Showing 18001 words to 21000 words out of 110552 words
Chapter 7 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt
saurin daukar karatu, dan na ga ko ina tsaf-tsaf ta sake saharewa. Na mata fadan sata in ma tana yi ka da ta taba na mu ." In ji Mami.
"Ta gwada tabawa ma ta ga yadda ake fasa bakin yarinya ." Asabe ta fada yayin da ta ke shirin shiga wanka .
Ko tari Nihal bata yi ba balle ta basu amsa, ta tashi ta fita ta yi alwalla ta zo tayi sallar magrib.Ta jira lokacin sallar isha'i ta tashi ta yi.Ta dade ta na addua ta na neman kariya da juriya da haske akan abinda ta tunkara.
Wasa-wasa Nihal ta yi sati uku ta na wuni a wajen daukar shirin fim, har wasu kauyukan kurkusa take raka su amma baa taba saka ta ba, sai kyara da aike kawai take sha. Abinci kuwa wani lokaci idan Mami ta ci tana rage mata, ruwan pure water ma sai wanda ya tausaya mata yake siya mata. Amma basu Kula da cewar idan ta karba ma bata sha kuma bata ci sai dai ta faki ido ta fita waje, ta bawa almajirai. Abincinta a boye take zuwa ta karbo a wajen Shazali ya nuna mata shagonsa haka ruwan roba take sha don tsoron shan pure water take gani take zata kamu da cuta. Idan zaa kai dare bata taba shan komai ba har sai ta dawo .
Ta na ta karantar yadda ake daukar Fim da yadda 'yan Fim suke acting. Tabbas akwai kurakurai masu dinbin yawa, za ta iya cewa ta basu maki 2%, kenan wannan ba Fim sunansa ba idan ta hada da yadda qa'idar fim take .
Darakta Tukur ne ya tausaya mata ya dube ta ya ce " ke yarinya zo karanta wannan script din kawai ki yi mana wannan sin din saboda Maimuna bata nan mun gaji da jira ."
Nihal ta cika da murna ta miqa hannu za ta karba sai.
Amina 'yar kwalisa ta zabura ta ce " waye zai karanta script? Wannan kucakar? Kai ma darakta da gangan ne ka so ka bata lokacinka. A ina ta taba zuwa makaranta balle ta iya karatu? Ai kawai ka fada mata da baki in kwakwalwar zata iya riqewa."
Maimakon darakta ya tsawatar sai ya yi dariya ya ce " Amina baki da dama .To shikenan bari in fada mata ."
Ya juya ya kalli Nihal ya ce " kada ki tsorata kada muryarki ta yi karkarwa in kin ga an dora kyamara a kanki. Abinda ake so ki yi shine ki zo da gudu ki ce kanwata ce ba lafiya ka taimaka a kaita asibiti . Sai ki durqusa kina roqar mai babur din. Za mu saka miki ruwa a ido yayi kamar hawaye."
"Yauwa ga Maimauna ma ta zo gara ta karbi sin din ta, wannan bata mana Fim zata yi . " Amina 'yar kwalisa ce ta fada cike da murna .
Dirakta ya juya da sauri ya kalli Maimuna wacce ta sauka daga kan babur.
Ya yi dariya ya ce " Shikenan ke baquwa koma ki zauna anjima zaa yi rawa zan saka ki a cikin 'yan rawa ."
Mami ta zabura ta ce " rawa kuma, wannan fa kamar ba zata iya komai ba . Kada a zo ana bata mana lokaci ka san mutumin da bai taba yin fim ba, fama ake yi da shi ."
Nihal bata yi magana ba sai ma tausayi da suke bata, ta koma ta zauna, zuciayarta tana tafasa kamar zata qone.
" wannan yarinyar tausayi take bani wallahi baa taba saka ta a Fim ba sai dai ta yi ta wahala abin tausayi. Gashi zaa saka ta aka yi mata bukulu. " Najaatu ce ta fadawa Mami.
Hawaye ya kwaranyo daga idanuwan Nihal dan ta fara jin tausayin kanta da kanta.
Najaatu ce ta tsaya a kanta ta ce " daina kuka qawata zaa saka ki, haka mu ma muka yi mun sha irin wannan wahalar kafin a saka mu. "
Hashim ne ya qaraso inda suke shima an gama yin na sa sina-sinan.
Ya ce " au Nihal kuka kike ? Meye abin kuka ? Darakta ya ce zaa saka ki a cikin 'yan rawa. "
Nihal ta goge hawaye ta kirkiri murmushi ta ce " ba kuka nake yi ba fa . Ya wuce ai. "
Da la'asar sakaliya bayan ta idar da sallar la'asar Hashim ya taho da sauri ya ce " Nihal ki zo in ji darakta da sauri . Ta tashi da sauri ta isa wajen da dandazon mutane suke .
" yauwa ku bata anko daya ta saka zata shiga cikin 'yan rawa. Doguwar rigar atamfa leda-leda ce aka dinkawa 'yan amshin rawa da waqa. Isma'il ne a bangaren Kula da sutura dan haka da ya dubi yanayi da tsayin jikinta sai ya zabo mata riga daya ya miqa mata daidai da jikinta .
Abin mamaki sai Nihal ta girgiza kai ta ce " ba zan yi rawa a Fim ba ."
Isma'ila ya maimaita cikin daga murya cike da mamaki " ba zaki yi rawa a Fim ba ? Kamar yaya ? "
Nihal ta maimaita cike da gadara " ba zan yi rawa da waqa a fim ba saboda ba ya cikin al'adarmu. "
Hankalin kowa ya juyo kanta mamaki marar musaltuwa ne ya bayyana a kan fuskokinsu. Aka zagaye Nihal ana yi mata tambayoyi na isgilanci da raini.
Amsa daya take bayarwa ita fa ba zata yi rawa a fim ba, acting ko wanne iri ne a bata zata amma banda rawa.
Amina da Mami suka yi shewa suka tafa suka ce " lallai yarinyar nan 'yar yi ce . Idan ta zama super star wacce gadara za ta yi ? A haka ma a cikin tsumma tana girman kai ."
Ran darakta Tukur yayi mummunan baci . Ya harare ta ya ce "sai kiyi ta zama a haka, kuma idan kika cika wata daya a dakin da kike zaune ki nemo kudi ki biya haya, yanzu ma roqarsu na yi na ce wata daya zasu baki kyauta. Ko ki hada kayanki ki tafi garinku, zan kira ma mahaifinki ya zo ya dauke ki dan baki da wani amfani ."
Ta fusata ta fice daga wajen, Hashim ya bi bayanta da sauri yana kwalla mata kira ta haye acaba ta tafi gida.
Maganar ake ta yi kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Sun fi zaton saboda baa saka ta a sin din Maimauna ba ne ta ji haushi .
" Amina ta ce "tunda na ga yarinyar nan na ji jinina da na ta bai hadu ba na tsane ta ashe bakin hali gara ta . In har ina garin nan ba zata taba zama jaruma ba kuwa wallahi. "
Da daddare Hashim ya zo qofar gidan su Nihal yana ta yiwa mata Nasiha akan ta zo su je su bawa darakta hakuri akan abinda ta aikata.
Da farko ta qi yarda, sai da ya dage sannan ta bishi. Gidansa suka nufa aka yi musu sallama da shi, ya fito qofar gida. Da ya ga Hashim tare da Nihal ne sai ya juya a fusace zai koma cikin gida . Da sauri Hashim ya kama hannunasa ya riqe ya durkusa har qasa yana bada hakuri. Nihal ma ta zo ta durqursa ta na bashi hakuri.
Darakta Tukur ya more albarkacin bakinsa, ya fadi duk wata baqar magana da ya tanadar mata sannan ya ji sanyi a ransa. Daga baya ya hakura .
Bayan an yi haka da kwana biyu ne Darakta Tukur ya kira ta, ya ce ta shiga wani Fim mai suna ' A TARE- ATARE. Narka-narkan shirme ne cikin shirin babu ma'ana ko daya. A ka bata matsayin budurwa da take taimakawa boka da dakan magani.
Kowa ya tsaya cak ya na so ya ga karkarwar da Nihal zata yi idan aka dora mata kyamara kamar yadda sababbin shiga suke yi a ranar farko . An cika da mamaki da suka ga ta dake kuma babu alamar tsoro ko jin kunya a tare da ita .
Duk abinda aka fada mata ba shi ta fada ba amma da aka lura sosai sai aka ga maganarta ta fi yin ma'ana kuma ta fi isar da saqon da ake buqata.
Har da su Amina sun fara yi mata cari akan ta fadi abinda baa ce ta fada ba sai Darakta da masu daukar hoto su ka jinjina mata har suna tafa mata.
Ran su Amina ya baci hankalinsu ya tashi da suka ga ana ta qarawa Nihal yawan sina-sinai.
Gashi Amina ta yi rantsuwa in har tana raye ba zata taba bari Nihal ta zama Jaruma ba .
An gama daukar shiri kowa yana kokarin hada kayansa, Nihal da Hashim sai dadi suke ji su na tafe su na labari. Sun zo wucewa Amina na zaune sai kawai ta sakawa Nihal qafa ta yi tuntube saura kadan Nihal ta kifa Hashim ya tare ta . Amina na tashi tsaye sai ta kifawa Nihal mari, ba wacce aka yiwa marin ba ma wadanda ke kusa sai da suka firgita.
Nihal ta kama kunci ta durqusa domin ta fita daga cikin hayyacinta har ta rasa duniyar da take ciki .
" yauwa qarawa shegiya. " Iyantu ta fada a lokacin da take sheqa dariya.
Amina 'yar kwalisa tana tsaye a kan Nihal tana gunzuma mata zagi wai taka ta ta yi .
Anan ne Darakta Tukur ya fusata ya nuna bacin ransa sosai har ya bawa Amina gargadi na qarshe in har ta qara zagi balle marin wata zai cire ta daga Fim kuma ba zai sake saka ta a wani Fim ba nan gaba.
Mazan wajen da ma wasu daga cikin matan sun bawa Amina rashin gaskiya kuma kowa ya ga abinda ya faru, Amina ce ta saka mata qafa da gangan.
Har yanzu Nihal na tsugunne ta na so zugin ya ragu ta dawo wannan duniyar da muke ciki kafin ta yi tunanin matakin da zata dauka . Domin ta tabbatar ba zata taba bari a mare ta a banza ba , ta san darajar kanta ta san hakkin kanta .
Hashim ne ya tari fadan yana zagin Amina tana zaginsa.
Ba su ankara ba Amina su ka hango an cillo ta can gefe, kafin ta yunkura ta miqe an bi ta da mari kwarara guda uku . Baa bar ta haka ba da qafa aka dinga ball da ita . Nihal Nuren Mubin ce ta nuna mata ita sojoji ne suka bata horo tun tana goye a baya . Qashinta yayi kwari sosai ya na lankwasuwa ko ta ina, ta yi tsallen kwado kala kala, ta yi fareti, an daga kafafuwanta sama kanta a qasa. Duk yayyata ne suke gana mata wannan azaba tun tana qarama. Dambe kuwa ita da Hamza da Mu' awiyya babu wanda baa yi ba, su ne saqonta. Allah ne ya raya ta kuma mahaifiyarta tana tsaye a kanta ba dan haka ba da mazan nan sun karairaya .
Nihal bata fada amma idan ta fara fada ba irin fadan mata take yi ba, na maza ne mazan ma sojoji.
Hohoho masu kawo gagaji wajen ceton Amina ma sun sami nasu elbow din, fadan chinees kawai take da qafa take harbi.
" ku taimake ni ku janye ta zata kashe ni ." Amina take fada cikin wahalalliyar murya .
Dakyar maza suka raba fadan nan . Nihal ta juyo da jajayen idanuwanta ta harari sauran matan su Mami kenan ta ce " saura ku ku yi hankali da ni ."
Dankwalinta da takalmanta ma'ana kuzajjen silifas dinta Hashim ya daukowa Nihal ya bata ta saka.
Darakta Tukur cewa yake " ta yi min daidai, domin kun takura mata kun kai ta qarshe ne ."
Aka tafi da Nihal gida dakyar ta yarda ta tafi .
Daga wajen shooting gidan me gyaran targade aka wuce da Amina 'yar kwalisa. Targade hudu ne wurare mabanbanta.
Dadi ya kama Hashim tabbas Nihal ta yi masa daidai domin baya son sokoncin nan da take yi duk su na ta aikenta da kyara.
Mami ta shigo daki a fusace ta ce iske Nihal ta harare ta ya ce "tattara kayanki ki bar dakin nan, daga yau zuwa gobe zama mu dake ya qare."
Ta razana da ta ji amsar da Nihal ta bayar " babu in da zan je ." Nihal ta ja fulo ta kwanta .
Sai aka hau kallon-kallo Mami da sauran 'yan dakin .Ba tare da kowa ya qara magana ba .
Asuba ta gari Nihal Nuren.
Bayan sati guda ne Hashim ya zo ya ce Nihal ta taho ga babban darakta daga kano ya zo zasu dauki wani shiri, tana so ta roqe shi ko zai saka ta a wasu Fina-finan na sa.
Ta tashi da sauri ta biyo shi su ka isa wani gida da suka ara zasu fara wani shiri . Nihal da Hashim suka Shiga falon kai tsaye, wajen darakta Idris suka nufa suka durqusa suka gaishe shi yayin da Hashim ya nuna Nihal ya ce ita ce yarinyar da ya taba bashi labari sabuwar zuwa da ya taimaka ya saka ta a Fim .
Kallon Nihal yayi ya yamutse fuska ya tambaya cikin isgili " wa zan saka a Fim,wannan yarinyar ?"
Jikin Hashim yayi sanyi suka koma gefe suka rabe yayin da darakta ya ci gaba da harkokinsa.
Nihal ta ga mata wayayyu da mazan ma, ba kamar na kauye ba tabbas wadannan 'yan Fim din birni ne .
Su na ta kallonta dai tana kallonsu.
Anan suka wuni babu Wanda yake kallonsu. Abinda ya bawa kowa mamaki shi ne yadda ta ke nunawa mai kyamara yadda zai saita kyamar da kuma yadda mai riqe fitila zai dinga riqewa.
Sai gashi ana tambayar ta wasu abubuwan idan sauti ya qi fita ko murya tayi karkarwa.
Actor mai tashe Bashir Auta sai yanzu ya karaso a cikin luntsumemiyar motarsa fara mai baqin gilasai Gaisuwa da shishigi qananan suke yi masa ,
Hashim ya zabura ya ce da Nihal " kin ga Bash Auta ."
Ta tambaya " waye shi?" Mamaki ya kama Hashim sai ta tuna ta yi sauri ta ce " Au bash Auta ne na gane shi ."
Yana tafe yana qobarewa yana taqama.
Aka fara daukar shiri, shine zai yi tsalle daga kan bishiya ya diro qasa. Su ka dinga shirme sai da Nihal ta tabbatar babu abinda suka sani sai ta yi carab ta basu shawara akan a daura masa igiya ya diro amma a zahiri ana riqe da shi .
Ta nuna musu dubarun yadda zasu yi abubuwa da yawa.Daga nan sai aka bata wani sin daya aka ce ta shiga.
Hohoho! Nihal bata gama da arnan gabar qauye ba ta zo ta qara tsokano 'yan birni. Rayukan jarumai mata 'yan birni ya baci.
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: GABA GADI
EP 8
Su ka hau yi mata gani-gani da harara da yamutsar fuska kamar sun ga kashi. Ita da Hashim suka cika da murna saboda ya tabbatar mata wannan babban fim ne kuma babban kamfani gashi ta fito a ciki .
Da yamma sai aka kawo motoci aka ce su shiga zaa tafi garin dutse wajen duwatsu anan ne zaa ci gaba da shooting .
Nihal da Hashim ba su saka ran bin su ba suka koma gefe suka tsaya su na kallo.
Darakta Idris ne ya hango su tsaye ya qaraso in da suke da sauri ya ce su shiga cikin babbar mota su ma a tafi da su . Su na shiga suka zauna sai suka yi kicibus da manyan hararar Jarumai har da alakoron tsaki.
Nihal ta sunkuyar da kai qasa ta ce a ranta " wannan tsanar ta menene ? A baya a rayuwata kowa sona yake ban taba ganin wanda ya tsane ni ba sai a garin nan ."
Su ka isa garin Dutse lafiya amma ba cikin gari ba ne wajen gari.
Aisa wacce aka yi mata laqabi da Aisa buzuwa Ita ce Jarumar fim din, akwai sin din da za ta yi gudu sannan ta yi tsalle ta dane wani tsauni. Abin haushi ta kasa yin katabus.
Nihal ta fada a ranta "wannan wasan yara suke yi ko Fim? Abinda ake so a dinga yinsa kamar da gaske kashi 80% da jikinka ake so ka yi kyamara ce zata qarawa sauran 20% din ."
Nihal ta ga abin nan ba zai taba tafiya daidai ba sai ta je ta fara nunawa Jaruma Aisa yadda za ta yi, da abu ya fassaka daraktan birni Idris Hayat ya ce Nihal ta saka kayan Aisa ta shiga ta yi wajen da duk zaa yi tsallen in ya so sai a dora fuskar Aisa.
Haka kuwa aka yi sun ga abin mamaki tashi sama kawai take yi ta na dira. Basu taba yin Fim da aka taba yin wannan bajintar ba. An sha tafi da ihu da jinjina domin ta burge su matuqa.
Aka gama wannan aka zo wajen fada, maza ne 'yan daba su ke rigima a tsakanin wannan kungiya da waccan kungiyar. Nan ma Nihal ta ga shirmen yayi yawa kaiwa dukan daban faduwar daban. Haka idan aka kai sara kwata kwata babu alamar an kusa taba wanda zaa sara sai ka ga mai saran yayi can wanda aka sara ya yi wani wajen. Dole rayukan masu kallo ya baci zasu ce an raina musu hankali.
Abin mamaki sai ga Nihal tana koya musu fadan canis. Juyi take tana tashi sama tana harbin iska. Tabbas wannan daga gani ta je makarantar koyon kareti ba a gari kawai ta koya ba. Ah sai mamaki ya sake mamaye zuqatan daraktoci da furodusoshi har da jarumai mata da maza .'Yan kallo kuwa baa magana ihu ake ana tafi.
Sunanta carab a bakin kowa fadi suke "sai Nihal Nuren an gaishe ki."
"Wannan yarinyar kuwa a qauyen nan ta ke?" Darakta Idris ne tambaya .
Darakta Tukur