Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 110552 words

Chapter 13 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

A hanya Hashim ya dube ta cike da takaici ya ce " Nihal kin kuwa san abinda ki ke yi? Rannan Tukur ya cinye miki naira dubu ashirin ya hana ki har yau, kuma yanzu ki kalli duk rashin kyautawar da yayi miki dazu amma kin ce a bashi kudinki dukka, alhali ba mu da ko sisi."
Najaatu ta ce " to ai nima kaina ya daure."
Nihal ta nisa ta ce "wannan shine maganin maqiyi, shine qarshen gaba da zargi.Idan mutum ya munana maka kai kuma in ka tashi ka kyautata masa. Ka da ku damu Allah Zai ba mu yadda zamu yi."
Ita ta biya musu kudin mota har Wudil, ba su isa gida ba, Abbas ya kira Hashim a waya ya shaida masa ya bawa Tukur naira dubu ashirin da biyar na Nihal.Sannan gobe su zo zoo road da wuri qarfe tara ta yi musu acan zaa tafi Kaduna da su.
Hashim ya amsa bayan sun kashe waya ya yiwa Nihal bayani.Ta yi kokonton zuwa Kadunar nan amma Najaatu da Hashim su ka yi mata magiya su ka bata qarfin quiwa.
Sai a yau Najaatu ta taba shiga cikin gidan Nihal tana ta santin kyawun gidan amma Nihal ta tabbatar mata masu gidan sun yi tafiya ne, su suka bata aro. Ta umarci da Najaatu ta kwana gobe sai su wuce kawai. Daki guda Najaatu ta dauka ta baje ita kadai, Najaatu ce ta yi musu girki su ka ci suka qoshi su ka yi wanka sai kowacce ta shige cikin dakinta ta kwanta.Kafin Nihal ta yi bacci sai da ta rubuce dukkan abubuwan da ya faru a yau a wajen daukar fim.Labarin rayuwarta a duniyar fim take rubutawa, shine Fim din da ta kudira za ta fara yi idan ta zama Ex. producer, producer kuma director.Ta kwatanta tsananin quna da zuciyarta ke yi a lokacin da kucakai su ke wulaqanta ta, babu wanda ya mallaki rabi-rabin abinda take da shi a rayuwa.
Asuba ta gari Nihal Nuren!!!


Tun daga sallar asuba ba su koma ba, bayan sun idar sai su ka yi karatun Qur'ani, su ka gyara gidan, su ka dafa karin kumallo sannan su ka yi wanka.
Qarfe takwas da rabi Hashim ya bayyana a bakin get, sai bugu yake da qarfi tana zaton bacci suke.
Nihal ta kalli Najaatu ta yi dariya ta ce " Hashim in maye ne idan ya kama mutum dakyar zai sake shi ya fiye naci.Gashi can yana buga qofa har da kwalla kiran sunana, idan ma makwabta ba su san sunana ba yau sun sani. Ki dauki abincin can ki kai masa ki hada masa shayi ya zauna a farfajiyar get daga ciki ya ci."
Najaatu ta yi dariya ta ce " ke kadai yake yiwa haka, cab Hashim baya shiga harkar kowa fa. Jininku ne dai ya hadu."
Naja'atu ta tashi ta fita wajen Hashim, sauri kawai yake yi ya na ta azalzalarsu su fito su tafi, da kyar ma ya yarda ya zauna ya ci abincin. Doya ce da kwai da shayi hadin kauri.
Qarfe tara da rabi a garin Kano ta yi musu, qarfe goma daidai su na ofishin Abbas har an fara taruwa. A doguwar bus aka dura 'yan camama su Nihal, yayin da Jarumai masu aji irin su Aisa su ke cikin tsala-tsalan motoci masu A.c.
"Allah kenan komai da lokacinsa." Nihal ta fada a cikin zuciyarta.
Sun isa location a Kaduna amma a wajen gari ne. Anan ma an wuni ana gwagwarmaya, Nihal ta koyawa maza fadan canis da sukuwa a doki gami da wasu siddabarun dubarun fim. Nihal ta burge jamaar dake wajen matuqa. Abbas bai taba zaton basirar ta ta kai haka ba ya ji dadi sosai,sai tattalinta yake yana bata kulawa ta musamman.
Ko abinci da aka siyo da kansa ya dauko ya kawo mata.
Aisa da tawagarta sun cika sun yi taf kamar za su mutu saboda ana ta yabon Nihal. Sun so ta kula su ayi fada amma ba ta kula su ba, hakan da ta yi ta burge kowa.
Kaduna za su wuce su kwana sai washegari su wuce Abuja can ma fim din zaa ci gaba da dauka. Amma ita sinasinan da za ta yi sun qare daga yau dan haka sai Abbas ya sallame su daga nan.Naira dubu ashirin ya qara ba ta, Hashin ya yi sauri ya karba kafin ta sake cewa a bawa Tukur.
Bash Auta ne ya yi wata magana da ta bawa kowa mamaki. Ya dubi Nihal ya yi murmushi ya ce " ke 'yar china ki shigo mota in kai ku Kano."
Nihal ta girgiza kai ta ce " ka bari mun gode."
Zai sake yin wata magana ta bar wajen da sauri har ta kusa isa bakin titi. Hashim da Najaatu ne su ka biyo ta da sauri dan sun ga alamar in har ta sami mota shigewa za ta yi ta tafi ta bar su.
Aisa ta qule kamar za ta fashe ashe ita duk duniya babu wanda take so irin Bash, shima ya gane haka kowa ma ya gane amma bai ta taba nuna mata ya san tana yi ba, share ta yake dan ba ta gabansa.
Habaici Aisa ta yi masa ta ce " amma an ci baya an fadi babu nauyi tunda kiyashi ya kayar da giwa."
Abbas ya dube shi ya yi dariya ya ce " in ba neman magana ba kai da za ka kwana a kaduna da safe ka wuce Abuja. Me ya mayar da kai kano? Da ta yarda ka kai su, yaya za ka yi?"
Bash ya yi dariya ya ce "wallahi da kai ta din zan yi har Wudil, in ya so sai na dawo da asuba. Ai mace da jan aji aka santa shiyasa take burge ni ba irin su oooh ba."
Shima ya rama abinda Aisa ta yi masa sai ranta ya sake baci. Dan haka ma ta qi shiga motarsa da zaa tafi, haka bata kula shi baya kula ta.
A Kano su Nihal su ka tsaya suka yi siyayyar kayan abinci na Naira dubu goma, sannan su ka wuce Wudil da misalin qarfe goma na dare.
Tsire da biredi da lemo su ka siya su ka ci su ka sha a falon Nihal. Sai yau Hashim ya taba shiga cikin gidan, ya na ta santin kyawun gidan har da kauyanci ya dinga yi, su na dariya. Da su ka taba 'yar hira sai ya tafi gida, bayan sun rufe gida sai su ka yi wanka su ka kwanta.Yau ma Nihal ta rubuta abinda ya faru a garin Kaduna.
Kwanansu biyu a gida ba su fita ko ina ba, zazzabi Nihal take yi saboda gajiya da kuma cizon sauro. Magani Hashim ya siyo mata ta sha.
Najaatu ce 'yar zaman jinya ta yi amfani da wannan damar sai ta tafi ta kinkimo gaba daya komatsanta daga dakin su Mami, daman su na ta yi mata ciwon baki akan ba ta biya kudin hanyar wancan watan ba ita kuma ba ta da kudi, dan ba a fim din ake saka ta ba ma. Ta ga fuska a wajen Nihal, ta ga mutunci da mutuntawa, ta ga kyauta ba tare da gori ba, komai na ta ta amince kowa ya ci dan haka ta zabi ta zauna tare da Nihal, duk inda Nihal ta saka qafa za ta bi ta.
Bacci ne kadai yake raba Hashim da gidan Nihal ko ya fita sai ya dawo. Aike kuwa ko ina shi ne yake je musu. Nihal ta na jin dadin zama da sababbin qawayenta masu qaunarta.
Darakta Tukur ne ya ke sallama da Nihal a qofar gida dan haka sai ta fito ta same shi da sauri cike da mamaki. Bayan ta gaishe shi cikin ladabi sai ta sake cika da mamaki da ta ji ya bude baki ya na bata hakuri akan abinda yayi mata na rashin kyautawa, amma duk da haka ita kuma ta saka masa da alkhairi, ta daga darajarsa a cikin mutane.
Sai ta yi dariya ta ce "babu komai ya wuce."
Ayyuka guda uku ya kawo mata ya ce biyu na sa ne guda daya kuma na Aliyu zaa fara yi.Ta amsa masa babu damuwa za ta yi.
Ya tafi ya na godiya ta na godiya sai yanzu ta sake gasgatawa cewar ka yiwa wanda ya baqanta maka alkhairi, ka da ka rama mugunta da mugunta.
Da ta bawa su Hashim labari sai su ka yi ta mamaki su ka sake jinjina wannan halin na ta mai kyau kuma abin koyi.
Nihal ita ce Jaruma a dukka finafinan nan guda uku, yayin da ta kutsa Najaatu da Hashim a ciki su ma su ka baje kolinsu. Mami da Amina da 'yan korarsu sun shaqi takaici, sun fusata dan baa basu wasu sinasinai masu muhimmanci ba. Abinda su ke gudu shi yake shirin afkuwa Nihal Nuren Mubin ta fara kwace musu waje.
Sun yi kwana goma sha daya su na ta fama sannan aka samu aka kammala dukka finafinan. Ba wani kudin kirki su ka samu ba ma dan Tukur baya biyan Nihal idan ta yi masa fim tamkar ya sami baiwarsa saboda ya ga ba ta damu ba. Aliyu ne ma ya ba ta naira dubu goma ko qirgawa ma ta yi ba ta miqawa Hashim.
Su ka taho hanya Hashim ya na ta mita ya raina ita kuwa ko uffan bata tofa ba wannan ba shine a gabanta ba.

*** *** ***


Bayan wata daya cur sannan Fim din Darakta Abbas ya fito. Cikin ikon Allah bajintar da Nihal ta yi a cikin fim din shi ya jawowa fim din farin jini da kasuwa kuma shi ya sake daukaka darajar Aisa. Ex. producer kuma Daraktan fim din Abbas ya sami kasuwa ya sami kudi, ya sami suna.
Abbas da Idris ne su ke zaune cike murna su na ta tattaunawa.
Abbas ya ce " maganar gaskiya sai na ke ganin kamar ba mu yiwa yarinyar nan Nihal adalci ba fa. Gaba daya nasarar da na samu a fim din nan a sanadiyyar abin da ta yi ne. Amma ka ga ba ta mori komai ba ita baa bata kudin kirki ba, ita baa nuna ta an san fuskarta ba balle ta samu daukaka."
Idris ya ce " na fada ma ka gara da ka yi haka a nuna jikinta a nuna fuskar da aka sani. Kai sai zancen adalci ka ke ta faman yi. Ba dai ka biya ta ba? 'Yar qauye ce ta na can ta na gwaguyar kudinta ta na murna. Aka bibiya ma ba ta taba riqe irin wadannan kudade ba."
Abbas ya ce haka ne na ba ta dubu ashirin da biyar sannan na qara mata naira dubu ashirin. Ka san wani abin mamaki kuwa? Yarinyar cewa ta yi in bawa Tukur kudin aikin, bayan zagin da Tukur yayi mata a cikin jamaa bai so ba ma aka saka ta a cikin fim din ba. Ta burge ni matuqa, yarinya ce mai ladabi, kudi bai dame ta ba kwata-kwata ma. Ga hakuri wallahi na dauka zagin da su Aisa suka yi mata za ta yi fushi ta fasa yin fim din sai gashi ta ce za ta yi. Kuma wallahi ta na da kyau in har ta sami gyara sai ta fi Aisa kyau."
"Haba dan Allah! kai haba Aisa fa farar fata ce. Yaya ma za ka hada ta da wannan baqar."
Abbas ya yi dariya ce " kai ba ka san ma shikashikan kyau ba, ba fari kadai ba ne kyau. Kai ne ka yi mata kallon tsoro amma Nihal ta na da kyau, ga kyan jiki ba za ka hada ta da Aisa ba ma. Ina nan da kai ka bari ta wanke ta fara riqe kudi. Ina so in qara mata wasu kudaden dan gaskiya ita ce ta yi silar wannan nasarar tawa."
Idris ya ce " ka da dai ka ba ta ta da kudi, mun sami garabasa yanzu muna bata dubu ashirin ta na murna, in ta saba da kudi fa mun shiga uku."
Su ka kwashe da dariya su ka tafa hannu.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI


Na


Jamila Umar Tanko
(JUT)


Nihal Nuren Mubin ta kwana biyu baa ganinta a garin Wudil, domin kullum da safe idan ta tashi wajen koyon sana'ar hannu take zuwa a cikin wani qauye da yake kusa da garin Gaya. Anan ta ke koyon yadda ake kwaba qasa (laka) a mayar da ita randar qasa da bankin qasa har da abin d'ana waina na qasa. Bayan an gama akwai wata kwalliya da ake yi musu na zane da fenti duk su take koyo a wajen wasu 'yan uwan Inna kakar Hashim.
Ta na jin dadin sabuwar rayuwarta tare da sababbin mutane, ta na jin tausayinsu su na jin tausayinta, su na mutunta ta ta na mutunta su. Riba biyu take samu ga koyon sana'ar hannu ga samun labarun da zata iya zamar da shi fim.
A yanzu ta gane matsalolin dake addabar qauyawa, ta san damuwarsu ta san abin da suke fatan su samu. Daman ta gama koyon saqar tabarmar kaba da muhuci a wajen Inna yanzu haka kowacce irin tabarma da muhuci zata iya saqawa in dai na kaba ne.
Da la'asar sakaliya Nihal ta dawo daga qauye, ta sauka daga kan babur a qofar gidanta. Ta na tafe ta na layi kamar za ta fadi saboda yunwa da qishirwa, rabota da ta ci wani abu tun ruwan shayi da safe shima rabin kofi.Ta kama gate din gidanta kenan zata bude sai ta ji qarar tsayuwar mota a bayanta, ta juyo da sauri sai ta ga Hashim ya fito daga bayan wata dalleliyar mota ja.Ransa a bace yake ya tunkaro ta yana ta balbalin fada har da kumfar baki, yana tafe yana baza hannu.
"dalla malama ina ki ke tafiya ne? Ana ta nemenki an rasa ki tun shekaranjiya. An ce ki sayi waya kin qi, na baki tawa aro kin qi karba. A ina aka taba zama Jaruma babu lambar wayar da zaa same ki? Ga manyan baqi nan daga Kano su na ta nemanki, tun su na kira a waya har sun zo da kansu."
Tsayawa ta yi cak tana kallon bakinsa cike da mamaki da takaici.
Ta ce a ranta " lallai wannan ya cika dan shishshigi mai daukar matsalar wani ya dorawa kansa, tabbas bashi da aikin yi ne in ba haka ba ina ruwansa da rayuwata? A turai a ina zaa aikata wannan danyen aikin? An bawa kowanne dan adam dama ya zabi abinda yake so yayi a lokacin da yake so."
Hashim ne ya katse tunanin da take ya ci gaba da cewa " ki taho da sauri wajen motar can su Bash Auta ne shi da Babban Darakta Abbas.H.Abbas."
Nihal ta rasa amsar da za ta bashi dan takaici.Ta juya ta ci gaba da qoqarin bude get, sai Hashim ya zabura ya fusge mukullin daga hannunta.
Ya murtike fuska tana zazzare mata ido ya ce " wallahi ba ki isa ba, in kin shiga gidan nan yau Allah Ya tsince min sai kin zo mun je wajensu.Haba Nihal Allah Ya kawo miki daukaka ki na wasa."
Ta fusata ta ce "bani mukullina, yau zan ga yadda za ka ce dole sai na yi abin da ba na so."
Hashim ya sassauta murya ya na magana cikin rada "ki rufa min asiri ki zo mu je dan na yi musu alkawari zan nemo ki, na nuna musu ke qanwata ce. Sannan in kin samu shiga babban fim nima zan samu ki saka ni. Ki taimake ni Nihal dan Allah."
Har wata kwalla ce ta cika masa ido saboda tsananin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads