta ci gaba da cewa na sha wuya sosai, sai na yi taga-taga zan fadi qasa kafin in kai qasa sai in saka hannu in tokare sai in miqe. Sai in sake yin tuntube ina qoqarin faduwa qasa sai in sake miqewa tsaye da qarfi. Har sai da na kai matsayin da ban sake yarda na yi tuntube ba balle in fadi qasa ba. Na tsaya kem da qafafuwana har ma wasu suke dafa kafadata su miqewa tsaye. Alhamdulullah wannan abin alfahari ne a wajena. Babu qabilar da na fi jin farin ciki irin in yi fim a cikin qabilata, ina son Hausawa ina son yaren Hausa."
Aka dauki tafi ana ihu ana mata jinjina.
General ne ya taso da sauri ya hawo kan stage ya zo ya rungume ta, ya dafa kafadarta sannan ya karbi lasifiqa yayi magana.
Ya ce "ni ne Nuren mubin mahaifin shahararriyar 'yar fim din nan Nihal Nuren Mubin. Tabbas labarin nan da ta bayar ya zaburar da ni kuma ya haska min in da na yi kuskure. Ina sane da abinda 'yata tafi so amma saboda wani alqawari da na qudira a cikin zuciyata na manta da na ta ra'ayinta, na manta da walwalarta, na manta da duk bacin ran da za ta sha domin ita ce za ta shiga aji ta sha wuyar yin karatun. Na shiga aikin soja ne don ina so sosai, ba dan iyayena su na so ba. Danginna kakaf ba sa so in zama soja saboda su na tsoron zaa kashe ni. Amma da yake ina so na shiga da qarfina kuma na yi abinda ya kamata, an yi alfahari da ni a qasar nan. Lallai na yi kuskure kwarai da gaske musamman da na qeqashe idona na rufe na qi kallon hawayen da masoyiyata abin qaunata Prof.Shatu Nuren ta dinga zubarwa ta ba ni shawara in bar Nihal ta zabi course din da take so amma na qi.
Daga yau ni Nuren Mubin na yi alqawari zan dinga duba ra'ayin iyalina ina ba su dama su yi abinda su ke so na daina zabar mu su kuma na daina tilasta mu su akan abinda basa so. Duk abinda suke so zan basa su dama su yi abinda suka ga zasu iya. Ina neman afuwa ga Nihal da 'yan uwanta maza guda bakwai Muhammad, Abubakar, Umar Usman, Aliyu, Hamza Mu'awiyya da mahaifiyarsu Haj. Shatu Nuren Mubin 'yar Aljanna. Mata ta gari, ta yi hakuri da ni da halayena."
Zazzafan hawaye ne ya sirnano daga idanuwansa sai ga Shatu da yaranta maza guda bakwai kakaf da Nihal mace daya tilo ta takwas akan stage suka rungume shi, su ma hawayen suke yi. Sai kowa ya miqe tsaye dan girmamawa ana tafa musu.
Bayan su General sun sauka sun koma mazauninsu Nihal ta buqaci da Hashim da Naja'atu su hawo kan stage don ta yaba musu kuma ta karrama su bisa goyon baya da taimako da suka yi mata a rayuwa. Kan ka ce kwabo sun bayyana. Kalaman Nihal sai da ya tayarwa da kowa tsikar jiki aka yi jinjina ga Hashim da Najaatu. kwalla ce take disa daga idanuwansu su dukka, bayan da ta gama na ta bayanan. Hashim ne ya karbi lasifika ya fadawa duniya ko wacece Nihal, kyawawan halayenta da tausayin talaka da taimakon da ta yi masa da iyalansa a rayuwa. Ya tabbatarwa da duniya cewar ko me ya samu ko me ya zama a rayuwa a sanadiyyar Nihal ne.
Najaaatu ta karbi abin magana ta yi bayanai masu ratsa jiki akan Nihal, ta na magana tana kuka har sai da kowa ya ji hawaye shima.
Ta ce Nihal ce ta tsame ta daga halaka ta dawo da ita kan hanya saboda ta gudo ta afka harkar fim ba tare da sanin iyayenta ba. Nihal ta dauke ta ta mayar da ita gida, ta gargade akan kada ta dawo sai da yawun iyayenta. Kuma sai da suka saka mata albarka sannan ta fara ganin haske. Nihal ce ta hada soyayyarta da mijinta Bash Auta dan haka Nihal ta yi mata komai a rayuwa.
Nihal ta karba ta cewa jama'a su taya ta murna da godiya Hashim da Najaatu da Siyama sun haifi 'ya'ya mata sun saka sunanta. Ana ta tafi ana jinjina wannan aminta ta tsakani da Allah. Daga qarshe Nihal ta karrarama Hashim da Naja'atu da kambun kyauta wato awards.
Bayan su Hashim sun sauko daga kan stage. Nihal ta gayyaci Siyama da ta jawo kan stage in da Nihal ta gabatar da Siyama a matsayin aminiyar gaskiya wacce ta amince gara ta fada cikin halaka akan ta bude sirrin aminiyarta. Siyama ce kadai ta san ta canza course amma bata taba fadawa kowa ba haka bayan an fara ganewa babu ukubar da baa sakata ba amma bata fada ba. Su ka rungume juna su na hawaye. Nihal ta karramata da kambun girma.
Nihal ta sami kyaututtuka da dama a wajen taron daga manyan kungiyoyi har ma da qanana.
Gwamna da kansa ya bata kyauta (award) game da yadda take yin aiki tana taimakon mata da yara hakan ya daukaka darajar gwamnatinsa. Taro ya tashi kowa da yabon Nihal Nuren Mubin.
Alhamdulullah godiya ga Allah Madaukakin sarki da Ya bani basira, dama da ikon kammala wannan qirqirarren labari.
Abinda na kuskure Allah Ya yafe min wanda na fada daidai Allah Ya hada mu ni da ku a cikin ladan.
Godiya ta musamman ga Khaleesat Haidar da Aleesa online writers da suka tarye ni hannu bibbiyu suka wayar min da kai akan yadda abin yake.
Godiya ga dinbin masoya da su ka sayi labarin nan.
Godiya ga wadanda suka bani karfin guiwa akan in dawo rubutu Nura Nasmat da Sumayya Takori.
11/14/21, 7:20 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 鉂�
GABA GADI
NA
JAMILA UMAR TANKO
(JUT)
Gwamna muse ya cikawa 'yan fim alqawuran da ya dauka, duk abinda ya ce zai yi musu yayi har ma ya qara wasu akansu.Ya bawa Nihal kwamishiniyar mata da qananan yara duk da ma da farko ta qi karba amma an matsa mata sai da ta karba dole. Dalili kuwa kowa ya tabbatar ita ce ta fi kowa tausayin mata da qananan yara da kudinta da jikinta ma yi musu take yi balle kuma ta zama hukuma. Ta na yaqi da mata masu shaye-shaye tun daga cikin gida wato 'yan fim har zuwa ga 'yan waje.
Amare da angwaye su na zaman lafiya cikin jin dadi da nishadi, arziqi da soyayya.
Cikin ikon Allah matar Hashim ta haifi 'ya mace aka saka mata suna Nihal. Watan da ya zagayo Najaatu ta haifi 'ya mace aka saka mata suna Nihal. Major Abubakar da Siyama sun haifi 'ya mace sun saka mata suna Nihal dole su saka sunanta mana dan ita ta hada wannan qaqqarfar soyayyar.
Nihal ta yi farin ciki matuqa kuma ta yi wa takwarorinta tara ta arziki. Ita ce dai ba ta sami haihuwa da wuri ba sai a yanzu ta sami ciki qaramin kuma an tabbatar mu su 'yan biyu ne. Ita da mijinta sun yi shiru tukunna basu fadawa kowa ba. Su na a addu'a kada a gane sai ya girma sannan kowa zai sani. Wannan babban abin farin ciki ne a wajensu.
*** *** ***
Yau ne daren karrama gwanaye(Award Night). Wanda wani babban kamfani da hadin guiwar gwamnati suka hada domin karrama wadanda suka yi wata bajinta a fim da wadanda suka kokari wajen taimaka ci gaban harkar.
Daren wata asabar a wani babban dakin taro in ka Shiga sai ka rantse a Amerika kake baa kano ba. Nihal kenan ta kwaikwayo wancan dan haka ta debo turawan ne suka zo suka tsara. Baa taba samun wajen da ya yi kyau kamarsa ba daman ta karantawa 'yan fim yadda ake yin taron da irin kwalliyar da ake yi. Dan haka kowa da kowa ya fito tsaf gwanin kyau. Ta basu shawara mata da maza da su yi Shiga irin ta al'ada wannan shine zai banbance taron Hausa fim da taron igbo fim da taron turawa. Manyan baqi daga turai Hausawa mazauna can da Turawan da 'yan fim din Lagos da Abuja na yarbawa da na inyamurai.
Shigar Nihal ta yi kyau sosai dinkin atamfa ne amma fa a turai aka dinka yankan da yadda aka kwalmada zaka zaci English wears ne. Ita da Muqaddas sun yi shiga matching color shima da shadda aka yi masa nasa dinkin aka rasa gane ko menene su ka saka.