Showing 30001 words to 33000 words out of 110552 words
Chapter 11 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
na dadewa bata ga dubu daya ba ma balle dubu na dukan dubu har guda goma sha hudu .
Nihal ta fice daga gidan ba tare da ta yi masa wani bayani ba. Hashim ya zabura ya biyo ta a baya ya na tambayarta menene dalilinta na yin haka? Kudinsu kenan fa kakaf ta dauka ta yi kyauta da su .
Ta tambaye shi "da na yi kyautar da kudin wa na bawa? Hashim kana da imani kuwa? Inna ta ban tarihi mahaifinka ya rasu tun kana ciki baa haife ba, mahaifiyarka ta rasu a ranar da ta haife ka ko ganinka bata yi ba. Kakanninka ne su ka dauke ka a cikin tsumma. Inna ta shayar da kai Nononta har kabilata kwari sannan sai sun yi noma sun yi surfe su ke samu su ciyar da kai. Amma yau ka zama mutum naira dari ta gagare su alhali kana da dubu goma sha hudu a aljihu. Ka bani mamaki ban ji dadi ba . Dan me kake tausaya min amma baka jin tausayin tsofafin da qarfinsu ya kare akanka? A yanzu ne suke tsananin bukatarka. Inna ba zata sake yin surfe ba kai ne kake da hakkin ka ciyar da su."
Ya ji kunya da nauyi ya kama shi ya tabbatar bai kyauta ba. Amma kuma hukuncin da Nihal ta dauka akansa yayi tsauri, ai da sai ta raba kudin gida biyu ta bar masa rabi.
Nihal ce ta katse masa tunanin da ya tsunduma ya na yi ta ce " a satin nan zan biya ka kudinka dubu goma sha hudu. Kada ka damu na san kana da bukata kai ma."
Ta juya ta tafi a fusace ta hau babur ta bar shi a tsaye ya na nadama.
Idan Nihal bata da aikin Fim to tana tare da Kakar Hashim tana daukar ilimi, shaquwar da suka yi ta kai har basa jin dadi idan basu ga juna ba. Nihal tana da takarda da biro tana rubutawa. Abu kamar wasa har unguwa suke tafiya tare ko su yi bulaguro zuwa kauye su wuni cur acan biki ko suna a kauyakun da ke kusa da Wudil. Ta na sake samun ilimin zamantakewa da al'adun Hausa domin har yanzu a qauyukan basu zubar da al'adunsu na gado ba na ainahin Hausa Fulani.
Qanin Inna bafaje ne ya yiwa sarkin kano hidima kafin tsufa da ciwo ya kama shi ya dawo gida. Ta sami tarihin sarautar qasar Hausa sosai a wajensa. Ya na jin dadin yin hira da Nihal domin ta na da saurin gane abubuwa, babban dadin da ya fi ki shine yawan kyautar kudi da ta ke bashi na ban mamaki.
Idan su ka kai yamma har dandali take zuwa tana zama tare da 'yan Mayan kauyen tana nade waqoqinsu irin na al'adarsu. Muryoyinsu gwanin dadi, zaqaqan baituka masu dauke da hikima, sakonni masu muhimmanci suke isarwa, babu kida sai tafi babu rawa babu girgiza babu shigar da zata fitar da tsaraici. Babban abin sha'awar babu cudanya da mata da maza, mata su na yin nasu maza ma haka .
Ta ga yadda budurwa ke haduwa da saurayi a yi soyayya har ta kai ga yin aure wanda yayi daidai da al'ada da addini cikin jin kunya da mutanta juna.
Ta halacci bikunkunan qauye da yawa ta nadi abubuwa da yawa wadanda bata taba sanin su na faruwa ba .
Laptop ta ce Shazali ya siyo mata, baa dauki lokaci mai tsayi ba sai ya kawo mata sabuwa fil a kwalinta . Ta na ajiye a gefen katifarta kullum da daddare in ta zo kwanciya sai ta yi rubutun fim . A haka ta rubuta fina-finai masu yawan gaske kuma masu ma'ana.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI
EP 10
Watannin Nihal uku cur a garin Wudil da kewaye, ta fito a cikin fina-finai goma sha uku, ban da wadanda ta dan firfito a na birni da kuma wadanda aka yi amfani da jikinta a ka dora fuskokin wasu.
Sai a yanzu ne aka fara sakin finafinan da Nihal ta firfito tabbas an fara hasko ta, mutane su na shaida fuskar yayin da sunanta ya fara reto a qwaqwalen masu kallo.
Aisa buzuwa ta samu daukakar da bata taba samu ba a lokacin da aka saki wannan fim din da ake tunanin ita ce ta yi bajintar nan. Ko ina yabonta ake ana sake jinjina abinda ta yi. Kafin ka ce kwabo ta sami goron gayyata daga manyan firodusoshi akan ta zo ta shiga manyan finafinan da za su yi. Sai dadi take ji tana taqama tana daga kai har zabe take yi. Yayin da aka dinga yi mata tayi da kudade masu yawa, tun daga nan ta ji a jikinta kakarta ta yanke saqa wannan shekarar ta ta ce. Darakta Idris bai isa ya tona wannan asiri ba saboda daukakar Aisa akan fim din shima daukakarsa ce har ma ya fita morewa saboda yana kwasar romon riba a kasuwa. An siyar da fim din sosai, an haska shi a manyan sinimomin dake cikin biranen qasar nan.
Idanuwan Muqaddas kem akan finafinan Hausa ya na so ya ga abar qaunarsa, sai a yanzu ya ci karo da Fim din da ta fito guda daya. Ya sha takaicin ganin Nihal a cikin tsumma ta na gwagwarmaya da qauyawa. Sunanta ne ma da ya gani ya sake gasgatawa ita ce amma ba kowa ne zai gane ta ba, in har ka san ta ada da.
Ya ja bakinsa yayi shiru bai nunawa kowa ba gudun kada rai ya baci, dan shi har yanzu ita ce zabinsa duk da mahaifansa sun ce sun gama magana ba zai aure ta ba.
Kasuwar Aisa tana ta ci amma in da gizon ke saqar shine da aka bata fili ta maimaita kwatankwacin abinda ta aikata a wancan Fim din sai abu ya gagara.
Kan kowa ya daure aka kasa ganewa, aka yi-aka yi ta kwatanta ma ko bai kai yadda ta yi a wancan karon ba amma ta gagara aka yi. Daga nan sai kokoto ya shiga zuqatan mutane aka kasa gano bakin zaren.
Darakta Abbas.H.Abbas ne ya zare farin gilashin da yake fuskarsa ya ajiye akan tebur ya kalli Darakta Idris Hayat ya ja doguwar ajiyar zuciya ya ce " na yi mamaki na yi takaici matuqa akan abinda Aisa Buzuwa ta yi mana jiya."
Darakta idris ya dauke kansa daga kan karatun script ya dubi Darakta Abbas ya tambaya cike da zumudi me "Aisa ta yi muku ?"
Abbas ya yi tsaki ya girgiza kai ya ce " ganin yadda ta yi bajinta a wannan sabon fim din da ka fitar kwanan nan mai suna SIRDi. Sai na gayyace ta akan ta zo ta yi min wannan babban fim din nawa, ta dinga yanga tana ja min rai sai da na lunkuba mata kudi sau uku akan kudin da nake biyan sauran jarumai. Could you believe an tafi location daga nan har Jos amma Aisa ta kasa katabus ko hawa qaramar bishiyo ta kasa. Na yi mata magana ta yi fushi kamar zata yi min rashin kunya. Bash Auta yana cikin fim din ya ce min in zo in same ka za ka fada min gaskiyar al'amari. Idris ka ajiye maganar adawa saboda kowa yana son na sa ya fi na kowa kyau. Kai abokina ne tun muna yara ba za ka so in yi asarar miliyoyin kudina ba. Ka fada min gaskiya wanne siddabaru ku ka yi ? "
Su ka kwashe da dariya su ka tafa hannu. Idris ya bude kwanfiyutarsa ya dubo fim din sai ya juyo masa da fuskar kwanfiyotar gabansa daidai fuskar Nihal ya ce "dubi yarinyar nan sosai ."
Abbas ya danna puse ya kalle ta ya sake kallonta ya ce " kai ban santa ba, ban ma taba kallon fim dinta ba ."
Idris ya gyada kai ya ce " ba za ka santa ba daman dan ba fitacciya ba ce, a qauye take hidimarta tana can cikin 'yan camama."
Abbas ya gyara zama ya ce "ban fahimce ka ba fa. Me kake so ka ce min ne ?"
Idris ya yi shiru na 'yan lokuta ya ce " maganar gaskiya baqauyiyar nan Allah Ya yi mata baiwa wajen iya tsalle da fadan canis. Kai in fada maka har yadda ake riqe fitala da saita kyamara ta iya. Amma za ka sha mamaki idan na fada maka cewar ko script bata iya karantawa ba, dan bata je makarbata ba."
Mamaki marar musaltuwa za ka iya gani a kan fuskar Abbas.
Ya tambaya " meye alaqar tattaunawar da muke yi da wannan baqauyiyar?"
Idris ya ce " na bar maganar nan a matsayin sirri kai ne kadai zan fadawa gaskiya saboda kai abokina ne kuma tabbas ka kashe kudi masu yawan gaske bana so ka yi asara. Duk acting din nan da ka gani Aisa ta yi a fim dina wanda ya burge ka ya ja hankalinka ka neme ta, to ba ita ce ta yi ba wannan baqauyiyar ce ta yi. Haka hoto da ka gani ya fito fes da taimakonta wajen saita kyamara. "
Gumi ne ya ke ta ketowa Abbas duk da A.c da ke busowa a cikin ofishin, kansa ne ya daure.
Bash Auta ne yayi sallama ya shigo bayan ya miqa musu hannu sun gaisa sai ya sami kujera ya zauna. Da alama shima ya zo wajen Idris ne ya na da magana da shi.
Abbas ya ce da Idris "zo mu fita waje mu qarasa maganar. "
Idris ya ce " ah! ba damuwa Bash ya san komai a gabansa aka yi komai shiyasa ma ya ce ka zo ka same ni zan fada maka komai."
Bash ya ce " oh maganar 'yar qauyen nan me hikima?Ai yarinyar nan garari ce gaskiya da ta yi boko kuma da 'yar birni ce zaa yi kata'i. Wato ita daban ce, ba normal mutane ba ce. Ba zaa taba samun kamar ta ba gaskiya abinda ta aikata babu mai iya yinsa. "
Abbas ya yi ajiyar zuciya ya ce " yanzu meye abin yi?"
Idris ya yi dariya ya ce "yadda mu ka yi haka kai ma za ka yi, kawai a dauko bayanta sai a dora fuskar Aisa. A tafi a haka domin fa 'yan kallo su na son buzuwar nan Aisa, farar fatarta da gashin nan har baya yana tafiya da imanin su ."
Bash da Idris suka kwashe da dariya suka tafa.
Abbas ya tashi ya saka farin gilashinsa a fuska yana ta kai kawo a cikin ofishin yana tunani, tabbas ya shiga damuwa sai su ka rasa meye dalilinsa na shiga damuwa haka.
Ya juyo ya dubi Idris ya ce "sake bude min hoton yarinyar nan in gani."
Idris ya zabura ya jawo laptop dinsa ya ce " Ah akwai sinasinan da ta dan firfito ma amma a 'yar aike ne dayan kuma a matsayin 'yar wanke-wanke amma duk da haka ta burge wasu da yawa akan kalaman da ta yi amfani da su wajen isar da saqon. Ka san na fada maka bata yi karatu ba ko script bata iya karantawa ba abinda ake karanta nata daban abinda take fada daban sai kuma ka ga abinda ta fada ya fi yin ma'ana."
Abbas ya dawo ya zauna su ka hada kai su 3 suna kallon sinasinan da Nihal ta firfito.
Tabbas ta iya magana kuma a nutse, ga ta da zazzaqar muryarta, maganganunta akwai hikima.
Abbas ya tsayar da fim din ya daga ido ya kalli Darakta Idris ya ce "ka na ganin an yiwa yarinyar adalci kuwa? A dinga daukar acting dinta ana hadawa da fuskokin wasu? Wannan kamar an dakushe ta ne, ba za ta taba zama jaruma ba kenan fa, kuma ana ci da guminta."
Idris ya dafa kafadarsa ya ce "abinda za ka lura shine ita fa wannan baqauyiyar ba ta da tsada, ko dubu goma ka bata ko ashirin murna take, daga ita har uban gidan na ta Tukur Wudil, Daraktan fim din shirmen nan na qauye. Su kuma Jaruman birni an san fukokinsu saboda fuskokin ake siya ana kallon fim. Idan ka dauko fuskar 'yar qauye ka saka komai acting din da ta yi babu mai kallon fim dinka, asara kawai zaka yi saboda baa santa ba."
Bash ya ce " wannan gaskiya ne gara dai a dinga daukar bayanta ana dora fuskokin manyan, tana dan firfitowa a wasu sinasinan a hankali idan ta yi suna sai a dinga nuna ta gaba daya din. Amma kasada ne ka saka miliyoyin kudinka, sannan ka saka 'yar qauye babu tantama sunan fim dinka asara."
Idris da Bash su ka kwashe da dariya. Abbas dai baya dariya sai wani tunani ne me rikitarwa ya dinga addabar kwakwalwarsa.
Can ya dago ya dubi Idris da Bash ya ce " ni kuwa zuciyata ta na tunzura ni in tunkari wannan al'amari ko da kuwa zai zame min asarar, zan dauki qaddarar."
Cikin rashin fahimta su ka dube shi suka tambaya "wanne al'amari kenan ?"
Abbas ya fada cikin muryar sadaukarwa ya ce " zan yi jihadi saboda Allah zan saka yarinyar nan a matsayin Jarumar fim dina gaba daya a saka acting dinta a dora fuskarta ko da kuwa fim din ba zai karbu ba. Dalilinna na yin haka shine sai na ga kamar ana daqushe ta, an qi nunawa duniya baiwar da Allah Ya bata saboda wasu dalilai na daban. Ko dan saboda bata da gata ko dan bata da hanya bata san kowa ba a industry ba. Hakan kuma da muke yi shine yake kawo koma baya a cikin sana'armu. Son kai yayi yawa kawai wa ka sani wa ya sanka ake yi."
" A'a abokina kada ka fara yin wannan kasadar an fada maka yarinyar nan fa ba fara ba ce, ga rashin wayewa ko boko bata yi ba. Ta yaya zata iya karanta script? Zama zaka yi ka yi ta fada mata daya bayan daya? "
Bash ya ce " amma yarinyar kalar fatarta mai kyau ce ko bata yi bleaching ba har ta fi wasu masu bleaching kyan fata. Ina ganin fa tana da kyau kawai rashin samun sutura me kyau ne da kuma rashin wayewa. Nima na fara ganin maganar Abbas ta na kan hanya in har an taimaka mata ta fito ta waye zata bada a abinda ake so. Ai yarinyar tana da saurin gane abu daga an fada mata take riqewa."
Idris yayi shiru kamar mai tunani can ya dago da kai ya dubi Abbas ya ce " ka je dai ka yi tunani sosai kafin ka yanke hukunci, gobe ka dawo min da abinda ka yanke kada ka yi saurin zartar da hukunci ka dawo kana da-na-sani."
Abbas ya gyada kai ya ce "haka ne, ka bani lokaci zan je in yi tunani ka tura min fim din a cikin hard drive dina zan je in kalla a nutse inga acting din yarinyar. Yaya ma ka ce sunanta?"
Bash ya yi carab ya ce "Nihal Nuren Mubin."
Abbas ya maimaita ya sake maimaitawa ya tambaya cike da mamaki ya ce " haka sunanta na gaskiya yake? Kuma ku ka ce 'yar qauyen qayayau ce ko makaranta bata taba zuwa ba? Anya sunanta na gaskiya kenan?"
Su ka kwashe da dariya su dukka ukun.
Bash ya ce " mu ma abinda ya dinga bamu mamaki kenan, har muka iso kano sunan nan muke ta nanatawa."
Idris ya tura masa Fim din a cikin hard drive ya miqa masa, Abbas ya karba ya yi masa godiya gami da yi musu sallama ya fice, ya bar su su na ci gaba da hirar Nihal da irin bajintar da ta yi a fim dinsa, da yadda mutane suka shiga mamaki. Da yadda sunan Aisa ya daukaka a duniyar yan kallo.
Ba Aisa kadai ba har Bash ma an jinjina masa yadda yake fada da hawa da sauka akan bishiya, duk kuwa a cikin irin aikin Nihal ne.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Jamila Umar Tanko
(JUT)
GABA GADI
Ta yi kuka har qarfinta ya qare, a kwance take kan kujera ta yi lamo babu kuzari a sanadiyyar rashin abinci da ruwa a jikinta. Ga qunar zuci da tafasar kwakwalwa.
Ta yi juyi sai gata ta runtoma qasa dabas ta fado. Ta na ta birgima akan kafet din da ya ke shinfide a tsakanin kujeru.
Ta fada a bayyane " ina ma qasa ta bude in fada ciki . Da ma ace kwanciyar nan da na yi in tsinci kaina a lahira . Ba na son in ci gaba da rayuwa a cikin duniyar nan da nake ciki. "Allah Ka yafe min, rayuwata ta salwanta. "
Hannunta ta ji ya taba wani abu, sai ta hau lalube ta jawo abinda take tabawa. Mujallar dazu ce dan haka sai ta daure ta yaga ledar da aka manne. Ta zaro mujallar ta qurawa hoton bangon ido, tabbas ko sau daya ka taba ganinta a duniya daga ka kalli hoton nan za ka shaida ta. Sunanta baro-baro a qasan hoton, Nihal Nuren Mubin sai aka fadi karin magana mai kama da habaici wanda yayi daidai da abinda ta aika.
Zaune ta tashi da sauri hannunta na rawa ta nemo fejin da labarin ya ke. Albishir ake yi wa masu bibiyar abin cewa bayan hotunan da aka saki zaa saki bidiyon a ranar asabar me zuwa, a manya-manyan sinimomin da ke ciki da Kewayen qasar, YouTube, Facebook, Instagram har da ma sauran ababen kallo na social media.
Ta zabura ta na laluben wayarta dan ta dakatar da mahunta sakin bidiyon nan, sai ta tuna da cewa ai wayarta ta dade a lahira ba za ta taba dawowa ba .
Ta yi magana cikin rawar murya " saboda kudi ne yasa su ka yi min haka ko? To zan biya ko nawa ne."
Wayar da take kan tebur wato 'land line' ta jawo ta danna lambobinsu ta ci saa an amsa. Da ta fadi sunanta su ka ji muryar sai suka shaida ta.
Ta fara magana cikin fushi da daga murya " ku fadi ko nawa ne