Showing 30001 words to 33000 words out of 227252 words
Chapter 11 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
Get ya yada zango Horn daya yayi aka buɗe masa ya shiga tsararren gida ne sosai wanda ya ƙawatu da komai na adon gida ba abin da babu aciki can nesa kadan wajan Parking Space ya nufa ya ajje motarsa ya fito hannusa rike da wayarsa sai faman latsa ta yake yi da alamun kira zai yi kafin ya isa kofar da zata sa dashi da Falon gidan ya kai wayar kunnansa sakan ni kadan ya fara magana.
"Am so Sorry Engr.Dangi wallahi lokacin da ka kira ni ina driver ne shiyasa ban dauka ba But Now na dawo gida dafatan dai lafiya?".
Ya karashe maganar tasa da dora tambaya.
Daga can dayan barin yaji sautin murmushi ya tashi kafin ace dashi.
"Albishirinka".
"Goro fari tas".
ya fadi cikin sauri domin tun da yaji Engr.Dangi yayi irin wannan zancen yasan akwai kayan farinciki da suka wanzu kenan.
"Kayi Kani Dr.Karami".
"seriuos don Allah Engr. Dangi ban son joking irin naka wallahi tell me the True Please".
Sautin dariyar Engr.Dangi ce ta sanya Dr.Karami kara gasgata maganarsa.
"seriuos Wallahi Safeenat tayi maka kani yana nan mai kama da kai".
"Masha Allah nayi farin ciki gaskiya Allah ya raya ya dayyaba amma gaskiya Baby din nan bai iya zuwa ba sam sai da ya bari na baro garin sannan zai duro duniya mai makon tun dadynsa na can ya kamata ace ya zo".
Engr.Dangi yasa ke kecewa da dariya kafin ya ce,
"kai Dalla waye dadyn nasa kai kasan a matsayin kani yake a wajan ka ni ne dady wallahi domin ba wanda zai kalli tazuru irin ka yace masa Dady don haka becarefull".
In da sabo ya kamata ace Dr.Karami ya saba da tsiyar da abokin nasa yake yi masa na rashin aure domin in sau goma.za su hadu sai yayi masa gorin mata amma sam haka bai ɗaɗashi da kasa ya san komai nufin Allah shi kasan yana son yin auren But bai san dalilin da har yau bai ga matar da ta kwanta masa har yake tunanin zai iya zaman aure da ita ba yanzu in bai manta ba yana 32years kenan a girma ya girmi Engr. Dangi da kusan shekaru Uku amma gashi nan har ya riga shi aure har matar tasa ta haihu.
Gyaɗa kai kawai yayi ya shiga cikin falon bayan ya bude dakin sa ya dosa yana shiga ya ajje wayarsa da key dinda ya zare suit din dake jikin sa ya ajje sannan ya cire fara rigar mai dogon hannu ta cikin suit din ita ma ya ajje sannan ya cire dogon wando bayan ya cire takalmin kafarsa ya tsaya daga shi sai Boxer da singlet Toilet ya nufa ya watso ruwa bayan ya fito ya tsan jikinsa sosai da sosai jallabiya ya zurawa jikinsa mai ruwan jinin kare wanda tayi matukar dacewa da jikinsa sosai Coffee yaje ya samarwa kansa mai zafi sosai sannan ya dawo cikin dakin sa ya zauna kan daya daga kujerun dake dakin sosai da sosai ya nutsu yana shan Coffee din a hankali duniyar tunani ya je fa kansa wasu abubuwa da ya ajje can kasar zuciyarsa ya ji su yo masa sama yana sake maimaita su sosai ya shiga tunano Dr.Aqeel da abin da ya wakana a cikin asibitin sosai yake tuno yar matashiyar budurwar nan da ya jima yana nazarinta wanda ashekaru ba zata haura 15years gyaɗa kai kawai yayi gami da murmusawa.
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA GOMA SHA DAYA.
Sosai yake kaiwa da komowa cikin dakinsa, hannayensa sarke a kirjinsa, lokaci-lokaci ya kan ja tsaki kamar harshensa zai tsine. duk sanyin da A-C din dake dakin take bayarwa hakan bai hana gumi samon mazauni saman goshin sa ba.
Sosai ya cigaba da zarya a dakin cikin rashin mafita akan abin da ya addabi zuciyarsa sosai yake jin zafi da raɗaɗi a zuciyarsa da ruhinsa sosai ya ji komai da ya faru dashi kwanakin baya sun hanashi sukuni ya naji a ransa bai taba ganin 'ya mace da ta raina masa hankali ta ci masa mutunci kamar wannan kankanuwar ƴarinyar wanda ko a zaben mata aka saka ta ba in da zata kai labari kwaila ma irin ta wacce sam bata san Darajar da mace ke da ita a wannan duniyar rayuwar ba ta yanzu ba amma har ta dubi tsabar idon sa ta gaya masa haka.
"Noo Impossible".
Abinda ya fadi kenan cikin daga murya mai sauti yana faman kai wa kirjinsa naushi kamar a nan mai laifin take.
Kamar wanda aka tsikara haka ya zari Key din Motarsa ya fara tafiya cikin sassarfa kamar zai tashi sama a haka har yafice daga cikin dakin sosai yake taka benen da zai kai shi zuwa kasa sashin babban falon cikin gidan kallo daya zaka yi fuskarsa ka fahimci halin da yake ciki na kunar rai sosai yake zakar wani abu a ransa wanda yake da tabbacin shi kadaine mafita gareshi dole ya dauki mataki dole ya dan hukuncin da zai dauka dole ya nuna mata tayi kadan ba kowan kowa bace a cikin jerin mata ba ta kai Level din da zata raina shi ba ba ta kai matakin 'ya mace da zai kalla har ya yaba ta raina masa hankali ba da wannan sakar zucci har ya fice daga sashin cikin gida ya doshi Mota Parkig ya fara kokarin fiddo da motarsa komai yake yin sa a hanzarce haka ya figi motar mai gadi na ganinsa ya doso shi da sauri ya mike ya nufi Get din ya bude sosai yake kallon fuskar Huzaif yanayin da ya ganta sai da gabanda ya fadi sosai.
"Allah Yakyauta".
Abin da ya fadi kenan yana margaya kai ya mai da Get ya rufe bayan Huzaif ya fice.
Sosai yake gudu kan titi zuciyarsa na faman wassafo masa abubuwa ma bambanta sosai yake jin komai na zuwa masa a bazata wanda ya hakikance ba wanda ya assasa hakan sai wacce kwailar yarinƴar wacce ko kyautarta aka bashi ba abin da za tayi masa a rayuwarsa illah wahala.
Cikin mintin nan da ba su haura talatin ba ya isa Kofar Asbitin baban alis sosai yake kallon asibitin bayan yayi parking ya fito yana mai wasa da Key din motartashi gaban motar ya usa ya yi tsalle ya hau gabanta ya zauna gami da harɗe hannayensa duk biyu a kirji ya kure kofar asibitin da kallo yana tunanin abin yi domin shi dai zuciyarsa ce ta kawo sa amma bai san takamaiman abin da zai gudanar ba abubuwa biyu suke masa sukuwa da tunanin sa haushin Mariya da kuma son ganinta wanda duk ya ajje a hurumi daya wanda sam ba su da alaƙa da juna numfasawa yayi gami da zaro wayarsa daga aljihu yana shuga dandannawa kamar mai kokarin kira kamar wanda ya ga takaici sai kuma ya ja tsaki gami da maida wayar aljihunsa yana faman sakin numfashi.
*****
"na rasa me zan yi komai ya kwance mani".
Abinda ta fadi kenan tana tura laɓɓanta cikin bakinta tana faman ya mutsa fuska kamar wacce aka sanya shan magani.
Sosai yake kallonta da yanayin da take ciki na yanayin rashin kwanciyar hankali komai ya bayyana a fuskarsa na tsananin damuwa har zurmawa tayi kamar wacce ta tashi daga gudawa.
"na rasa ta ina zan miki bayani ki fahimta, na rasa mai zance miki wanda zai ganar dake komai da komai kin kasa daukar abin da nake fada miki, ya zan yi dake Mariya?".
gyaɗa kai kawai take yi tana faman dauke kwallar da taji suna kawo mata farmaki.
"Hakuri Dr.Aqeel. bani da komai da zai taimaka min domin samun natsuwa ta ka tuna yau kwanansa Biyar ban gan sa ba, yau kwanan sa biyar ban san a wani hali yake ba, dole dole ne na damu sosai da sosai zuciyata taki hakuri taki natsuwa".
Ta karashe cikin karfin hali kamar mai som fashewa da kuka kai ta cigaba da gyaɗawa.
"ban san abin da yasa yaki jin magana ta ba, ban san abin da yasa bai yi amfani da abin da nace ba komai da komai Dr.Karami yace zai amma yaki yarda da hakan".
Ya fadi yana kallon Mariya wacce gabadaya hankalin ta na wajan Habeeba wacce take sharar barcin ta hankali kwance kamar bata da wata matsala a duniyarta mai da kai tayi wajan Mu'azzam wanda shi barci yake yi. sosai take jin tausayin sa na damunta a rai sosai take tausayawa rayuwarsa.
Mikewa tayi ba tare da ta dubi Dr.Aqeel ba ta fara tafiya sannu hankali sai ka rantse rashin jini ne ke damunta.
"Uhmm nace ba".
Ya fadi yana mai kallonta cak! tsaya ba tare da ta juyo ba.
"ina zaki kuma?".
"waje zan fita".
ta bashi amsa tare da kara saurin tafiyarta don ba ta so ta sake furta ko da kalma daya ne gareshi
So take ta je waje ko za ta samu sa'ida a zuciyara ba wai ta yarda dari bisa dari bane a,a kawai dai zaman dakin ne ya fara gunduranta dalilin Dr.Aqeel ba ta son a daidai wannan lokacin ace maganar wani na ratsa mata kunnuwa tana bukatar natsuwa ko yaya ne amma ta lura Dr.Aqeel ba zai bata wannan damar ba sam! Ba ta san me yake nufi da ita ba ta rasa ina zata sa kanka ko yaya ne ta samu hutun rai da ruhi.
"MACE ƘYANƘYAWA".
Sautin muryaar da taji ne ya sanya ta katse tunanin da ta afka sosai gabanta taji ya bugu har sai da ta sanya hannu ta dafe tana ambaton 'innalillahi wa'inna ilaihir raji'un'
Sosai ta fiddo da idanuwanta waje tana mai sauke so akan sa sosai taji komai yana kwance mata cikin kwakwalwarta.
Gabadaya idanuwansu suka sarƙe sosai suke ƙallon junansu an rasa mai dauke kallonsa daga dan'uwansa fuskar Huzaif ba abin da take saki sai murmushi sabanin ta Mariya da take a cungune waje daya kamar wacce aka aikowa da mutuwar wani cikin dangi
A hankali ya fara kokarin saukowa daga kan motar shi yana faman sakin murmushi wanda daka gan shi kasan akwai alamun tambaya akan sa.
Sosai yake tunkaro ta gabanta na sake tsananta faduwa komai take ji na kanta na wargaje mata ba abin da zuciyarta keyi sai ɗaci sosai.
Ba ta son ganinsa, bata muradin ganinsa cikin duniyar rayuwarta, ylta tsani shi a zuciyarta tun daga kalaman sa take jin wani irin ɗaci tun daga kasar ruhinta a dalilinsa sai dai wani bangare na zuciyarta sam yaki kin yarda da Huzaif domin kullum cikin tono mata sunan yake.
"Yaa Allah!".
Ta fadi tana mai haɗe laɓɓanta waje tana cusa su cikin bakinta a hankali take daura hakoranta akai tana dannawa kanta a kasa tana jin saukar numfashin Huzaif kusa da ita hakan yakara tsinka mata zuciya ji take kamar ta kurma ihu don haushi.
"wai ke mai yasa kullum in za a ganki, sai an ganki tare da kunci ne?".
Ya fadi yana kallonta sosai yana kallon yanayin Emotion dinta da ya sauya lokaci guda yana kallon yarda fuskarta ke wanzar da haushi da ƙi kuma ya tabbata akan sa ne Murmushi ya saki ganin tana kokarin barin wajan ya kai hannu ya riko mata nata hannu.
Ai ji tayi kamar an daura mata garwashin wuta a hannun nata nan da nan jikinta ya dau wani irin Shock har sai da komai ya motsa a jikinta da sauri ta dago kanta sosai take kallon Huzaif da rinannun idanuwanta ji take kamar ta tsinke shi da mari don takaci da bakin ciki bakin tane ya fara motsi alamun son magana laɓɓanta dake cikin bakinta har wannan lokaci ta shiga motsa su.
"Don Allah ka rabu dani!".
Ta fadi cikin murya mai sauti da karamar tsawa a cikinta tana mai dauke kallonta daga gareshi bayan ta watsa masa wani mugun kallo.
Sosai yake mamakin yar mitsilar yarinyar nan, da yarda take yin komai nata cikin rashin tsoro ko fargabar abin da zai je ya dawo ya lura akwai tsoro a zuciyarta sai dai bata barinsa yayi tasiri a zahirinta ba.
A hankali ya saki hannunta da ya rike gami da jan guntun tsaki mara sauti amma hakan bai hana Mariya ji ba ko kallonsa ba tayi ba amma ta lura yaji haushin abin da tayi masa gyaɗa kai tayi ta fara hanzarin barin wajan amma maganarsa ce ta sanya ta saurin tsayawa.
"mai yasa baki son mai sonki da alheri, na lura wani naki ne bashi da lafiya amma kin ki bani damar da zan samu ikon duba shi, ko da yake ban san abin da kike tunani akai na ba ni dai ban dauke ki na ajje a zuciyata ba akan wani mugun nufi sai dai na ajje ki a zuciya a dalilin tausayinki da jin kai".
Sosai maganganunsa suka shiga shigarta ta ko ina sosai take jin sautinsu na haifar mata da wasu lamura a kasar zuciyarta sosai take jin tasirinsu a kasar ruhinta sosai zuciyarta ta fara kokarin gasgatawa tunaninta ya karbi lamarin a saukake sosai take ajje numfashi a duk wani kalma daya da ya furta a hankali ta fara kokarin kallonsa idanuwanta a dan tsuke bata bari tasirin maganganunsa sun fito zahiri ba ta fara motsa laɓɓanta.
"bana tsammanin zan yarda waki bugun ya sake gintawa a tsakaninmu kasan ance dukan farko shine duka kuma ka lalata damar ka tun a karo na farko don haka ina mai rokan ka ka fice mani daga rayuwa bana so komai ya faru tsakanina da kai kaji ko kawai ka kama gabanka kowa yayi rayuwarsa ba abin da ya hada kifi da kaska balle kuma har su da zauna inuwa daya".
yanayin yarda ta ajje furucinta cikin halin-ko-in-kula yayi matukar kara zafin zuciya gareshi sosai yake kallonta yana jin rashin wayon da ya nuna akanta har ya tsaya yar yarinyar nan na fada masa abin da ta so a ranta tsaki yaja sam bai lura ta wuce ba sai da ya fara motsa baki yana son yin magana sannan ya lura bata wajan naushi ya kai sa iska gami da cizon Laɓɓa sosai ya ke kallon kofar aasibitin domin ya hango shigarta sosai zuciyarsa take shiga kunci a hankali yana mamakin yarda akayi yake wahalar da kansa akan wannan halintar wanda ko a farkinsa ban yi zaton zai ganta har ta samu damar shiga rayuwarsa ba dole ya san abin yi dole ya dau mataki akanta domin tsana yake hangowa tasa a idanunta ya tabbata ta tsanshi haushi sa take ji a ranta har a bayyane a fuskarta.
"l'm Huzaif!".
Ya fadi yana nuna kansa da dan yatsansa yana mai sakin murmushi gami da gyaɗa kai ya juya ya koma motarsa da gudu ya fuzge ta ya bar harabar asibitin.
*****
Sosai Dr.Karami yake aikinsa cikin kwanciyar hankali da kware a harkar cikin kwanaki talatin da biyar komai ya fara kamo hanyar samun waraka ga Habeeba ba wai Mariya kadai ba hanta su Dr.Aqeel sunyi matukar yin farinciki da hakan domin sosai suke ganin komai na zama Normal izuwa wannan lokaci Habeeba ta fara samu sauki sosai don yanzu duk na fizge fizge da rashin magana ya kau sai da lokaci-lokaci in kana hira da ita tana kau ce hanya cikin hirar zaka ji tana wani zance na daban wanda bashi kuke yi ba hakan ya so damunsu Mariya sai dai Dr.Karami yana kwantar musu da hankali gami da sanar da su dole hakan sai ta faru gareta a hankali komai zai daidaita kamar bata tabayin cutar ba.
Kamar ko yaushe yau mariya ce zaune ita da Dr.Karami suna hira domin shakuwa ce ta shiga tsakaninsu sosai da sosai Mariya tana matukar girmamashi gami da kunyarsa hakan yasanya Dr.Karami yake jinta a ransa sosai take burgeshi komai nata yanayi masa musamman da ya lura tana da hankali gami da natsuwa sosi a rayuwarta gata da gamun kai.
Dr.Karami ya numfasa bayan ya gama wayar da yake yi ya dubi Mariya da take ta faman wasa da Mu'azzam dake hannunta shikuma yana faman ƙyalkyala dariya.
Murmushi yayi yana gyaɗa kai kafin ya motsa laɓɓansa.
"Na lura sosai da sosai ki ke son Mu'azzam, anya za ki iya rabu dashi kuwa in wani abu ya taso na zuwa wani waje".
Kasa tayi da kai alamun jin kunya sosai ya kureta da ido.
"kin fiye kunya Mariya anya kuwa".
ya sake fadi yana dariya.
A hankali ta dago kanta ta kalle shi sannan ta ajje kallonta gefe.
"Uhmm Dan'uwana sosai nake son sa ban son rabu dashi ko na sakanne".
"kenan yanzu ko lokacin aurenki yayi ba zaki iya rabu dashi ba a matsayin ki na 'ya mace yar gidan wani".
Ji tayi kamar ta tsune kasa don kunya dalilin aure da ya ambata gabadaya sai ta rikece sai motsu motsu take yi ta rasa abin yi gabadaya.
"wai shin ina zancen makarantarki ya kwana ya kamata ace kin koma makaranta Mariya zaman haka ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba ke 'ya mace ce sosai karatu ke da muhimmanci a rayuwarki ya kamata ace kin mai da hankali sosai zuwa ga karatun ki ita ce dama daya jal da kike da ita ko don taimakawa iyayenki wata rana kece babba ko da dai ke yar gidan wani ne amma duk da hakan kiyi karatu".
Sosai kalamansa suke samun masauki a zuciyarta sosai take jin dadin yanayin furucinsa cikin sanyin murya mai cike da karfafawa zata so ace hakan ta kasance gareta zata so ace ta samu wannan damar za ta so ace tayi karatu na sosai da sosai domin ta lura karatu a rayuwar zamanin nan yana da muhimmanci sosai musamman 'ya mace ko ba don komai wasu abubuwan na rayuwa da suke gudana a duniyar nan ya kamata ace mata suna samun wannan damar domin wasu fannonin 'YA'YA MATA ya kamata ace a wajan ba maza ba musamman harkar likitanci ko ba komai taimako ne na al'umma ku hakan zai wuce takaicin da wasu ke yi wa mara hali a rayuwarsu.
Sosai take jin tausayin kanta da na iyayenta da kaninta Mu'azzam ta sani ƙaddara ta fado rayuwarsu gami da talauci da ya hana su gudanar da wasu abubuwa sosai da ya kamata ace sunayin sa ba wai rayuwar jindadin duniya take nufi ba a,a wasu abubuwan a rayuwar dangin rai dole yayi a karan kansa ba wai sai ya tsaya wani yayi masa ba musamman duniyar zamanin nan a yanzu in baka dashi ba mai yi da kai balle ya ya jikanka ta sani a duniyar nan in baka dashi kai