Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 110552 words

Chapter 12 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

zan biya ku amma kada ku tona min asiri . "


Dariya ta ji an barke ana ta yi ana qyaqyatawa har da buga qafa. Biliyoyin euro din da aka zaiyano mata zaa iya siyan rabin kasarta Nigeria da shi. Duk tulin dukiyar da take tutiya zuri'arta su na da ita ba zata fanshe ta ba .


Ta fada cikin tsawa
" kotu zata raba ni da ku muddin ku ka nuna bidiyon nan ."


" Shin Nihal kin manta kin saka hannu? Ai da amincewarki aka yi ." Steven ne ya tuna mata .


Kafin ta yi magana sun katse wayar. Da ta sake kiran wayar ba su amsa ba .


Ta sulale ta kwanta yayin da ta fara tunanin qasashen da baa cika zuwa ba, wadanda ba sa cikin lissafin duniya . Wadanda ba su taba ganin baqar fata ba ma. Wadanda aka ce su na cinye mutane . Tabbas idan ta kutsa cikin qasar har ta mutu babu wanda zai yi tunanin nemanta a can. Idan kuma an ci saa sun cinye ta shikenan ma an huta . Qasashen masu qananan ido cikin kauyukansu da basu da hanyar mota sai gada da kwale-kwale, idan aka ci saa ma Kada ce a cikin ruwa take zama ajalinsu.


Ta fada a bayyane " Allah Ya sa idan na je tsallake ruwan kada ta cinye ni in huta."


A guje ta tashi ta shiga cikin daki, riga t-shirt da wando Jeans ta saka ta dauki jakarta karama wato puse, abinda ta tabbatar ta saka a ciki shine ATM card dinta da kuma passport dinta. Kanta babu dankwali balle mayafi. Ta saka takalmin shiga bandaki wato silifas. Ta fito da gudu daga cikin gidan bata damu da rufe kofofin gidan ba . Burinta kawai ta matsa daga inda aka taba saninta.


Kano Nigeria...


Dare yayi misalin karfe takwas, Yayyan Nihal sun hallara a babban falon gidan, fuskokinsu gaba daya a cikin damuwa dan ada su na zaton abin nan wasa ne, yanzu sun tabbatar babbar matsala ce. Sun rasa Nihal a waya da duk wata kafa ta social media. Sun tuntubi duk wanda su ka san zasu sami labarinta a acan, sun duba ta baa same ta ba .


General Nuren suka hango ya fito daga cikin dakinsa a sukwane. Ya na tafe da sauri har yana tuntube ya kusa faduwa. A waya yake magana cikin fushi da daga murya .


" Ambasador! Ka tura yaranka kowacce kusurwa, boda da filayen jiragen sama da na qasa da suke fadin garin. A hana ta fita daga qasar, Nihal nake so in gani a qasata, a damka min ita a hannuna ko a raye ko a mace. Na sake fada na maimaita a shiga ko ina a fadin kasar a nemo min ita ."


Ya harare su ya wuce su ya fita da sauri, dukkansu su ka bude baki su na kallon-kallo . Zabura su ka yi da gudu su ka bi bayansa amma tuni ya shige mota ya fita da gudu, wannan karon ma da kansa yake tukawa baya bukatar direba. Ko ina Zai tafi? oho.


Major Abubakar ya daki bango ya fada cikin fushi "me yake faruwa ne? Mu na da haqqin mu sani mu ma fa, amma ake boye mana kamar wadansu bare. Me ya sami Nihal?"


Wayarsa ya zaro da sauri ya kira Siyama, bata amsa ba sai ya kira yayanta Muqaddas.


Muqaddas ya amsa da sauri. Abubakar ya ce " Ina Siyama? Ta qi amsa wayata . Ka fada mata duk abinda ya cutar da qanwata kwaya daya tal a duniya, ba zan yafe mata ba. Sai na tabbatar na yi mata hukunci daidai da abinda ya sami Nihal."


"Malam ka rabu da ni. Ka san halinda muke ciki ne? Yanzu haka za ka ji alamar ina ta nishi, gudu nake da qafata a cikin filin jirgin kano.Ina neman Siyama ance jirginsu ya tashi zuwa Abuja. Ta bar wasiqa cewa ta tafi London su hadu da Nihal zasu shiga duniya ba zaa sake ganinsu ba har abada." Muqaddas yana gama fada ya kashe wayar ba tare da ya jira amsa ba .


Tashin hankali ya sa Abubakar ya yi wani qara da kururuwa, shi ya jawo hankalin sauran a guje su na tambayarsa.


Ya dago da jajayen idanuwansa ya dube su ya ce komai ya gama dagulewa, Siyama ma ta gudu za su hadu da Nihal su shiga duniya."


A tare su ka fada "mu je wajen Mummy ko qofar mu balla mu duba mu gani ko tana raye ma, idan tana raye kuwa yau sai an fada mana mugun abinda yake faruwa ake boye mana ."


Da sauri suka isa bakin qofar dakin mahaifiyarsu, Aliyu da Umar sun tukirkire sun yi baya zasu tako da gudu su doka da qafa su balla qofar sai Muhammad ya hana su .


" ku dakata Ciwon Mummy baya son hayani da tashin hankali. Mace ce mai saukin kai idan mun lallabata zata fada mana komai ."


Su duka suka ja da baya suka bashi waje. Ya qarasa jikin qofar ya qwanqwasa sau daya sau biyu sai ya saka kunne a jikin qofar domin ya jiyo motsin bude qofar bandakinta, yana magana cikin sanyin murya da lallashi.
" Mummy 'ya'yanki ne gamu nan gaba daya mu 7 muna cikin tashin hankali. Ki bude mana qofa mu shigo dan mu duba lafiyarki. Mummy ke kadai muke gani mu ji dadi a ranmu, idan damuwa ta taba lafiyarki ko kika rasa ranki na tabbatar mun yi sallama da farin ciki mu ma. Mummy ki yafe mana, ki tausaya mana muna sonki "


Gaba daya suka hada baki "Mummy muna sonki ki bude kofar ."


Baa dauki lokaci mai tsayi ba su ka ji an bude qofa . Professor Shatu ce ta bayyana a bakin qofar idanuwanta sun yi luhu-luhu abin ka da farar fata. Ta rame ta kuje. Su dukka suka durkusa suka gaishe ta . Ta amsa amma dakyar take magana daga gani bayan bacin rai akwai karancin rashin abinci a jikinta.


" Mummy ki fada mana dan Allah me yake faruwa da Nihal? " Usman ne ya tambaya cike da damuwa.


Za su yi mata magiya ta daga hannu ta tsayar da su sannan ta daddana wayarta ta miqa mu su. Muhammad ne ya karba ya fara karanta sakon a bayyane . Sakon Nihal ne da ta turo mata wanda take neman gafara daga wajen Allah da iyayenta da Yayyanta da saurayin da zata aura. Sakon qarshen ne ya gigita su da ta ce a daya zaa yi biyu ko ta bar duniya ko ta shiga duniya. Ka da ma su yi wahalar nemanta a London don ta qara gaba .


Da gaske babu wanda bai gigice ba su ka fara jejjero mata tambayoyin da ba ta san amsoshinsu ba .


"Mummy me aka yi mata ? Me ya faru da ita? Da ta turo miki saqon ke me kika ce mata? Ba ki tsayar da ita ba ? "


Amsa daya zuwa biyu ta basu ta ja qofarta ta rufe " Ban san abinda ta aika ta ba gaskiya, mahaifinku bai fada min ba ya ce idan na amsa wayarta bai yafe min ba . Abinda nake so da ku shine ku gaggauta barin bakin qofar dakina kafin ya zo ya tarar da ku yayi zaton wani abu mu ke kunsawa. Nihal kuma ina yi mata addua Allah Ya jikanta ku yi mata hukunci daidai da laifin in har ma ta dawo qasar kenan ."


Bayan nan sai ta shige ta kulle dakin da mukulli. Hamza zai sake bugawa Muhammad ya riqe shi ya ce " kada ka buga mata qofa . Ku zo mu fita kawai ,"


Ya wuce gaba su na biye da shi a fusace kowannensu yake .
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI


Na


Jamila Umar Tanko
(JUT)


Da su ka isa unguwar zoo road sai Hashim ya kira Darakta Abbas a waya sai ya fada masa inda za su tsaya, zaa zo da mota a dauke su.
Ba jimawa wata mota qirar Honda civic ta zo ta dauke su, direban bai tsaya a ko ina ba sai Tiga kwanar dawaki.
Sun isa wajen sun iske dandazon mutane ana tsaka da daukar shirin.Nihal na dosar wajen abinda kunnuwanta su ka fara jiyo ma ta shine.
"yau ma tsinanniyar 'yar qauyen nan su ka sake kwaso mana." Aisa buzuwa ce ta fada.
Yayin da dukka 'yan matan da su ke zaune da ita su ka juyo su ka kalli Nihal.
Tafiya su ke yi cikin sanyin jiki kasancewar sun shigo cikin wata duniya da baa qaunar ganinsu.
" wannan ce wannan me tsallen?Jin ta ya fi gabinta."
Wasu samari ne su ke gulma, maganarsu ta gangaro ta fado cikin kunnuwan su Nihal.
Har yanzu dai tafiya su ke su na kutsawa cikin jamaa, fatansu su isa wajen Darakta Abbas wanda su ka zo dominsa.
Su ka ci karo da Bash Auta da su ka gaishe shi sai ya amsa dakyar cikin rashin sakin fuska, ya wuce abinsa kamar bai taba saninsu ba.
Nihal ta isa in da Darakta ya ke zaune, ya na ganinta ya zabura ya miqe cike da murna.
"Yauwa zo nan Nihal." Abbas ya fada .
Su ka koma gefe ya na yi mata bayanin abubuwan da ake so ta yi.
Ya ci gaba da cewa "an ce baki iya karatu ba kada ki damu da bayan ki da jikinki kawai zamu yi amfani ba magana za ki yi ba."
Ta gyada kai ta ce "babu damuwa Darakata."
Ya nuna mata wani saurayi mai jar riga ya fada mata sunansa Ahmed Usman ya ce ta je wajensa ta karbi kayan da za ta saka. Cikin sauri Nihal ta nufi wajen Ahmed Usman ta fara yi masa bayani.Ya na ji ya yi kamar bai ji abinda take cewa ba, ya ci gaba da hirarsa da su Aisa.
Nihal ta sake maimaitawa "Darakta Abbas ne ya ce ka bani kayan yaqi zan saka."
Sai can bayan ta dade a tsaye ya juya ya dube ta sama da qasa.
Ya ce " au wai da ni kike? Kamar yaya in baki kaya ban sanki ba."
Aisa ta kwashe da dariya su ka tafa ita da Hasiya carkwai su ka ce " kai ma ka fada, kwashe-kwashen Darakta Idris ce shima ya jonawa Darakta Abbas ya kwasa."
" Au wannan ce wannan me tsallen da su ka samu take burge su? Ni fa ban ma san haka take ba ." Ahmed ya fada cikin isgili.
Su dukka su ka kwashe da dariya su ka yi shewa.Sai da su ka gama isgilancin sannan ya miqa mata kayan. zuciyarta sai tafasa kawai take yi kamar za ta ce ta fasa sai ta daure kawai.Ta karba ta juya za ta tafi sai su ka yi kicibus da wani mutum. Har sai da kayan hannayensu dukka su ka zube a qasa, daga nasa har na ta.
A fusace ya dago zai rufe ta da fada sai su ka hada ido, Darakta Tukur ne shima ya qaraso dauke da wasu kayan .
" ke! Nan ki ka zo? me na ce miki dazu? Wallahi tunda baki da kunya ki ka yi min rashin kunya ba za ki sake yin aiki ba."
Su Aisa su ka taso da sauri su ka zo aka kewaye Nihal kowa yana fadar tasa baqar maganar akanta. Hayaniya ta hargitse Hashim da Najaatu ne su ka fuskanci da Nihal ake sai su ka rugo da gudu wajenta.Ta na tsaye ta sunkuyar da kai qasa hawaye ne ke ta kwaranya.
Abbas ne ya qaraso da sauri ya na tsawa" wai meye yake faruwa ne ake ta hayaniya haka? "
Tukur ya cije baki ya nuna Nihal da yatsa ya ce "wannan marar kunyar ce ta bangaje ni bayan dazu a Wudil ta gama cashe min da rashin kunya.Na yi rantsuwa ba zan sake saka ta a fim ba kuma duk abokaina ba zasu sake saka ta a fim ba ."
"ba ita ce aka ce a hannunka Babanta ya damqa ta ba? Ko rannan ma ai kai mu ka nema da ake nemanta." Abbas ya tambaya cike da mamaki da damuwa.
" Tukur ya ce " eh mana da ta daina saka barkakkiyar riga sai ta fara ta kai na. Wato na wayar da ita yanzu tafi qarfina."
Aisa ta yamutse fuska ta ce "Darakta ka dai gani da idanuwanka,ka nace sai ka yi aiki da ita.Ba ta da mutunci fa ga girman kai,gaskiya in har da yarinyar nan zaa yi aikin nan ni ba zan yi ba."
Najaatu ta ja hannun Nihal ta ce "zo mu tafi Nihal ki daina kuka, rabu da su."
Abbas ya zabura ya ce " ku tafi ina? Nihal kin fasa yin aikin ko za ki yi?"
Hashim ya zabura ya ce " za ta yi mana Darakta, ai abinda mu ka zo yi kenan."
Tukur ya zabura ya kaiwa Hashim mari sai ya tsugunna.
Tukur ya ce " ka ji dan iska na ce ba za ta sake yin kowanne fim ba kana cewa za ta yi.Munafuki kai ne ka ke zuga ta ka na fasa mata kai ka na nuna mata ta fi kowa, kana tuttura ta har ta ke ji daidai take da kowa."
Hashim ya fusata ya ce " shine kuma za ka mare ni. Me nayi maka?"
Nan dai hayani ta kaure tsakanin Hashim da Tukur. Tukur ya na surfa masa ashar Hashim ya na yi masa gargadi akan ya daina domin idan ya gaji zai rama shima.
Bash Auta ne ya qaraso ransa a bace ya daka tsawa sai kowa yayi shiru ya nuna Aisa da hannu.
Ya ce " ke baki da kirki wallahi kin tsani yarinyar nan.Me ta yi miki? In kin yarda da kanki me yasa kike tsoron wata ta zo itama ta gwada ta ta gwanintar? Ina zaune a can duk abinda ya faru ina gani.Kai kuma Tukur da kake rantsuwa ka daina saka ta a fim na ji na yarda fim dinka ne kana da dama amma baka da damar da za ka biyo ta har wani gari ka ce ba za ta sake shiga wani fim ba."
An dade dai ana musanyan yawu qarshe aka bawa Nihal haquri aka ba ta kaya ta shiga wani daki ta canja.
Ranta a bace yake matuqa da jikinta take yi amma kowa ya san da zuciya take yi,da alama a fusace take dan haka bajintar da ta yi a yau har tafi ta ran nan.Ta yi sukuwa a doki,ta kai sara da takobi, ta hau tsaunuka ta diro.
Har ta yi ta gama bata ce wa kowa uffan ba.Ta na gamawa ta wuce cikin wannan dakin ta canja kayanta ta fito.
Ta kalli Hashim ta kama hannu Najaatu ta ce "ku zo mu tafi."
Abbas ya zabura ya tari gabanta ya ce " yaya za ki tafi?Ai da saura gobe zaa qarasa, akwai gida na musamman da zaa sauke ku, ku kwana sai gobe ku qarasa. "
Ta girgiza kai ta ce " ba na kwana a location a gida zan kwana, gobe ku fada min in da za mu same ku sai mu dawo."
Ya gyada kai ya ce "toh babu damuwa, ga kudin aikinki na yau."
Ta girgiza kai ta ce " ba na buqata a bawa Tukur domin shi ake bawa."
Tukur ya cika da mamaki sai kunya ga nadama su ka kama shi.Ta wuce ta bar shi a tsaye sororo.
Abbas ya ce " ka ji ta ce a baka saboda ita har yanzu a uban gida ta dauke ka."
Bash Auta ya gyada kai ya ce "kun gani ko? Yarinyar nan ba ta da matsala da kowa amma kun bi kun uszura mata. Ita rayuwarta kawai take bata damu da kudi ko neman suna ba."
Mamaki ya hana kowa sakat a wajen gata dai talaka futik amma ba ta da kwadayi,an rasa in da ta nufa ko kuma yadda zaa fasalta halinta.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads