Showing 27001 words to 30000 words out of 227252 words
Chapter 10 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
kafeshi da idanuwanta da suke a hargitse.
Shiru yayi ba tare da ya bata amsa ba har ta fara tsire tsammani da amsawar tana kokarin sake magana taga ya motsa laɓɓansa.
"Barci take yi".
"Har yanzu bata tashi ba?".
Ta sake tambayarta domin lokacin da ta bar asibitin a cikin halin barci ta bar ta.
"Ta farka ta sake komawa".
Mariya ta fara motsa laɓɓanta ta na son yin magana sai ga Dr.Aqeel yayi Sallama garesu amsawa sukayi Mariya tayi masa Sannu da zuwa. Murmushi yayi kafin ya ce,
"Mariya har kin dawo kenan. na zo dazun Abban ki ke cewa dani kin je gida".
Gyada kai tayi gami da kalato Yaƙe ta ajje a fuskarta.
Shiru ne ya tsake ziyartar wajan ba wanda ya sake magana sai ajiyar zuciyoyi dake fiddo da sauti sosai lokaci yaja a tsakanin su har zuwa lokacin ba wanda yake kokarin tsinkawa.
Dr.Aqeel da ke tsaya hannunsa rike da wani File yana dubawa bayan ya gama ya dube su.
"Hala ciki da zafi kuka zauna a nan?".
"Ko daya Likita kawai gani nayi tana barci na fito nan na zauna".
Gyaɗa kai kawai yayi bai sake magana ba ya juya bayan yayi musu sallama ya tafi.
Mariya ta bishi da kallo sosai halin Dr.Aqeel ke burgeta natsuwarsa gami da karamcin sa yana kara mata mutuncinsa a idanunta sosai take ganin girmansa tabbas ta yarda ba duk mutane bane suke iri daya a duniyar nan ta yarda halintar Dan-adam daya ne amma halin kowanne ya bambanta ba ta taba tsammanin za su samu mutum mai karamci da taimako irin Dr.Aqeel a da can ta dauka kowa ba mai kirki bane ashe da bambanci.
"Amma Mariya naga kin jima kafin ki dawo ina kika tsaya?".
Bello ne ya katse mata tunanin zuccin da take yi da sauri ta dube shi tana faman gyada kai sosai ya kafe ta da idanu ganin halin da ta nuna hakan ya kara daburta mata tunani ta rasa amsar da zata baiwa mahaifin nata shin ta fada masa haduwarta da mutumin da ya kusan kashe ta tun lokacin ta bai yi ko kuwa...
"Kika yi shiru?".
Ya katse mata tunanin da ta afka.
"Uhmm dama ba abin da ya tsaida ni kawai dai wani ne...".
Sai kuma tayi shiru ta kasa krasaw domin yanayin da ta ga Mahaifin nata ya nuna sai tayi da nasanin sakin bakin da ta so yi domin ta san tabbas sai ya ji ba dadi in har ta fada masa.
"Wani mutum yayi me?".
Ya fada ya na kafe ta da idanu sosai hakan ya sanya ta shan jinin jikinta a dan daburce ta daga laɓɓatanta.
"Bakomai".
Shiru yayi yana nazarin maganar tata ya tabbata akwai wani abu amma da alamun ta na tsoron sanar dashi.
"Allah ya kyauta".
Abin da ya fadi kenan ya koma ya zabga tagumi.
'Ameen'
Mariya ta amsa ita ma a ranta gami da mikewa domin kai kayan da ta zo da su cikin dakin.
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA GOMA.
Dr.Aqeel zaune cikin Office din sa gabadaya hankalinsa ya ta'allaka ga File din dake gabanda yana dubawa tsayin lokaci ya shafe a haka lokaci-lokaci yana sanya biro a bakin sa yana cizawa kamar son samu wata amsa daga gareshi.
Kamar dag sama yaji ana knocking din kofarsa a hankali ya daga kai ya kalli kofar na yan dakiku kafin ya mai da File din ya rufe ya ajje shi gefe sannan ya motsa laɓɓansa.
"Yes Come in".
ya kafe kofar da ido yana jiran ya ga waye zai shigo sai da aka shafe yan sakanni kafin sautin murɗa kofar ya fara kaiwa kunnuwan Dr.Aqeel sako sosai yake kallon kofar har ta gama bude wani matashi me ya bayyana fuskarsa ba yabo ba fallasa ya shiga takowa har ya iso gaban Table din Dr.Aqeel tun da ya shigo yake bin sa da kallo kallon kamar na san ka amma na kasa tuna baya.
"Dr.Aqeel Munka'il".
ya fadi yana kokarin zama kan daya daga kujerun dake girki kusa da table din fuskarsa dauke da murmushi.
Sosai Dr.Aqeel yake kallon sa shi ma yana sakar masa murmushin yaƙe.
"Dr.Hisham Muktar Karami".
Wata irin zabura Dr.Aqeel yayi yana mai zaro idanuwa gami da sakin wata yan kara kadan.
"OH My God! Da gaske kake wai ko wasa ko a tunani ban kawo hakan ba".
ya fadi yana mai hanzarin baro in da yake zaune ya iso gareshi gami da kai masa wata irin runguma sosai suka sarke a junansu fuskokinsu dauke da murmushi da jin dadi da farinciki sosai sun jima haka kafin su saki juna har zuwa lokacin idanuwan Dr.Aqeel su na kan Dr.Hisham sosai yake kallon sa gani yake yi kamar ba shi ba.
"Please Zauna mana Dr.Hisham ashe rai kan ga rai a duniyar nan ko a mafarki ban yi tunanin zan sake ganin ka ba".
ya karaeshi yana kokarin isa wajan karamin firij din dake girke a can gefe.
"Hmm Dr.Aqeel kenan ka yada zumunci shiyasa sam ka man ce da in da nake".
shima ya fadi yana dariya yana bin cikin Office din da kallo yana mai murmushi sosai da sosai ya burge shi musamman tsayin da akayi masa komai nashi tsaf-tsaf dashi.
"Yaa Allah! stop saying wannan maganar ma cos ba ta dace ba sam ka fade ta kai kanka ka sani ba haka nake ba".
Dr.Aqeel ya fadi yana mai murɗe murfin robar Ruwan EVA mai rangwamin sanyi ya tuntula cikin glass cup din dake aje.
"Bismillah".
ba musu ya dauka ya kai bakin sa sai da yayi rabon cup din sannan ya ajje gami da ajiyar zuciya fuskarsa da murmushi yake kallon Dr.Aqeel wanda shima idanuwansa na kan sa.
"ka canza gabadaya kamar ba kai ga kayi kiba ga wani tumbi da aka ajje".
ya fadi yana mai kyalkyalar dariya
" ni da kai waye yafi zama kato ka dube ka fa Dr.Aqeel".
"Five years is not 2years fa wallahi".
Dr.Aqeel ya fadi yana mai harararsa cikin sigar wasa kafin dakin ya dau shiru na dan lokaci.
"gaskiya kam! na yarda tun da gashi nan nagani har ka kasa gane ni da alamun nan da shekara goma in ba ka ganni ba ko nace ni ne Dr.Karami ba zaka yarda ba".
"No ba haka bane wallahi, yanzu dai yakake ya kuma aiki ya bayan rabuwa?".
"Alhamdulillah mun godewa Allah kasan yanzu ina can Delhi ne acan nake aiki da wani Privter Hospital".
"Ba Shakka ka ji manya mu ku ga mu nan muna ta fama da asibitocin nakasarmu".
Murmushi Dr.Karami yayi kafin yace.
"nikam narasa abin da ke damun kasar tamu har yanzu jiya-i-yau ba abin da cigaba na a zo a gani da aka samu".
"Uhmm kai dai ayi sha'ani kawai Dr.Karami".
Sosai Dr.Karami ya kafe shi da ido kamar mai nazarin wani abu kafin ya murmusa.
"Ina Family?".
Ya fadi yana kafe shi da idanuwa.
Murmushi yayi shima yana gyaɗa kai.
"Har yanzu...".
"Ban yarda ba".
Da sauri ya tare shi.
"seriuos".
Shima ya fadi yana murmushi
Sosai Dr.Karami yake kallonsa kamar wanda bai yarda da abin da yace ba ko daya ke ba zai yi mamaki ba in ya yi la'akari da kansa wamda shima ko dam tsako bai ajje ba.
"Anya kuwa Dr.Aqeel kana nufin har zuwa wannan lokacin kai ma bakayi aure ba?".
Sosai Dr.Aqeel yake kallonsa yana nazarin maganarsa da yarda yake danganta kansa da maganarsa.
"kana nufin kai ma baka yi ba kenan?".
Gyaɗa kai yayi yana murmushin yake.
Kofar da aka banko ne ya sanya su saurin duban kofar Mariya ce ta shigo a hargitse sam ba ta lura da ko su waye a cikin office din ba idanunwanta gabadaya sun rikice bakin ta ba abin da yake ambata sai sunan Dr.Aqeel.
Duk kan su ido suka zuba mata suna kallonta sosai cike ganin tashin hankali cikin idanunwata da gangar jikinta sosai suke kallon yarda jikinta ke ƙarƙarwa kamar wacce aka tsamo daga kogi Dr.Aqeel ya mike da sauri domin shi yasan komai akan Mariya rike yayi sosai da hannunsa yana faman kiranta amma ina tashin hankalin da take ciki duk ya tafi da yan guntuwar natsuwarta.
"Yaa Allah Mariya me kuma ya faru ne?".
Sai a lokacin ta lura da Dr.Aqeel da ke rike da ita sosai take kallonsa idanuwanta sai faman zubda kwalla suke bakin ta na rawa tana faman ajje zuciya.
"Ummata Dr. Don Allah...".
Sai ta rushe da kuka sosai hakan ya kara rikita Dr.Aqeel da sauri ya fara kokarin jan hannunta.
"Dr. Aqeel What is wrong with her?".
Dr.Karami ya fadi yana mikewa tsaya ya fara takowa har ya iso gabansu sosai yake kallon Mariya tun daga yatsun kafarta har izuwa cikin kwayar idanuwanta da sauri ya kau da kansa ya mai da idanuwan ga Dr.Aqeel.
"Tell me now Please what is wrong with her".
ajje Numfashi Dr.Aqeel yayi kafin ya dubi Mariya sosai yaji tausayinta na kara samun mazauni azuciyarsa.
"Dr.Karami wallahi mahaifiyarta ne ke cikin Matsala".
Da sauri Dr.Karami ya dubi Mariya wacce a lokacin ta tsagaita da firgicin da take yi na tashin hankali sai faman ajje numfashi take kamar wacce tayi gudun famfalaƙi sosai yake kallonta wasu abubuwa ne wanda bai dan ina suka dosa ba suke sukuwa cikin zuciyarsa sosai yake jin tausayinta a zuciyarsa tun kafin yasan abin da yake dawainiya da duniyar rayuwarta ita da mahaifiyarta yarinya ce karama wacce ba zata haura shekaru sha biyar ba amma yanayin ta ya nuna tana cikin MATSALAR RAYUWA ba kadan ba daga yanayin ta zaka gane haka.
"Meke damun mahaifiyar ta ta?".
Dr.Karami ya fadi yana sauke idanuwansa kan Dr.Aqeel.
"eclampsia take fama dashi wallahi haihuwa tayi to tun bayan haihuwan lamarin ya afku".
Gyaɗa kai ya shiga yi yanayin fuskarsa na sauyawa sosai da sosai tausayi da jin ƙai duk suka kara bayyana sosai.
"Tana ina yanzu haka?".
"Tana cikin Asibitin nan a kwance yau kimanin sati uku kenan da faruwar abin amma lamarin sai a hankali nayi iya bakin kokarina amma abun ya ci tura domin abin kara hauhawa yake yi".
"Yaa Allah!".
Dr.Karami ya fadi yana mai dafe kansa sosai yaji wani iri a game da abin da Dr.Aqeel yace dashi sosai yaji yana son ganin matar yana ji a ransa zai iya taimaka mata domin kuwa yana cikin fannonin da yake aiki akai.
"Muje na ganta".
Abin da yace kenan ya fara taku yana kokarin ficewa daga Office din kamar ya san in da dakin mara lafiyar yake da sauri Dr.qeel yaja hannun Mariya suka bi bayansa sannu a hankali har suka isa dakin da Habeeba take suna shiga suka tadda ita tayi firgai-firgai da ita alamun ya nuna duk ta hargitsa kanta amma izuwa wannan lokacin tayi lakwas ta hada jikinta waje guda ta saka laɓɓanta cikin baki sai faman cizawa take yi da sauri Dr.Karami ya isa gareta hannunta ya kamo gami da sauri ta fizge ba tare da ta kalleshi ba ya sake kai hannunsa ya kamo hannunta nan mata ta shiga kokarin fizgewa amma rikon da yayi mata a wannan karon bana wasa bane hakan bai bata damar kwace kanta ba illa dago idanuwanta da tayi ta watsa masa su sosai ya shiga karantar komai nata tsayin wasu dakiƙu kafin ya sake ta ya dubi Dr.Aqeel da Mariya da suke tsaya suna kallon duk abin da yake yi.
"yanayin ta ya nuna abun yayi karfi sosai a gareta wanda hakan ya kusan zame mata tamkar hauka ta gaskiya ya kamata ace ta samu kulawa sosai da sosai a wannan matakin".
Dr.Karami ya fadi Dr.Aqeel ya ja numfashi.
"ka ga dai yanayin asibitin namu Dr.Karami ba komai bane ake samu a cikin sa wai don ma ina cikin sa ne ka gan sa a haka nayi iya bakin kokari akanta amma abin ya so ya faskara".
Gyaɗa kai yayi cikin yanayi na gamsu da maganarsa ya san Dr.Aqeel gwani ne kuma jarumi ba zai ga gazawarsa ba a fannin aikinsa domin yasan kwarewarsa akan aikinsa sai dai matsalar da ya fara lura da ita a nan ita ce rashin kulawa daga gwamnati da kuma rashin wadatartun kayan aiki da babu dole duk wani likita ya fuskanci kalubale sosai a fannin aikinsa in har asibitin da yake ba kayan aiki numfasa yayi a ransa yace,
'dadin kasashen waje kenan kumin kankantar Asibiti ba zaka rasashi da kayan aiki ba amma ban da kasarmu ta najeriya komai na su sai ka ga ragwanci a ciki'.
Amma a zahiri sai yace,
"Shikenan Dr.Aqeel ina son wannan lamarin ya dawo hannu na nayi maka alkawari nan da KWANA SITTIN in Allah ya yarda zan yi iyakar bakin kokari na don ganin komai ya zama Normal".
Dr.Aqeel yayi shiru yana kallon sa yasan ALHERI irin na Dr.Karami tun suna tare acan kasan America ya san shi farin sani mai taimako da jin kai ba wannan bane karo na farko da yake taimaka masa a aikinsa sosai yaji dadin abin da yayi masa fuskarsa da murmushi ya dube shi.
"Anya za ayi haka daga zuwan ka Dr.Karami zaka daukarwa kan ka aiki ko hutawa baka yi ba please leave it I'll do my Best to Help her...".
"Please Dr.Aqeel stop saying that, ka bar ni kawai nayi, ai ni nace naji na gani ko, sai dai ban sani ba ladar ce kila baka so na samu kaso na nima".
ya karashe yana mai murmusawa alamun joking cikin maganarsa.
Shi ma Murmushi yayi masa gami da gyaɗa kai.
"But at Now zan je gida na huta kafin zuwa gobe na zo domin gudanar da komai".
"Bakomai Dr.Karami ko sati kace zakayi ai ba zan haka wannan damar ba".
Duk kan su sukayi dariya gami da yin musabaha.
Mariya tun lokacin da suka iso cikin asibitin ta ke gefe tayi musu kuri da idanuwa tana jin maganganunsa sai dai wani lokacin ba ta jin turancin da suke jafawa cikin zancen nasu sosai take mamaki musamman ganin Dr.Karami da yarda lokaci guda ba tare da sanayya a tsakani ba ya bada lokacin sa har yake ikirarin taimakawa mahaifiyarta tabbas na Allah ba sa karewa a duniya nan ba ta taba zaton zata samu mutane masu imani irin haka ba wanda za su ji kansu ba tare da sun san su suwaye ba tabbas ta kara gasgata maganar mahaifinta akan DAN-ADAM ba duk bane halayen su daya suffa ce kawai ta kasance iri daya ba ta dan lokain da wani guntun murmushi ya suɓuce mata ba mai dauke da hawaye hannu ta saka tana dauke su a daidai lokacin Dr.Karami ya sauke ganinsa akanta sosai ya kureta da idanu yana kallo kamar wanda ya ga wata sabuwar halitta sosai Mariya ta kaɗu da irin kallon da ta ga yana yi mata da sauri tayi kasa da kanta gabanta na bugun uku-uku ba kadan ba ta tsorata da kallon da yake mata ta shiga nazarin dalilin kallon nashi akan me yake mata kallo ko ya san ta ne a ina? da sauri ta girgiza kai domin bata tsammanin ya taba ganin mai kalar hauka irin ta firgitacciya sosai ta saka a ranta daga ganinsa dan kasar waje ba dan najeriya bane domin irin yanayin da ta ganshi fes-fes kuma muryarsa bata fita sosai kamar na Dr.Aqeel haka ya kara tabbatar mata kila ba bahaushe bane
"Excuse me. whats is you Name?".
Ya fadi yana murmushi a fuskarsa gabanta taji ya fadi domin ta tabbat da ita yake magana abu daya ta fahimta a maganarsa wato tambayar da yayi mata sunanta wannan kalmar tambayar kuwa ta ji ma da haddace ta a kwakwalwarta domin tun tana Primary ta san abin da furucin ke nufi a hankali ta dago ta kalle shi sannan ta kalli Dr.Aqeel wanda shi ita yake kallo da alamun jiran abin da zata ce yake yi domin irin kureta da yayi da ido amma da murmushi a fuskarsa a hankali ta motsa Laɓɓanta.
"Mariya".
Dr.Aqeel da ya yi kasaƙe da baki sai gashi ya zaro ido mamaki da al'ajabi ya cika shi da yaji ta ambaci sunata da alamun ta fahimci abin da Dr.Karami ya tambayeta sosai ya shiga tambayarsa kansa yarda akayi har ta iya bada amsa sam bai yi tunanin za ta iya ba bai yi tunanin ma ta taba shiga aji da sunan daukar karatu ba ganin yanayinta mamaki ya hana shi sakat har sai da ya dubi Mariya yace,
"dama kin iya turanci ne dama kina makaranta ne?".
Sai ta taji wani iri a ranta ji irin tambayar da yayi mata wato kallon BAGIDAJIYA yake yi mata ma rashin ilimi dakikaya yar kauye sosai taji ranta ya sosu wato shi tunanin sa saboda rashin babun sa yana tunani ya hanata shiga aji har ta nemi ilimi gyada kai kawai tayi gami da kau da idanuwanta daga gareshi gabadaya ta mai hankalinta wajan kaninta dake kwance yana faman barci cikin kwanciyar hankali yaron da aka yiwa Huɗubar suna Ibrahim wanda suke kira Mu'azzam cikin asibiti saboda tashin hankali da suke ciki...
"kiyi magana mana".
Dr.Karami ya fadi ganin ba ta da niyyar cewa komai kallonsa tayi a hankali ganin murmushi a fuskarsa wanda ta lura kamar hakan a jininsa yake yawan fara'a wanda hakan ke kara masa kyau matuka gaya.
"Eh ina makaranta aji na biyu a sakandiri...".
"A haka din?".
Dr.Aqeel yayi hanzarin katse ta da fadin haka yana nuna ta da hannu cikin alamu da mamaki sosai a ransa.
"Masha Allah!".
Abin da Dr.Karami yace kenan ya kastewa Dr.Aqeel hanzarinsa ta hanyar cewa su tafi sai da suka sake duba Habeeba wacce a wannan lokacin ta daina komau da take yi har da cizon laɓɓanta a tausaye sukayi wa Mariya Sallama suka bar cikin dakin.
Ajiyar numfashi Mariya ta saki gami da zamewa ta zauna kasa kamar wata kayan wanki ta zabga tagumi hannu bibbiyu tana faman kallon mahaifiyarta da kaninta Mu'azzam a wani sashin na zuciyarta kuwa Dr.Karami ne da Dr.Aqeel tana ji ba dadi akan yanayin da Dr.Aqeel ya nuna akanta yarda ya nuna yana mamaki da tace masa tana makaranta me yake nufi da yanayin da ya nuna kenan yana nufin 'ya'yan talakawa marasa galihu basa makaranta ne ko mi yana zaton rashin 'yancin 'ya'yan talakawa har ya kai suka sa yin makaranta su zauna cikin duhun jahilci to tabbas yayi kuskure in har haka tunaninsa ya bashi bai san masu son yin karatu ba bai son masu burin yin karatu a duniyar 'ya'yan takalawa ma naso sai dai babu ita ce take zame musu katanga da karatu.
Haka Mariya ta zauna tayi ta zancen zuci har zuwa wani lokaci.
******
Dr.Karami cikin Motarsa Kirar 2019 Mercedes-Benz GLA yake tuki bayan ya baro Asibitin Baban Alis tafiya mai dan tsayi yayi kafin ya isa cikin garin Minna Unguwa Tunga daidai wani katafaren