Showing 24001 words to 27000 words out of 110552 words
Chapter 9 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
ta ba ce . Kudinta naira dubu takwas ne ya fado daga cikin buhun suka kwashe suka ce a kudin hayar dakinsu zaman da ta yi. Burushinta na baki da sabulu da soson wankanta duk a zube a tsakar gida.
Najaatu ce take bi tana kwashewa tana zubawa a buhu. Itama sabon suna suka rada mata su na kiranta da Munafuka annamimiya.
Ta na ta amsa musu da " na gode , ba zan yi zalumci ba haka hassana ce ke damunku kuma insha Allah Nihal sai ta shahara."
Darakta Aliyu ne ya aiko yaro ya ce ya yi masa sallama da Nihal. Yaro ya rada sallama ya ce " wai Nihal ta zo in ji darakta Aliyu yana kofar gida."
Mami da Iyantu ne su ka fice da sauri suka iske Darakta. Ya sanar musu Nihal yake nema zaa tafi wajen daukar fim . Sai gabansu ya fadi aka hau kallon-kallo a junansu.
Mami ta ce " yanzu Aliyu mu na garin nan ka tsallake mu ka nemo wannan wawuyar qazama a cikin tsumma."
Ya ce " zamu yi maganar nan gaba ina take yanzu sauri muke ."
Iyantu ta ce " waya ya ga son maso wani ai kai kake ta tata ita kuwa ta sami wadanda suka fi ka maiqo da kayan aiki da kudi ."
Kansa ya daure ya kasa fahimta sai da suka tambayi sunayi, su ka shaida masa da luntsumemiyar mota aka zo aka dauke ta ita da dan korarta Hashim zuwa daukar shiri tare da Darakta birni Idris Hayat. Sai gaban darakta Aliyu ya fadi hankalinsa ya tashi banda Nihal babu wacce zata yi masa yadda yake so . Sun zaci zai zabi daya ta meye gurbinta sai ya hau babur dinsa ya tafi jikinsa a sanyaye.
"Nan gaba fa ban san iya shahara da yarinyar nan zata yi ba, kalli ku ga har an fara yi mata layi tana har sai ta zaba ." In ji Asabe
Mami ta ce " ya kamata mu hadu da su Amina 'yar kwalisa mu yi meeting mu nemo mafita domin idan muka zaune a garin kallon ruwa kwado zai yi mana qafa."
Nihal Nuren Mubin ce da su Aisa ake kallon-kallo a lokacin da motarsu Darakta ta tsaya a gaban su. Nihal ta fito daga gidan gaba, ga ta ga babban darakta ga Bash Auta Jarumi mai tashe mai kudi ga Jan aji.
Nihal ta fara tafiya tana sanda, Hashim ya rada mata ya ce " ki cire tsoro zasu raina ki fa , duk wacce ta taba ki ki yi mata irin yadda kika yiwa Amina ."
Nihal ta ji wani karfin zuciya ya tunkaro ta sai ta saki jiki . Bata kallon idanuwansa ma balle ta san su na harararta .
Aiki yayi aiki Nihal ce ke sukuwa akan doki Kamar ba mace ba. Amma yadda tsarin yake a matsayin Amina ce. Idan aka dauki bayanta sai a dauki fuskar Amina. Domin Amina ba zata taba yin kwatankwacin abinda Nihal ke yi ba .
Haka kowa ya fuskanci Amina tana jin haushin Nihal musamman da Amina ta yi wani furuci a gaban kowa ta ce "ada da Nihal din bata nan ba hakuri kuke yi da yadda muke yin acting din ba, sai yanzu dan ta yi mu ku rufa ido zaa dinga tafa mata ana ihu."
Da aka zo rawa da waqa darakta ya ci gaba da tambayar Nihal ko tsarin yayi ? Ya nemi da ta shiga cikin 'yan rawa ta nuna musu domin sun tabbatar zasu sake samun wata sabuwar idea. Sai Nihal ta ce bata taba yin rawa ba, ba zata iya ba. Sun dai ji ta ne kawai amma basu yarda baa yadda suka ga alamar ta zata iya yin rawa sosai, yadda jikinta yake malkwadawa duk yadda take so .
Aka wuni a wajen kuma a ranar aka qarqare shirin . Darakta Tukur yana wajen duk abinda ya shafi Nihal shine wakilinta. Haka maganar kudi, da shi aka yi tsada , amma darakta idris ya fi son ya damqawa Nihal kudin aikinta a hannunta don kada Tukur ya cinye mata nan gaba ta qi zuwa . Abin mamaki yana miqa mata naira dubu ashirin sai ta miqawa darakta Tukur. Wannan abu ya ba su mamaki kuma ya burge su sun tabbatar Tukur ne wakilinta yanzu .
" shikenan Tukur za mu dinga tabo ka ta waya idan ana buqatar Nihal a Fim." In ji Idris.
" ke 'yar kauye ki sayi waya mana ance ki bada lambar waya kin ce baki da waya ko kunya bakya ji. Ashe ma ba ki hadu ba." Bash Auta ne yake yiwa Nihal wasa a gaban kowa. Mutum mai Jan aji da ji da kai yau gashi yana shishshigewa yar qauye.
Sai su Aisa suka tabbatar yarinyar nan fa zata zame musu barazana nan gaba .
Hashim ya zabura Hashim cewa Bash " ga wayar da muke sharing ni da ita kullum mu na tare dan korarta ni . Ba mu lambar taka. "
" Ah ai shikenan tunda ta ce bata da waya kuma bata damu ko a takarda ta rubuta lambata ba."
Hankalin Hashim ya tashi ga samu ga rashi sai qifqiftawa Nihal ido yake akan ta zo ta karbi lambar waya .
Ta kada kai ta yi gaba abinta ko kallonsa bata sake yi ba yayin da mamaki ya kama kowa .
Darakta Tukur ya miqawa Hashim naira dubu daya ya ce su yi kudin mota shi da babur ya zo, su hadu a gidansa da dadare.
'Yan kano suka shiga motocinsu suka zo suka wuce Nihal da Hashim a bakin titi su na jiran mota mai zuwa Wudil. Su ka Kula Hashim ne ke daga musu hannu Nihal ko kallonsu ba ta yi ba .
A hanya ne suka yi ta hirarta Bash Auta ya ce " Darakta tabbas idan yarinyar can ta zana super star yaya zata dinga kallon mutane ne ? Ka ga wani jan aji da take yi tana yanga. "
Darakta ya yi dariya ya ce "tana cikin tsumma ga talauci wanne jan aji kuma? Yadda na fahimta halittar ta ce yanga, wallahi akwai wadanda Allah Ya ke halittarsu a haka kuma ka gansu a kauye amma yanayinsu da dabi'unsu na 'yan birni.
Babban furodusa Umar ya ce "sunanta ne ma yake bani mamaki. Na qanqararrun yan gayu.Tsakani da Allah ina 'yan kauye suka san wannan suna Nihal ?"
Suka kwashe da dariya Bash ya ce " maganar gaskiya fa idan ma ita an shigo birni an aro Nihal din Babanta fa Nuren Mubin ta ina bakauye zai yi wannan qaqalen?
Darakata dariya kawai yake yi ya ce " haka kawai take burge ni ."
Aisa ta tabe baki ta ce " gara da ku ka gane da kanku Cesar yarinyar nan mayaudariya ce, a sunanta ma sai da ta yi rinto. "
Bash ya ce "koma dai menene ta taimaka ki, yanzu za ki burge kowa a fim din nan, sai a zaci ke kika acting din nan . Duk abinda ta yi fa a matsayin kece kika yi. Z aki kara yin suna da daukaka akan abinda ta yi ."
Hasiya ta ce " maganar gaskiya gara bakauyiyar nan ta daina burge ku, rufa ido ne duk wannan tashi saman da take yi. Haba dan Allah kamar ba mace ba ta dinga wani dogon tsallen da maza ma sun kasa yi ."
Su Bash dariya kawai suke sheqawa da suka ji wannan kalmar ta rufa ido . Sun san ta tsorata mata, hassana ce kawai .
Nihal da Hashim sun isa gida da magruba suka iske wannan wulaqancin, kayanta ne a zube a waje ashe bayan Najaatu ta harhada kayan a buhu da ta fita sake zazzagewa suka yi a qasa suka barbaza.
Kafin ta yi magana Mami ta fito ta bata amsa " a qara gaba tunda nan ba gidan tsoho ba ne, mai face majina ya goge a riga ."
Nihal ta ji ba zata iya daure jin kalaman tozarcin da ake yiwa mahaifinta ba wanda ya yi mata komai a rayuwa.
Ta cije baki ta kalli Mami gami da nuna mata hannu ta ce " na yarda ki yi min dukka wulaqanci amma kada ki kuskure ki sake zagin Mahaifina, iyayena su ne gaba da komai bayan Allah da Manzonsa. "
Mami ta tuna casuwar da Amina ta sha har yanzu tana can ta na jinyar targade din haka sai ta yi shiru .
Hashim ya fusata ya ce "nawa ne kudin hayar na wata in biya ku daga nan zuwa anjima? Amma ku bar ta ta shiga ko salla bata yi ba ."
" Naira dubu Goma ne kash. In ka isa ka biya yanzu ba sai anjima ba ." Asabe ta fada
Nihal ta daga hannu ta dakatar da shi ta ce " kada ka roqe su, ba zan sake zama da su ba. Sai gashi kun yi min sata alhali ku ne masu gargadina akan kada in yi muku sata, tunda make ban taba sace kudin kowa ba ku dauki komai ma bana so ta juya ta fice a fusace . Hashim ya yi dibi-dibi yana neman daya sabuwar atamfar da ya siyo mata itama bata ciki sun dauke sai tsummakarai su ka bari.
Hashim ya tsaya ya zage su tas ya na kiransu da barayi sai Allah Ya saka mata . Ya ji zafin kudinsa da ya tatike ya mata dinki suka sace dan ma ta saka guda daya da sauki .
Bayan sun fito kofar gida ne Hashim ya ce " yanzu yaya zaa yi kenan? A ina zaki kwana? Ko gidan Tukur zamu je ki kwana daya a gidansa ki fada masa yadda aka yi ya biya miki haya da kudinki na wajensa. Ke ma kiyi kuskure da kika dauki kudinki dukka kika bashi mayen kudi ne fa. "
Nihal ta girgiza kai ta ce " ba zan sake kwana a gidansa ba matarsa ta yi min wulakanci. Haka kada ka sake ka tambaye shi kudin nan in zai riqe ma dukka na yafe masa. Ka tafi kawai zan san yadda zan yi. "
" A a ba zan bar ki a titi ba mu je gidan Marka mai dinki ki kwana ita ta sanki kuma ita kadai ce a gidan daga ita sai yaranta mijinta ba mazauni ba ne ."
Nihal ta qi sai da ta ga naci da magiyar Hashim ta ishe ta sannan ta yarda suka tafi .
Marka ta sakar musu fuska ta yi Amanna Nihal ta kwana daya a gidan. Tun a gabansa aka kawo mata tuwon dawa miyar kuka baqiqirin sai warin daddawa take yi da ruwa a kwanan sha. Sai da ya tabbatar ta sami masauki sannan ya tafi. Yana fita Nihal ta miqe ta ce zata je ta dawo a kwashe abincin ta koshi.
Wajen shazali ta nufa ta karbi abinci da ruwa ta zauna ta ci a cikin office dinsa, sannan ta shaida masa tana son ya fita gobe ya samo mata karamin gida na haya sabo fil take so na sumunti mai dauke dakuna uku ko dakuna biyu . Sannan kowanne daki a sayi katifa babba a saka da labule da zannuwan gado, tana son bokitai da manyan robobin tara ruwa .
Ya tabbatar mata ta bashi daga yau zuwa gobe da yamma . Ta sake karbar naira dubu goma a wajensa ta tashi ta tafi.
Ta isa shagon Musa in da take karbar duk abinda take so, rigar bacci sabulu, omo soson wanka ta karba . Ta kwashi alewa da biskit mai yawa ta kai wa yaran Marka . Suna ta murna kuwa dan haka Marka ta sake sakar mata fuska, suka yi ta hira har sai da suka raba dare.
Asuba ta gari Nihal Nuren .
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI
EP 9
General Nuren Mubin yana zaune a babban falonsa yana kallon labaran tara . Gefensa kuwa uwar gidansa ce Prof. Shatu, bata sakar masa fuska har yanzu shishshige mata yake ta yi duk in da zai je sai ya takura mata ya ce sai ta raka shi . Kallon ma dole yayi mata ta zauna, kallo take ba dan tana fahimtar abinda ake cewa ba. Shi kadai yake kidansa yayi rawarsa, ya yi kallonsa yayi sharhinsa da eh kawai take binsa.
Tabbas ya san bai kyauta ba amma kuma taurin rai da taurin kai da jajircewarsa ta sa ba zai janye ba har sai Nihal ta cika wa'adin da ya kudira a ransa. Shi a cikin lamuransa baya yafiya, ka na b'ata masa rai toh sai ya linka maka linkinsa .
Sallama suka ji suka hada ido suka kalli masu shigowa garadan maza a layi su na ta shigowa da yake kowannensu dogo ne masha Allah. 'Ya'yansu ne tun daga kan Muhammad babban har zuwa Mu'awiyya dan autan maza bayan sun shishshigo sai suka durqusa suka gaishe da mahaifansu, sun amsa musu cikin sakin fuska sai kowa ya sami kujera ya zauna aka rasa wanda zai fara magana a cikinsu. Saboda daman haka ne sai sun shirya magana a waje daga sun zo gabansa sai yayi musu kwarjini su kasa magana .
Aka fara qifce-qifcen ido wannan na cewa wannan ya fara wancan na zungurar wancan .
Prof.Shatu ta fahimci hakan dan haka ta zubawa sarautar Allah ido ta tabbatar wannan al'amarin babba ne. Ta ce a ranta "in ma da niyyar ku yi masa nasiha ku ka zo akan Nihal ina mai baku shawara da kun fasa ba zai taba sauraronku ba."
Asp.Aliyu ya fi su taurin zuciya tun su na yara shine yake iya tunkarar General da magana duk da yana iya haduwa da mari ko harbi da qafa amma baya dainawa.
Aliyu ya ce" Daddy wajenka muka zo. Daman tun bayan tafiyar Nihal fiye da wata daya kenan, ba ma cin abincin gidan nan, ba ma sakin fuska, bama zaman falo saboda muna fushi da hukuncin da ka yanke akan qanwarmu. "
General ya dago da sauri ya dube shi ya fada a shelaqe " da wa kuke fushin. Ai ban ma san ku na yi ba. Oh daman fushi ku ke yi ai bana kallon fuskarku balle in san ku na yi .Yaya aka yi yanzu, kun huce ne ? Ko yunwa ce ta koro ku, ku na so ku ci abincin ne ?"
Aliyu ya juya ya kalli 'yan uwansa saboda wani ya kawo masa agaji ya karbe shi, domin kalamansa sun qare.
Muhammad ya gyara zama ya ce Daddy " na tsayar da shawarar kawai zan koma Enugu da zama ba zan iya zama a arewa ba, zuciyata ba zata iya daurewa ina ganin kanwata a fim tana tiqar rawa ba ."
General tabe ya ce " ina baka shawara dama Afghanistan ka kaura can ne ake yaqi ka je ka kwantar da tarzoma. Ka ga acan babu yadda zaa yi Fim din Hausa ya qarasa musu can ."
Muhammad ya bude baki yana mamaki da wannan baqar amsa.
Major Abubakar ya murtuke fuska ya ce " gaba daya ma a kaina abin ya qare na rasa abokina Maqaddas, na rasa matar da zan aura Siyama gaskiya nima dai gara in tafi Malaysia karatu daman an tura ni ban tafi ba tun last year yanzu gara in tafi ."
General ya qirqiro wani murmushi mai kama da kuka ya ce " dama qasar koria ka kaura anan ake hada bom da Mizanai.
Dr Hamza ya ce " daman ina so in je in yi PHD jamia ta bani damar tafi London zan tafi yanzu.
General ya ce " ka yi kokari Idan ka gama doctoring degree din Department din su Nihal su dauke ka lecturing, kada ka dawo qasar nan ma."
Mu'awiyya ya ce " ga shi sunana ya bazu a harkar aikin jarida sunan nan ba boyayye ba ne daga Fim dinta ya fito zaa gane kanwata ce daman mun fi yin kama da ita . Gaskiya ban san yadda zan yi da zaman garin nan ba ."
General ya ce " ka koma birnin sin China ."
Umar ya ce " gaskiya gara in shiga duniya ."
General ya ce " duniya tana da fadin gaske na yafe maka ka shige ta, kada ka dawo daga can ka wuce qiyama. "
Bar.Usman ya ce " ni dai zan iya maka duk Daraktan da ya saka ta a fim saboda wannan laifi ne.
General ya ce " wanda ya kai ta fim zaka maka a kotu ba furodusa ko Darakta ba . Ina ga mun yi sallama ko ? Kowa ya tashi ya fara hada kayansa gobe da safe ina so in ga gidana wayam daga ni sai mata."
Su ka juya su ka kalli mahaifiyarsu suka hada baki " Mummy kina ji ko ? "
Ta gyada kai ya ce " ina jin ku. Ku daina damun kanku na fada muku addua kawai za ku yi mata Allah Ya tsare ta a duk in da ta ke ."
General ya yi tsawa ya ce " dalla a tashi a tafi ina kallon labarai ku na damuna."
Su ka tashi su na tafe su na layi saboda takaici. A farfajiyar tsakar gidan su ka tsaya su na shaqar iska dan ta rage musu takaici.
Dariya Aliyu da Hamza suka yi ta yi, yayin da hawaye ya dinga kwaranya a idanuwan Muhammad da Abubakar saboda baqin ciki ya ishe su.
Mu'awiyya ya ce " Allah zan Daddy buga Daddy a jarida kowa ya san halin da yake jefa mu. Haba dan Allah kamar wasu bayi ."
Muhammad ya harare shi ya ce " baka da hankali ka buga shi a jarida ka tonawa kanka asiri. Ai mutane ma zasu yi shaida cewar uban nan na mu yayi mana komai rayuwa kai zasu zaga ."
Qarshe dai sauran suka huce akan masu dariya Aliyu da Hamza da gudu su