Header Ads
Showing 90001 words to 93000 words out of 110552 words

Chapter 31 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

wannan hukuncin da na yanke. Idan su basu sani ba ku kun sani Nihal daman can 'yar Fim ce, ta riga da ta yi fim dinta a turai. Me yayi saura? Dan haka na ce mu ma ta zo nan ta yi mana mu ma buqatarta. Hakan da na yi na tabbata Nihal ba zata sake yanke wani hukunci Gaba Gadi ba."
Ina bibiyar labarunta a industry na ji labarin dukka gwagwarmayar da ta sha har ta kai ga samun nasara. Daga ranar asabar mai zuwa har zuwa wata guda zaa dinga haska fim din Nihal mai suna Gimbiya Nihal. ina so gaba dayanmu mu je mu taya ta murna."
"Murna kuma Daddy meye abin murna dan an ga kanwarmu a fim? Ai mu kunya zamu ji ma." In ji Aliyu.
Hamza ya ce "mu je mu gani dan kowa sai yabonta yake, an ce baa taba yin bajintar da ta yi a fim ba."
Mu'awiyya ya ce " jaridun arewa fa gaba daya labarinta aka buga yadda ta shigo da yadda ake tunanin 'yar attajirai ce."
Prof. Shatu ta ce " ina ganin punishment din da aka yi mata ya isa haka a dawo min da 'yata gida. Dazu da safe ma na ji hirarta a BBC radiyo"
" This is serious wai daman Hausa fim har sun samu karbuwa a haka a duniya?" Muhammad ya tambaya.
Major Abubakar ya ce " ni kuwa Muqaddas ce min yayi ya ganta rannan duk ta rame ta lalace, yararo-yararo da ita a cikin tsumma."
Nan dai kowa ya yi ta fadar albarkacin bakinsa. Aka tsayar da shawara Zaa dunguma a je cinema cikin shoprite ranar asabar da yamma.
Siyama da Muqaddas sun hada baki sun cewa iyayensu zasu je unguwa sai kowannensu ya fito daban daban a cikin motocinsu.
A shoprite suka hadu sai gata ga Major Abubakar, bayan tsawon lokaci ba su hadu ba sai dai a waya, iyayensu sun raba alaqarsu auren da aka dade da tsayawa ya rushe.
Major Abubakar ya harare ta ya ce " meye abin zuwa kallon Hausa fim kuma ku da aka ce ku guje mu?"
Siyama ta yi gatsine ta ce " na zo na ga qawata ne ba dan kai na zo ba."
" fadi gaskiya dai." major ya fada cikin faraa.
Cinema ta cika damqam da jamaa jaruman fim kusan gaba daya sun hallara amma kowa waigawa yake ko zai ga Nihal anma babu ita babu kamanninta.
Sai ga Abbas ya iso shi kadai babu Nihal. Tawagar Tukur ma sun samu isowa su Hashim, Najaatu, Mami da su Amina 'yar kwalisa.
Abbas ake tambaya shima yana tambayar su Nihal. Hashim yayi ta kiran wannan wayar da Bash ya bata amma tana shiga baa amsa ba. Haka Bash ya kira ya fi sau hamsin babu amsa.
" Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Abbas yake ambato domin duk wadannan jifgin jamaar masu son ganin Nihal ne in bata zo sun ganta ba ba zasu ji dadin kallon fim din ba.
Haka su Abbas suke ta bada hakuri cewar Nihal na kan hayar zuwa.
Shishshigin Hashim ne ya kai shi wajen mahaifan Nihal ya gaishe su ya gabatar da kansa a matsayin babban amininta. Su dukka suka taru su na jeho masa tambayoyi har ya tsorata, dan bai san in da Nihal take yanzu ba. Ya yi wuqi-wuqi da ido yana kame-kame.
" Lah ga Nihal din can." Naja'atu ta fada cikin murna. Sai kowa ya waiwaya ya dube ta.
Nihal Nuren Mubin ce ke tafe cikin nutsuwa da Jan aji, ta yi kyau ta bawa kowa sha'awa. General ya dubi Conel Muhammad ya ce " Nihal ta na buqatar security ka tura yaranka su yi mata exco. 'Yan jarida da dandazo Jamaa ne su ka yi kanta tun ana iya hango ta har aka daina hango ta sun kare ta.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 鉂�


GABA GADI


NA


JAMILA UMAR TANKO
(JUT)


Kan ka ce kwabo sojoji sun shiga tsakiyar ta da mutane, camak su ka yi ka yi kwana da ita baa san ma ta qofar da aka shiga da ita ciki ba, sai dai aka fadawa su General su shiga ta baya su ma.
Sun Shiga cikin cinema an fara nuna fim din Gimbiya Nihal. Bilal, Halima,Aisa sai suka disashe kai ka ce baa taba rububinsu ba,babu wanda yake ta ta su kowa sai Nihal.
Sun yi nadama da su ka qi yin fim din nan, wannan fim ya yi matuqar yin kyau amma sun manta wacce ta sa fim din ya qayatar. Daman masu iya magana na cewa daidai kudinka daidai shagalinka. Nihal ta saki kayan aiki dan haka dole fim ya yi kyau. Sannan acting din da ta yi babu wanda zai iya kwatanta irinsa ma.
Bash Auta yana kusa da su sai murmushi yake yi kawai, don yana son irin haka ta faru mutum ya tafka tsiya tun daga duniya Allah Ya yi masa kamun talala.
Ya na jin dadin yadda Nihal ta samu daukaka a cikin dan qaramin lokaci ya tuna irin hakurin da ta yi da wulaqancin da ta sha, tabbas mai hakuri shi ke da riba dan bata yin fushi sam. Ya dinga aiyano ranar da Nihal za ta amince da soyayyarsa ta yarda ta zata aure shi. Daman can ya rasa dalilin da ya sa take burge shi gata a cikin tsumma kuma yanzu ma ta ci gaba da burge shi.
Aisa ce a kusa da shi ta lura murmushi ne cike da fuskarsa, baya ma taya su takaici ko yayi kishin kansa.
Ta kula daga an nuno Nihal aai murmushin ya qaru. Ta yi tsaki ya yi qwafa ta harare shi. Bai kalle ta ba, gyada kai kawai yake ta yi kamar mai jin kida.
"Lallai iska tana wahalar da me kayan kara."
Bash ya lumshe ido ya ce "Allah sarki Nihal tawa ta gaji arziki, ta gaji mulki, ta gaji ilimi. Allahu akbar. "
Bilal ya fusata ya ce "Bash! wannan cin fuska ka ke yiwa Aisa fa, babu kyau."
Bash ya ce " ka ji na ambaci sunan wata Aisa a maganata ne?"
Halima Jabir ta fusata ta ce "ke ma Aisa kin cika naci ki rabu da shi ya je ya qarata da wannan banzar. Masoyanki burjik wadanda suka fi shi komai, masu kudi ma da kamala."
Bash ya tuntsire da dariya ya ce " da ma ya fi wallahi da na huta."
Aisa ta fara zubar da hawaye zazzafa.
Hasiya carkwai ce a kusa da ita ta yi mata rada ta ce " ki kwantar da hankalinki wallahi sai mun kaita wajen baka anyi ma ta a asirin da ba zaa sake kallonta a industry ba kuma sai mun yi musu farraqu da Bash din, sai ya ji ya tsane ta."
Aisa ta yi murmushi ta share hawaye. Bash ya harari Hasiya Carkwai ya ce "in junanki gulma da hassada haka za ki qare babu ci ga, sai dai ki yi ta rakiya gashi dai kina zaune Nihal din da ku ka tsana ta zo ta haye ta barki."
Ta fara magana tana daga murya, sai Bash ya tashi ya bar wajen dan ba zai iya zama a kusa da wadannan ba. Hassada ta gama cinye musu zuqata. Wajen Abbas ya koma suka zauna. Tabbas an cika damqar a cikin cinema nan, sai ihu ake ana jinjina. Nihal ta kawo canji a cikin masana'antar nan sai ka rantse ba Hausa fim kake kallo ba, kai ka ce turawa ne su ka shirya komai kamar gaske ga jini nan ga kayan ciki a waje duk Nihal ta tsara kuma ta qara wasu a wajen editing.
General da Prof. shatu sai suka zuba ido Prof kallon Nihal a fim, su na fada a zuciyarsa "yanzu 'yar mu ce ta yi wannan bajintar kamar a mafarki? Haka 'yan uwanta maza suka saki baki su na kallo, kansu ya daure yanzu ace Nihal ce ta yi wannan bajinta. Siyama ce kadai ta samu ta kutsa aka shiga da ita wajen da aka boye Nihal daman ita ta san komai ko a turai su na jinjinawa fasaharta.
Muqaddas ya zaci zai ganta ta na rawa ko wani shirme a fim, amma bai gani ba fim ne mai nishadantarwa in ka kalli sin din farko ba za ka iya tashi ba sai ka so ka ga me zai faru a nan gaba.
Ta yi shigar mutunci ta yi amfani da kalamai masu muhimmanci, ta yi waazi, ta fadakar. Shi dai a yau ya daina ganin illa a fim da har ake cewa ba zai aure ta ba.
Toh in haka ne babu illa a fim din Hausa kenan sai dai su 'yan fim din ne suke bata rawarsu da tsalle wajen yin abinda bai dace a zahiri da badini ba. In har zasu kare mutuncinsu da martabar gidansu gami da Addininsu su shirya fim mai ma'ana, Me zai sa a zage su? In har zasu yi qoqarin yin acting kamar na Nihal din nan su fitar da sako da darasi ta sigar wa'azi tabbas zaa daina zaginsu da sukarsu da zargi akan su na lalata tarbiyya.
Sai tafa hannaye ake ta yi ana ihu ana kiran " sai Gimbiya Nihal Nuren."
Masu kallo sun yi amanna tunda su ke basu taba kallon fim din Hausa mai maana kamar wannan ba.
'Yan gidan su Nihal basu taba zama sun kalli fim din Hausa tun daga farko har qarshe ba sai yau. Sun ga nutsuwa sun ga fasaha ga hikima. Tabbas sun yi jinjina sai suka ji kansu yana fadi yana fashewa saboda kowa a wajen Nihal da Nuren Mubin yake kira, dan haka Nihal ta yi suna, mahaifinta yayi suna, danginka gaba daya sun yi suna.
Sai da aka gama aka firfito. Nihal ta fallo da gudu ta rungume mahaifiyarta da 'yan uwanta gaba daya sai hawaye kowannensu yake an tafi shekara guda kenan basu ganta ba. Mahaifinta kuwa yayi-yayi ta zo wajensa amma ta qi zuwa. Da alama tana fushi da shi ne tana zargin baya sonta yanzu tunda ya kai ta ya wutar ya tafiyarsa.
Da ya ce ta zo su tafi gida sai ta ce ba zata koma gida yanzu ba don bata gama ayyukan da ta dauki alqawari ba. Nan fa su ka ja itama ta cije sai da ta ga alamar in bata bi su gida da qafarta ba sojojin nan zasu cicvibe ta su saka ta a cikin mota da qarfin tsiya.
Kalaman mahaifiyarta ne ya tayar mata da hankali sai ta ji dole ma ta koma gida.
Prof Shatu ta matse hawaye ta ce " ni kuma laifin me na yi mu ku da ku dukka ku ke azabyar da ni? laifin junanmu ya na shafa ta. General ya azabtar da ni da ya dauke ki daga gabana ya kai ki in da ban taba sani ba balle na je na nemo ki duk a sanadiyyar ya na so ya hukunta ki. Ke kuma yanzu kin ce ba za ki dawo gare ni ba a sanadiyyar kina jin zafin hukuncin da ya yi miki."
Nihal ta goge mata hawayen fuskarta ta ce "Mummy ki daina kuka zan bi ku gida. Shikenan?"
Tawagar Bilal da tawagar Tukur da tawagar Abbas da sauran wasu 'yan fim din ma haka suka yi carko-carko a gefe su na kallon 'yan gayu da qarshen gayu wato Nihal da 'yan gidansu. Babu yaren da yake tashi sai turanci, Original turanci ba irin na Lagos ko a Abuja ba.
Mami harka ta kama baki ta ce " ikon Allah. wai yanzu wannan Nihal ce da ta zo tana tsamin dusa da hayaqi na dingi cin ubanta ashe kadara ce ba irinmu ba ce. Amma yarinyar nan ta yi mana ba zata, ta cuce mu da bata nuna mana martabar ta ba sai da muka gama tafka kuskure."
Asabe da Iyantu suka ce "ai shikenan kashinmu ya bushe babu mu babu wannan tagwamashi da 'yan fim za su samu ta hanyar Nijal."
Tukur ya ce :zata yafe mana tana da imani, nima na yi mata rashin mutunci kala-kala wallahi har kunya ta nake ji, nadama nake.
Amina ta yi a ajiyar zuciya ya ce "ni ce har da rantsuwa idan ina raye Nihal ba zata zama super star ba a she ma super star ce a turai ba ma a Wudil ba."
Aisa kallon Bash kawai take yi ya qurawa Nihal da iyayenta ido ko giftawa baya yi, ta tabbatar ta gama rasa shi don yayi nisa a son Nihal.
Bilal kuwa kamar yayi fuffuke ya kamo Nihal saboda tsananin son ya shiga harkarta, shi kula shi ma ko sau daya ne abu ya gagara.
Idris ya dubi Abbas ya ce " mu na neman alfarma ka yi mana iso ko Nihal zata yarda ta yi min fim ko guda daya ne. Ashe rabon a wajenka yake nayi-nayi ka bari kada aka saka ta a fim ka qi yarda. Allah Ya sa bata ji labarin yadda na dinga kushe ta ba."
Su ka yi dariya su dukka.
Nihal ta sa Abbas ya zama shugaba a cikin Daraktoci saboda kowa kamun kafa yake yi da shi akan ya gayyato masa Nihal.
Hashim da Najaatu su na ta murna su na kallon kowa daya bayan daya duk me son yin magana da Nihal dole ya biyo ta kansu. Fim ya karbi jamaa su na ta zuwa suna gaisawa suna daukar hotuna da Hashim da Nakaatu abin mamaki babu mai kallon su Aisa sosai.
Tsala-tsalan motocin su Nijal ne ke wucewa daya bayan daya sojoji ne a gaba da bayansu suke yi musu rakiya.
"Tabbas su Nihal ba dan qaramin kudi gare su ba fa. Masu kudi ne kawai.: In ji Bilal.
Tukur ya cusa ashar ya ce "wallahi mun kwafsa da muka bari dama ta wuce mu. Yanzu sai gyaran Allah kawai."
Kowa ya tafi da labarin Nihal a bakinsa mamaki ya kasa barin zuciyar kowa.
Nihal Nuren ce ta ganta a gida a cikin dakinta tamkar a mafarki sai hawaye yayi ta sirnano mata da ta ga an hada kayanta komai a waje daya kamar wacce ta mutu, komai an kife shi har da hotunanta.
Ta bude durowar kayanta ta ga tsala-tsalan kaya na miliyoyin kudi sai ta tuno lokacin da take hada yagaggun kaya tana kullewa. Ta tuna lokacin da Hasiya carkwai da Aisa suka yaga mata riga, su Mami su na yi mata dariya da gori.
Ta tuna lokacin da Hashim ya suturta a lokacin da komai ya yayyage ta fada a bayyane ni kuwa da me zan sakawa Hashim da Najaatu a rayuwata su sururta ni a lokacin da maqiya suke so su yi min tsirara.
Ta hango wayoyinta da laptops dinta an ajiye su a gefe sai ta dauko ta saka a caji. Da ka jima sai ta kunna.
Hohoho jerin gwanon sakonnin ne suke ta shigowana daga turai da na nan gida. Harkar arziki tako ina ake nemanta wasu har sun wuce ta wasu kuma na yanzu ne. Alert ne rututu ke luguden shigowa. Miliyoyin kudin ba zasu qirgu ba, wasu kudin daga yayyanta ne ashe sun ci gaba da bata kudaden da suka saba bata duk qarshen wata. Haka

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads