Showing 3001 words to 6000 words out of 110552 words
Chapter 2 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
ko ta bar duniya ko ta Shiga cikin duniya . Ta na me basu hakuri da shawara akan kada su tarki nemanta a waya ko a London. Don ba zasu same ta ba . Bissalam .
Tana turawa ta cire layin wayar ta kakkarya, waya me matukar tsada a take ta kwarankwatsata a kasa tayi filla-filla.
Qararrawar kofar falonta ce ta hau qugi babu qaqqautawa. Ta yi kamar ba zata bude ba ta ga basu da shirin bari. Ta taso a Sanyaye ta je ta leqa ta huda. Tabbas ha wanda zata huce haushinta a kansa ya iso . Dan haka a fusace ta bude qofar.
Sitibin ne fuskarsa cike da faraa ya Miqa mata wata magzine gami da ce mata Congratulations Na'ila Good job . "
Bata amsa masa ta juya gefensa ya Ganshi tare da wani bature . Ya Miqa mata hannu da Zimmer su gaisa sai ta kawar da kai gefe ya qi Mike masa hannu . Yayi murmushi shima kalmar Congratulations ya furta mata . Ta cika da mamaki. Ta Duba bangon mujallar wani katon hotonta ne ya cika bangon. Sai ta zabura ya Dafe kirji ta fada a bayyane " innalilahi me yake shirin qara faruwa da ni kuma ? "
Sutivin ya fada " my Shiga daga ciki na zo miki da babban bako John. Baki gane shi ba ne ? John kuwa popular ne kowa ya san shi a kasar nan dole ma zaki san shi ."
Ta kalle su biyun a shelaqe " idan na gane shi me Zaa iyu ? "
Sityvin yana kokarin tura kai zuwa cikin falo Na'ila ta sa hannu ta kare bata yarda ya Shiga ba .
Ya yi murmushi ya ce " sorry ko kina da bako ne ya sa ba kya so mu shigo ? A gaggauce mu ma sauri muke yi . Na zo miki da Albishir cewa John zai yi aiki da ke za ki samu kudin da kowa a danginki sai ya yi sallama da talauci ....."
Bai rufe bakinsa ba ta " bana so . Bana buqata. "
Ta sa hannu zata rufe kofa sitivin ya jawo ta wannan Karon mari ta sakar masa gami da yi musu tsawa mai firgitarwa . Leave me alone I don't want see u in my house again.
Stevin ya yi sauri ya kama Kunci baki a bude dan mamaki, yayin da John ya ja da baya a tsorace yana tambaya . Lafiya ? Me yake faruwa kuma ?
Bata amsa musu ba ta Shiga ta datse gidanta. Kallo dayabra sake yiwa mujallar sai ta runtse ido ta wurgar a kasa ta fada kan kujera ta bude sabon shafin runtuma kuka mai tafe da kunar zuci .
Domin karanta sabon littafina GABA GADI a biya # 500 ta cikin wannan acct din . Zaa a yi adding din wadanda su ka biya a sabon grp .
Unity Bank
Jamila umar tanko
0023843938
Evidence of payment ta wanan number 08037196708
11/14/21, 7:18 AM - MY MTN 2: GABA GADI
EP 2
Ta yi kuka har qarfinta ya qare, a kwance take kan kujera ta yi lamo babu kuzari a sanadiyyar rashin abinci da ruwa a jikinta . Ga qunar zuci da tafasar kwakwalwa.
Ta yi juyi sai gata ta runtoma kasa dabas ta fado. Tana ta burgima akan kafet din da yake shinfide a tsakanin kujeru.
Ta fada a bayyane " ina ma qasa ta bude in fada ciki . Dama ace kwanciyar nan da na yi in tsinci kaina a lahira . Bana son in ci gaba da rayuwa a cikin duniyar nan da nake ciki . Allah Ka yafe min, rayuwata ta salwanta. "
Hannunta ta ji ya taba wani abu, sai ta hau lalube ta jawo abinda take tabawa. Mujallar dazu ce dan haka sai ta daure ta yaga ledar da aka manne. Ta zaro mujalla ta qurawa hoton bangon ido , tabbas ko sau daya ka taba ganinta a duniya daga ka kalli hoton nan za ka gane ta. Sunanta baro-baro a kasan hoton, Nihal Nuren Mubin sai aka fadi karin maganar mai kama da habaici wanda yayi daidai da abinda ta aika .
Zaune ta tashi da sauri hannuna na rawa ta nemo fejin da labarin yake . Albishir ake yi wa masu bibiyar abin cewa bayan hotunan da aka saki zaa saki bidiyon a ranar asabar me zuwa, a manya-manyan sinimomin da ke ciki da Kewayen qasar, YouTube, Facebook, Instagram har da ma sauran ababen kallo na social media.
Ta zabura tana laluben wayarta dan ta dakatar da mahunta sakin bidiyon nan , sai ta tuna da cewa ai wayarta ta dade a lahira ba zata taba dawowa ba .
Ta yi magana cikin rawar murya " saboda kudi ne yasa suka yi min haka ko ? To zan biya ko nawa ne."
Wayar da take kan tebur wato 'land line' ta jawo ta danna lambobinsu ta ci saa an amsa. Da ta fadi sunanta su ka ji muryar sai suka shaida ta.
Ta fara magana cikin fushi da daga murya " ku fadi ko nawa ne zan biya ku kada ku tona min asiri . "
Dariya ta ji an barke ana ta yi ana qyaqyatawa har da buga qafa. Biliyoyin euro din da aka zaiyano mata zaa iya siyan rabin kasarta Nigeria da shi. Duk tulin dukiyar da take tutiya zuri'arta su na da ita ba zata fanshe ta ba .
Ta fada cikin tsawa
" kotu zata raba ni da ku muddin ku ka nuna bidiyon nan ."
" shin Nihal kin manta kin saka hannu ? Ai da amincewarki aka yi ." Steven ne ya tuna mata .
Kafin ta yi magana sun katse wayar. Da ta sake kiran wayar ba su amsa ba .
Ta sulale ta kwanta yayin da ta fara tunanin qasashen da baa cika zuwa ba, wadanda ba sa cikin lissafin duniya . Wadanda basu taba ganin baqar fata ba ma . Wadanda aka ce su na cin mutane . Tabbas idan ta kutsa cikin qasar har ta mutu babu wanda zai yi tunanin nemanta a can. Idan kuma an ci saa sun cinye ta shikenan ma an huta . Qasashen masu qananan ido cikin kauyukansu da basu da hanyar mota sai gada da kwale-kwale, idan aka ci saa ma Kada ce a cikin ruwa take zama ajalinsu.
Ta fada a bayyane " Allah Ya sa idan na je tsallake Ruwan kada ta cinye ni ."
A guje ta tashi ta shiga cikin daki, riga t- short da Wando Jeans ta saka ta dauki jakarta karama wato puse, abinda ta tabbatar ta saka a ciki shine ATM card dinta da kuma passport dinta. Kanta babu dankwali balle mayafi. Ta saka takalmin shiga bandaki wato silifas. Ta fito da gudu daga cikin gidan bata damu da rufe kofofin gidan ba . Burinta kawai ta matsa daga inda aka taba saninta.
Kano Nigeria...
Dare yayi misalin karfe takwas, Yayyan Nihal sun hallara a babban falon gidan , fuskokinsu gaba daya a cikin damuwa dan ada su na zaton abin nan wasa ne, yanzu sun tabbatar babbar matsala ce. Sun rasa Nihal a waya da duk wata kafa ta social media . Sun tuntubi duk wanda su ka san zasu sami labarinta a acan, sun duba ta baa same ta ba .
General Nuren suka hango ya fito daga cikin dakinsa a sukwane. Ya na tafe da sauri har yana tuntube ya kusa faruwa. A waya yake magana a cikin fushi da daga murya .
" Ambasador! Ka tura yaranka kowacce kusurwa, boda da filayen jiragen sama da na qasa da suke fadin garin. A hana ta fita daga qasar, Nihal nake so in gani a kasata, a damka min ita a hannuna ko a raye ko a mace . Na sake fada na maimaita a shiga ko ina a fadin cikin kasar a nemo min ita ."
Ya harare su ya wuce su ya fita da sauri , dukkansu su ka bude baki su na kallon-kallo . Zabura su ka yi da gudu su ka bi bayansa amma tuni ya shige mota ya fita da gudu, wannan karon ma da kansa yake tukawa baya bukatar direba. Ko ina Zai tafi oho.
Major Abubakar ya daki bango ya fada cikin fushi " me yake faruwa ne ? Mu na da haqqin mu sani mu ma fa, amma ake Boye mana kamar wadansu bare .Me ya sami Nihal ?"
Wayarsa ya zaro da sauri ya kira Siyama, bata amsa ba sai ya kira yayanta Muqaddas.
Muqaddas ya amsa da sauri Abubakar ya ce " Ina Siyama? Ta qi amsa wayata . Ka fada mata duk abinda ya cutar da qanwata kwaya daya tal a duniya, ba zan yafe mata ba . Sai na tabbatar na yi mata hukunci daidai da abinda ya sami Nihal."
"Malam ka rabu da ni. Ka san halinda muke ciki ne ? Yanzu haka za ka ji alamar ina ta nishi, gudu nake da qafata a cikin filin jirgin kano . Ina neman Siyama ance jirginsu ya tashi zuwa Abuja . Ta bar wasika cewa ta tafi London su hadu da Nihal zasu Shiga duniya ba zaa sake ganinsu ba har abada." Muqaddas yana gama fada ya kashe wayar ba tare da ya jira amsa ba .
Tashin hankali da karar da Abubakar ya yi shi ya jawo hankalin sauran a guje su na tambayarsa.
Ya dago da jajayen idanuwansa ya dube su ya ce komai ya gama dagulewa Siyama ma ta gudu zasu hadu da Nihal su shiga duniya .
A Tare suka fada "mu je wajen Mummy ko kofar mu balla mu duba mu gani ko tana raye ma, idan tana raye kuwa yau sai an fada mana mugun abinda yake faruwa amma ake boye mana ."
Da sauri suka isa bakin qofar dakin mahaifiyarsu Aliyu da Umar sun tukirkire sun yi baya zasu tako da gudu su saka qafa su balla kofar sai Muhammad ya hana su .
" ku dakata Ciwon Mummy baya son bayani da tashin hankali . Mace ce mai saukin kai idan mun lallabata Zara fada mana komai ."
Su duka suka ja da baya suka bashi waje. Ya karasa jikin qofar ya kwankwasa sau daya sau biyu sai ya saka kunne a jikin kofar domin ya jiyo motsin bude kofar bandakinta, yana magana cikin sanyin murya da kallashi.
" Mummy 'yayanki ne gamu nan gaba daya mu 7 muna cikin tashin hankali. Ki bude mana qofa mu shigo dan mu duba lafiyarki. Mummy ke kadai muke gani mu ji dadi a ranmu, idan damuwa ta taba lafiyarki ko kika rasa ranki na tabbatar mun yi sallama da farin ciki mu ma. Mummy ki yafe mana ki tausaya mana muna sonki "
Gaba daya suka hada baki " Mummy muna son ki ki bude kofa ."
Baa dauki lokaci mai tsayi ba su ka ji an bude kofa . Professor Shatu ce ta bayyana a bakin kofar idanuwanta sun yi luhu luhu abinka da farar fata. Ta rame ta kuje.
Su dukka suka durkusa sua gaishe ta .
Ta amsa amma dakyar take magana daga gani bayan bacin rai akwai karancin rashin abinci a jikinta.
" Mummy ki fada mana dan Allah me yake faruwa da Nihal? " Usman be ya tambaya cike da damuwa.
Zasu yi mata magiya ta daga hannu ta tsayar da su sannan ta daddana wayarta ta Miqa musu Muhamma be ya karba ya fara karanta sakon a bayyane . Sakon Nihal ne da ta turo mata wanda take neman gafara daga wajen Allah da iyayenta da Yayyanta da Saurayin da zata aura. Sakon karshen ne ya gigita su da ta ce a daya Zaa yi biyu ko ta bar duniya ko ta shiga duniya . Kada ma su yi wahalar nemanta a London don ta kara gaba .
Da gaske babu wanda bai gigice ba su ka fara jejjero mata tambayoyin da ba ta san amsoshinsu ba .
"Mummy me aka yi mata ? Me ya faru da ita ? Da ta turo miki sakon ke me kika ce mata ? Ba ki tsayar da ita ba ? "
Amsa daya zuwa biyu ta basu ta ja kofarta ta rufe " Ban san abinda ta aika ta ba gaskiya, mahaifinku bai fada min ba ya ce idan na amsa wayarta bai yafe min ba . Abinda nake so da ku shine ku gaggauta barin bakin kofar dakina kafin ya zo ya tarar da ku yayi zaton wani abu muke kunsawa. Nihal kuma ina yi mata addua Allah Ya jikanta ku yi mata hukunci daidai da laifin ."
Bayan nan sai ta shige ta kulle dakin da mukulli. Hamza zai sake bugawa Muhammad ya rike shi ya ce " kada ka buga mata kofa . Ku zo mu fita kawai ,"
Ya wuce gaba su na biye da shi a fusace kowannensu yake .
11/14/21, 7:18 AM - MY MTN 2: GABA GADI
EP 3
A farfajiyar get suka tsaya kowannensu gwani ne wajen zafin zuciya , babban abinda ya fi damunsu shine rashin sanin takamaiman abinda yake faruwa . Tun kafin ma su ji abinda ta aikata, sun qudiri niyyar sai sun casa Nihal, sai ta gwammace bata fito a tsatsansu ba .
Abubakar ya juya ya dube su ya ce " me ku ke tunani ta aikata haka da har ya tunzura Daddy , ya firgita Siyama ta kasa fada? Ku duba ku ka biyayyar da Siyama ta ke yi min, ta san bana son karya da boye- boye amma ta kasa fada min har ta gwammace in rabu da ita in fasa auren , har ta gwammace ta gudu ta bar iyayenta akan ta fadi abinda yake faruwa . Ba kwa ganin abin nan ba karami ba ne ? "
Usman ya ce " na kasa tunano me Nihal zata aika da har ya rikita su haka . Kalli yadda Daddy yake magana a waya har yana tuntube saura kadan ya kifa. "
Mu'awiya ya ce " kalmar a kawo masa Nihal a raye ko mace ta gigita ni ."
Muhammad ya dago da jajayen idanuwansa ya dube su ya ce " kowa ya fada min me yake tunanin Nihal zata aikata da zai jawo London da Kano gaba daya ta hargitsa haka ? "
Aliyu ya ce " ko kirista ta zama zata auri kirista. In ba haka ba me zai sa Daddy da Mummy su shiga irin wannan damuwa haka ? "
Gaba daya suka hada baki "wa'iyyazu billah. Allah Ya kiyaye ."
Hamza ya ce " ko wani ta kashe acan ? "
Suka hada baki " A'uzubillahi Allah ma ya kiyaye."
Umar ya ce " Allah Ya sa ba cikin shege ta kunso ba . Kun san fa karatun mace a turai babu muharrami. "
Muhammad ya cije baki ya daki kansa ya ce " kai haba . Muna raye kanwarmu ta aikata daya daga cikin wadannan abubuwa wallahi wallahi da kuwa da hannuna zan kashe ta kuma na kashe banza ."
Abubakar ya ce " abin dai da baa so a fada ne amma na san an yi daya daga cikin abubuwan nan da muka yi harsashe. In ba haka ba me zai tayar da hankalin Daddy da Mummy haka ?"
"Mummy fa ta san komai boye mana take yi kawai don girman laifin ba zai fadu ba ." Hamza ya fada yayin da kwalla ta cika masa ido .
Muhammad ya buga qafa ya ce " daya daga cikinku ya shirya, London din zamu je mu taho da ita . Kamar yadda Daddy ya fada ko a mace ko a raye . Daga ita har kawarta Siyama zasu gwammace dama ba su taba sanin ire-irenmu ba . "
Gaba daya suka hada baki "da ni Zaa je, da ni Zaa je."
Shigowar Motar mahaifinsu suka Hango, yana tsayawa ya fito sai ya gansu sun zagaye shi .
"Sannu da dawowa Dad. " Suka hada baki a lokaci guda.
Bai amsa musu ba sai ma harara da suka samu . Kokari yake ya keta ta tsakiyarsu ya wuce.
Muhammad ya ce " Daddy muna cikin damuwa , muna so mu ji abinda yake faruwa."
Daddy ya ce " idan ta yi tsami za ku ji ." Ya wuce abinsa.
Abubakar ya zabura ya ce " Daddy mu na da hakkin mu sani don 'yar uwarmu ce ."
Daddy ya fada cikin fushi a lokacin da ya bude qofar falo tana qoqarin shiga ya ce "babu ruwana da dangantakarku da ita ." ya barsu a tsaye.
Umar ya fusata ya ce " wannan tsohon fa ya manta da cewa yanzu mun girma ne ? Mun zama magidanta, mun wuce yara. Yadda yake mana hukunci da horo irin na da kamar a bariki, iron sojoji sun kama masu laifi yanzun ma haka yake so ya ci gaba da yi mana."
Muhammad a fusace ya ce " ku jira anan bari in je wajensa. " ya wuce ya tafi .
Babu jimawa sai gashi ya fito a guje, suka tare shi cikin dimuwa suka tambaya ko lafiya ?
Ya na sheshsheqa ya ce " could u imagine da bindiga ya biyo ni."
Aliyu ya kwashe da dariya, gaba dayansu suka yi kansa da tsawa " meye abin dariyar?"
Ya ce " hukuncin Daddy ne ma ya fara bani dariya ma."
Wannan karon Abubakar ne ya juya da sauri ya shiga cikin motarsa ya fice ,
Muhammad ya dubi sauran ya ce "kowa ya tafi, mu hadu gobe da sassafe a babban falo."
Ya na gama magana ya Shiga motarsa ya fice .
Mu'awiya ya bi bayansa shima a cikin motarsa. Yayin da sauran