Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 110552 words

Chapter 6 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

talaka dan uwansa? Domin mu masu kudi a kullum ana yi mana wa'azi akan kada mu wulaqanta talaka, mu taimaka musu da dukiyarmu. " Ta tambayi zuciyarta.


Ta fita qofar gida tana wuwwurga ido tana neman mai yin sallama da ita . Hashim ta hango tabbas ta gane fuskarsa don ta ganshi jiya a cikin 'yan rawa a wajen daukar fim. Murmushin da ya ga tayi sai ya saka shi murmushi, suka gaisa sannan ya sake yi mata bayani .


"Babu damuwa, mu tafi." Nihal ta fada .


Tafiya suke yi Hashim yana bata labarin irin shaharar da yayi da yawan finafinan da ya firfito. Tambayar ta yake ko ta taba ganin Fim mai suna kaza? To ai shine abokin actor. Ba ta isa ta ce masa bata taba kallon Fim din Hausa ba.


Dole ta amsa masa da "eh na gani ai na shaida ka, ka iya acting gaskiya ka burge kowa."


Sai ya ji kansa ya fashe tabbas ya shahara, ya ci gaba da bata dubarun yadda zata bi ta karbu a masana'antar Finafinai . Wadannan hanyoyi kuwa su ne: ta yiwa manyan stars biyayya kuma dole ta dinga yawan shishshigewa daraktoci da furodusoshi. Ta yi masa alkawari zata yi hakan sannan ta yi masa godiya sosai.


Tafiyar babu nisa sosai, suka isa wani gida na suminti ne mai dauke da dakuna tara . Tabbas gidan haya ne kowanne daki mata ne daga adadin biyar zuwa shaida . Amma wasu dakunan na matan aure ne .


Abin mamaki kai tsaye ta ga Hashim ya fada cikin gidan, su ka isa bakin qofar wani daki, ya kwalla kiran sunan Mami Harka.


Mami Harka ce ta bayyana a bakin qofa, fuskar nan ta dafe ta yi jajawur saboda bilicin, an sha jan janbaki da hoda ga shudin eye shadow kai kace da tabarya ta yi kwalliyar, ga hudar hanci an makala katuwar barima ana taunar cingum kamar wata saniya, duk a cikin shikashikan wayewa ne. Dariya ce ta kusa subucewa Nihal sai ta daure.


" Irin wannan kira haka kamar na kashe 'yar sarki .Hashim meye ? " Mami Harka ta fada cikin yamutsa.


Hashim yayi dariya ya ce " ranki ya dade super star ayi min afuwa. Ga baquwar da darakta ya ce a kawo, za ku zauna tare. "


Ta harari Nihal sama da kasa ta yamutse fuska.


Nihal ta zabura ta duka ta gaishe ta. Sai Mami ta ji kanta ya fashe, haka sai ta sauke haushin ta da ta fara ji .


Ta ce " shige ciki za ki ga tabarma baqa nan ne kwanarki. "


Hashim ya ce " ba zaa bata aron 'yar katifa ba ma sai tabarma?"


Ta harare shi ta ce " ka ji dan rainin hankali. Waye ya bamu tabarmar ma a lokacin da mu ka zo? Idan ta yi fim sai ta tara kudin katifarta kowa da kudinsa ya siya ."


Nihal ta shiga dakin ta iske dakin tas-tas a share kuma qato ne sosai, katifu guda hudu ne a jejjere, kusa da kowacce katifa akwatuna ne masu taya. An malala sabuwar leda ga sabbabin bokitai da butoci sai qamshin turaren wuta ne yake ta tashi.


Sai Nihal ta ji dan sanyi a ranta. Ta ajiye kayanta a gefe amma bata zauna ba ta sake fitowa ta same su a bakin qofa a tsaye har yanzu su na magana .


Nihal ta dubi Mami cikin ladabi ta ce " Mami harka dan Allah ina son ki bani aron bokiti zan yi wanki ."


Mami ta harare ta, ta ce " ai baki kira ni da kalar sunan da zan iya ara miki bokiti ba ."


Hashim ya ce "Aunty Mami zaki ce , tuba take ranki ya dade."


Nihal ta dukar da kai ta ce "Anty Mami ayi hakuri."


Mami ta baje katuwar murya mai kama da muryar maza ta ce " ban ma fada miki dokokin zaman dakin nan ba. Ba na son kazanta dan na ga alamar ki tsabtar ki ragaggiya ce, kalli kayan jikinki duk dauda.Ki na mace wai kuma da sunan kin zo ki shiga harkar fadakarwa, ai a jikinki ya kamata a fara ganin misali. Ba na son raini, babu aron kaya ki nemi komai naki, banda kawo mana gayyar qawaye cikin daki. Banda shaye-shaye da kawo samarin banza cikin daki. Banda sibarannabaiye. "


Da alama Nihal bata San wannan kalmar da ta fada ta karshe ba.
Dan haka sai ta nanata ta "Sibaren- na -bayye."


Hashim fahimci bata gane ba don haka sai ya fassara mata hausar. Ua ce " bi ma'ana bata son sata."


Sai Nihal ta sunkuyar da kai qasa hawaye ya cika mata ido, tana jin zafin wannan kalma ta sata da ake danganta ta da ita.


" Shiga ki dauko baqin bokintin, in an gama a wanke a dawo min da shi." Mami ce ta fadawa Nihal .


Nihal ta yi godiya ta dauko buhun kayanta da bokiti ta fito.


Mami ta na yamutsa kamar ta ga kashi ta nuna mata bakin famfo da igiyar shanya .


Hashim ya lura Nihal bata da omo ko sabulu kuma sai ya tuna cewa har sai da darakta ya cikawa Babanta kudin acaba dan haka bata da komai. Da sauri ya fita waje babu jimawa sai gashi ya shigo dauke da sabulu kato, da omo da sabulun wanka gift ya miqa mata. Ta jika kayan a bokiti kafin ma a cuda ruwan yayi bakikirin kamar ruwan kwata. Ta ji dadi sosai da kyautar da ya yi mata .


Mami Harka ce ta fito rataye da gyale da jaka, ga wani takalmi mai tsini tana tafe tana yanga ana dage hannu.


"Zan fita, ke baquwa ga dakina nan a hannunki kada in rasa komai nawa. Idan za ki fita ga kwado nan akan windo ki datse min. " Mami ce take bada umarni.


Nihal ta amsa cikin ladabi .


Hashim ya ce " za a fara daukar shiri Fim din Tataburza ko? Nima ina cikin Fim din, Darakta ne ya aike ni Kano amma yanzu zan dawo in Allah Ya yarda, zan same ku acan. An ce a hanyar Gaya zaa yi shooting din ko ? "


Mami ta ce " sai ka zo." Ta fice tana karairaya.


Ya fuskanci Nihal ta rasa yadda zata cuda kayan, sai cakudawa take kamar ta sami kwado yauwa ko na zogale. Hashim ya cika da mamaki .


Ya yi dariya ya ce " ke yanzu kina nufin a haka kayan nan masu uban datti zasu fita . Ah shiyasa mana kayan suka yi datti da yawa, ashe jika-jika kike yi. Kawo ki gani ."


Ya karba ya dinga sabawa da qarfi sai baqar kumfa ce take kwaranya. Ya daga ido da sauri ya kalle ta sannan ya sake kallon kumfar. Ko bai yi magana ba Nihal ta san abinda yake nufi, kunya ta rufe ta, hawayen takaici ya cika mata ido .


Sallama su ka jiyo a zaure, muryar wani mutum ne ya ke magana ya ce " ana neman baquwa me suna Nihal Nuren Mubin."


Sai ta ji gabanta ya fadi ta leqa da sauri ta kalli mutumin, bata taba ganisa ba tunda take a duniya. Ya tambaya ko ita ce Nihal? Ta masa da eh ita ce . Sai ya fara yi mata bayani, nan da nan ta gano bakin zaren. Dan haka sai ta nemi da su fita qofar gida su qarasa maganar a can, don bata son Hashim ya jiyo abinda suke fada.


Mutumin tsaf da shi a waye yake yana ta qamshin turare, ya gabatar mata da kansa, ya ce sunansa Shazali shi dan asalin nan garin ne amma ya fi zama a Kano . Babanta Alhaji Nuren ne bar kudi ya ce a dinga siyo mata abinci safe da rana da dare daga Kano. Abinci masu kyau da lemo da ruwan roba ana kawo mata. Sannan kuma ya ce duk wani abu da take so akwai qaton shagon da zata dinga zuwa tana karba. Sai ya hau yi mata kwatancen shagon don ya zaci 'yar gari ce.


Sai ta yi murmushin takaici duk da ta ji dadi sosai a ranta. Ta yi imanin duk in da mahaifinta ya ke yanzu ya fi ta shiga damuwa da tunanin halinda take ciki. Ta san ba zai bari Mummy da sauran yayyanta su san in da ya kawo ta ba . Zasu zaci wani katafaren gida da kudi zai bata wanda zata fara shirya fim dinta.


Ya miqa mata wasu manyan ledoji guda biyu, daya tana dauke da robobin take away guda uku manya . Sannan ya miqa mata wata katuwar leda mai dauke da flask din ruwan zafi da kayan shayi.


Ta gyada kai ta yi godiya . Sai ya nemi data bashi lambar wayarta in zai aiko da sako ya sanar mata ko in ta na bukatar wani abu ta kira shi. Ta ce bata da waya, dan haka sai ya rubuta lambar wayarsa ya bata. Ta karba kamar ranta ba ya so .


Shazali dai ya tafi zuciyarsa cike da mamaki ya kasa gane abinda ya ke faruwa anan. Shi dai ya san an bashi kwangila ta maqudan kudi kuma zai cika aikinsa.


Ta shiga cikin gida amma sai ta boye kayan a cikin mayafinta .


Hashim ya kalleta ya ce " ashe kin san mutane a garin nan?"


Sai ta zabura ya girgiza kai ta ce " a a ban san kowa ba, abinci ne aka kawo min 'yan uwanmu ne zasu je Gaya sai suka tsaya suka bani. "


Ya ce " Allah sarki! shiga daki ki ci, zan karasa miki wankin in shanya ."


Ta yi ta godiya har ta shige daki tana gode masa gami da addu'oi na albarka .


Ta ji dadin hakan sabo da masifar yaunwa take ji .
Ta na shiga ta haye kan tabarmarta ta bude kayan nan, sai ta ji kamar sakon daga aljanna aka kawo mata don farin ciki.

Kaza ce guda a gashe ta sha kayan hadi, daya robar dankalin turawa da soyayyan kwai , daya robar kuwa fried rice ce da nama, ga lemo kala-kala da ruwa masu sanyi .


Ta gyara zama ta dira a kan kazar nan, tana hadawa da dankali da wainar kwai tana cikawa gami da korawa da lemo.


Tabbas ta na jin baqar yunwar kwana da kwanaki babu abinci, rabon ta da cin abincin kirki ta manta daga biskit sai dan lemo, ta dade bata iya ci tun a London. Saboda fargaba da furgici da tunanin hukuncin da zaa yanke mata, amma yanzu ta san makomarta an yanke mata hukuncin hankali ya kwanta .
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI


EP 7


Ta ci rabin kaza da dankali da kwai gaba daya ta ji ta koshi har kamar ma koshin zai zame mata illa. Ta na zaune tana tunanin yadda za ta yi domin tana so ta taimaki Hashim ta bashi sauran ya ci , amma bata so ya gane tana da wani abu ta fi so su dauke ta yadda su ke daukar ta din . Ga shi har omo da sabulu ya siyo mata don ya na zaton ba ta da ko kwabo. Idan ya ga kaji da kwai ai zai yi tunanin tana da wani abu ashe. Amma yadda ya taimaka mata ta so ta taimake shi don ta tabbatar ya dade bai ci kaza da lafiyayyen abinci irin wannan ba.


Hashim ne ya katse mata tunanin da ta tsinduma a ciki .


Ya ce " Nohel na shanya miki, zan tafi ."


Ta yi dibi-dibi ta zaro dubu daya daga cikin dubu biyar din da mahaifinta ya bata zata bashi sai ta tuna da cewa ita fa talaka ce liqis, ina ita ina kyautar dubu daya . Dan haka sai ta mayar ta miqe da sauri ta fito tsakar gida .


Ta yi dariya ta ce " har yanzu baka iya kiran sunana ba ? Nihal ne ba Nohel ba ."


Ya kwashe da dariya ya ce " sunan ne kamar sunan Yamalawa wato larabawan Yemen, gashi ke kuma ba daga Malam madori kike ba balle in ce larabawa ne . Amma dai kin yi kama da baqaqen buzaye. "


Ta girgiza kai ta ce " ko daya, ni bahaushiya ce ."


Ta yi masa godiya sosai ta raka shi har zaure . Har ta juya zata tafi sai ya zabura ya tsayar da ita.


Ya ce " kin ga da kin shirya da na biya miki kudin mota mun tafi Kano, daman wajen wani babban darakta aka aike ni, da sai in gabatar da ke in an sami Fim a saka ki ."


Nihal ta ce " nan gaba sai in bika . Yanzu dai idan ka dawo ka zo ka raka ni wajen tela ta dinke min kayan da su ka yage kuma a rage min girman wuyan, wasu zannuwan kuma a mayar da su siket. "


Ya kalle ta cike da tausayi sannan ya ce " na ga kayan ma duk sun tsufa kamata yayi a sami wasu atamfofi ko biyu ne a dinka kawai, kada a bata lokaci akan kayan da suka tsufa . Amma bari a biya ni kudin aikin fim dina ko atamfa leda - leda 'yar dubu bibbiyu sai in siya miki, na yi miki wannan alkawarin ."


Hawaye ne ya cika mata ido sai ya lura da hakan don haka sai ya gaggauta barin wajen dan kada ta sa shi kuka shima .


Ta sulale ta zauna a kan dakilin qofar gida tana ta rusa kuka . Ashe haka rayuwar talaka take kasancewa abin tausayi? Wani ya tausaya masa wani ya wulakanta shi . Allah sarki Hashim kai ne mutum na farko da ka damu da ni ka taimake ni a yadda nake talaka .


Almajirai take kallo kaya a yayyage suna ta neman yadda zasu yi su rayu. Ta tashi da sauri ta shiga gida ta raba shinkafar nan gida biyu ta kazar ta zo ta basu . Zo ka ga wawaso da danbe. Suka dinga jero mata mata addu'oi. Tabbas ta ji dadin wannan addua "Hajiya Allah Ya karba. Allah Ya sa ki ga annabi. Allah Ya biya miki bukatunki na alkhairi. "


Sai sake zabura ta zaro naira dubu daya ta basu ta ce su je su ci wani abinci . Sai addua ta lunku akan ta da .


Kunci da zafin zuci da su ke ta addabarta sun gushe . Tabbas sadaka maganin masifa ce, ta kudiri aniyyar kullum zata dinga yin sadaka tunda ga almajirai nan sun wadata a ko ina. Lallai ya kamata ka kasance mai yawan sadaka a rayuwa idan kana da shi . A London ko a unguwanninsu na masu kudi ga abin da zaka bayar sadakar amma babu mabuqatan.


Ta jima a zaune ta na kallon masu wucewa da yake gidan yana daf da babban titi. Sai ta ga kamar kowa a gigice yake, wasu suna tafiya su na surutai wasu kuwa tuntube suke a sanadiyyar rashin nutsuwa. Da yawa shigarsu ta tsumma ce 'yarkace- yarkace da su. Kujajjun takalma ne sanye a qafafuwansu, kaushi da faso kuwa sun wadata ba za ka taba cewa qafar bil'adama ce ba, babu mata babu maza , babu babba babu yaro .


" Allah sarki 'yan qasata, qabilata, In har za ku kalli Finafinaina da nake niyyar yi nan gaba tabbas zan kawo muku gyara da mafita a rayuwa. Allah Ya taimake ni Ya cika min burina. Amin ." Nihal ta fada yayin da ta tashi ta shiga gida.


A daki ta zauna ta na jiran kayan su bushe sannan tayi wanka ta canja. Sai ta ji zaman kadaicin ya ishe ta akwai wahala babu wuta balle ta ji fanka, babu talabijin, babu waya da zata yi chatting tayi browsing.


Ta shiga wanka ta dade tana dirzar jikinta saboda da dattin da tayi da yawa.Ta saka wankakkiyar atamfa sai ta ji wasai babu wari sai dai qamshin omo.


Da yamma Hashim ya dawo daga kano ya kawo mata tsarabar biredi, dariya ce ta subuce mata ya zaci murna ce nan kuwa mamaki ta yi yadda ake tsaraba da biredi . Ya takura mata akan zaman daki ba zai yiwu ba ta zo su je wajen daukar shirin da ake yi, idan su na ganinta a wajen shine zasu tausaya mata su saka ta a cikin shirin, kuma shine abinda ya kawo ta garin kenan .


Su ka isa wajen da ake daukar shirin ta na gaishe su bata ishe su kallo ba ma, haka ta lura Darakta Tukur bai sakar mata fuska ba . Ta na gefe tana kallokawai. Da magruba ta kawo kai sai aka tashi kowa ya watse. Mami Harka ce ta kalle ta a shelaqe ta ce ta dauko mata jakar kayanta ta biyo ta da ita zuwa gida . Haka ta dauka ta na biye da ita har suvka iso gida . Sai suka iske 'yan dakin sun daddawo, Asabe da Iyantu.


Bayan Nihal ta gaishe su sai Mami ta gabatar da ita . Suvka kwashe da dariya suka tafa .


" Au ita ma Fim din ta zo shiga?" A hakan ? Iyantu ta fada cikin gatsali.


"Kuma an saka ta ?" Asaba ce ta tambaya.


Mami ta ce " ina fa ? Ai za ta dade ta na jira . Shiga Fim wasa ne? Ki taho yarkace- yarkace da tsumma ki ce kin zo shiga Fim. Babu wayewa, babu kayan gayu. Babu 'yar farar farar nan ta bilicin, lallai za ki dade."


Asabe ta ce " amma yarinyar tana da fata mai kyan gaske mai sheqin duhun haske ." Ta zo ta shafa kumatun Nihal .


Nihal ta qufula, hakuri kawai take bawa zuciyarta . Ba ta iya jure wulaqanci. Kallonta suke yi sama da qasa kallo na qasqanci .


Iyantu ta cewa Mami "kin fada mata dokar zaman dakin nan kuwa?"


"Na karanto mata komai da komai, amma na ga alama ta na da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads