Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 110552 words

Chapter 1 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

: *GABA* *GADI*
*Littafi* *na* *daya*


*Labari* *Da* *rubutawa*
*Jamila* *umar* *tanko*
( *JUT* )



Bissmillahir rahamanurahim*


GABA GADI


Babi na daya :


Sun tafi da murna sun dawo da gagarumin bacin rai, bacin ran da ba zai musaltu ba .Tun daga Airport na Malam Aminu Kano da ke birnin kano direban da ya je daukarsu ya fahimci hakan. Babu walwala, babu Annuri a fuskokinsu. Ko gaisuwarsa ma basu amsa ba. Haka suka bude bayan mota suka zauna. Hakan ne ya tabbatar masa cewar Mummy da Daddy babu lafiya abinda bai taba gani ba tunda ya fara yi musu aiki.


"Wai shin meya bata musu rai haka ? Ko sakon rasuwa aka aika musu, don sun dawo da wuri ba kamar yadda suka saba dadewa idan suka je London ba ? Ko fada suka yi a junansu? " Habibu direba yake tambaya a zuciyarsa.


Har suka isa gida ko tari babu wanda yayi a cikinsu.
Wannan bacin ran nasu shi ya hana su cin abinci balle hira, ko kallon talabijin. Babu wanda yake ganin gilmawarsu tunda kowannensu ya Shiga dakinsa ya datse.


Kwanaki uku kenan da dawowarsu 'yan sannu da zuwa sun zo ba adadi sai dai 'yan hidimar gidan su ce su na daki su na baccin gajiya, dan haka baa samun damar ganinsu.


Masu aiki koda yaushe su na jere abinci akan tebur haka suke zuwa su tarar da shi baa ci ba su kwashe, su jera sabo shima kuma a haka zasu zo su tarar baa ci ba . Tabbas jikinsu ya fada musu gidan nan babu lafiya. Domin basu taba ganin irin haka ta faru a rayuwarsu ta gidan nan ba.


Kullum da safe yaransa sai sun shigo don su gaishe su amma sai masu aiki su ce su na daki su na bacci. Wannan ma sabon al'amari ne wanda basu saba gani ba. Kwanaki uku kenan dan haka sun tabbatar ba lafiya ba gashi wayoyinsu dukka a kashe. In ma a kunne ko an kira baa dauka.


Yaransu su bakwai yau sun hallara a cikin babban falon gidan da zunmar yau sai sun ga mahaifansu ko da kuwa dakin Zaa balla .


Bugun kofar da suke yi ya karfafa in dai mutum ba bacci mutuwa yake yi ba dole ya farka .


General Nafi'u ne ya bayyana a bakin kofar dakin fuskarsa murtik babu walwala, babu annuri, idanuwansa sun kada sun yi jajawur, ya wurgawa kowannensu harara yana yi musu duba irin na rashin fahimta.


Su dukka suka duka suka gaishe shi, bai amsa ba ya kawar da kai gefe ya fada cikin fushi " lafiya ku ke buga min kofa? Ko na ci bashin wani ne ban biya ba ?"


Daga Jin wannan amsar sun san tabbas General ya kai kololuwar fushi . Sai suka hau kallon-kallo a junansu aka rasa wanda zai bashi amsa. Sai Sosa keya da gashi suke yi .


General ya sake daga murya cikin tsawa " shin wa ya baku izinin ku wuce falo har guda uku, ku zo kofar dakina ku buga min kofa ?


Muhammad ya yi karfin hali ya ce " Oga, kwana biyu ba mu ganku ba daga kai har Mummy tunda ku ka dawo daga tafiya. "


Abubakar ya ce " kwana uku ma kenan idan za mu tafi wajen aiki kullum da safe mu na shigowa don mu gaishe ka sai mu iske baka falo masu aiki sai su ce kana bacci ."


General ya ce " me ya shafe ku da baccinmu? "


Umar ya Sosa keya ya ce "ranka ya dade baccin ne yayi yawa kamar ba lafiya ba hankalinmu ya tashi ."


Aliyu ya ce " gaisuwa ce baba ."


General ya ce " ku rike gaisuwarku ."


Ya na fada ya buga kofa ya rufe dakinsa. Ya barsu anan a tsaye aka hau kallon-kallo.


Usman ya kwashe da dariya "yau Boss fa ba kanta. Me aka yi masa haka ne ? "


Muhammad ya harari Usman ya ce " kada ka sake yi mana dariya ba abin dariya ba ne . This matter is serious. "


Mu'awiyya ya ce " normal ne kawai , ku zo mu kauce kawai sai ya yi normal ma dawo ."


Hamza ne bai ce komai ba ya yi shiru kawai yana tunani ya juya ya nufi kicin ya sami masu aiki yana jero musu tambayoyi game da matsalar da take afkuwa a cikin gidan nan. Rabecca ta zaiyana masa duk abinda suka lura da su tun bayan dawowarsu daga tafiya .


Hamza ya fito a Sanyaye, a falon farko ya sami 'yan uwansa a zazzaune su na tattaunawa.


Abubakar ya zabura ya kalli Hamza ya ce "ka tambayi masu aikin abinda yake faruwa ? "


Hamza ya gyada kai ya ce " sun shaida min tun ranar da suka dawo daga tafiya basu kara cin abinci ba kuma basu sake jin motsin su ba . Kowanne yana dakinsa ya kulle. "


Suka zauna har tsawon awa guda su na tattaunawa akan yadda Zaa shawo kan wannan matsalar don a samo mafita . Hakan ya cinma ruwa . Gashi gaba daya wajen aiki zasu tafi kasancewar yau litinin har wasunsu ma sun makara . A dole suka tashi suka watse an tsaya akan a hadu da daddare a cikin gidan . Amma su dukka sun yi amanna Na'ila ce kadai take da amsar wadannan jerin tambayoyin.


Motocinsu tsala-tsala a jejjere guda bakwai haka kowa ya Shiga tasa ya kama hanyar ofishinsa.


Birnin London


Na'ila na zaune a takure a bisa gadonta a dakinta. Wayar da ke gabanta ta fara ruri, ta zabura ya Duba sunan lot.col Muhammad ne wato babban yayansu. Ta safe kirji yayin da ta ja da baya daga kusa da wayar kai kace hannu zai zuro daga cikin wayar ya kama ta. Har wayar ta katse bata amsa ba , sabon kora ne daga Con.Muhammad . Daga nan ta tabbatar wani babban al'amari zai fada mata amma tsoro ya hana fa dauka . Yana gama kira sai ga kiran Hamza shima take dauka . Abu kamar wasa kiran major Abubakar ne babban yaya na biyu . Rigiji gafji sai ta daka tsalle ta bar kan gadon ta bar wayar akan gado tana ta ruri. Ta dafe baki dan idan bata rufe ba zata iya sakin sakin ihu. Kiransa na katsewa babu jimawa kiran Asp Aliyu ne ta fallo da gudu ta leka wayar sai ta daka tsalle gefe tabbas babban mugun da ya fi kowa fushi ne ke kira.


Ta fada a bayyane ina zan sa raina? Yaya zan yi ? "


Kira biyu Asp Aliyu ya yi mata sannan abin mamaki sai ta sake jin wani kiran ya shigo wannan Karon Bar. Usman ne, ah ai shikenan ta tabbata sun ji komai kuma da alama su na tare .


A guje ta shige bandaki ta datse ji take kamar zasu fito daga wayar su damko ta. Ta godewa Allah da ba a kasar take ba da bata san yadda Zaa yayyaga ta ba .


Karar wayar ce dai ta ci gaba da tashi babu Tantama wannan Karon tasan yaya Mu'awuya be cikakken dan jarida kuma ta san ba zai Duba ta a matsayin kanwarsa buga labarin nan zai yi .


"Na Shiga uku" ta fada yayin da ta sulale ta zauna a gefen bahon wanka. Hawaye zafafa ke kwaranya.


Babu abinda kwakwalwarta bata fada mata ba shin ta kashe kanta ne a zo a tsinci gawarta kowa ma ya huta ko kuwa ta Shiga duniya a rasa ta ne har abada ?


"Kada ki fara tunanin kashe kanki, kin san hukuncin mutumin da ya kashe kansa a wajen Allah a addini ya mutu kafiri. Azabar Allah kuwa tafi ta Sojoji da 'yan sanda da yan jaridar da kime gudu a duniya ." In ji zuciyar Na'ila.


Ta fada a bayyane " tabbas gara in sha azaba a duniya da in je in hadu da ubangijina ina kafura. Wa'iyyazu billahi ."


Ta yi zunbur ta Mike ta bude kofar bandaki ta fito tana tafe tana sanda. Tana dosar wajen wayarta haske ne ke ta kai kawo da alama sakonni ne suke ta shigowa. Nan ma ta hadu da gagarumin tashin hankali. Ta zauna a hankali ta jawo wayar ta bude sakonnin. Duk wanda ya kira ta ya turo sako wasu da Hausa wasu da turanci su na bata umarni idan taga missed calls dinsu su ta kira su ana nemanta da gaggawa, kiran tana da amfani matuka.


Haka tana Shiga watsapp ta sami sakonnin wasu daga cikinsu akan ta kira su da gaggawa.


Hannunta na rawa ta ya goge WhatsApp dinta gaba daya ma .sannan ta koma Facebook shima ta goge shi yadda ba zaa sake samunta ba . Ta Shiga U-tube da Instagram a inda take da fellowers sama da milliyan 1 ta goge su gaba daya.


Ta rusa kuka kamar ranta zai fito ta fada akan gado wannan Karon babbar aminiyarta ce Siyama ta ke kiranta ta yi kamar zata amsa sai ta fasa ta na tunanin tana tare da Major Abubakar dan shi zata aura . Siyama ta ci gaba da kira ba kakkautawa amma Na'ila ta ki amsawa. Sakon Siyama ne ya shigo tana mai fada mata ta masa waya su yi magana ta gaggawa.


Ta dafe kirji ta ce " innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Shikenan ai abinda nake gudu ya afku ." Kiran Siyama ne ya dawo da tunaninta kan wayar ta yi sauri ta masa ba tare da ta yi magana ba .


Siyama ce ke magana cikin rada " Na'ila kina ji na ? Bandaki na shigo ina yi miki waya , ha Major Abubakar nan a falo yanzu ya shigo da sassafe kamar yana cikin damuwa . Ya na ya yi min tambayoyi akanki da abinda ya faru a London sun ga Daddy da Mummy a cikin damuwa . Na'ila yaya zan yi ? Me zan ce masa ? Ki amsa wayarsa ki fada musu gaskiya kawai . Yau na Shiga uku yaya zan yi ? Kin san hukuncin da Abubakar zai iya sauka akai na idan na yi masa karya . Ki fitar da ni Na'ila zai iya fasa aurena ma . "


Siya ma ta fashe da kuka. Na'ila ma kukan take ta ce Siyama ba zan iya fada musu ba na yanke shawara daga nan ma gaba zan kara ba zan iya dawowa Nigeria ba . Kuma kada ki sake ki fada musu ke ce sirrina kuma na baki amana ."


Siyama zata yi magana kenan Na'ila ta katse wayar ta ma kashe gaba daya .


Tashin hankali ya tabbata a zuciyar Siyama a lokacin da ta kara kira ta ji wayar a rufe. Ta bi ta WhatsApp zata yi mata magana ta ga wayam ta bita Instagram da Facebook babu ma acct din .


Ta wanke fuskarta a Sanyaye ta fito tana tafiya dakyar .


Ta isa falo ta iske abin kaunarta saurayin da ta fara so wanda take tsakiyar so masu burin yin aure nan da wata 3 wato Major Abubakar Genaral Hassan .


Yana tsaye a tsakiyar katafaren falon gidan yana ta kai kawo daga wannan bango zuwa wannan da alama wani abu yana nukurkusarsa.


Yanayin da ya ganta bai saba ganinta ba dan haka wani katon zargi ya sake zargo ta. Data ga alamar haka sai ta yi karfin hali ya kirkiri wani basasshen murmushi dakyar. Ta gaishe shi cike da ladabi ya amsa . Ya fada a shelake " bacci kike ne na tashe ki . Amma tunda a Duba muke waya muna chats na ji ki garau daga cewa gani a kofar gidanku na ji kina in'ina. Gashi kin dade baki fito ba na kira wayarki na ji number busy . Da wa kike waya bayan kin san na iso ina cikin falonku? "


Daga na ta bude baki ta kasa Mayar da labbanta su rufe, kalma daya ta kasa furta da amsa masa wadannan jerin tambayoyin.


"Hmmmm, Hmmm. Kawai take fadi . Ka zauna mana." ta fada jikanta na rawa . Ya Girgiza kai ya ce " sauri make zan wuce Kaduna NDA na makara ma . Na zo in ji amsa kawai . Me ya ke faru ne a wajen Graduation dinku a London? "


Bai rufe bakinsa ba ta zabura ya ce " Komai wallahi ."


Ya kura mata ido sai ya ga ta kasa ido da shi jikanta yana karkarwa.


Can ya gyada kai ya ce " ba komai ko ? Kuma kin tabbata kin fasa min gaskiya ? "


Ta dago da Sauri ta dube shi cikin rawar murya ta " eh haka ne ."


Ya gyada kai ya ce " ok . Tunda kin tabbatar ba ki Boye min komai ba . Kin yi waya da Na'ila da safen nan kuwa ? "


Ta sake zabura har da dafe kirji sai ta tunawa kanta cewa zai gane fa . Sai ta daure ta yi murmushi ta ce " A a ba mu yi ba . "


Ya tambaya a shelake " kin tabbata ? "


Ta gyada kai kafin ta ce wani abu a bakin kofa ta tsince shi har ya isa can yana tafiya . Ta bi bayansa da gudu ta ce " tafiya babu sallama ? Ka tsaya ka sha tea ."


Harara ya wurgo mata mai firgitarwa har suka isa jikin motarsa babu wanda ya kara magana a cikinsu . Da alama ransa ya sake baci .


Kalmar da ya fada mata kafin ya rufe kofar motar ita ce " kinsa hukuncin da zan iya dauka akan mutumin da ya yayi min karya ko ?"


Kafin ta ce wani abu ya rufe motar ya ja dogon ribas. Masu gadi suka danno a guje suka bude masa get . Ya fice da gudu.


Siyama dakyar ta kai kan baranda ta sulale ta zauna . Ta Dora hannu akai ka fashe da kuka zafafan hawaye masu kama da hawayen tiyagas ne suke ta rugugin fitowa daga idanuwanta layi layi.


Ta yi sauri ta sauke hannu daga kanta a lokacin da ta yi ido hudu da yayanta Engr. Muqaddas .


Ta yi saurin warwarewa ta tsatsafo da murmushi amma hakan bai hana shi ganewa da halinda take ciki ba. Ta gaishe shi ya amsa a ciki-ciki gami da galla mata harara ya wuce abinsa. Sanye yake da bakar suit kafadarsa a rataye da jakar laptop dinsa a kafada.


Ya bude motarsa kenan zai Shiga sai ya ji magana daga bayansa. Bai firgita ba ya ji muryar Siyama ce .


" Yaya ! Na'ila kuwa ta masa kiran wayar da ka yi mata ? "Ya ji haushin tambayar nan matuqa. Ko amsa bai bata ba . Ya ajiye jakar laptop dinsa a kujerar gefensa ya Shiga mota ya zauna ya kunna. Ta yi sauri ta riqe kofar motar ta rike Zata sake tambayarsa wani abu .


Tsawa yayi mata kada ki karaso nan, matsa min da gani. Shi munafunci dodo ne ya kan ci mai shi . Kuka kuwa yanzu ku ka fara da ke da ita dayar munafukar Na'ila . Kada ki sake tara ta da maganar da ta shafe ta in ba haka ba zan fasa miki baki . Na ga fitar Major a fusace shima karyar kika yi masa ? Kin san halinsa ai. Ku ci gaba . "
Ya ja motarsa da gudu ya fice, ya bar ta anan a tsaye tana makerketa. Masu gadi kawai take kallo ta ji su na bata shaawa ina ma ta zama su don rayuwarsu ta fi ta ta kwanciyar hankali da walwala. Tabbas bala'in da ya tunkaro su ba a san iyakarsa ba . Ubangijin da Zai kare ta Shi ya umarce my da mu fadi gaskiya duk runtsi dan haka Shima sun yi masa laifi.


London


" Mummy! Mummy !! ki amsa min waya dan Allah ke kadai kika rage min a duniya " Na'ila take fada cikin kuka da hawaye faca-faca, a lokacin da take kira tana sake kiran mahaifiyarta fiye da sau ashirin amma ta qi ta amsa. Karshe ma ji ta yi an katse wayar, da ta kara kira ta ji an kashe wayar gaba daya .


Ta dora hannu aka ta fasa kuka mai tsanani , wayarta ce ta fara ruri ta suro da sauri a tunaninta zata ga sunan Mummy sai ta ga sunan Siyama.


Ta yi kamar ba zata amsa ba sai ta zabura ya dauka .


"Siyama na kashe kaina da kaina . Mummy ma bata amsa min waya ba tun ranar da suka tafi ." Na'ila ta fada cikin rugugin kuka.


Siyama ta face majina da hankici ta " Na'ila na mutu kin kashe ni nima . Yau na rasa Major Abubakar na yi masa qarya. Ke kuma kin rasa Engr. Muqaddas kin yi masa qarya. Mun rasa mazan aure. Kada ki tafi ko bar ni gani nan zuwa London din mu Shiga duniyar tare babu yadda Zaa in iya rayuwa a cikin mutanen nan kashe ni zasu yi. " Siyama na gama fada ta kashe wayar, ba tare da ta jira masa daga Na'ila ba , don ta gama yanke hukunci bata neman wata shawara kuma .


Babu sauran kuzari a jikin Na'ila tana kwance akan kafet din gaban gadonta ne a lokacin da take rubuta wani sako mai firgitarwa ta wayar hannunta. Dakyar take ganin kalaman da take jerawa.
Ta na rubutawa mahaifiyarta da mahaifinta sako ne, sakon dai iri daya ne . Da farko ta nemi gafara a wajen Mahaliccinta Allah , ta Allah gafara a wajensu iyayenta, Sannan ta ce su nemar mata gafara a wajen Yayyanta guda bakwai , neman gafara a wajen masoyinta mijin da zata aura Engr . Muqaddas. Daga yau sun rasa ta . A cikin daya Zaa yi biyu:

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads