Header Ads
Showing 66001 words to 69000 words out of 110552 words

Chapter 23 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Nihal ta yamutse fuska ta ce "nina baccin na yi ban dade da tashi ba bana jin dadi ma zuciyata ke tashi kamar ulcer tana son ta kama ni."
"Hashim ina Nihal?" Bash Auta ne ya dira a gabansu kamar an jeho shi daga sama. Babu alamar nutsuwa a tattare da shi. Da yake in da suke tsaye babu haske sosai bai gane Nihal ba. Sai su dukka su ka ji gabansu ya fadi.
Cike da fargaba Hashim ya ce "ga ta nan ai. Lafiya kuwa?"
Bash ya qurawa Nihal ido ya dube ta sama da qasa ita ce dai sanye da kodaddiyar atamfarta leda-leda ta wajen Hashim da ya dinka mata, yarkace-yarkace da ita. Kallon da ya ke yi ma ta yayi kama da na zautaccce.
" Malam Bash lafiya kuwa?" Nihal ta tambaya cike da mamaki.
Sai ya ji har muryar sak kamar waccan baiwar Allah.
Ya zabura ya girgiza kai ya ce "Ah babu komai. Fita za ku yi ne? Yau gaba daya ba ki fita ba ki na daki ko kin je wani waje?"
Ta girgiza kai ta ce "ban fita ba, ina kwance a daki bani da lafiya ma yanzu ma chemist Hashim zai raka ni in siyo magani?"
Yayi Jugum sannan ya ce " ki na da 'yan uwa a Nijer ko a faransa? Ko ke 'yan biyu ce?"
Ta sake cika da mamaki game da wannan tambayar ta ce " ban taba shigowa Nijer ba kuma bani da 'yan uwa a qasar nan. Wani abu ne ya faru?"
Hashim ya zabura ya ce "wani sharrin aka sake yi mata? Oga Bash kai ne ka ke kaunar ci gaba Nihal wallahi duk sun tsane ta. Ba ruwanta da kowa ko me aka fada maka qarya ne Nihal a kwance ta wuni ba in da ta je ina tare da ita."
Wannan kalamai na Hashim ya sake rikirkita Bash ya sake zunduma cikin wani yanayi.
Bash hannu ya ke ta wurgawa ya na magana shi kadai ya juya ya tafi ba tare da ya yi musu sallama ba.
Hashim ya dubi Nihal ya ce " wani qazafin aka sake yi miki dan kawai baa so ki yi fim. Na ce miki ai ki zo mu je gidan Malam ya baki maganin farin jini kin ki amma anan Nijer ma an ce garin malamai ne, ki zo a raka mu ki sha rubutun daukaka da farin jini."
Nihal ta kwashe da dariya ta ce " ashe baqin jini gare ni kai ne me farin jini ko? Wato ka sami daukaka kenan?"
Ya gyada kai ya ce "gashi nan kuwa tun ina zuwa kano har na fara shigo wata qasar yin fim."
Nihal ta ce " na dauka ni ka rako ni da bana shan rubutun, ba a dalilina ake dan soka ka a fim din ba? Nan din ma da ka zo kana da tabbacin zaa saka ka ne?"
Sai wani tunani mai karfi ya sauko ma sa ya dawo hayyacinsa maganar Nihal gaskiya ce.
Ta ci gaba da cewa "ina son duk abinda za ka yi ka riqe Allah Shi kadai ka yarda Shine kadai mai bayarwa kuma mai hanawa. Duk duniya babu mai baka idan Ya hana ka. Haka babu mai kwacewa idan Ya baka. Ban hana ka ka yi addua ba ko ka sa a taya ka ba amma kada ka zaci Malam ne ya baka. Babu wajen Malamin da zan je. Ya kamata ka koma islamiyya Hashim, mu na komawa gida zan sa Inna ta kai ka makarantar Islamiyya."
Su ka kwashe da dariya su dukka. Su ka fara tafiya su ka nufi kofar get din fita.
Hashim ya ce " na yi makarantar allo Allah sosai ma,da zan bude miki bayana da kin ga shatin duka,har na kusa yin sauka na gudu saboda tafkar da ake yi mana. Ki tambayi Inna."
Ta ce "ai karatun allo daban na islamiyya daban. A islamiyya ne za ka ko yi Tauhid , fiqihu, Hadisai da tarihin yadda Annabi Muhammad S.A.W yi rayuwa."
"Nihal kin yi bakuwa." In Fati dangerous ce da wata mata su ka diro a gabansu ba tare da sun san ta inda su ka bullo ba.
"Baquwa kuma?" Hashim da Nihal su ka hada baki su ka tambaya cike da mamaki.
Kafin Nihal ta rufe bakinta sai ta ga bakuwar ta runguma ta. Daga nan ta sanqare a tsaye tana mamaki.
Hashim ya zabura ya ce " Lah Najaatu ce ai."
Najaatu ta yaye gyalen da ta yi lullubi, fuskarta ta bayyana.
Mamaki marar musaltuwa za ka gani a bayyane akan fuskokin Nihal da Hashim.
Nihal ta ce " Najaatu daga ina? Garin yaya ? Ta ina ? Yaya aka yi kika san muna nan?"
Fati dangerous ta ce "team din Darakta Tukur ta biyo su Mami harka."
Nihal ta ji gabanta ya fadi da aka ambaci su Mami.
Fati dangerous ta fella da gudu ta bi qeyar Danjuma ta daka. Su ka hau kokawa ta na so ta kwace lemon gwangwani a hannunsa. Nihal ta shiga tunanin yadda wasu 'yan fim su ke irin wannan hali, tabbas su ne wake daya bata gari da suke jawowa dukka 'yan fim zagi.
Maganar Najaatu ce ta katsewa Nihal tunanin da ta tsunduma ta na yi.
Najaatu ta ce " tare da Tukur da Amina 'yar kwalisa da Mami Harka mu ka taho sai wasu maza guda biyu a motar, dayan ne ya tuqo.Na je gidanki a rufe, na je gidan su Hashim Inna ta ce ke da shi kun yi mata sallama kun tafi Maradi, ba ni da yadda zan yi ga kaya sai na tafi dakin su Mami Harka na tarar za su fito su ka ce min Maradi za su je na ajiye kayanna na zabi kala uku na biyo su. Da suka ce ba zasu zo da ni ba sai na roqi Tukur, dakyar ya bar ni amma naira dubu takwas ya karba a wajena."
Hashim ya ce "ai Tukur mayen kudi ne in dai za ki bashi kudi ko abu haramun ne zai aikata."
Tukur ne ya dira a gaban Hashim aka hau kallon-kallo babu tantama ya ji abinda ya fada ko kokonto babu yadda suka ga shaida akan fuskar Tukur babu annuri.
Hashim ya zabura ya zazzare ido ba shi da mafita, babu wata kwaskwarima da zai yiwa maganarsa ta canja maana akan abinda ya fada. Dan haka titi ya dauka ya dankara da gudu, tun su na hango shi har su ka daina.
Tukur ya juyo ya harari Nihal itama ta harare shi. Gefensa Amina 'yar kwalisa da Mami harka ne su ma harar su ke yi mata.
" Munafukan banza toh Allah Ya toni asirinku kuma Hashim zai dawo ya same ni. Saboda kun kware da gulma da munafunci har aka dauke aiki baki fada min ba, sai kawai na ji ance kin jawo wancan dankorar na ki kun taho. Zan ga yadda Abbas zai saka ki a wannan fim din."
Amina da Mami su ka yi shewa su ka tafa hannu suka hada baki suka " Sai Darakta namu, ka yi min daidai."
Su ka juya suka tafi kamar daga sama Tukur ya ji Nihal ta ce " ka shirya kuwa dan za ka sha mamaki." Gaba dayansu su ka jiyo suka bude baki su na mamaki yadda Nijal ta waye har take mayarwa da Tukur magana."
Za ta sake yin magana Najaatu ta zabura ta rufe mata baki.
Tukur ya ce "haka kika ce ko? To za ki gani."
Amina ta ce " na fada maka daman ba ta da kunya."
Mami harka ta ce " ah ta fara wayewa har ta fara fita wata qasar yin fim dole ta yi ma ka butulci."
Su ka tafi su na ta zagin Nihal.
Najaatu ta fashe da kuka ta rungume Nihal ta ce "mutanen nan sun tsane ki tun daga kano gaba daya motar hirar ki ake, su na ta zaginki. Da na fara rama miki ashar Tukur ya cusa min ya ce idan na sake magana zai ajiye ni a cikin daji."
Nihal ta yi murmushi ta sa hannu ta gogewa Najaatu hawaye ta ce " kada ki damu, yawan makiyana gwargwadon daukakar da zan samu ne. Zo mu je dakinsu ki ajiye kayan ki mu je mu nemi wajen siyar da abinci mu ci.
Nihal da Najaatu suka shiga gida su ka nufi dakinsu Nihal kai tsaye, babu kowa kuwa. Najaatu ta ajiye akwatunta a kusa da ta Nihal ta shiga bandaki ta yi alwalla ta fito ta dinga jero sallolin da ake bin ta, da ta idar su ka fito.
Hashim ne a rabe ya na ta boye-boye sai da ya gansu sannan ya taho su ka hadu suka dunguma. Su ka yi ta dariya su dukka.
Nihal ta ce " ba ka da aiki sai gulma ai ga irinta nan, ya ce sai ya yi maka shegen duka idan ku ka hadu."
Najaatu ta fara bawa Nihal labarin abinda ya faru bayan da ta kaita gidansu. Tabbas an yi tashin hankali ba dan kadan ba daga baya kuma aka sauko aka daidaita. Da kansu iyayenta su ka ce sun amince ta zo ta shiga fim.
"Alhamdulullah. Amma wannan wanne abu ne ya kai ga canjawa iyayenki ra'ayi har su ka amince.
Naja'atu ta ce "kin san kin bani shawara kada in dinga yin rawa a fim ko? Finafinan duk da mu ka yi sun firfito, sai Babana ya gani kuma ana ta magana a gari, bayan sun gama zagin aka dawo ana yabona yadda na ke acting a nutse na ci saa aka saka ni a mutuniyar kirki a Malama ina ta wa'azi ina jan aya ina fassarawa, na burge sosai daga nan suka ka ce ashe ma wa'azi mu ke yi sannan gaba daya garinmu su ka dinga robubin zuwa ganina, 'yan gidanmu su ka sami daukaka sosai daga sun ce su 'yan gidanmu ne sai ka ga ana rububinsu. Babana rannan mota ya shiga direban ya qi karbar kudin mota ya ce saboda Najaatu an yafe aka ci gaba da yabona sai akwai ya dawo gida da murna ya ce yayi Amanna in yi."
Hashim da Nihal su ka cika da murna su na masu godiya ga Allah.
Sun zo giftawa ta wani katafaren shagon siyar da abinci, ta cikin galas Nihal ta hango Bilal da Halima da Aisa su na zaune su na cikin abinci.
Nihal ta zabura ta ce " ku zo mu shiga nan mu ci abinci."
Hashim ya kalli ciki ya kalli haduwar wajen sai ya ce "ba za mu iya siyan abinci anan ba zai yi tsada, ki na ganin wannan wajen kin san na manya ne. An ce akwai wata me tuwo anan gaba, ku zo mu je mu ci abincinmu a acan akan tebura a bakin hanya. Lah kin ga Bilal da su Aisa a ciki su na cin abinci. Na fada miki wajen nan na manya ne irin su Bilal."
Bai rufe bakinsa ba har Nihal ta fada cikin shagon su ka biyo ta a baya dan babu yadda su ka iya. Sai ga su a tsaye a tsakiyar haske yarkace-yarkace da su a cikin tsumma. Aka hau kallo-kallo tsakaninsu da Bilal dukka fara'ar da su ke yi ta gushe, bacin rai ya mamaye fuskokinsu. Su ka sha kunu su ka hau harara. Nihal ta tafi gaba gadi GADI ta jawo kujera ta zauna a teburin da ya ke kusa da su saitin Bilal, ta qura masa ido shima ya qura mata ido.
Halima ta ce "cabdijam yau akwai drama, za mu ga yadda zasu biya kudin abinci plate daya ma anan. Sun zaci fa irin abincin su ne na kauye na naira hasim."
Aisa ta kwashe da dariya ta ce "sun zaci wajen 'yan tuwo-tuwo da ake bajewa a kan tabarma a kofar gida ne. Ba su san har da kudin Ac da suka sha za su biya ba."
Farin ciki ya kama Bilal ya yi murmushi ya ajiye cokali ya nade haddu ya ce "ina murna ina jira in ga qarshen wannan fim din, in ga yadda zata kaya tsakanin boss da actor."
Sai karaf a kunnen Nihal ta yi kamar bata ji su ba.
Dariya su ka kwashe su dukka, su na ta kunshe baki.
Najaatu da Hashim sai labe-labe suke yi sun kasa zuwa su zauna, su na tsoron oganninsu da tsoron disgi dan sun san ba su da kudin biya.
"Dalla ku zo ku zauna mu zabi abinda zamu ci." Nihal ce ta fada cikin gadara.
Hashim ya duka ya gaishe da su Bilal, babu wanda ya amsa masa yana sanda ya ja kujera ya zauna haka ma Najaatu a takure take zaune. Gaba daya 'yan gayu ne a wajen riga da wando suka saka, su kadai ne masu kodaddun atamfofi.
Da alama ma ma'aikatan sun raina su sai can a shelaqe wata ta qaraso ta yi musu yaren faransanci. Me zaa ba ku? Su Hashim babu bihim su ka bi ta da kallo kawai, Bilal da su Aisa suka kwashe da dariya .
Nihal ta ce " babu me Jin yarenki, hausa za kiyi mana da mu ka shigo nan na ji ku na yin Hausa. Me yasa zaki yi mana faransanci yanzu?"
Bilal yayi mamakin yadda har Nihal ta iya yin magana haka cikin qasaita a qasar mutane. Budurwar ta dawo yin magana da Hausa daman rainin ne. Ta miqa musu doguwar takarda na jerin abinci da kudadensu sai Nihal ta hau duddubawa ta na ta zazzaba, abinci kala uku da abin sha ta nuna, ka ji zalla da kifi da dankalin turawa. Ta miqawa Hashim ta ce ya zabi duk abinda yake so ko ya kai kala 10 ne, ya na kallonta yana kifta mata ido.
Can ya rada mata ya ce "ba zamu iya biya ba ki zo mu fita."
Ta harare shi ta ce "dalla ka zaba kawai ko me kake so."
Hashim ya zabi kala biyu shikafa da taliya babu nama. Nihal ta cewa a saka masa kaza guda kada a raba. Hashim ya zazzare ido zai yi magana, ta wurgo masa wata uwar harare, sai ya yi shiru. Najaatu da ta ga haka itama bangaren naman ta fi karfi sai shinkafa aka hada da abin sha kala-kala.
Maaikaciyar nan dai rubutawa take amma cike da tsoro, ta sake maimaitawa "dukka zaa kawo muku?"
Nihal ta amsa cike da taqama " Eh dukka."
Bilal su na jin dadin kallon dramar nan za su so su ga fadan karshe. Su na ta rada su na dariya su na kallo. Nan fa aka dinga jerewa su Nihal abinci kala-kala a gabansu. Da cukula da wuqaqe na turawa.
"Ku ci kawai Nihal ta fada a lokacin da ta dauki wuqa da cukali. Haske ta ga gani da alamar an dauke a hoto, a boye Aisa take daukarsu a hoto.Yayin da Halima ta saita wayarta ta na yi musu bidiyo, tabbas social media ta na daf da samun sabon labari. Nihal ta gane amma ta yi kamar ba ta gane ba.
Mamaki ya kama su da su ka ga ta iya yankawa da wuqa ta kwasa da cokali mai tsini (fork) ta kai baki ba tare da sun rikito daga bakinta ba. Naja'atu da Hashim ne dai su ka

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads