Header Ads
Showing 93001 words to 96000 words out of 110552 words

Chapter 32 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ma Muqaddas ya sha turo mata kudade ya zaci wayarta na hannunta ko Atm card dinta. Kudi me yawa daga Mahaifiyarta. Mahaifinta ne bai tura mata kudi ba dan ya san tsiyar da ya tsula, ya san inda ya kai ta ya zubar ya tafi.
Nihal ta san ta yi kudi kudi na kwatance sai ta ci gaba da yiwa Allah godiya ta fara tunanin yadda zata infants rayuwar bayin Allah wato talakawa. Ta dandana yanzu ta san zafin ciwon talauci.
Ta ta sami gayyatar wasu Finafinai daga Hollywood tabbas tana shaawar ta je ta yi musu Fim tasan zasu biya ta maqudan kudi sosai ita yanzu ta san darajar kudi.
Nollywood ma na nemanta, babbar qawarta Nkechi da suka yi karatu tare ta dawo gida ta bude kamfanin fim dinta ta nemi da Nihal da ta zo ta yi mata fim.
Nihal ta kai dare tana bawa kowa amsa sai farin ciki ya kama kowa da aka ji motsinta maimaikon shiru wata da watanni. Ta yi qoqarin dawo da wasu tsofaffin accounts dinta na social media ta goge. Sannan ta bude wasu sabbabi da wannan suna da aka san ta da shi wato Nihal Nuren Mubin. Tun bata bar wajen ba aka dinga adding dinta ana turo mata friend request.
Lallai Nihal! Ashe 'yar rigima ce, ta na da waya a boye a jikinta da masu aikinta kadai take waya babu wanda ya san lambarta. Ta kira maau aikinta ta fada musu su rufe gida ba zata dawo ba sai bayan kwana biyu. Wayar wajen Bash kuwa ta bar ta a gidanta har cajin ya qare ta kashe kanta. Bash da Hashim sun kira har sun gaji.
An ci saa an ganta a Instagram dan haka duk can suka bi ta su na ta shishshigi, ta hadu da sakonnin Bash da yawa. A wancan account din nata da ta dawo da su na da ta ga Bilal yana yi mata magana, bata amsa masa ba. Ya dawo ya biyo ta sabon account dinta, shima ba ta tanka shi ba.
Ta shaidawa iyayenta akwai alqawuran yin fim da ta dauka da yawa dan haka ta na so ta cika ma su alkawura.Sun amince ta je ta yi.
Satinta biyu a Lagos ta na fafatawa da inyamurai, su a dole sai dai ta yi abinda suke so ita kuma a dole sai dai ta farke fim din ta sake dan bai yi ma'ana ba, dan ba zata yi abinda zai yaga mutuncinta da na addininta ba. Daga qarshe dole suka bar ta ta yi abinda take so. Sai daga baya suka gane abinda ta ce ayi shine daidai.
Kudi me yawa ta samu haka kuma ta samu suna mai yawa da yabo.
Ta na dawowa aka fara yin fim din Abbas da ta yi masa alqawari za ta yi masa. Zaa fara yi a kano sai a wuce Kaduna da Abuja.

*** *** ****
Da yammacin wata asabar Nihal ce ta shigo location cikin tsaleliyar motar ta da ta bawa miliyan goma sha biyu baya. Tun da motar ta tunkaro wajen babu wanda bai yi maganar motar ba sabo da kyawunta. Babu zato babu tsammani motar na tsayawa a gabansu sai ga wata dalliyar budurwa ta fito wato Nihal Nuren Mubin ce.
Su kansu producers da Directors ba sa hawa irin ta dan haka kowa ya san ba kudin fim ba ne ya bata.
Ta na fitowa sai ta zare baqin gilashin ta dubi kowa tabbas kamar an bi an yado maqiyanta kusan su ne gaba daya wajen.
Hashim ya washe baki ya yi dariya ya yi tafi yayi tsalle ya ce "Rangadi. sai aminiyarta wallahi. Yarinya me tashe a fim, mai tashen kudi."
Najaatu ce ta taso da sauri ta zo ta tare ta da murna. Nihal ta miqa mata hannu suka gaisa sannan ta qaraso wajen dandazon jamaa. Ta yi sallama ta gaishe su daga dukkan alamu dukka sun amsa har da alakoron fara'a wanda a baya bata samu haka ba. Abin mamaki kujera aka bata da sauri ta zauna sannan Abbas ya fara yi mata bayani.
Jigon labarin shine matsalar da take addabarmu ta shaye-shaye da 'yan mata ke yi da samarin har da matan aure ma abin takaici.
Shin daga ina matsalar take? Saken iyaye ne ko abokai ko malamai? Talauci ne ko kuwa arziki ne idan yayi yawa yake jawo shaye-shaye?"
Nihal ta ce zata fito a mataayin jami'a mai kama 'yan shaye-shaye da ladaftar da su kuma ta yi musu nasiha. Ta ji dadin roll din nan da aka bata. Ba ta yarda an fara shooting ba sai da ta tabbatar babu Bilal a fim din amma akwai Bash kuma daman ta ce lallai-lallai a saka Najaatu da Hashim dinta.
Nasir Zakar ne Jarumin fim din shi da Bash. Jigon fim din yayi mata haka, amma ta hango kura-kurai da dama kuma ta na gyarawa.
Sun kai dare su na daukar shirin, dan haka ta fara duba a agogo domin a gida za ta kwana. A dole aka tsaya sai kuma gobe.
Hashim da Najaatu ta dauka a cikin dandatsetsiyar motar nan ashe ma baa ga komai ba kyau sai an shiga cikin motar. Ga sanyin Ac ga kida mai sanyi daga cikin hadaddiyar speaker radiyo. Kidan buzaye na cikin fim din data yi da busarsu take saurara domin kidan yayi dadi a nutse. Ta kai su Hashim gidanta ta ce su kwana ita a gida zata kwana dan iyayenta ma ba su san ta kama gida ba.
Dadi ya kama Hashim da Najaatu su ka ji a wata duniya mai kama da Aljanna. Komai akwai a gabanka Zaa jere maka ga dakuna da garaje na alfarma. Kudi mai yawa na cefane Nihal ta qirgo ta bawa Ngozi. Ta nanata mata ta Kula da bakinta sosai sai gobe zata dawo. Haka ta bawa Baba Balaraba ma kudi mai yawa ko zata aika garinsu. Su ka yi sallama ta fito ta tafi.
Tana fita wayar Hashim ce ta dauki ruri bai san lambar ba shima har da irin wulaqancin nan na ya zama celebrity an fara damunsa. Najaatu ta harare shi ta ce " lallai kana daf da daina samun nasara kuwa in har wulaqanci zaka yiwa masu sonka. Ka yi koyi da Nihal mana bata da daga kai kowa na ta ne ko bayan da aka bayyana ko ita wacece.
Hashim ya zabura ya masa wayar ce ta sake shigowa. Ya na amsawa kafin ya ce komai sai ya ji wata murya a gigice an ce "Hashim ne ko?"
Hashim ya gyada kai ya ce " Eh ni ne Jarumin cikin fim din Gimbya Nihal wato Hashim Ibrahim Wudil. "
Ya fada cikin gadara "Nine Jarumi Bilal Sani. Nihal Nuren nake nema."
Sai Hashim ya zabura ya miqe tsaye a gigice. Har sai da Najaatu ta razana itama ta miqe da sauri tana tambaya ko lafiya.
11/14/21, 7:20 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 馃グ


GABA GADI


NA


JAMILA UMAR TANKO
(JUT)


Hashim ya gaishe shi cikin murna, babban farin cikinsa yadda yau babban Jarumi irin Bilal ya kira shi.
Hashim ya ce "ranka ya dade ba ma tare da Nihal daga location ita gida ta tafi."
Bilal ya tambaya "kai yanzu kana ina? Na sami labarin ba ku koma Wudil ba ku na kano."
Najaatu wacce ta ke jiyo abinda ake fada sai ta dinga girgiza masa kai alamar kada ya fadi in da suke. Ta rada nasa " mNihal ta ce kada a nuwa kowa gidanta."
Hashim ya ce " eh mu na kano amma gidan 'yan uwanmu ne."
Bilal ya murmushi ya ce "gani a qofar gidan 'yan uwanku ai, mai gadi ya qi bude min get ya ce bai san ni ba, ka fito ka shigo da ni."
Hashim ya hau in-ina da kame-kame.
Ya ce "wanne gidan kake magana?"
Bilal ya ce " gidan Nihal da ta kama haya a nan no. 1111 Sultan road."
Saboda tashin hankali bai san sanda wayar ta katse ba, ya dora hannu a kai.
Ya ce " Najaatu na shiga tsaka mai wuya. Me Bilal ya zo yi? Yaya aka yi ya san mu na nan? Ga shi can a qofar gidan nan har ya fadi lambar gidan kuma haka take."
Najaatu ta fusata ta ce " ya zo yayi mana me? Dalla ka daina jin tsoronsa, zo mu je qofar gidan."
Ta jawo gyalenta a fusace ta yi gaba Hashim na biye da ita a baya. Su na fitowa sai suka ganshi a zaune a cikin mota daf da get. Su ka tsaya a saitin direba, ba sa ganin komai a sanadiyyar ya kulle gilashin wundan kuma baqiqirin ne.
Ya zuge gilashin cikin taqama ya dube su sama da qasa ya ce "ku bude min in shiga?"
"Ka shiga kamar yaya?"
Najaatu ta tambaya cikin fusata.
Ya dade ya na dubanta cike da takaici yadda wannan kucakar har ta samu damar fada masa magana.
Ya ce " malama ki matsa ba wajenki na zo ba. Hashim bude min get ina da magana da kai amma a nutsu a zaune."
Najaatu ta tafa hannu ta murguda baki, ta kama qugu ta ce "abinda ya yi Nihal shi ya yi Hashim kuma shi yayi Najaatu. Dan haka ka fadi komai anan ba sai mun shiga ciki ba. Nihal bata so a san inda take amma sai da aka binciko ta. Tunda aka ce ba ta nan dan me zaa shigar mata gida?"
Bilal ya Leqo da kansa ya kalle ta tun daga sama har qasa. Ua ce " haka ne ko 'yar kora ?"
Ta harare shi ta ce "fadi ka qara fadi ni 'yar kora ce amma ba ta wani qaton banza ba ta Nihal ce. Ko ba ka ganni a cikin hoton da ku ka dauka ku ka watsawa duniya ba ne? A lokacin da muka ci abincin da muka kasa biya, ai kullum tare muke."
"Hashim zagayo ka shigo mota za mu yi magana." In ji Bilal.
Najaatu ta tare gaban Hashim ta ce "ba zai shiga motar nan ba fa baqiqirin da ita aje ayi tsafi da shi. Hashim wuce mu tafi gida."
A gaba ta sa Hashim su ka wuce cikin get, ta nunawa mai gadi Bilal ta ce kada ya sake ya bude masa get ko ya dawo dan ba mutumin arziki ba ne.
Bilal ya dade a zaune a mota ya na jin zafin tsuyuwar da Najaatun qauye ta yi masa. Shi fa a tsarinsa baya yafiya, tabbas sai ya koya mata darasi a gaban nan ba jimawa ba. Dakyar ya iya kunna motar ya ja ya tafi. Ya kwana bai runtsa ba saboda takaici.
Da sassafe Hashim ya ji luguden kira Inna ce da tawagarta yau za su zo su yiwa Nihal godiyar gidan da ta siya musu.
Hashim ya ce kada su zo Nihal ta ce ta yafe amma ta qi yarda. Ashe ma sanda suka kira shi har sun shiga motar Kano, sai dai daga tasha ba su san yadda zasu yi su zo gidan ba. Da suka iso sai suka kira shi a dole ya katse baccinsa ya fita a cikin adaidaita sahu ya taho da su. Mata biyar ne su da buhun kayan tsarabarsu a daure dadawa ce, kukar kadi, kubewa, fura da man shanu.
Hashim an fara wayewa sai ya ji gaba daya warin dadawa suke yi. Ya karbi buhun ya ajiye a bakin qofar shigowa falo ya ce kada su shigar mata falo da kayan wari. Su ka shiga suka zazzauna a qasa.
Hashim ya zabura ya ce "ah haba ku zauna a kan kujera ku ji laushi mana, ba ta so inyamurai masu aiki ta su raina baqinta.
Kowacce ta saki baki ta na kallon falo dan basu taba ganin irinsa ba.
Najaatu ma ta fito su ka gaisa sannan Hashim ya kira Ngozi ya ce ta yiwa baqi abincin karyawa, kakanni Nihal ne.
Sai Ngozi ta duqa ta gaishe su, babu abinda yake burge Hashim irin yadda Ngozi ta ke duqawa masa cikin ladabi ta ce yes sir. Sir din nan da take kiransa dadi yake ji.
Hashim ya ce " inna ku jira ku ga kayan dadin da zaa hada muku amma fa da wuqa da cokali ake ci baa saka hannu hannu doka ce"
"wuqa kuma?" Su dukka su ka hada baki suka tambaya.
Najaatu ta ce " ku rabu da shi wai shi dan birni. Ku saka yatsunku guda biyar ku damqo kwai da doya ku kai bakinku."
Su ka yi dariya su dukka.
"Ina Nihal din ne?" Inna ce ta tambaya.
Najaatu ta ce "ta na zuwa , ta na wancan daya gidan na su."
Inna ta zabura ta ce "au bayan wannan aljannar duniyar akwai wani gidan kuma?"
"Me ku ka gani ma? Ai kyau na wancan gidan."
Su inna sai ambato su ke " ikon Allah yarinya marar girman kai."
Kayan abinci kala-kala Ngozi ta dinga jerawa akan dining table. Hashim yana yi musu lecture yadda ake hawa da yadda ake ci. Ba a son ransu aka qawaba su akan tebur ba, dan dai Hashim ya yi musu dole ya ce dokar gidan ce gidan sai an hau sama.
Nihal Nuren ce ta shigo get din gidanta a cikin luntsumemiyar motarta, yau kuma farar mota ce. Ta cika da mamaki da ta shigo gidan ta ga su Inna sai ta daka tsalle ta rungume Inna su na ta murna su dukka. Da ta juya ta kalli sauran sai ta shaida su 'yan uwan Inna ne na qauye tana zuwa gidansu, acan ma ta koyi ginin randa.
Su ma ta gaishe su cike da murna a gigice ya kira Ngozi za ta ce a kawo musu abinci, sai Hashim ya tabbatar mata da cewa sun ci sun qoshi.
Sai su Inna suka bude shafikan kukan dadi da godiya da adduoi akan kyautar gida sukutum da ta yi musu.
Buhu aka kinkimo a baje kayan tsaraba kan ka ce kwabo warin dadawa ya gauraye falon. Babu yadda Nihal ta iya ta karba tana godiya amma tabbas ta kuaa ta kelayo amai. Ta cewa Najaatu ta karba ta kai bayan kicin dan ta san Ngozi ma bata san wasu irin abinciccikanmu ba.
Nihal ta kalli agogo sai Hashim ya ce "Inna mu zamu tafi location ana jiranmu. Ko za ku wuni anan ne da yamma sai a kai ku tasha ku koma gida?"
Su ka ce tafiya zasu yi daga nan ma wani qauye zasu je bikin suna.
A motar ta Nihal ta dauko su suka fito gaba daya. Ta kai su tasha, shatar mota guda ta dauko musu sannan ta bi kowaccensu da kudi naira dubu goma -goma sababbin 'yan dubu-dubu. Ta basu naira dubu ashirin ta ce su siyo mata kabar da ake saqawa yi tabarma da muhuci, ta ce su hado mata da laka da Fenton da ake yin randa da tulu in sun siyo su turo mata ta tasha gobe, a bada lambar wayar Hashim.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads