Header Ads
Showing 57001 words to 60000 words out of 110552 words

Chapter 20 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ya dubi Bash ya ce " kai amma yarinyar nan tana da nutsuwa da hankali wallahi ita ce ma take bani hakuri akan kada in damu. Kuma bata yi fushi ba ta ce a saka ta a ko ina ma."
Bash ya yi tsaki ya girgiza kai ya ce " mutuniyar kirki ce wallahi na dade da sanin haka, ai kai ka biyewa Bilal shi kadai ne actor, kada
Allah ya sa ya yi fim din. Ai tun jiya ya bani haushi mu ka yi kaca-kaca akan yarinyar nan. Ya san ita irin daukakar da Allah zai yi mata nan gaba, yake wulakanta ta."
Abbas ya ce don a zauna lafiya ne na bi shi a haka, ka san bai kamata ka bata da mutanen da ka dade tare da su ba, akan sabon zuwa. Amma kamar yadda ta fada din ne zaa hadu nan gaba."
Dakyar Hashim ya miqa tsaye daga inda ya zube, hawaye tab ya cika masa idanuwansa.
Nihal ta kwashe da dariya ta ce "Hashim har da kuka? Kai da ka kwana kana sallah. Ka ga kenan Allah bai bamu ba kasancewar ba alkhairi ba ne a wajenmu. Baa fushi da hukuncin Ubangiji ka jira ka ga sakayya."
Ya matse hawaye ya yi Jugum.
Nihal ta ce "zo ka raka ni wani waje, waqila in muka fita ka ga mutane za ka ji sanyi a ranka."
Ya tsaya kawai ya na kallonta cike da mamaki saboda yadda ya ga bata damu ba kwata-kwata ma.
Su na tafe su na labari ya ce " wallahi da kin yi fim din nan da kin yi suna kuma kin zama mai tsada. Yin Fim da Bilal ma wata daukaka ce shi ba da kowacce mace yake yin Fim ba. Sannan in baa biya ki da yawa ba Allah watakila ki sami zunzututtun kudi naira dubu sabain Wallahi."
Nihal ta kwashe da dariya ta ce" har dubu sabain?"
Hashim ya zaci tana nufin sun yi yawa ne sai ya ce " bari dai in rage Allah sai ya baki dubu sittin ma."
Ta sake kwashewa da dariya ta ce " lallai da mun yi kudi."
Ya ce " amma Allah Ya isar mana, Bilal ya cuce mu."
Ta yi sauri ta katse shi ta ce "Hashim ba na son irin wannan abin da kake yi fa. Yaushe za ka waye ne? Gaskiya ka koma islamiyya dan ka qara samun ilimi ka san hukuncin yarda da qaddara.
Su na isa sai ga Shazali ya fito daga ofis yana ganinta sai ya cika da murna da girmamawa. Ya gaishe ta sai ta shaida masa ko zasu koma gefe ta na da magana da shi.
Hashim ya na tsaye a gefe yana kallonsu ya kasa sanin a lokacin da Nihal ta san 'yan garin nan, dan duk in da su ka je sai ya ga ana gaishe ta.
Nihal ta dubi Shazali ta ce " maganar gidan da nake haya ne ga shekara ta zagayo amma na ji kamar ka ce sun fi so su siyar. Ina so zan siya."
Sai Shazali ya dago da sauri ya kalle ta ya cika da mamaki amma dai ya san daman masu kudi ne dan haka gara ma ya tsagaita da mamakin. Shi dai ya kasa gane abinda ya sa ta kaure garin nan.
" Nawa ne kudin? "
Nihal ta tambaya.
Shazali ya ce " miliyan daya da rabi suke nema amma idan aka zauna zasu rage watakila miliyan daya da dubu dari biyu ko da uku ma sai su bari."
Ta gyada kai ta ce " ka je ka zauna da su yau gobe insha Allah sai in biya ."
Ya amsa da cewa yanzu kuwa Hajjaju zan je wajen mai gidan duk yadda muka yi za ki ji ni. Har yanzu baki da waya ko?."
Ta amsa " eh amma kada ka damu goben da yamma zan zo sai mu tafi mu biya kawai. "
Su ka yi sallama tana godiya ya na godiya suka tafi ba tare da Hashim ya san abinda su ka tattauna ba. A hanya Hashim ya ke tambayarta yaya aka yi ta fara sanin mutane a garin nan?
Ta amsa masa da cewa "na kusa cika shekara guda fa na fi watanni shida ya kamata daman ace na san jamaa."
Ya amsa "haka ne fa. Ina zamu je ne naga kin kama wata hanya ba hanyar gidanki ba?"
Ta yi dariya ta ce " Inna da Baba zan je wa hira sai bayan sallar isha'i zan dawo."
Hashim ya harare ta ya ce "har wata hira kike zuwa yi ke kwata-kwata ma wannan abinda aka yi miki baki damu ba."
Nihal ta yi dariya ba tare da ta san amsar da za ta bashi ba kuma.
Ta ce a ranta "da ka san ma kyautar da Allah Ya baka da ba za ka damu akan naira dubu sittin ba."
Ba ta bar gidan Inna ba sai da ta yi sallar isha'i su ka yi sallama da su Hashim, ta ce zata yi tafi wani waje gobe kada ya neme ta domin sai da daddare za ta dawo.
Da safe ta shirya ta shiga garin Kano bayan ta gama da kasuwar 'yan gwal da kasuwar canjin dalar sai ta boye hamlin kudinta a qasan jakarta ta nufi unguwar zoo road ofishin Darakta Abbas.
Abbas ne tare da darakta Idris da kuma Halima Jabir yarinya me tashe da farin jini a duniyar fim. Itace za ta maye gurbin Nihal.
Har Nihal ta daga qafa daya zata shiga ofishin sai ta ji ana ambaton sunanta dan haka sai ta ja baya ta tsaya ta kasa kunne ta na sauraro.
Tabbas kunnuwanta sun jiyo mata abinda zai hana ta bacci sai ta ji dama bata zo ba. Meye ma ya kai ta ta yi musu labe?
Hohoho da sun san Nihal za ta ji da basu fadi wasu maganganun akanta ba. Sai a yau Nihal ta san menene ake nufi da rayuwa, dan ada bata san komai a game da rayuwa ba.
Kafin ka ce kwabo ta hada gumi sharkab yayin da hawaye ya gagara tsayawa daga idanuwanta. Ta ci gaba da yin shawara ita da zuciyata. Shin ta shiga ne ko ta tafi ta yi kamar bata ji ba? Anya maganar nan ya kamata ace ta dauke kai akanta kuwa? Gara dai a yi ta ta qare kawai.


*** *** ****


TALLA! TALLA!! TALLA!!!
Me talla shi ke da riba marmaza a garzayo...


鉂も潳鉂も潳鉂も潳鉂も潳鉂�
Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you馃
Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go馃槈
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product鉁�
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 馃挴 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day馃拑
We have herbal whitening black soap now nd beauty set available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it馃
Just gv it a try now nd see wonders鉁�
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k


Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare


what are you guys waiting for hurry nd grab urs馃拑 now is the time to glow馃鈥嶁檧锔�
Pamper ur skin馃Φ
Shine like a bride 馃懓
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders馃槝






Do not forget to follow us馃憜
Like nd comment pls dearies馃槝
Patronize us馃檹
mg's always serve you the best鉁呪潳锔�
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne鉂�


GABA GADI


NA


JAMILA UMAR TANKO
(JUT)


Nihal ta na ta dauki ba dadi da zuciyarta wata zuciyar tace ta shiga ciki kawai su san ta ji, wata zuciyar ta ce ta juya kawai kada ta nuna musu ta ji.Daga qarshe ta yanke hukuncin gara kawai ta juya ta tafi kawai babu amfanin ta nuna ta ji, ta bar su da Allah.
Dan haka sai ta yi sauri ta juya za ta tafi, da Bash Auta ta yi kicibus saura kadan ta bangaje shi. Ya dago a fusace zai yi ma ta fada sai ya ga Nihal Nuren Mubin ce wato gwanarsa. Yarinyar da take burge shi haka kawai bai san dalili ba.
"Ah Nihal ina za ki tafi kuma? Na ga kin yi kamar za ki shiga ba ki shiga ba kika fasa."
Kamar daga sama su Abbas suka jiyo sunan Nihal, wannan kalma ta " kamar za ki shiga kika fasa" ta tabbatar musu da cewa ta ji abinda su ka fada shiyasa ta fasa shiga.
Bash ne ya sako ta a gaba su ka shigo ta bi kowannensu da kallo yayin da gumi ya fara ketowa kowannensu.
" Ah Nihal ke ce a gari? Ga kujera ki zauna." Abbas ne ya fada gami da nuna mata wata kujera dake gefensa.
Nihal ta girgiza kai ta ce " A a Darakta babu komai sauri nake, na gode. Sako na kawo zan ba ku in wuce."
Ta saka hannu a jaka ta zaro himilin script din da ya bata don a karanta mata. Maimakon ta miqawa Abbas sai ta miqawa Halima Usman gami da cewa " Ga wannan na ki ne shine sina-sinan da kika maye gurbi na."
Halima ta sa hannu ta karba a sanyaye yayin da Bilal ya maqale hannu a qirji ya na hararar ta sama da qasa tabbas ya tanadar mata duk wasu shikashikan rashin mutunci a yau muddin ta tare shi da wata magana. Gulma ce ya san yayi kuma baya tsoron masu aji ma balle kucaka irin ta marar gata, marar kudi, marar ilimi.
Nihal ta ci gaba da magana da Halima " a zatona ciwon 'ya mace na 'ya mace ne haka duk wanda ya zagi 'yar fim guda daya ya na shafar gaba daya 'yan fim tunda kudin goro ake yi. Tabbas duk wata baraka daga gida ake yaga ta , na waje basu da laifi idan sun ji sun yada sharri akan 'yan Fim. Kin ga baki taba ganina ba ban taba ganinki ba amma kina rantsuwa da cewa Darakta Tukur ya gama yin lalata da ni shiyasa nake fitowa a dukka finafinansa. Wa'iyyazu billah! daga bakin 'yar Fim ce ta furta wannan abu akan 'yar uwarta 'yar fim. Malam Abbas ka duba fa ka gani. Duk duniya akwai wanda ya isa ya wanke wannan maganar. Ai daga gida ta fito daga bakin dangi. Ina mai baki shawara ki guji yarfe da qazafi domin wataran sai ya dawo kanki. Ba sai kin batawa wata suna kafin ki sami wani abu ba, bawa baya wuce rabonsa......"
Bilal ne ya zabura ya dakawa Nihal tsawa "dalla malama ki wuce ki ba mu, waje wa'azin ya isa an yi gulmarki din ki yi abinda za ki yi."
A fusace Nihal ta nuna masa yatsa ta ce " kada ka sake, kada ka fara yi min tsawa. An fada maka kowacce 'yar Fim wulaqantacciya ce kamar ka."
Wannan kalma ta yi masa zafi musamman daga bakin da ta fito, na bakauyiya ma irinta. Zabura yayi ya miqe tsaye watakila niyyarsa ya mare ta. Bash Auta Auta ne ya shiga tsakaninsu.
Bash ya fada a fusace "me ya kai ka kaiwa mace hannu? Kada ma ka fara, Nihal mutum ce kamar kowa dole ta ji zafin qazafin da aka yi mata. Kuma a cikin maganarta menene ba gaskiya ba? Baraka daga gida ake samunta sannan 'yan waje su samu su yi gaba da ita. Na tabbatar da zaginta ku ka yi ko kushe ta Nihal ba za ta taba daga ido ta dube ku ba amma wannan qazafin da ku ka yi mata ne yayi mata ciwo shiyasa ma ta yi magana, kuma maganar ma nasiha ce. Ke Halima da kin san halin Nihal ma da ba sai kin yi mata qazafi ba ma. Dan za ki kwace gurbinta da kanta za ta dauka ta baki . To ko manyan Jarumai ma ba sa gabanta balle Tukur, idan ta yi fim a gaban kowa take cewa a bawa Tukur kudin saboda girmamawa shine me gidanta a hannunsaaka damqa ta. Abbas an yi haka ko baa yi ba? Ku ba ku san ta ba kawai kun dauki zargi da yarfe da qage ku na jifanta da shi."
Bilal ya fusata ya ce "Bash! babu ruwanka da maganar nan ka ja bakinka ka yi shiru ka barni da ita, daqiqiya ma irinta. "
Nihal ta ce " Zaa gane waye daqiqi a tsakanin ni da kai nan gaba."
Sai kan kowa ya daure a wajen ke da ko furamare baki yi ba ki na ja da mai masters.
Abbas ne ya zabura ya katse Bilal ya ce " A a Malam Bilal banda cin
zarafi irin wannan. Tabbas an yi ma ta laifi ba dan kadan ba, dole ta yi magana ta fi mu gaskiya. Nihal ki yi haquri ki yafe mana."
Bash ya yi dariya ce " Au Darakta daman har da kai aka yi gulmar? 'yar gidanka ce fa."
Abbas ya sunkuyar da kai yayin da gumi ya dinga keto masa. A lokacin ya dinga tunano iya furucin da yayi a cikin hirar.
Nihal ta ce " Darakta ka ba ni script din da zan karanta a roll din da ka ga ya dace da ni. Ina son in shiga Fim din nan ko da kuwa zan fito a 'yar aike ne. Domin idan daqiqi ya mu'amulanci masu ilimi jahilcin zai ragu.
Darakta ya yi dibi-dibi ya miqa mata wasu takardu ba tare da shi kansa ya san ko wadanne ba ne saboda nauyi da kunya. Nihal da Halima da Bilal ne ake ta kallon-kallo har ta fice abin ta.
Bilal ya ce " bata da zuciya ko kadan an kore ka a cikin fim ka dage sai ka yi saboda naci."
Murmushi Nihal ta saki ta ce "ga wanda ya san darajar sana'arsa ba ya fushi. Sannu a hankali zai zama mai riba. Domin a haka zan zama Jaruma wataran."
Wannan kalma da ta fada ta tuni masa da nasihar da Princess last born take yi masa amma cikin karshen turanci, abu daya su ka fada da Nihal.
Princess ta kan ce masa "Bilal in har ka san kanka ba za ka taba yin fushi da sana'arka ba, ko me aka yi maka kuwa. A haka za ka zama Jarumi wataran."
Nihal ta fice abin ta yayin da Bilal ya ji kansa ya daure yadda wannan kalmar masu ilimi irin su princess ta fito daga bakin wannan jahilar.
Bash ya bi bayanta da sauri su na tafe ya na jero mata tambayoyi ya na so ya ji takamaiman abin da su ka ce akanta. Ba ta da wannan lokacin na nanata magana daya, ko kallonsa ba ta yi ba ta ci gaba da tafiya. Sai ya ba ta hakuri kuma yayi mata jinjina a bisa matakin da ta dauka cikin sanyi.
" Na gode." kalmar da ta fada masa kenan ta tsayar da me adaidaita sahu, ko in da za ta je bata fada masa ba, ta shiga ta zauna ta ce su tafi. Bash ya qame a tsaye ya bi babur din da kallo har su ka yi nisa, zuciyarsana sosuwa akan abinda Nihal ta ke yi masa na nuna halin ko in kula. Ya fara jin haushin kansa da kansa akan yadda ya damu da wacce bata damu da shi ba, bata ma kai matsayin ya damu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads