Header Ads
Showing 48001 words to 51000 words out of 110552 words

Chapter 17 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Ya ci gaba da cewa "an ce baki iya karatu ba kada ki damu da bayan ki da jikinki kawai zamu yi amfani ba magana za ki yi ba."
Ta gyada kai ta ce "babu damuwa Darakata."
Ya nuna mata wani saurayi mai jar riga ya fada mata sunansa Ahmed Usman ya ce ta je wajensa ta karbi kayan da za ta saka. Cikin sauri Nihal ta nufi wajen Ahmed Usman ta fara yi masa bayani.Ya na ji ya yi kamar bai ji abinda take cewa ba, ya ci gaba da hirarsa da su Aisa.
Nihal ta sake maimaitawa "Darakta Abbas ne ya ce ka bani kayan yaqi zan saka."
Sai can bayan ta dade a tsaye ya juya ya dube ta sama da qasa.
Ya ce " au wai da ni kike? Kamar yaya in baki kaya ban sanki ba."
Aisa ta kwashe da dariya su ka tafa ita da Hasiya carkwai su ka ce " kai ma ka fada, kwashe-kwashen Darakta Idris ce shima ya jonawa Darakta Abbas ya kwasa."
" Au wannan ce wannan me tsallen da su ka samu take burge su? Ni fa ban ma san haka take ba ." Ahmed ya fada cikin isgili.
Su dukka su ka kwashe da dariya su ka yi shewa.Sai da su ka gama isgilancin sannan ya miqa mata kayan. zuciyarta sai tafasa kawai take yi kamar za ta ce ta fasa sai ta daure kawai.Ta karba ta juya za ta tafi sai su ka yi kicibus da wani mutum. Har sai da kayan hannayensu dukka su ka zube a qasa, daga nasa har na ta.
A fusace ya dago zai rufe ta da fada sai su ka hada ido, Darakta Tukur ne shima ya qaraso dauke da wasu kayan .
" ke! Nan ki ka zo? me na ce miki dazu? Wallahi tunda baki da kunya ki ka yi min rashin kunya ba za ki sake yin aiki ba."
Su Aisa su ka taso da sauri su ka zo aka kewaye Nihal kowa yana fadar tasa baqar maganar akanta. Hayaniya ta hargitse Hashim da Najaatu ne su ka fuskanci da Nihal ake sai su ka rugo da gudu wajenta.Ta na tsaye ta sunkuyar da kai qasa hawaye ne ke ta kwaranya.
Abbas ne ya qaraso da sauri ya na tsawa" wai meye yake faruwa ne ake ta hayaniya haka? "
Tukur ya cije baki ya nuna Nihal da yatsa ya ce "wannan marar kunyar ce ta bangaje ni bayan dazu a Wudil ta gama cashe min da rashin kunya.Na yi rantsuwa ba zan sake saka ta a fim ba kuma duk abokaina ba zasu sake saka ta a fim ba ."
"ba ita ce aka ce a hannunka Babanta ya damqa ta ba? Ko rannan ma ai kai mu ka nema da ake nemanta." Abbas ya tambaya cike da mamaki da damuwa.
" Tukur ya ce " eh mana da ta daina saka barkakkiyar riga sai ta fara ta kai na. Wato na wayar da ita yanzu tafi qarfina."
Aisa ta yamutse fuska ta ce "Darakta ka dai gani da idanuwanka,ka nace sai ka yi aiki da ita.Ba ta da mutunci fa ga girman kai,gaskiya in har da yarinyar nan zaa yi aikin nan ni ba zan yi ba."
Najaatu ta ja hannun Nihal ta ce "zo mu tafi Nihal ki daina kuka, rabu da su."
Abbas ya zabura ya ce " ku tafi ina? Nihal kin fasa yin aikin ko za ki yi?"
Hashim ya zabura ya ce " za ta yi mana Darakta, ai abinda mu ka zo yi kenan."
Tukur ya zabura ya kaiwa Hashim mari sai ya tsugunna.
Tukur ya ce " ka ji dan iska na ce ba za ta sake yin kowanne fim ba kana cewa za ta yi.Munafuki kai ne ka ke zuga ta ka na fasa mata kai ka na nuna mata ta fi kowa, kana tuttura ta har ta ke ji daidai take da kowa."
Hashim ya fusata ya ce " shine kuma za ka mare ni. Me nayi maka?"
Nan dai hayani ta kaure tsakanin Hashim da Tukur. Tukur ya na surfa masa ashar Hashim ya na yi masa gargadi akan ya daina domin idan ya gaji zai rama shima.
Bash Auta ne ya qaraso ransa a bace ya daka tsawa sai kowa yayi shiru ya nuna Aisa da hannu.
Ya ce " ke baki da kirki wallahi kin tsani yarinyar nan.Me ta yi miki? In kin yarda da kanki me yasa kike tsoron wata ta zo itama ta gwada ta ta gwanintar? Ina zaune a can duk abinda ya faru ina gani.Kai kuma Tukur da kake rantsuwa ka daina saka ta a fim na ji na yarda fim dinka ne kana da dama amma baka da damar da za ka biyo ta har wani gari ka ce ba za ta sake shiga wani fim ba."
An dade dai ana musanyan yawu qarshe aka bawa Nihal haquri aka ba ta kaya ta shiga wani daki ta canja.
Ranta a bace yake matuqa da jikinta take yi amma kowa ya san da zuciya take yi,da alama a fusace take dan haka bajintar da ta yi a yau har tafi ta ran nan.Ta yi sukuwa a doki,ta kai sara da takobi, ta hau tsaunuka ta diro.
Har ta yi ta gama bata ce wa kowa uffan ba.Ta na gamawa ta wuce cikin wannan dakin ta canja kayanta ta fito.
Ta kalli Hashim ta kama hannu Najaatu ta ce "ku zo mu tafi."
Abbas ya zabura ya tari gabanta ya ce " yaya za ki tafi?Ai da saura gobe zaa qarasa, akwai gida na musamman da zaa sauke ku, ku kwana sai gobe ku qarasa. "
Ta girgiza kai ta ce " ba na kwana a location a gida zan kwana, gobe ku fada min in da za mu same ku sai mu dawo."
Ya gyada kai ya ce "toh babu damuwa, ga kudin aikinki na yau."
Ta girgiza kai ta ce " ba na buqata a bawa Tukur domin shi ake bawa."
Tukur ya cika da mamaki sai kunya ga nadama su ka kama shi.Ta wuce ta bar shi a tsaye sororo.
Abbas ya ce " ka ji ta ce a baka saboda ita har yanzu a uban gida ta dauke ka."
Bash Auta ya gyada kai ya ce "kun gani ko? Yarinyar nan ba ta da matsala da kowa amma kun bi kun uszura mata. Ita rayuwarta kawai take bata damu da kudi ko neman suna ba."
Mamaki ya hana kowa sakat a wajen gata dai talaka futik amma ba ta da kwadayi,an rasa in da ta nufa ko kuma yadda zaa fasalta halinta.
A hanya Hashim ya dube ta cike da takaici ya ce " Nihal kin kuwa san abinda ki ke yi? Rannan Tukur ya cinye miki naira dubu ashirin ya hana ki har yau, kuma yanzu ki kalli duk rashin kyautawar da yayi miki dazu amma kin ce a bashi kudinki dukka, alhali ba mu da ko sisi."
Najaatu ta ce " to ai nima kaina ya daure."
Nihal ta nisa ta ce "wannan shine maganin maqiyi, shine qarshen gaba da zargi.Idan mutum ya munana maka kai kuma in ka tashi ka kyautata masa. Ka da ku damu Allah Zai ba mu yadda zamu yi."
Ita ta biya musu kudin mota har Wudil, ba su isa gida ba, Abbas ya kira Hashim a waya ya shaida masa ya bawa Tukur naira dubu ashirin da biyar na Nihal.Sannan gobe su zo zoo road da wuri qarfe tara ta yi musu acan zaa tafi Kaduna da su.
Hashim ya amsa bayan sun kashe waya ya yiwa Nihal bayani.Ta yi kokonton zuwa Kadunar nan amma Najaatu da Hashim su ka yi mata magiya su ka bata qarfin quiwa.
Sai a yau Najaatu ta taba shiga cikin gidan Nihal tana ta santin kyawun gidan amma Nihal ta tabbatar mata masu gidan sun yi tafiya ne, su suka bata aro. Ta umarci da Najaatu ta kwana gobe sai su wuce kawai. Daki guda Najaatu ta dauka ta baje ita kadai, Najaatu ce ta yi musu girki su ka ci suka qoshi su ka yi wanka sai kowacce ta shige cikin dakinta ta kwanta.Kafin Nihal ta yi bacci sai da ta rubuce dukkan abubuwan da ya faru a yau a wajen daukar fim.Labarin rayuwarta a duniyar fim take rubutawa, shine Fim din da ta kudira za ta fara yi idan ta zama Ex. producer, producer kuma director.Ta kwatanta tsananin quna da zuciyarta ke yi a lokacin da kucakai su ke wulaqanta ta, babu wanda ya mallaki rabi-rabin abinda take da shi a rayuwa.
Asuba ta gari Nihal Nuren!!!


Tun daga sallar asuba ba su koma ba, bayan sun idar sai su ka yi karatun Qur'ani, su ka gyara gidan, su ka dafa karin kumallo sannan su ka yi wanka.
Qarfe takwas da rabi Hashim ya bayyana a bakin get, sai bugu yake da qarfi tana zaton bacci suke.
Nihal ta kalli Najaatu ta yi dariya ta ce " Hashim in maye ne idan ya kama mutum dakyar zai sake shi ya fiye naci.Gashi can yana buga qofa har da kwalla kiran sunana, idan ma makwabta ba su san sunana ba yau sun sani. Ki dauki abincin can ki kai masa ki hada masa shayi ya zauna a farfajiyar get daga ciki ya ci."
Najaatu ta yi dariya ta ce " ke kadai yake yiwa haka, cab Hashim baya shiga harkar kowa fa. Jininku ne dai ya hadu."
Naja'atu ta tashi ta fita wajen Hashim, sauri kawai yake yi ya na ta azalzalarsu su fito su tafi, da kyar ma ya yarda ya zauna ya ci abincin. Doya ce da kwai da shayi hadin kauri.
Qarfe tara da rabi a garin Kano ta yi musu, qarfe goma daidai su na ofishin Abbas har an fara taruwa. A doguwar bus aka dura 'yan camama su Nihal, yayin da Jarumai masu aji irin su Aisa su ke cikin tsala-tsalan motoci masu A.c.
"Allah kenan komai da lokacinsa." Nihal ta fada a cikin zuciyarta.
Sun isa location a Kaduna amma a wajen gari ne. Anan ma an wuni ana gwagwarmaya, Nihal ta koyawa maza fadan canis da sukuwa a doki gami da wasu siddabarun dubarun fim. Nihal ta burge jamaar dake wajen matuqa. Abbas bai taba zaton basirar ta ta kai haka ba ya ji dadi sosai,sai tattalinta yake yana bata kulawa ta musamman.
Ko abinci da aka siyo da kansa ya dauko ya kawo mata.
Aisa da tawagarta sun cika sun yi taf kamar za su mutu saboda ana ta yabon Nihal. Sun so ta kula su ayi fada amma ba ta kula su ba, hakan da ta yi ta burge kowa.
Kaduna za su wuce su kwana sai washegari su wuce Abuja can ma fim din zaa ci gaba da dauka. Amma ita sinasinan da za ta yi sun qare daga yau dan haka sai Abbas ya sallame su daga nan.Naira dubu ashirin ya qara ba ta, Hashin ya yi sauri ya karba kafin ta sake cewa a bawa Tukur.
Bash Auta ne ya yi wata magana da ta bawa kowa mamaki. Ya dubi Nihal ya yi murmushi ya ce " ke 'yar china ki shigo mota in kai ku Kano."
Nihal ta girgiza kai ta ce " ka bari mun gode."
Zai sake yin wata magana ta bar wajen da sauri har ta kusa isa bakin titi. Hashim da Najaatu ne su ka biyo ta da sauri dan sun ga alamar in har ta sami mota shigewa za ta yi ta tafi ta bar su.
Aisa ta qule kamar za ta fashe ashe ita duk duniya babu wanda take so irin Bash, shima ya gane haka kowa ma ya gane amma bai ta taba nuna mata ya san tana yi ba, share ta yake dan ba ta gabansa.
Habaici Aisa ta yi masa ta ce " amma an ci baya an fadi babu nauyi tunda kiyashi ya kayar da giwa."
Abbas ya dube shi ya yi dariya ya ce " in ba neman magana ba kai da za ka kwana a kaduna da safe ka wuce Abuja. Me ya mayar da kai kano? Da ta yarda ka kai su, yaya za ka yi?"
Bash ya yi dariya ya ce "wallahi da kai ta din zan yi har Wudil, in ya so sai na dawo da asuba. Ai mace da jan aji aka santa shiyasa take burge ni ba irin su oooh ba."
Shima ya rama abinda Aisa ta yi masa sai ranta ya sake baci. Dan haka ma ta qi shiga motarsa da zaa tafi, haka bata kula shi baya kula ta.
A Kano su Nihal su ka tsaya suka yi siyayyar kayan abinci na Naira dubu goma, sannan su ka wuce Wudil da misalin qarfe goma na dare.
Tsire da biredi da lemo su ka siya su ka ci su ka sha a falon Nihal. Sai yau Hashim ya taba shiga cikin gidan, ya na ta santin kyawun gidan har da kauyanci ya dinga yi, su na dariya. Da su ka taba 'yar hira sai ya tafi gida, bayan sun rufe gida sai su ka yi wanka su ka kwanta.Yau ma Nihal ta rubuta abinda ya faru a garin Kaduna.
Kwanansu biyu a gida ba su fita ko ina ba, zazzabi Nihal take yi saboda gajiya da kuma cizon sauro. Magani Hashim ya siyo mata ta sha.
Najaatu ce 'yar zaman jinya ta yi amfani da wannan damar sai ta tafi ta kinkimo gaba daya komatsanta daga dakin su Mami, daman su na ta yi mata ciwon baki akan ba ta biya kudin hanyar wancan watan ba ita kuma ba ta da kudi, dan ba a fim din ake saka ta ba ma. Ta ga fuska a wajen Nihal, ta ga mutunci da mutuntawa, ta ga kyauta ba tare da gori ba, komai na ta ta amince kowa ya ci dan haka ta zabi ta zauna tare da Nihal, duk inda Nihal ta saka qafa za ta bi ta.
Bacci ne kadai yake raba Hashim da gidan Nihal ko ya fita sai ya dawo. Aike kuwa ko ina shi ne yake je musu. Nihal ta na jin dadin zama da sababbin qawayenta masu qaunarta.
Darakta Tukur ne ya ke sallama da Nihal a qofar gida dan haka sai ta fito ta same shi da sauri cike da mamaki. Bayan ta gaishe shi cikin ladabi sai ta sake cika da mamaki da ta ji ya bude baki ya na bata hakuri akan abinda yayi mata na rashin kyautawa, amma duk da haka ita kuma ta saka masa da alkhairi, ta daga darajarsa a cikin mutane.
Sai ta yi dariya ta ce "babu komai ya wuce."
Ayyuka guda uku ya kawo mata ya ce biyu na sa ne guda daya kuma na Aliyu zaa fara yi.Ta amsa masa babu damuwa za ta yi.
Ya tafi ya na godiya ta na godiya sai yanzu ta sake gasgatawa cewar ka yiwa wanda ya baqanta maka alkhairi, ka da ka rama mugunta da mugunta.
Da ta bawa su Hashim labari sai su ka yi ta mamaki su ka sake jinjina wannan halin na ta mai kyau kuma abin koyi.
Nihal ita ce Jaruma a dukka finafinan nan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads