Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 110552 words

Chapter 14 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

son sai ta je kiransu. Sai ya bata tausayi ta fara tafiya a nutse ta nufi wajen motar. Gefen direba aka bude sai ga Bash Auta ya bayyana, ya kira sunanta gami da dubanta sama da qasa.Ta yi budu-budu da ita da qura.Qafafuwanta fututu, tun daga nan ya tabbatar wannan ba za ta iya zama shararriyar Jaruma ba a shekaru kusa. Babu alamar wayewa a tare da ita ko ta kwabo.
Bash ya yi dariya ya fada a cikin gatsali "Darakta wannan ita ce Nihal Nuren Mubin me abin mamaki."
Darakta Abbas ya na zaune a gefen Bash sai leqe yake.
Ya yi dariya ya ce "Malama Nihal bismillah zagayo ta nan mana mu yi magana."
Ta zagaya ta gefen qofar da ya ke zaune, ta durqusa ta gaishe shi cike da ladabi.
Tun daga qafarta har kanta ya kalla, ta yi fururu kai ka ce dambe ta yi a cikin yashi.
Ya murmushi ya tambaya "daga ina kike ne haka?"
"Daga qauye." GABA GADI ta amsa masa.
Ya sake maimaitawa "daga nan qauyen ki ka sake shiga can cikin qasurgumin wani qauyen?Maimakon ki taho gari irin su Kano."
"Na fi jin dadin rayuwata tare da 'yan karkararmu." Ta bashi amsa daidai da tambayarsa.
"Na ga bakinki a bushe kamar kina jin yunwa da qishir ruwa.Bash bata sauran tsiren nan da lemo ta ci ko ta dawo hayyacinta." Darakta ya fada a lokacin da ya ci gaba da dubanta sama da qasa.
Nihal ta girgiza kai ta ce "ba zan ci ba,na gode."
Hashim ya zabura ya ce "kawo in riqe mata,kunya ce da ita."
Bash ya miqa masa, hararar Hashim kawai take yi.
Darakta ya ce " meye abin harararsa dan ya fadi gaskiya?Kowa ya ganki ya san ki na jin yunwa watakila ma noma ki ka yi, ga ki nan kin yi bududu. Ko fadan canis ku ka yi a kan yashi?"
Da ta yi dariya sai su ka ga ta qara yin kyau, ga wata siriryar wushirya da dimful a kumatunta sun bayyana.
Darakta ya ce " ko ke fa da da ki ka yi dariya kin fi kyau, amma mu zo tun daga uwa duniya Kano ki na ta sha mana kunu."
Ya saka hannu a aljihu ya zaro naira dubu biyu ya miqa mata. Ya ce "ki je ki ci abinci. Zan yi magana da Tukur ko wannan yayan na ki Hashim don ya ba mu lambarsa idan buqatar hakan ta taso. Ni Sunana Darakta Abbas dan naga kamar baki san da wa kike magana ba ma."
Ta girgiza kai ta ce " ka bar kudinka, na gode sosai."
Kafin mamaki ya bar fuskokinsu ta juya ta tafi, ta fisgi mukullinta daga hannun Hashim ta wuce.
Sun dade su na kallonta har ta bude get ta shige. Hashim ya na ta bayani akan su kawo dubu biyun ya kai mata ita me kunya ce.
Bash ya tamabaya "wannan gidan waye me kyau ta bude ta shiga?"
Hashim ya zabura ya ce "gidan 'yan uwansu ne take dan zama kafin mu tara kudi mu kama mata dakin haya."
" ko kudin kama dakin haya bata da shi amma ta ke jan aji?Har a bata kyautar kudi ma ta qi karba? Darakta rufe qofar mota mu tafi kawai." Bash ne ya fada cikin fushi gami da jan dogon tsaki.Ya fusgi mota su ka tafi rayukansu a bace.Maganar ta su ke ta yi har su ka iso Kano.
Bash ya na ta bambamin fada ya na cewa " ka san mutumin qauye kuma ya hadu da jahilci.In ba rashin wayewa ba ki na kucaka ki kaga danqareriyar mota da manyan baqi. Baqin ma Bash Auta da Darakta Abbas ne da kansu amma ki nuna baki taba saninmu ba kuma baki damu ba. Ka da ma ka saka ta a fim dinka, kawai ka rabu da ita ta qare a qauyen."
Abbas ya yi dariya ya ce " nima dai na yanke hukunci ba zan saka ta ba ma kawai a bar maganar ta, amma na yi mata uzuri saboda a galabaice take."
Hashim ne a fusace yake ta bugun get din Nihal, sai can da aka jima ta fito ta dube shi ransa a bace.
Ya ce " shikenan kin yiwa kanki, sun yi fushi sun tafi."
Ta yi murmushi ta ce " ba rabona ba ne idan rabona ne zan samu."
Akan dakali su ka zauna Hashim ya na ta cin tsire da lemo saboda baqar yunwar da ta addabe shi.Ya na zaiyano mata wuraren da ya tafi nemanta.
Tukur ne ya ja ya tsaya akan babur dinsa har da tayar da qura dan a fusace yake.
Ya kira sunanta sannan ya danqara ashar ya dora da cewa " ba na son wulaqancin banza.Mutanen nan tun shekaranjiya suke yi min waya na sa a nemo ki aka rasa ki, ba su haqura ba suka taso da kansu su ka zo, aka dinga nemanki tare da su. Da su ka ganki sai kika yi musu wulaqanci.Ke wacece da za ki wulaqanta babban Darakta? Da me kike taqama? Wannan da baa san asalinki ba ma ba qaramin girman kai za ki yi ba. Kuma da kin yi boko da an shiga uku.Wawuya kawai sai shegen girman kai ba ki da ko sisi.Bari ki ji wallahi in kika sake yi min haka in ga samu na ga rashi, ba zaginki kadai zan yi ba dukan tsiya zan yi miki. Dan haka ki shirya gobe mu je Kano mu ba su haquri."
Kanta a sunkuye a qasa zuciyarta na tafasa kunnuwanta na zuqar baqaqen maganganunsa masu muni.Saura kadan ta taka masa burki ta dai daure. Har ya gama ya ja babur dinsa ya tafi ba ta dago da kanta ta dube shi ba.Hashim ne ya karba shima ya ci gaba da zazzaga mata ta sa masifar, shima haushinsa kenan sun ga samu sun ga rashi.
Da ya leqa fuskarta sai ya ga hawaye ne yake ta disa daga idanuwanta sai ya ji tausayinta.
Ya shiga lallashi "Au Nihal kuka kike yi? Ki daina kuka.Kece da abin haushi wallahi."
Ya ciro wani daddaudan hankici daga aljihunsa ya naninqa mata a kumatu. Ba ta san sanda ta rufe shi da duka ba, ta tashi a fusace ta shige gida ta datse get dinta.
Hashim ne yake ta shafa wuyansa inda ta mammake shi.
Ya yi dariya ya ce "shegiya uwar qarfi, wallahi qashi daya gare ta. Gara in bar qofar gidan nan kada ta sake dawowa ta yi fadan canis da ni kamar yadda ta yi wa Amina 'yar kwalisa."
Nihal na shiga gida sai ta barke da kuka me tsanani, ta na takaicin yadda ta tsinci kanta cikin qasqantacciyar rayuwa wacce kowa ke da ikon zaginta da kyara da wulaqanci. Daman Tukur ya saba yi mata irin wannan tijarar, yanzu kuma ga Hashim abokinta kwaya daya kacal wanda take samun sauqi a wajensa shima ya fara kyararta.
" Ina zan saka raina?" Nihal ta fada a lokacin da ta kifa kanta a kan filo tana rusa kuka.
Da daddare Shazali ya zo ya kwankwasa mata qofa, ta bude da sauri suka tsaya a qofar gida.Bayan ya miqa mata ledar abinci sai ya shaida mata mahaifinta ya ce ya hada su a waya zai yi magana da ita.
Da farko ta qi yarda dan bata so su sake jin muryarta a shekaru kusa,sai dakyar ta yarda ta karbi wayar. Da ta ji muryar mahaifinta sai ta ji dadi, wani hawaye mai sanyi ya dinga kwaranya.Amma da ya isar mata da saqon da zai fada sai ta ji tamkar tunda Allah Ya halicce ta bata taba jin labari mai zafi irin na sa ba.Ya fada ya maimaita yau ce rana ta qarshe da zai ci gaba da kashe mata kudi.Ya ciyar da ita har na tsawon watanni uku ya kamata in har aikin take ace yanzu tana da wasu kudaden aikin da aka biya ta, dan haka sai ta fara yiwa kanta komai da su. Ya tabbatar mata da cewa ya janye siya mata abinci, kudin kashewa,da biya mata kudin haya.Dan haka idan bacci take ta farka dan baya ganin finafinata su na yawo a gari.Har Shoprite yake shiga sinima in zaa saki sabon fim amma bai taba ganinta ba.Ya na so ta sani ba bacci ya ce ta je ta yi ba, aiki tuquru yake so ta yi.
Ta runtse ido zafafan hawaye ke kwaranya ta fada cikin rugugin kuka ta ce " Daddy! ka yi hakuri ka daina bibiyar rayuwata, ka bar ni zan san yadda zan yi in tafiyar da rayuwata.Ni Nihal Nuren na yi maka alkawari ba zan sake neman komai daga wajen kowa ba. Fina-finaina kuwa zasu cika gari, zasu kai in da ma baka taba zato ba insha Allah, ka bani lokaci kawai kuma ka yi min addu'a. Na gode."
Ta miqawa Shazali waya ta shige ciki gida ta datse. Sai a yanzu ta yi kuka na gasken-gaske. Ta ji kamar duk duniya sun tsane ta, bata da kowa kuma. Qarfin zuciya ne kawai yake ta sauko mata.Haqiqi yanzu ne zata fita ta yi gwagwarmaya ta daina bacci.Tukur da Hashim sun fada mata gaskiya cewar tana wasa da damarta, haka ta daina ganin laifin Amina da Mami akan zagin da suke yi mata tabbas su na tsoron kada ta zo ta meye musu wajen cin abincinsu. Gaskiya ne idan aka fito filin daga baa yi da wasa kowa qoqari yake ya kayar da abokin adawarsa.
" Ni Nihal Nuren Mubin na yi alkawari daga rana irin ta yau ba zan sake zama koma baya ba." Alkawari Nihal ta yi.
Kusan a tsaye ta kwana ta na ta kai kawo a cikin gida har sai da assalatu ta kusa, sannan ta je ta yi alwallah ta dinga jero nafilfili ta na neman tsari daga dukkan sharri, ta na neman alkhairan da suke cikin wannan harka. Ta yi addua Allah Ya daukake ta,Ya cika mata burinta ta kuma cikawa mahaifinta na sa burin.Ta na neman tsari daga jin kunya da dariyar maqiya.
Satin ta guda tana wuni a qauye tun daga safe har dare a wajen koyon aikin kwaba laka, har sai da ta tabbatar ta iya sosai.
Hashim da Tukur sun neme ta a garin har sun gaji baa ganta ba domin bacci ne kadai yake dawowa da ita ta buga sammako ta sake fita kuma. Kayan abinci ta siya sai ta dawo take girkawa ta ci.
A yau ba ta fita ba dan haka Hashim ya same ta a gida, daya kwankwansa sai ta fito.
Bayan sun gaisa sai ya ce da ita " fushi kike yi da ni kenan shiyasa ma kika qaura kika bar garin har sati guda. Ran Darakta Tukur ya baci ya ce ki zo ku je Kano mu basu hakuri kin qi zuwa.Ya na ta fada yanzu ma shi ya ce in kira ki. Fim din Darakta Abbas dai kin rasa dan har an fara shooting, jiya ma acan Tukur din ya wuni ya kai musu hayar wasu kayan. Haba Nihal ki na wasa da damar da Allah Ya baki amma ki sani ita dama zuwa take sannan ta wuce dan haka kada ki bari ta wuce ki."
Ba ta bashi amsa ba ta shiga ta kimtsa ta fito ta kulle gida suka nufi ofishin Tukur.
Daga shigarta ko sallamarta basu amsa ba a fusace Tukur yake yi mata magana ya na tsawa kamar zai mare ta. Amina, Najaatu da Mami ne a zaune a cikin ofishin.
Hannu Nihal ta daga ta dakatar da shi ta fada cikin fushi " dakata Darakta ya isa haka.Ka dade kana zagina har kana marmarin kai hannu jikina, ban yarda ba bazan taba daukar wannan ba.Fim ne in baa saka ni ba sai me? Ba rabona ba ne idan rabona ya zo zan yi. Menene damuwarku? Menene matsalarku? Idan na qi yi meye na tayar da hankali dan na qi yin fim? Babu mai ciyar da ni ko biya min haya. Ina ganin girmanka ka tsaya a haka kada ka kai ni bango."
"Ke Nihal ki na da hankali kuwa? Da Darakta Tukur kike magana fa." Hashim ne ya fada a gigice gami da tasowa da gudu zai toshe bakinta. Ta tunkude shi gefe.
Mami da Amina su ka dauki salati har da mimmiqewa tsaye su na dafe kirji.
Tukur ya koma ya zauna ya na shessheqa cewa yake "ku bar ta ta dake ni. Ai na wayar da ita, ta daina saka yagaggiyar atamfa."
Ta juya a fusace za ta fita daga ofishin sai ya ambaci sunanta. Ta waiwayo a fusace ta dube shi.
Ya harare ta ya ce " ba zan sake saka ki a cikin fim dina ba kuma dukkanin abokaina na nan garin da na Kano sai na tabbatar ba zasu sake saka ki a fim ba. Sai zaman garin nan ya gagare ki wallahi da ni kike zance."
" Ina jira." Nihal ta fada ba tare da fargaba ba . Ta fice abin ta.
Hashim ne ya durqusa a gaba Darakta yana magiya yana bada hakuri amma kamar zuga shi yake sai fada yake ya na kumfar baki. Amina da Mami sun ji dadin da basu taba ji ba dan haka sai suka baje murya su na sake tunzura Darakta su na qarawa da sharri.
Najaatu ce ta fito a guje ta tari Nihal a hanya ta na bata baki tana yi mata nasiha. "Haba Nihal yaya za ki yi haka, ina haqurin nan na ki da juriya? Su Mami ma bazanye suka zage ki kika yi haquri dan Darakta ya zage ki me ya sa za ki ji zafi har kiyi masa rashin kunya?"
Ba ta bata amsa ba tafiya kawai take ba tare da ta san in da take jefa qafarta ba.
Najaatu bata fasa bin ta ba tana ta bayani har suka isa qofar gidanta. Akan dakali ta zauna tana huci yayin da Najaatu ke zaune a kusa da ita. Sun dade a zaune sun yi shiru.
Sai yanzu Nihal ta bata amsa " haba Najaatu, Tukur ya na wuce gona da iri so yake ya fara kai hannu yana dukana bayan zagi.Ni akuya ce ko baiwarsa? Ba zan dauki wulaqanci ba kuma dan adam baya wuce rabonsa."
Najaatu ta dafa kafadarsa ta ce " haka ne amma da kin daure musamman da yake a gaban maqiyanki ne, yanzu gasu can su na jin dadi."
Hashim ne ya qaraso ya zo gefe ya zauna a sanyaye ya ce " yauwa Najaatu ki taya ni fada mata. Nihal taurin kai ne da ita tanzu,amma da farko zuwanta kamar mai sauqin kai."
Wayar Hashim ce ta dauki ruri ya na dubawa ya ga sunan Darakta Abbas, ya zabura ya miqe tsaye yana durqushe-durqushe dan ladabi.
" Ina Nihal? Ta na tare da kai ?" Darakta ya tambaya.
Hashim ya ce " eh gamu nan tare."
Hashim ya naniqa waya a kunnen Nihal gami da yin magana cikin rada "Darakta Abbas ne."
Nihal ta ji gabanta ya fadi, ta gaishe shi sannan ta tsaya ta na sauraron abinda yake fada.
" ki taho Kano da sauri ki same mu a zoo road zan sa a kawo ki qauyen da muke, akwai wani aiki da zamu yi da ke. Please dole sai da ke zai tafi daidai. Idan baki da kudin mota ki ranta.Tunda baki san Kano ba Hashim ya rako ki."
Ta amsa cike da ladabi "gamu nan zuwa."
Hashim ya daka tsalle ya dire yana murna ya ce "Alhamdulullah shikenan Darakta Tukur da su Mami sai su mutu. Me ya ce miki?"
Nihal ta maimaita abinda Darakta Abbas ya ce sai Najaatu ma ta hau murna ta na magiya itama zata raka su.Hashim ya zabura ya ce ba za ta je ba, amma Nihal ta ce su tafi tare babu damuwa .
Ko gida ba ta shiga ba kawai babura suka tare su ka hau suka tafi tasha, su na zuwa su ka hau

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads