Header Ads
Showing 63001 words to 66000 words out of 110552 words

Chapter 22 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Duduwa ta ci gaba da cewa "daman maganar gaskiya ke ma Nihal babu yadda zaa yi ace 'yar fim din qauye ta fito kai tsaye ta tari manyan jarumai na birni ta ce za ta fara yin fim da su. Ki dai bari ana sa ka ki a 'yar rawa da 'yar aike a hankali wataran sai ki fito sosai a sanki lokacin kin dan waye kin sami dan kudin siyan mai da sabulu me saka dan farin nan. Kin san 'yar farar fatar nan ake sha'awa mu baqaqe baa ta tamu."
Hashim ya yi carab ya ce "in Allah Ya so kwanan nan itama Nihal za ta fara bleaching in dai dan fari ne ya sa su Halima Jabir suke kwace mana waje."
Wani takaici ne ya kutso cikin zuciyar Nihal ta harari Hashim ta ce " me ya hada ka da maganar mata ? Me ka sa ni akan bleaching? Allah Ya sawaqe in shafa mai in yi fari saboda wani abu wai shi fim. Kun kuwa san menene illar bleaching? Kun san kallon da masu hankali suke yiwa masu bleaching? Ko ni nan ba na yiwa masu yin bleaching kallon masu wayo, rashin dubara ne da rashin mafadi da rashin tunani. Kun kuwa san menene natural beauty? Kun san yadda irin kalarmu ta ke da tsada a turai?"
Jamaa da dama suka dinga waiwayowa su na kallon mai magana domin Nihal ta manta shagalab, ta shiga ingausa wato kalaman turanci da na Hausa take gwamutsawa. Sai ta tuna ashe ba ta taba zuwa makaranta ba dan haka sai ta yi shiru. Har da Hashim a ma su mamakin yadda take magana ta na saka turanci kuma ta na ta bada labarin turai.
" A ina ma ta taba ganin turawa balle ta san yadda suke a turai? Turai ta Dan ciyau garinsu ko ta Gumel?" Hashim ya ke tambaya zuciyarsa?
Tun daga nan Nihal ba ta sake yin magana ba sai takalo ta su ke da hira dan su sake jin wasu kalaman na ta a hada a yanke mata hukunci amma sai ta qi tankawa. Yunwa da tashin zuciya ne ya dame ta ga qura da ta cika ma ta kunnuwa da idanuwa. Tafiya ta qi ci ta qi cinyewa.
Bayan sun iso garin katsina sai aka sake nausawa aka nufi garin Jibiya har sun fara murna sun zaci an zo sai su ka ga an tsunduma cikin bodar Nijer, a wajen Immigration gaba daya motocin su ka taru domin a yi musu kudin goro su wuce akan qa'ida.
Nihal ta bude ido tana ta kallon sabuwar duniya,tana son Nijer daman ta dade tana so ta shiga ta gani da idanuwanta. Musamman sahara da rakuma, tabbas ta fara ganin canji da banbanci da qasarta. Sai ta tsinci kanta tana mai murmushi da farin ciki. Yayin da Hashim ya cika ta da surutu wai shi ya taba zuwa daga nan har Niamey babban burninsu.
Garin Maradi su ka nufa nan ma ya na cikin manyan biranen qasar. Nihal ta ga abubuwa da yawa da qauyuka da dama dan haka ta haddace su a cikin kwakwalwarta tana da buri ta yi rubutu wataran akan rayuwa da al'adun Africa.
Wani gida aka kai su aka sauke su, gidan yana da kyau yana dauke da dakuna da yawa. Nihal sai wurga idanuwa take ko za ta ga sauran manyan jaruman su Bash su Bilal da Halima amma bata gan ba daga nan ta tabbatar nan gidan mararsa galihu ne irinta.
Sai ta ji tausayin talaka bawan Allah tabbas a ko ina sai an nuna masa banbanci. A da ba ta lura amma yanzu da ta dandana rayuwar talauci za ta dinga kokarin jawo talaka a jikinta tana daidaita shi da kanta, ya kamata a daina wariya a dinga daidaito a tsakaninsu da su masu kudi.
Abbas ne ya zo da kansa ya rarraba daki, dakin mata daban na maza daban, amma a kowanne daki sun kai su uku-uku a daki daya wasu ma su hudu ne.
Nihal da Duduwa Indiyana da fati dangerous ne aka hada su a daki daya. Tunda daga jin sunayensu ta san ba za su daidaita ba saboda ba tsarinsu daya ba. Wasu manyan asharai Fati Dangerous ta kwasa ta makawa wani saurayi mai suna Danliti Ado. Nihal ta karbi akwatin ta daga hannun Hashim ta gaggauta barin wajen ta Shiga dakin da aka nuna mata. Ta na shiga ta ga gado ne guda daya sai ta shiga tunanin yadda manya mata guda uku zasu gwamutsa, ga su da qiba duk sun fita qiba. Ta waiga ko ina babu wata katifa da wata daga cikinsu za ta shinfida a qasa.
Zuciyarta ce take hautsinawa kamar zata yi amai a sanadiyyar rashin abinci a cikin hanjinta tun jiya da yamma, jiri ta dinga ji dan haka ta laluba gefen gado ta zauna.
A bakin kofar dakinsu ta ji ana ta hayaniya data leqa sai ta ga babban daro ne shaqe da shinkafa ana rabawa kowa ya dauki plate din roba kamar wasu almajirai. Hashim ya tabbatar Nihal ba zata fito wajen damben karbar abincin nan ba dan haka sai ya kutsa da qarfin tsiya ya karbo plates biyu. Ya kwankwasa mata kofa sai ta fito, ya miqa mata gami da tambayar ta yaya ya ga kamar bata da lafiya. Dakyar ta bashi amsa ta ce gajiya ce kawai.
Ta tura qofa ta koma ta zauna ta kalli qandararriyar shinkafar nan ta hango wani qaramin qashi shine ya nuna an saka nama amma Allah bai sa tana da rabo a ciki ba domin na ta babu nama.
Dole ta daure ta luma hannu ta damqo lauma daya ta kai baki, sai yaji da qauri da rashin dandano suka gauraye bakinta har da kunnuwanta. Ta yi juyin duniyar nan ta iya hadiyewa saboda bakar yunwar da take addabar ta amma abu ya gagara. A dole ta tofo ta a cikin kwandon sharar da yake gefen gadon.
Bakinta ya hau radadi dan haka ruwa kawai take buqata. Ta suri plates din abincin ta fice daga cikin dakin ta iske kowa ya baje qafa group-group ana ta kai lauma. Saboda dadi Hashim ko hango ta bai yi ba.
"Nihal kin koshi ne? Kawo nan ." Fati dangerous ta fada.
Nihal ta miqa mata sai ta afka akan babban farantin da suke ci su uku. Ashe anan su ka juye naman dukka dan su ne masu rabo. Ta hango yankan nama sun fi guda biyar- biyar a gaban kowaccensu.
"Ku bani ruwa in sha." Nihal ta tambaya a rikice.
"Ungo sauran da na sha domin babu wani duk sun wawashe." In ji fati dangerous.
Nihal ta tsaya kawai tana kallon bakin da ya sha ruwa ya rage ma ta dargaje-dargaje da shinkafa da wasu jajayen hakora."
Nihal ta zabura ta ce "babu wanda baa bude ba?" Domin ita har yanzu bata iya shan pure water ba sai na roba gani take zata kamu da ciwo idan ta sha, amma yau a bisa larura in ta sami sabo za ta sha.
Duduwa Indiyana ce ta fusge ruwan daga hannun fati dangerous ta zuqe ta wurgar da leda ta ce " dadi ta yi miki ma da kike neman ruwan da baa bude ba."
Nihal ta koma daki ta zauna ta jawo jakar ta ta bude ta dauki alewa bounty da ta siya ta zuba ta sha dan ya shashe mata yajin da ya addabi bakinta.
Alamar ciwon ulcer ta fara ji qirjinta yana suya sai ta tabbatar ta yiwa kanta azabar rashin cin abinci kwanan nan, idan bata yi da gaske ba zata kwanta ciwo a garin da bata san kowa ba. Ta shiga tunanin yadda zata ceto kanta- da kanta. Zip din qasan jakarta ta zuge in da take ajiyar kudadenta ta dago da wani kudi bandir guda 'yan naira dubu-dubu ya kama naira dubu dari kenan? sai ta hango wani bandir din shine ta zazzara amma shima ya fi rabi. Ragowar kudin gidan da ta siyawa Hashim ne. Sai ta fara tunani a ranta ina ma ta san wani a garin da zai kai ta ta yi canji ta sami wajen abinci mai kyau ta ci ta qoshi.
Shigowar su Duduwa ne ya sa ta yi sauri ta mayar da kudin cikin jaka ta rufe. Hayaniya Su ke ta yi da ihu ba za ka ce mata ba ne, duk magana daya ana rakawa da ashar, ya zame musu ado.
Ta bude akwatinta ta dauko tawul da ledar soso da sabulu na wankanta ta fada bandaki, ba laifi a wanke ya ke amma ta cika da kyama kasancewar bata san su waye su ka yi amfani da ita ba.Dakyar ta iya zama akan toilet din bayan data ta yi mata yayyafin dettol dan da shi take yawo. Ta yi wanka ta dauro alwalla ta bude qofa daure da tawul zata fito. Qartan maza ta ga sun shigo Danjuma Ado ne ya daka tsalle yayi super a akan a tsakiyar gadonsu yayin da Duduwa da Fati sun tube daga su sai zani daurin qirji, ga wasu samarin su na tsatstsaye ana ta hira ana hayaniya. Da sauri Nihal ta koma bandaki ta Mayar da qofa ta rufe. Babu abinda ta tuna sai nasihar mahaifiyarta tun tana qarama ta koya mata yadda zata dinga yin kaf-kaf da jikinta a gaban maza. Mazan gidan ma yayyata ne uwa daya uba daya amma kullum ana koya mata yadda zata dinga zama,babu wawan zama, babu fito da hannun rigar nono, babu sakin jiki da gogayya tsakaninta da maza musamman wadanda ba muharramanta ba.
A dole ta mayar da rigarta me datti ta fito sai ta iske dakin ya qara cika,ta jawo jakarta ta bi ta bayansu ta fice ba tare da kowa ya ganta ba.
Ba ta san dakin su Hashim ba ta dade a tsaye a farfajiyar gidan bata ga fitowarsa ba sai ta fito qofar gida. Ta ga masu adaidaita sahu burjik su ma kamar dai a kano. Ta tsayar da guda daya ta shiga ta zauna ba tare da ta san in da zai kai ta ba. Yaren Hausa yayi mata dan haka ta kwana a gidan sauqi sai ta ce ya kai ta kasuwar da ake yin canjin kudi. Ba tare da bata lokaci ba ya fahimta ya fisgi babur dinsa ya lula.
Da la'asar liqis Bash Auta da Bilal ne suka fito farfajiyar katafaren hotel din da aka sauke su sanye da gajerun wanduna da riga mai qananan hannaye. Wajen swimming pool su ka nufa a inda su ka ga kusan duk mutane da suke zaune a wajen turawan faransa ne, faransanci ake yi. Su ka tsinci kansu su na masu nishadi a kusa da fafararen fata tabbas an sami wajen daukar hotunan da Zaa zuba a Instagram.
Wayar Bilal ce ta hau qara ya dauko ya duba Halima Jabir ce ta je tasha ta taho da Aisa buzuwa domin ita dazu bata gari ta tafi wani aikin dan haka a motar haya ta taho.
Bilal ya ce " ku zagayo ta baya mu na wajen Swimming pool. "
Halima ta ce "ai sai mun je daki mun yi sallah mun ci abinci zamu fito Aisa a gajiye ta ke daga Abuja fa ta zarto Maradi."
Bilal ya kwashe da dariya ya ce shegiya dole ta daku, ba dai tana so ta zama super star ba."
Bai gama dire maganar sa ba sai ya ga wani abu da ya gigita shi har ya gagara qarasa maganar da yake yi a waya. Halima ta gaji da hello hello ta katse wayar. Irin wannan gagarumin tashin hankalin ne ya faru da Bash Auta sai ya zabura ya zare baqin gilashin da yake fuskarsa su ka zunguri juna a lokaci guda.
Bilal ya zabura ya dafe qirji ya ce " ka ga Princess last born da nake baka labari rannan, wacce na ce Bahaushiya ce amma tana american fim."
Bash ya zabura ya ce " wacce irin princess Nihal Nuren Mubin ce kai."
Gaba daya suka bude baki su ka bi ta da kallo sanye take da riga da Wando masu tsada ga wani takalmi mai tsinin gaske kanta babu dankali sai gashi da ya zubo har bayan qeyarta ta na tafe tare da wani bature su na hira abin mamaki yaren faransanci suke yi.
Bilal ya zabura ya kwalla kiran sunanta princess bata amsa ba yayin da Bash ya kwalla kiran sunan Nihal Nuren ko waiwayowa bata yi.
" Yaya ma zaa ce wannan ba Nihal ba ce ?'" in ji Bash. Bilal ya ce "wai wacce Nihal? Wannan kucakar? ko da wasa ma kada la kawo a ranka Nihal ce, wannan princess ce bari ka gani ma."
Ya tashi ya nufi wajensu ya yi sallama amma basu amsa ba.Ya fara magana cikin karshen turanci "Princess za ki iya tuna Bilaliboy abokinki dan Fim a Nigeria? Har kike bani shawara akan yadda zan daukaka."
Ina fa? Ba su ma san me ya ke cewa ba suka bi shi da kallo.
Bash Auta ne ya qaraso ya ce "ga Nihal ka na gani a zahiri ga dimple dinta nan da wushirya ga irin dariyarta nan. Ke Nihal wai ba ki gane mu ba ne ?"
Ta kalle su galala ta juya ta kalli baturen da suke tare cikin rashin fahimta. Yaren faransanci ta yi mu su, daga nan su ka tabbatar bata ma san me su ke cewa ba."
"Ikon Allah wannan al'amari ya daure musu kai ga Nihal nan sak, ga princess nan sak amma ba ita ba ce.
Su ka koma gefe waya Bash ya dauko ya kira Abbas ya tamabaya "Darakta ina Nihal Nuren Mubin take?: Abbas ya ce yanzun nan na fito daga gidan na raba mu su daki."
A' a ka dai sake dubawa ga Nihal anan hotel din da mu ke."
Abbas ya yi dariya ya ce " ba dai Nihal ba ce yanzu na bar ta a gida. Amma bari in kira Duduwa in tabbatar ma ka."
Su ka kashe waya Darakta Abbas ya kira Duduwa ba ta dauka ba sai ya kira Fati dangerous. Bugu daya ta masa.
" ina Nihal Nuren?"
Fati ta ce " ta na wanka." Darakta ya kashe waya ya sake kiran Bash ya ce " Nihal ta na gida yanzu haka su na tare da su Fati dangerous. "
Sai Bash da Bilal su ka sankare a tsaye su ka ci gaba da kallon wannan baiwar Allah Wacce ta yi mu su kama da mutane biyu mabanbanta. Bilal bai taba karewa Nihal kallo ba dan haka bai santa ba amma babu tantama wannan Princess ce. Har muryar su daya dan sun sha yin magana a waya amma abin mamaki sai ga wannan ko turanci ba ta ji sai faransanci.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da Ya halicci Nihal Ya halicci wannan yarinya." Bash ne ya fada a bayyane yayin da ya bude baki yana dubanta, ta zo ta wuce ta gabansu. Wajen shan lemo su ka je su ka zauna ita da bature su na sha su na hira da dariya. Ko da wasa ba ta ma kalli in da su ke ba balle ta nuna ta taba saninsu.
Bonjour ca va Nihal Nuren Mubin.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 馃グ鉂�


GABA GADI


NA


JAMILA UMAR TANKO
(JUT)


Da daddare ne Hashim ya fito neman Nihal domin kusan kowa na gidan ya fita ganin gari, wasu sun tafi gidan kallo, wasu sun tafi wajen Gala, wasu sun shiga gari kawai don bude ido.
A bakin qofar dakinta ya ganta a tsaye rataye da jakarta da alama wani waje take son zuwa itama.
Hashim ya dube ta ya yi murmushi ya ce "baccin gajiya na ke ta yi dakyar aka tashe ni na yi sallar magruba. Mu ma ki zo mu fita waje mu ga gari."

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads