Header Ads
Showing 54001 words to 57000 words out of 110552 words

Chapter 19 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

kurakurai da ake ta maimaitawa a sanadiyar rashin neman ilimi a harkar. Kowa kai tsaye kawai yake fadowa ba tare da sanin qa'ida ba, shiyasa babu ci gaba har yanzu an barmu a baya.
Abbas ne ya katse tunanin da ta tsunduma tana yi ya ce " mu qarasa tattaunawa akan abinda ya kawo mu, ga magruba ta kusa sannan Nihal ba a garin nan suke ba zasu koma kauyensu."
Wani kallon banza Bilal ya yi mata ya ce " ah daga qauye ma ta ke? Ai ni ba ni da ta cewa, Fim dinka ne amma ya kamata mu tattauna kafin ka aiwatar da wannan tunanin naka darakta."
Kowa ya gane abinda ya ke nufi. Dan gudun kada yayi katobara sai Abbas ya yi sauri ya katse shi. Ya ce "za mu yi wannan maganar daga baya amma yanzu dai nan da kwana uku nake so ku shiryo ku fito, wuraren Nijer za mu shiga cikin sahara. Kowa zan bashi script ya je ya duba sinasinan da zai yi, ba na son a sami matsala kada a yi kuskure."
Abbas ya miqawa Nihal na ta himilin takardun, ta karba cike da ladabi tana jujjuyawa.
Abbas ya dubi Hashim ya ce "ku je ka dinga karanta mata, ko a sami wanda yayi boko ya karanta mata sosai ta haddace."
"Au ba ta ma iya karatun Hausa ba?" Bilal ya zabura ya tambaya.
Bash Auta ya qifta masa ido alamar ya yi shiru.
Nihal ta zabura ta miqe ta dubi Abbas ta ce "na gode Darakta za mu tafi dan kada mu rasa motar qauyenmu, sai na ji ka a waya."
Abbas ya dube ta yayi murmushi ya ce "toh zan tuntube ku a waya zuwa gobe, ki dage a karanta abin nan sosai a gane. Ga kudin mota."
Ya saka hannu a aljihu ya zaro naira dubu uku, Hashim ya cafke da sauri dan ya san Nihal cewa za ta yi a bari, ai kuwa har ta kai bakin qofar fita.
Sun fito baranda kenan sai ga Bash ya biyo su a baya, ya zaro kudi naira dubu biyar ya miqawa Hashim ya ce " Hashim ga wannan a qara ayi kudin mota. Ko da yake na ga har saurayi ta yi a birni watakila ma shi xai kai ku gida."
Nihal ta dube shi kawai sai ta kawar da kai gefe bata ce masa komai ba, gaggawa take ta bar wajen duk da bata hango Muqaddas ba amma ta hango motarsa a wajen. Watqila masallaci ya tafi dan an kira sallar magruba.
Nihal har ta kai bakin titi a lokacin da Hashim ya biyo ta da gudu.
"mu tambayi masallacin mata ka kai ni in yi sallah." In ji Nihal.
Su na tambaya aka nuna musu, bayan sun idar sai suka hau adaidaita sahu su ka nufi tasha.
A hanya ne Hashim ya kiyasta maqudan kudaden da Allah Ya basu a yau. Kudin wajen Muqaddas naira dubu ashirin, kudin wajen Abbas naira dubu uku, ga kudin Bash dubu biyar. Naira dubu ashirin da tawas cib. Wani qaramin kwali ne a cikin ledar da Muqaddas ya ce a bawa Nihal amma kwalin an liqe shi ba zai budu ba sai an saka reza.
Hararar da Nihal ta wurga masa ita ce ta sa ya fasa kokawar budewa ya Mayar cikin leda ya kunshe.
Sun nufi garin Wudil gadan-gadan ba su tsaya a ko ina ba sai a qofar gidan Nihal saboda kafin a kai tasha gidanta yake a bakin titi dan haka su suka fara sauka.
Hashim ya raka Nihal qofar gida ya kalle ta yayi murmushi ya ce " Allah sarki yau sai ke kadai Najaatu bata nan. Sabo turken wawa sai na ji babu dadi amma za ki fi ni shiga damuwa."
Nihal ta gyada kai ta ce "kamar ka shiga cikin zuciyata wallahi, ban san ta in da zan fara ba na saba zama da ita, ga ta da aiki."
Hashim ya harare ta ya ce " ba ke kika yanke danyen hukunci ba. Meye abin Mayar da ita gidansu? Aka bibiya ma ta girme ki kike ganin yarinya ce ta yi kuskure."
Ta harare shi ta ce "ba ka da hankali ma kai wallahi, ana yi maka maganar daraja da hakkin iyaye da ya rataya akanmu. Duniya fa ta shigo, su na can su na nemanta dole in mayar da ita."
Hashim ya zabura ya ce "kin san Bilal Sani ai ko ? Wallahi in kika samu kika yi fim kwaya daya da shi kin gama hayewa, dan sarauta ne fa gashi ya fi kowa ilimi matakin masters gare shi da. Ga turanci duk wata talla shi yake yi idan ta turanci ce ya na da kudi sosai. Kwanaki ma yayi aure kin ga shagalin da aka yi kuwa. Ya auri 'yar gidan wani gwamna me ci. Amma fa Nihal sai min dage da addua saboda na ga fa kamar so yake ya ce a cire ki ba zai yi fim da ke ba. Saboda ya ganki a kauye babu wayewa. Kin san dan wulaqanci ne fa sosai yana ji da kansa, a junansu ma maganar da ake ta yi kenan.
Nihal ta yi shiru ta na tunani, tabbas duk abinda Hashim ya fada gaskiya ne abinda Bilal yake shirin fadawa Abbas kenan, yana nufin bata dace da yin babban fim ba kuma tare da shi.
Nihal ta fada a ranta "Bilal Sani ya karkace ya na ta yabo da irin taimako da shawarwarin da princess last born take bashi don ganin ya ginu kuma ya samu ci gaba. Sai gashi yanzu wani yana qoqarin ya yunkura ya tashi amma yana daqile shi baya so. Ba ma fim dinsa ba ne, na wani ne amma yake hassada ba zai bari ba wani ya ci gaba ba."
Tabbas gagarumin yaqi ne a gaba domin ba zan bar Bilal Sani ya samu galaba a kaina ba. Zan nuna masa kurensa, zan nuna masa cewar taimakon wani abu ne da idan ka yi shi a gaba za ka tsinta. Zan nuna masa talaka da bakauye ba abin gudu ba ne. Zan nuna masa dan adam ba abin wulaqantawa ba. Kada ka wulaqanta mutum baka san ko shi wanene ba. Har yana maganar so, ashe kuwa ba don Allah Ya ke sonta ba sai don wata manufarsa.
Hashim ne ya katse tunaninta ya ce " ga ledarki in kin bude za ki gani ko menene a ciki. Yaya zaa yi da kudin nan?"
Ta harare shi ta ce "ka je ka riqe na bar maka dukka."
Ta bude gidan ta shige ta datse. Ya san daman zaa runa, hakan ne zai faru.
Ya yi dariya ya wuce ya tafi gida su. Ya iske kakannunsa a tsakar gida anan ya zauna ya narki tuwon masara miyar kuka.
Inna ta tambayi Nihal ya kai sau goma daga nan Hashim ya tabbatar ba ta da kudi ne. Naira dubu goma ya qirgo ya miqa mata ya ce "ga sakon da ta ce in baki, aiki ne yayi mata yawa shiyasa ba ta shigo ta ganku ba, ta ce in gaishe ku."
Sai murna ta rufe su, Nihal na shan yayyafin albarka.
Hashim ya yi sallar isha'i da kyar saboda gajiya, ya na layi ya shiga ya kwanta akan ragargajejjiyar katifarsa a cikin daki ginin qasa yana ta juyi, da nan ya saba bashi da in da ya fiye masa wannan katifa dadi. A tsakar gida ya manta ledar Nihal. Asuba ta gari Hashim Wudil.
Nihal ta raba dare tana rubutu a laptop dinta domin abubuwa manya-manya har guda uku ne su ka faru a wannan rana ga kai Najaatu gidan iyayenta, haduwa da Muqaddas sai haduwa da Bilal Sani.
Sai ta tsinci kanta ta na murmushi domin Bilal ya nuna yadda halin dan adam ya ke, a zahiri bai san ita ba ce yana ta yabonta ya na fatan su sake haduwa a rashin sani, ga ta a zahira amma ya na gyamarta saboda bata da kudi.
Sai da ta gama rubutu sannan ta yi wanka ta kwanta sai a lokacin ne ma ta tuna yau gaba daya bata ci abinci ba ga mai girkawa ta yi nisa. Daqyar ta tashi ta hada shayi da biredi ta yayyaga ba dan tana so ba sai don dole. Da ta kwanta sai idanuwan su ke ta haske mata fuskar matsayinta Muqaddas.


Asuba ta gari Nihal Nuren Mubin.
Kamar yadda Nihal ta raba dare ba ta kwanta ba saboda rubutun abubuwan da suka faru haka Darakta Abbas ya raba dare yana juyi ya kasa bacci ya na tunanin abinda Bilal Sani ya fada masa akan Nihal. Ya bashi shawara akan kada ya yi kasadar saka ta a matsayin Jarumar Fim dan bata dace ba, sannan ya yi rantsuwa shi dai ba zai iya fitowa a matsayin saurayin ko mijin wannan kucakar baqauyiyar nan ba domin ajinsa zai zube. Dan haka sai dai Darakta ya zaba ko Nihal ko Bilal.
Abbas ma kunyar Nihal yake ji,ta ina zai fara kiranta ya fada mata an fasa yin Fim da ita bayan an saka mata rai. Bai san me yasa ba ya ji kawai ya na so ya taimake ta ya na da kyakkyawan zaton idan an bata dama zata iya. Tabbas ya shiga tsaka mai wuya .
A cikin wannan dare daidai wannan lokaci kuwa Bash Auta ne ke ta juyi ya kasa bacci bai san me ya sa abin nan ya tsaya masa a rai ba, yadda ya ga Muqaddas da Nihal a tsaye su na magana. Me yasa yake jin haushi? Me yasa ya ji ya damu da Nihal? Shi kansa ya rasa amsar wannan tambaya.
Haka a bangaren Muqaddas bacci ya gagara ganin Nihal a cikin wannan yanayi ya dame shi. Ko a mafarki daidai da rana daya bai taba zaton zasu kai war haka basu yi aure ba, bai taba kqwowa a ransa zai rabu da ita ba. Gashi abu kamar wasa iyayensa har sun fara maganar ya auri wata a cikin dangi ana ta naniqa masa Samira. Amma babu babban mai laifi sai General Nuren shi ya hargitsa komai. Idan ya duba wani bangaren kuma laifin Nihal yake gani, duk ita ta jawo musu ba dan ta canja course ba da duk haka bata taso ba. Yana jin kamar in ba ita ya aura ba tabbas zai shiga duniya a rasa shi. Ya daga kai ya dubi hotunanta da suka cika bangon dakinsa. Sai hawaye me radadi ya sirnano masa.
Asuba ta gari Engr. Muqaddas.




*** **** ****
Washegari Hashim ya iso gidan Nihal bayan sallar azabar ya buga get ta bude su na hada ido sai ya zabura ya dafe kirji ya ce " na manta ledar nan a tsakar gida bari in je in dauko. Kiransa ta ke amma ina ya fallada gudu, ya tsayar dan acaba ya hau. Ta yi dariya ta koma cikin gida, ya dade sannan ya dawo dauke da ledar cike da murna.
A qofar gida suka zauna ya bata labarin irin walagigin da aka sha yi da ledar nan, ya manta ta a tsakar gida, Inna kuma ta share ta zuba a shara aka dauki sharar aka kai juju. A takaici dai a Juji ya tsinto ta kusa da wani gandareren kashi.
Nihal ta harare shi ta ce ka tsaya daga nesa ka bude kada ka kawo min kayan kazanta kusa da ni. Ya na gefe yana ta faman farkewa domin bayan kwalin da yake ciki an sami leda mai gyalli an nannade, ya warware ya bude kwalin ya duba.
Hashim ya kwalla ihu zabura da gudu wajen Nihal ya nina mata kudin America daloli ne 'yan dari-dari guda ashirin qasan kudin kuma sar1ar zine ce da dankunne da zobe.
Ya miqawa Nihal ya ce "taya ni gani wanne irin kudi ne wannan? Kuma sarkar kamar ta qwal."
Nihal ta yi shiru tana mamaki amma bata yi mamakin da yawa ba saboda wannan kadan ce daga cikin irin kyaututtukan da ya saba yi mata, sai dai ta fi yin murna a yanzu saboda tana da matukar buqata. Ba ta nunawa Hashim kudi ne masu daraja ba dan kada ya yada haka ta ce masa sarar ba ta gwal din gaske ba ce jabun gwal ne, sai ta sami sauqin suruntunsa.
Ta ci gaba da yin kasafin yadda zata yi da kudina nan a ranta . Dallar dubu biyu ta kai naira dubu dari tawas a lokacin sannan sarqar kuwa akwai resitinta da dirham ya saye ta da alama ya yi tafiya zuwa dubai kudinta dubu dari shida da hamsin. Ta yanke hukuncin gara ta siyar ta harhada ta saye gidan da take ciki kawai ko ba komai za ta mallakawa Hashim da kakaninsa su huta da zaman gidan qasa yana rugujewa kullum.
Ta dauka ta je ta adana a can qasan jakarta tana jira sai ta ta je kano sannan ta canzar su dawo Naira.
Tabbas Muqaddas masoyi ne a kowanne hali take yana tsaye a kanta. Hawayen tausayin su ya sirnano mata ba tare da Hashim ya gane kuka take ba ta yi sauri ta goge. Shi kuwa ya na can yana ta zuba ba tare da bana fahimtar labarin da yake yi ba.
Qarya ya shirga mata cewar a tsaye ya kwana ya na salla yana addua kada Allah Ya sa Bilal Sani ya rusa musu budget dan ya ga alama yana kawo musu barazana. Hashim bai rufe bakinsa ba sai wayarsa ta yi qara yana dubawa yaga sunan Darakta Abbas ne sai su dukka gabansu ya fadi. Hashim ya amsa, a sanyaye ya ji muryar Darakta yana magana. Nan da nan Hashim ya yi saranda ya ji a jikinsa labarin babu dadi.
Abbas ya ce idan ka na kusa da Nihal ka koma gefe mu yi magana ."
Hashim ya zabura ya tashi daga kusa da ita ya koma gefe ya ce " eh ni kadai ne yanzu. "
Darakta Abbas ya fara yiwa Hashim bayani saboda tashin hankali sai da Hashim ya sulale ya zauna. Darakta ya roqi Hashim da ya bi duk wata hanyar da zai bi ya fadawa Nihal ba tare da hankalinta ya tashi ba Bilal ya ce ba zai yi fim da ita ba sai dai a zaba ko ita ko shi, shi kuma yana ganin Bilal ne kadai ya dace da fim din.
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun". Hashim yake ambato kamar wanda aka bashi labarin mutuwar Inna. Bai san Nihal tana tsaye a bayansa ba, duk da bata ji dukka ba amma ta gane abinda yake faruwa. Sai ta kwace wayar, ta yi sallama ta gaida Abbas. Sai ya ji gabansa ya fadi.
"Malam Abbas kada ka damu in ban yi a wannan ba zan samu a gaba. Ai ka nuna min ka na da son ci gabana, kada ma ka ji nauyina."
Ya ji kamar zai nutse a qasa dan kunya sai ya sosa qeya ya ce amma in ba za ki damu ba akwai wasu wurare da za ki iya shiga a fim din."
Ta gyada kai ya ce " ba damuwa ko ina ne a saka ni zan yi. Na gode sosai."
Su ka kashe waya daman a gaban Bash Auta Abbas yake wayar bayan sun katse Abbas ya dafe kai sai gumi kawai yake yi.
Ya dago

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads