Header Ads
Showing 51001 words to 54000 words out of 110552 words

Chapter 18 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

guda uku, yayin da ta kutsa Najaatu da Hashim a ciki su ma su ka baje kolinsu. Mami da Amina da 'yan korarsu sun shaqi takaici, sun fusata dan baa basu wasu sinasinai masu muhimmanci ba. Abinda su ke gudu shi yake shirin afkuwa Nihal Nuren Mubin ta fara kwace musu waje.
Sun yi kwana goma sha daya su na ta fama sannan aka samu aka kammala dukka finafinan. Ba wani kudin kirki su ka samu ba ma dan Tukur baya biyan Nihal idan ta yi masa fim tamkar ya sami baiwarsa saboda ya ga ba ta damu ba. Aliyu ne ma ya ba ta naira dubu goma ko qirgawa ma ta yi ba ta miqawa Hashim.
Su ka taho hanya Hashim ya na ta mita ya raina ita kuwa ko uffan bata tofa ba wannan ba shine a gabanta ba.

*** *** ***


Bayan wata daya cur sannan Fim din Darakta Abbas ya fito. Cikin ikon Allah bajintar da Nihal ta yi a cikin fim din shi ya jawowa fim din farin jini da kasuwa kuma shi ya sake daukaka darajar Aisa. Ex. producer kuma Daraktan fim din Abbas ya sami kasuwa ya sami kudi, ya sami suna.
Abbas da Idris ne su ke zaune cike murna su na ta tattaunawa.
Abbas ya ce " maganar gaskiya sai na ke ganin kamar ba mu yiwa yarinyar nan Nihal adalci ba fa. Gaba daya nasarar da na samu a fim din nan a sanadiyyar abin da ta yi ne. Amma ka ga ba ta mori komai ba ita baa bata kudin kirki ba, ita baa nuna ta an san fuskarta ba balle ta samu daukaka."
Idris ya ce " na fada ma ka gara da ka yi haka a nuna jikinta a nuna fuskar da aka sani. Kai sai zancen adalci ka ke ta faman yi. Ba dai ka biya ta ba? 'Yar qauye ce ta na can ta na gwaguyar kudinta ta na murna. Aka bibiya ma ba ta taba riqe irin wadannan kudade ba."
Abbas ya ce haka ne na ba ta dubu ashirin da biyar sannan na qara mata naira dubu ashirin. Ka san wani abin mamaki kuwa? Yarinyar cewa ta yi in bawa Tukur kudin aikin, bayan zagin da Tukur yayi mata a cikin jamaa bai so ba ma aka saka ta a cikin fim din ba. Ta burge ni matuqa, yarinya ce mai ladabi, kudi bai dame ta ba kwata-kwata ma. Ga hakuri wallahi na dauka zagin da su Aisa suka yi mata za ta yi fushi ta fasa yin fim din sai gashi ta ce za ta yi. Kuma wallahi ta na da kyau in har ta sami gyara sai ta fi Aisa kyau."
"Haba dan Allah! kai haba Aisa fa farar fata ce. Yaya ma za ka hada ta da wannan baqar."
Abbas ya yi dariya ce " kai ba ka san ma shikashikan kyau ba, ba fari kadai ba ne kyau. Kai ne ka yi mata kallon tsoro amma Nihal ta na da kyau, ga kyan jiki ba za ka hada ta da Aisa ba ma. Ina nan da kai ka bari ta wanke ta fara riqe kudi. Ina so in qara mata wasu kudaden dan gaskiya ita ce ta yi silar wannan nasarar tawa."
Idris ya ce " ka da dai ka ba ta ta da kudi, mun sami garabasa yanzu muna bata dubu ashirin ta na murna, in ta saba da kudi fa mun shiga uku."
Su ka kwashe da dariya su ka tafa hannu.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Wannan littafin na kudi ne 馃グ馃グ馃グ馃憤馃徎




GABA GADI


NA


JAMILA UMAR TANKO
(JUT)


Nihal ta juya da sauri Hashim na biye da ita a baya.
"Malam Hashim ! Nihal Nuren Mubin ina kuma za ku je? Ga office din fa." Abbas ne ya fada cikin daga murya sai da kowa ya waiwayo.
Cak ta tsaya a tsakiyar hanya ba tare da ta iya waiwayo ba abinda take gudu shine ya afku kuwa, akwai wanda ba ta so ya ganta amma sunanta da aka kira ta san dole sai ya waiwayo.
"Hashim ne ya katse tunaninta ya ce "Nihal ki zo mu je ga Darakta Abbas din can ya na kiranmu."
Ta na waiwayowa sai ta yi ido hudu da abinda take gudu. Muqaddas Abba Muse ne ya qame qem ya na kallonta. Tabbas abinda ya dade ya na fitowa nema ya samu yau.
Ganinsa ya bata mata rai matuqa tabbas barazana ce a gare ta don koma tonar asiri ne. Ta shigo duniyar da baa san ko ita wacece ba ba ta so ta dinga haduwa da mutanen da ta sani a waccan duniyar ta da.
Da su ka qaraso in da a Abbas ya ke tsaye sai ya yi dariya ya ce " ai ina zaune ina ganinku ta cikin gilashi ku ka yi kamar za ku shigo sai na ga kin juya. Har kun manta ofishin ne? Nihal duk wannan basirar ta ki ashe ki kan kidime wataran. Hashim kai ma har ka manta ofishina kenan?"
Hashim ya yi dariya ya ce" ba mantawa muka yi ba har mun zo sai na ga ta juya ina zaton ko mantawa ta yi ta juya."
Muqaddas da yake tsaye a jikin motarsa a daf da ofishin Abbas sai kallon-kallo suke yi da Nihal. Ya fuskanci irin kallon da take yi masa domin ya karance ta tas, ya na gane duk irin yanayin da take ciki. A yanzu dai ta fada yanayin fushi da tsana ne.
Abbas ya wuce Hashim ya bi bayansa yayin da ta bi bayan Hashim.
Da Muqaddas ya ga zata shige ya zabura ya ce "Baby! tsaya mu yi magana wajenki fa na zo, na dade ina zuwa nan dan in hadu da ke ban taba samun nasarar ganinka ba sai yau."
Ta yi sauri ta kalli su Hashim Allah Ya sa sun yi gaba basu ji abinda ya fada ba. A fusace ta juyo ta nuna shi da yatsa ta ce " Kada ka sake, kada ka fara nunawa ka sanni. Ka daina bibiyata ka dauka ranka baka taba sanin Nihal ba, ka dauka a yanzu ba jinsinmu daya ba. Ba na so kowa ya san ko ni wacece a wannan duniyar da na shigo. MuqaddasMuqaddas kada ka bata min shirin da na dade ina yi a lokacin da na yi daf da samun nasara."
Hashim ne ya sake fitowa da sauri yana nemanta dan ya ga bata shigo ba har yanzu.
Hashim ya ce "Nihal ki shigo mana ana jiranki."
Ta juya za ta shige Muqaddas ya kira sunan Hashim, sai su dukka suka cika da mamaki. Sun manta da cewa yanzu Abbas ya kira su a gabansa. Hashim ya washe baki ya zaci a fim ya sanshi domin ya fara saka ran duniya gaba daya ta fara sanin fuskarsa.
Nihal ta harari Hashim ta ce " kada ka je ka wuce mu tafi."
Abokina Hashim zo mana saqo zan baka." Muqaddas ya sake fada fuskarsa cike da faraa.
Kafin Nihal ta sake yin wata magana Hashim ya dire a gaban Muqaddas sai ya miqa masa hannu su ka gaisa.
Hashim ya washe baki ya ce "eh kwarai ka gane ni kuwa nine Hashim Ibrahim wudil. A wanne fim ka sanni?"
Muqaddas ya yi dibi-dibi ya ce "su na da yawa ai ni Fan dinka ne sosai."
Ohoho zo kaga bakin Hashim har kunne yana ta jin dadin da ba zai musultu ba. Ya ce a ransa "ashe har qanqararrun 'yan gayu sun san da zamanna."
Nihal ta qi matsawa daga wajen dan kada a tona mata asiri.
Muqaddas ya bude mota ya dauko wata leda ya miqawa Hashim sannan ya saka hannu a aljihu ya dauko 'yan dubu-dubu ya sake miqa masa ya ce "kyauta ce na yi mata, ka bawa gwanata Nihal Nuren Mubin nima Fan dinta ne. Kudin kuma na ka ne."
Hashim ya washe baki ya na godiya ya dauko kwarababbiyar wayarsa zai karbi lambar wayar Muqaddas, sai ya ji an cacimo shi an hankada shi gefe.
Nihal ce ranta a bace matuqa ta fada cikin Fushi "Hashim wuce mu tafi kada ka bari raina ya baci ."
Simi-simi ya wuce cikin ofishin Abbas amma fa ya rugume ledar nan da kidinsa ram a hannunsa. Ya na godiya ga Allah da Ya sa sai da ya karba ta koro shi.
Ta juya ta harari Muqaddas ta ce " ba da wasa nake ba kada ka sake nemana, gargadi nake yi maka ba neman shawara ba."
Kallonta yake yi kallo irun na so da qauna, ya na murmushi.
Bash Auta ne da Bilal Sani su ka zo zasu wuce cikin ofishin Abbas sai aka hau kallon-kallo a tsakaninsu. Gaban Nihal ya yanke ya fadi a lokacin da su ka yi ido hudu da Bilal Sani domin ya santa ta san shi amma a intagram ya na cikin manya abokainta na social media. Bilal Sani babban Jarumi ne kuma Ex producer kuma Darakta wanda ya shahara kuma ake ji da shi.
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun me yake shirin faruwa da ni ne yau? "
Nihal ta fada a cikin zuciyarta yayin da ta yi nadamar zuwanta Kano yau, dama daga Darazo Wudil dinta ta wuce.
Bash Auta ne ya tsaya qem yana hararar Nihal da Muqaddas duba na rashin fahimta da alamun kishi.
Bilal Sani ne ya zungure shi ya ce "zo mu tafi mana." Dogon tsaki Bash ya ja sannan ya shige cikin ofishin. Yayin da Nihal ta harari Muqaddas itama ta ja na ta tsakin ta wuce ciki.
Kalmar Innalilahi wa inna ilaihi rajuun Muqaddas yake ta ambato yayin da ya hau kan motarsa ya zauna ya ci gaba da jira. Ransa ya baci sosai ba dan uba uba ba ne da sai ya kai mutumin da ya jefa Nihal a wannan harkar.
Bayan ta gaishe su sai ta sami waje ta zauna daga gani ba ta cikin hayyacinta. Abbas ya fara gabatar musu da juna.
Ya kalli Nihal ya ce " kin san Bash Auta ai kun taba yin aiki tare, ga Bilal sani duk duniyar Fim dai an san shi na san kin san shi kema shine dai nake tunanin bai sanki ba. Bilal ga Nihal Nuren Mubin sabuwa ce amma kuma malamarmu ce ita ce wannan me tsallen. "
Bilal ya kalle ta sama da qasa ya yamutse fuska ya ce "ban taba jin labarinta ba ma. Wai kana nufin da ita za mu yi fim din ne?"
Kowa ya gane dalilin da ya sa ya yi wannan tambayar, raina ta ya yi.
Sai Nihal ta godewa Allah dan ta tabbatar bai gane ta ba. Ta ji dadi da Allah Ya sa bata shiga social media da sunanta na gaskiya, ya santa a social media da sunan princess last born.
Kamar daga sama ta ji Bilal ya ce " ka ga an nemi princess last born ko sama ko qasa babu account dinta gaba daya ta shafe su, babu number wayarta ko an kira a kashe.Ta yi min alkawari za ta bani shawara akan wani sabon fim dina da zan yi, wallahi na ji haushi wallahi sosai na yi rashi. Na nemi qawarta ma Queen Siyama itama an shafe fejinta. Ko ina su ka shiga oho."
Bash Auta ya ce " akwai abar banza irin social media, aka bibiya ma da wani qaton namiji ka ke chating ba mata ba ne"
Su dukka su ka kwashe da dariya. Yayin da Nihal ta sake sinne kanta dan kada ya tunano fuskarta domin jifa-jifa ta kan saka hotunanta a dp ko status.
Bilal sani ya girgiza kai ya ce " wannan macece kumar 'yar Kano amma ta na zama a London, wato yarinyar nan ta hadu ga kyau ga ilimi ga brain. Wallahi idan ta na turanci ba za ka taba cewa ba da baturiya kake magana ba. Duk turancin nan nawa wani abu sai dai in bi ta da ehh. "
Su ka sake kwashewa da dariya suka tafa.
" Ita me ta ke yi a London din?"Bash Auta ya tamabaya
Bilal ya ce " kai! wata shegiyar attajira ce 'yar gata Babanta ya kai General a soja Yayyanta sojoji ne, mamarta furofesa ce ilimi tana lecturinga manyan jami'oin qasar nan. Ka san me ita ce mace Bahaushiya ta farko da ta karanci fim ta yi degree ta yi masters a London. Ni fa ina ta bincike a kanta aka ce turawa rububinta suke ta yi akan ta yi musu fim. Ka san abinda ya sa suke sonta saboda fatarta ita ce original baqar fata da babu mix bata bleaching sannan ta iya acting na masifa."
Bash ya zabura ya ce" Hollywood kake nufi?"
Bilal ya ce kwarai da gaske mu kan yi chat da ita a lokacin ta na location amma ina ga baa fara sakin finafinanta ba amma tabbas za ka ga bahaushiya a Hollywood."
Bash ya ce " Ah la ce wannan babbar harka ce ba za ta kula ka ba, ina ganin shafe ka ta yi ba account dinta ta shafe ba. Ta raina 'yan Kanywood ne kawai."
Bilal ya ce "kuma bata da wulaqanci gata da son ci gaban farfadowar Hausa fim. Gaskiya na yi asarar rasa ta saboda ta yi min alkawarin taimakona da abubuwa da yawa. Ka san wani abu kuwa? wallahi bala'in sonta nake san yadda zan fada mata ba saboda ta fi ni a komai. Ita fa ba ta iya daura zani ba idan ta yi wata shiga cikin Wando oh my God na ce a raina su Aisa Buzuwa su zo su ga 'yar Fim din asali ba kamar su ba."
Bash ya ce " ka fada mata kana sonta kawai, shi so ai ba ruwansa da kudi ko wayewa watakila ta so ka yadda ka ke dogo fari santalele, ga ka jinin kudi da sarauta. Aka bibiya ma itama ta na sonka a ranta ta kasa fada maka ka saka kai kawai abokina."
Bilal ya yi dariya ya ce " kada ka ingaza ni dan kulanin da take ta daina me jan aji ce bata ma san ina yi ba. An fada maka ta bata ma gaba daya ko sama ko qasa kana yi min wata magana. Ita fa wannan komai bai dame ta ba, ba ta san ma ina yi ba amma dai idan na yi mata tambaya ko neman shawara akan fim ta na bani amsa musamma idan na tura mata saqo ta email dinta. Sunan email din zulaihatshatumubin@gmail.com amma yanzu na tura sakonnin har na gaji shiru ba amsa."
Abbas ya yi ajiyar zuciya ya ce " ka ga da ta na kishin yarenta da ta dawo gida an amfana da ita. To irin wannan kuskure mutanenmu suke yi sai su je su farfado da al'adar wata qabilar su zubar ta su mu na buqatar irinsu anan. Ai tunda ta yi karatu mai tsada irin wannan, gida ya kamata ta zo ta wayar mana da kai mu ma mu qaru. Har ta bai haushi ma."
Sai yanzu Nihal ta jinjinawa basirar mahaifinta da ya ce ta zo ta yi Hausa fim anan ma ana buqatarta, tabbas haka ne gaskiya. Ta kudiri niyyar kawo agaji ga masana'antar nan kuma kyauta. Akwai himilin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads