Header Ads
Showing 96001 words to 99000 words out of 110552 words

Chapter 33 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Yau Nihal ta sha addua tun tana amsawa har Amin din bakinta ta dauke.
A kan hanyarsu ta zuwa location ne Hashim da Najaatu suka bata labarin abinda ya faru jiya tsakaninsu da Bilal.Ta cika da mamaki matuqa yadda ya san in da take ta tabbatar Hashim da Najaatu ba zasu ci amanar ta ba. Babu tantama a baya ya biyo su ko ya sa yaransa suka biyo su a baya aka ga inda suka shiga. Amma koma dai menene ta shirya masa.
Sun isa location sun iske kowa ya hallara sai da Nihal ta ga kallon da ake yi ma ta ya yi yawa. Sai daga baya ta tuna da cewa ai irin motar da zo da ita ne. Sai ta ji ba dadi zaa ce fariya ce kiya ta zo da baqa yau ta zo da fara. Wannan motar Mummy ce don ta fito zata tafi ta iske a Usman ya tare ta, an yi ta tashinsa yana bacci bai tashi ba ita kuma zata makara kawai ta dauki ta Mummy. Tabbas kowa zai zaci fariya take yi kullum da sabuwar mota daban.
Ta ja ta tsaya a inuwa sannan su ka firfito, yayin da Najaatu da Hashim suka bayyana. Sai kallonsu ake yi duk in da suka dosa sai qamshi me sanyi ne yake tashi ko baka saka turare ba idan ka zauna a cikin motar qamshin 'yan gayu ne yake maqalewa a jikinka.
Nihal ce a gaba tana sanye da wani danyen leshi kalar pink an yi yi kwaliyar fulawa da royal blue gown ce mai kyau kuma simple sai ta nade kanta da wani qaramin gyale royal blue. Ta isa wajen mutanen sai ta yi sallama ta gaishe su wasu sun amsa wasu basu amsa ba ashe Aisa da Hasiya carkwai su na wajen su ne basu amsa ba.
Ba ta kalle su ba ta isa wajen Abbas aka fara shirya yadda zaayi.
Najaatu ce a kusa da su sai suka fara habaici da zagi kai tsaye Nihal suke zagi su na kiran Najaatu da Hashim 'yan kora.
Najaatu fa bata shiru bata barin ta kwana bata da tsoro. Daman Nihal ce ke hana ta yau an ci saa Nihal bata kusa dan haka ta cancare musu. Tun ana yi a hankali cikin sirri har na kusa da su suka fara jiyowa, abu yana qara girma har ya fito sannan kowa ma ya ji.
Hayaniya ta rikice tun ana yi a zaune har aka miqe tsaye. Nihal da take nesa sai ta juyo luguden ashar, sai ta fahimci da Najaatu ake fadan. Kafin ta qaraso Murtala Dalla ya kai hannu ya dallawa Najaatu mari har sai da ta kai qasa ta kwanta.
" Yauwa qarawa shegiya." in ji Hasiya carkwai da Aisa.
Hashim ya fusata ya kai hannu zai rama mata Murtala ya daga hannu zai wankawa Hashim mari ta bayansa sai yaji wani wawan mari har guda biyu ta kowanne gefe. Nihal Nuren ce, ranta a bace ta zaro waya ta kira wata lamba. Kalmar farko Major Abubakar ta furta an zo wajen sun san soja ta kira kalamanta yayi kama da kalaman a turo motocin sojoji.
"Mun shiga sojoji ne zasu zo wajen nan ai kuwa tattare my zasu yi gaba daya." In ji Danjuma Ado.
Mota guda ta ce a kawo sai kowa ya rude. Ta basu cikakken adashin wajen da take.
Abbas ya dinga roqonta akan kada a kawo sojoji ta ce ba dan komai ba ne sai dan su sami security, ba zata dinga hulda a cikin maqiya babu security ba.
Kowa ya bawa su Murtala rashin gaskiya. Murtala ya rude sai gashi yana tsuma yana ba wa Nihal haquri.
Na san wani ne ya aiko ka gara ka fada tun da wuri. Sojoji sun iso sai ta ce tana so a tambaye shi waye ya aiko shi har da zai shiga fadan da babu ruwansa. Kafin ya ji matsa ya fadi gaskiya ya ce Bilal ne ya ce ya ladaftar masa da Najaatu. Haka su Hasiya carkwai ma suka fada Bilal ne ya ce ta yi masa rashin kunya jiya su ladaftar da ita.
Nihal ta ce " lallai a nemo Bilal a ja masa kunne l babu duka babu zagi amma a fada masa kada ya kara taka qafarsa kofar gidanta kada ya sake zuwa in da take ma.
Aka kira Bilal a waya aka bashi mintuna talatu aka ce ya kawo kansa kafin a kawo shi. Ya ji maganar sojoji sai jiki sa ya dauki rawa kafin ka ce kwabo ya qaraso. Tun daga nesa ya hango Murtala a shanye a rana yana kneel down ya tabbatar yau babu mutunci.
Yau dai su Bilal aji ya zube ya na ta bada haquri. Ba dan Nihal ta hana ba da sai yayi tsallen kwado, aka karanto masa karatun Nihal na kada ya sake Shiga harkarsu balle ya taka gidanta sai yayi amanna.
Bash ya qaraso ya tarar ana hayaniya a lokacin ya ji labarin abinda Bilal ya aikata sai ya sake jin haushin Bilal . Kowa yana Allah wadarai da wannan abu. Abbas ya sallami Aisa da Hasiya daga fim dinsa aka maye gurbinsu da wasu sabbabin yara masu neman wajen shiga.
Bayan sojoji sun tafi a fusace Bilal da su Aisa suka Shiga motarsa ya fita daga farfajiyar a guje ya tayar da qura. 0ho ko ma dai menene dole ka shiga taitayinka.
Shooting yayi kyau yayi ma'ana. Da aka tashi daga location Nihal ta kwashi Hashim da Najjatu ta kai su gidanta kamar jiya ta wuce gida.
Washe gari da sassafe Hashim ya amsa wayar direba ya ce za su taso daga Wudil ya ce an bashi sako ya zo tasha ya karba su na hanya.
Kafin su qaraso ma Hashim ya je tasha yana jiransu su na zuwa ya karba.
Nihal ta ji dadin kayan nan sosai dan sun iso a lokacin da take buqata. Hashim da Najaatu dai kansu ya daure sai su ka rasa me zata yi da wadannan kayan, sun tambaya ta qi amsa musu. Ta ce su taya ta zubawa a but din motarta su ka wuce da su location.
A sin dinta na yau ne bayan an kama mata 'yan shaye-shaye an kai su wajen hukumar da ta killace su ana kKula su (rehabilitation centre).
Nihal ta yi musu nasiha mai shiga jiki sai da koya a wajen ya zubar da hawaye kuka take yi kamar da gaske. Sannan ta fara koya musu sana'oin hannu. Kowa ya cika da mamaki da suka ga ta yi zaman dirshen ta barbaza kaba ta fara dinka tabarma, ta dinka muhuci ta dinka hular maza da zare da allura sai gata tana lailaya qasa tana gina tukunya da tuli har da zancen fentin ta yi kwalliya a bayan tukwanen.
An yi kwanaki biyu a wajen koyar sana'ar nan saboda ta burge matuqa. Tun daga nan Abbas ya yi saranda ya gasgata baa taba samun 'yar fim din da take yin komai na ta kamar gaske ba sai Nihal.
Ya tabbatar za su sake samun yabo a wannan fim din ma kamar wancan.
Bayan kwana biyu aka wuce Kaduna da Abuja aka kammala a sati guda, sannan kowa ya wuce gidansu. Ta tafi da original copy na fim din don ta yi masa editing a nutse da fassarar turanci.
Fim ya fito kuma ya sha yabo Nihal ta qara samun masoya abin mamaki kyauttutuka ta dainga samu da tallace-tallace daga manyan kamfanoni irin su mtn, glo, etisalat, maggi, kayan electronic da dai sauransu.
Ta yi wa Idris alqawarin zata yi masa fim kuma ta cika masa alqawari maimakon daya ma sai da ta yi masa guda uku domin shima yayi mata halicci a rayuwa.
A takaice dai finafinai Hausa guda goma sha biyu ta yi ciki har da guda daya na Bash Auta. Babu fim din data shiga wanda bai yi kasuwa ba, saboda dole ma sai yayi ma'ana.
Kasuwar Nihal ta bude a kudancin qasar nan ma, tun da ta yi fim sau daya sai kowa ya yi kanta, sun yi mamakin yadda bahaushi take turanci mai kyau haka da yadda take acting ya burge su sosai. Dakyar ta samu ta gudu bayan da ta yi musu Finafinai guda tara.
Ta shiga Amerka ta yi fim da manyan jaruman duniya, haka ta yi wasu Finafinai a kamfaninsu John da Williams wadanda suka fara sakata a fim din farko. Nihal ta yi Fim da indiyawa.
Sunan Nihal ya cika duniya dan haka bata sha'awar ta sake yin fim sai dai ta taimaki al'ummarta kuma. Ashe ta gina katafaren industry mai suna N.N Mubin Movies ciki har da makarantar koyar da makamar aikin fim.
Akwai bangaren masu koyar daukar hoto da sauti, da masu koyon kwalliya irin ta fim da masu koyon acting , da bangaren koyar da editing. Ta dauki masana malamai daga kudu da kuma turai.
'Yan fim kadai take dauka domin su take so ta ingantawa sana'a dan ta ga kurakurai da rashin wayewar ta yi yawa. A sanadiyyar rashin fita su nemo ilimin da za su inganta sana'armu ne.
Kafin ka fara shiga aji sai dole an yi maka lecture sai ka san menene ma shi kansa fim din? Meye asalin samuwar shi kansa fim din? Sannan idan kika tsinci kanki a matsayin 'yar fim me ya kamata ki yi ki kare darajarki da kimarki, da ta danginki da kuma kacokan addininki.
Tabbas ta na jin haushin zagin da ake yiwa mata 'yan fim ace musu karuwai, ace masu shaye-shaye, masu bleaching. Tabbas wasu abubuwan an yi amma wasu baa yi ba ma ake qagowa ace an yi. Su waye su ke bada qofar da ake zaginsu? Amsar ita ce su suke bada qofa a zage su. Wasunsu ba sa kama kansu.
Nihal ta tantance duk wata matsala da take addabar duniyar fim, ta nemo mafita tsaf.
Ta kan Hashim da Naja'atu ta fara, sai da ta samo musu malamai ana koyar da su har na tsawon watanni shida ana koya musu turanci. Sannan ta biya musu suka tafi turai suka yi wasu kwasa-kwasai na share fagen akan koyan aiki. Iyayen Najaatu sun amince da Najaatu ta je sun yarda da kamun kanta kuma sun yi mata addua. Najaatu ta canja rayuwar kowa a danginta sun fita da ga tsantsar talauci.
Su Hashim an je London an dawo sai suka shiga wannan kwaleji ta Nihald, su ka fara karatun acting din fim.
Mata da maza suka dinga tururuwar cike form neman admission a wannan makaranta amma sai dai kash akwai adadin mutanen da za ta dauka duk shekara dole wasu su jira wasu su gama.
Ta bangaren koyon aikin directing ma akwai kwararrun masu koya musu. Ta kan Abbas da Idris ta fara, yadda tsarin yake duk shekara daraktoci guda biyar kacal za ta dinga yayewa dan haka dubbunan masu neman admission dole su saurara. Tukur ma ya nema bai samu ba amma abokinsa Darakta Aliyu ya samu dan haka Tukur ya sha jinin jikinsa ya fara girba zunuban da ya tafka.
Bash Auta ya na daga sahaun gaba-gaba da aka fara dauka, a bangaren koyon aikin directing. Ya ce mata Idan ya gama zai koyi acting ma da editing. Ta yi amanna da shi saboda bata manta alkhairi ta daraja wadanda su ka qaunace ta a cikin tsumma.
Duk wannan abu da ake yi babu ko sisinsu komai kyauta ne Nihal ta dauki nauyin.
Ko ina maganar taimakon da take yi ake ta yi a fadin arewacin qasar nan, har ma da ma kudu, su na fatan ta zo ta musu wannan tagomashi su ma.
Maqiyan Nihal sun kasa qarasowa su zo su tare ta su ce su na so. Gashi su na da buqatar Shiga amma kunya, tsoro da nauyin ta suke ji. Ta na sane da su ta yi kamar bata san su na yi ba.

*** *** ***
Ambassador Abba Muse ya fito takarar gwamnan jihar Kano. Gabansa zakuna, baya kuraye, qasansa kada , samansa damusa ce an saka shi a tsakiya ta ko ina so ake a murqushe shi. 'Yan adawa fa sun hade kai sai sun kayar da shi sun fara siye masoyasa da kudi.
Kowa ya tsorata har an fara fitar da rai, gashi zabe ya kusa an rusa dukka kanfen din da ya dade ya na yi na shekara da shekaru.
Abba Muse ya hada zufa a falonsa ya dubi 'yan jam'iyyarsa ya ce "an kusa cinmu da yaqi fa. Menene shawararku?"
Wasu su ce a saki kudi, wasu su ce a bazama kanfen, wasu su ce a je a ga shugaba qasa.
Isa lawan ya ce "mafita daya ce ka je ka sami General Nuren ya ba mu aron 'yarsa Nihal ita kadai wacce talakawa suka sonta suke gane yaronta. Ko ina fostar ce a qasar Hausa har ma da kudu."
Nan da nan kowa ya gasgata hakan.
Abba ya yi shiru yana tunani can ya ce "Muqaddas da Siyama fa sun dade su na bani wannan shawarar, na zaci dan su na neman shiri da ita ne ya sa suka ce haka.
Yanzu 'yar Hausa fim sai ta yi min sanadin cin zabe kuma ta fitar da ni daga wannan gagarumin hargitsin?"
Su ka kunna masa fim din Nihal a waya, ya gani suka kunna masa yadda ake dandazon zuwa duk taron da ta shirya na wayar da kai ko na sallah, Har a wasu qarshen ma irin su Nijer Cameroon da Ghana da Lagos. Su ka nuna masa yadda ake ji da ita a amerika har da excot take yawo.
" Ta yaya zan tari mahaifinta General in ce Nihal ta zo ta taimake ni bayan saboda fim din na raba auren 'yayansa da 'yayana?" In ji Abba.
Qungiya guda aka yi aka je aka sami Geneeal da wannan bukata ta Ambassador Abba. Lallai an zo wajen a lokacin allurar General ta tashi ya goga rashin mutunci ya bada da saqo masu zafi ya ce a kaiwa Abba. Nihal 'yar Hausa fim ce ba zata iya taimakon gwamna ba.
Washe gari Genaeral ya ce Nihal ta tashi ta tafi London, ya yankar mata ticket kada ta dawo sai an gama zabe. Kanta ya daure ta kasa gane abinda yake faruwa. Tana da abubuwan da zata koyar a makarantarta amma dole ta bari ta tafi.
Abba ya shiga damuwa shi da iyalinsa ne suka dungumo suka zo sai wajen General sai suka iske da gaske ya dauke Nihal ya sa ta bar qasar ma.
Babu riqon da basu yi masa ba amma ya qeqasa qasa ya ce ba dai 'yarsa Nihal ba. Wasu daga cikin yaransa irin su Muhammad sun bi bayan mahaifansu yadda Ambassador ya kama hannun 'yayansa ya fice ya ce ba zasu hada zuria da 'yan Hausa fim ba. Dan haka a yanzu ma 'yan hausa fi ba zasu shiga harkar siyayarsa ba.
Nuren ya ce "ka kama hannun 'yayanka, matarka ta bi ku a baya ga qofar fita can. Haka aka yi kuwa suka fice fusace.
Abubakar ne ya damu saboda kada a kwabe gaba daya ya rasa Siyama ga Muqaddas abokinsa. Major da Miqaddas a boye suka shirya su ka tafi london wajen Nihal sai a lokacin ne ma ta san abinda yake faruwawa Suka dinga shirya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads