Header Ads
Showing 210001 words to 213000 words out of 227252 words

Chapter 71 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1374

Ads at the middle of Article

akayi mata a bainar jama'a sai ta sake rushewa da kuka kamar numfashinta zai dauke a soro suka ya da zango Abulle sai mai da numfashi take yi ita kuwa Hafsat zubewa kan gwuiwowinta tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana hadiyar zuciya sai shassheka take yi idanuwan nan nata sunyi luhu-luhu jikinta na faman kyarma.
"Ya isa haka Hafsat dai na kukan fada min abin dake faruwa?".
Dago jajayen idanuwanta tayi ta sauke su kan Abulle cikin wani irin yanayi muryarta na rawa ta shiga bata labarin abin da ya faru da ita a yanzu...
Wani kuka ne ya sake kufce mata ta rarrafo ta riko mata kafa.
"Don Allah Umma ki yafe mani na tuba wallahi ba zan sake ba ina cikin bala'in rayuwa ita cikin kazamar rayuwa wacce ni ne na zama silar faɗawa cikin ta don Allah ku yafe mani abin da nayi muku na san ban kyauta muku ba a matsayin ku na iyaye na...".
Da sauri Abulle ta toshe mata baki tana mai duba kofar gidan da soron gidan ganin ba kowa ya sanyata duban Hafsat wacce gabadaya ta fice daga hayyacinta.
"Hafsat kukan ya isa haka nan kiyi shiru karki haifarwa kanki da wata matsalar ciki ne a jikinki wannan kukan kuma da kike yi kina ta da hankalin ki sai ki fuskanci matsala...".
"Nafi kaunar in shiga matsalar da zan mutu akan wannan rayuwar da nake yi na tsani wannan rayuwa na tsani wannan duniyar na tsani kaina...".
Da sauri ta rufe mata baki ita kanta 'yarta ta tausayi take bata kwalla ne suk cika mata idanu da sauri ta kau da kai ta dauke su ta janyo Hafsat jikinta.
"Ya isa haka ki daina fadin haka komai da kika ga yana samun bawa a duniyar nan ƙaddararsa ce haka...".
"A,a Umma wallahi ba ruwan kaddara ni ne sila komai da yake faruwa dani ni ce sila kiyi hakuri Umma ku yafe mani na gaji da rayuwar nan nafi kaunar mutuwa da wannan rayuwar na san ko a wajan Allah ni mai laifi ce nayi abun da yake fushi dani nayi abin da ya kauce hanyar addini na kaico! Umma nasan na aikata kuskure Umma duk abin da kika ga yana faruwa Goggo ce sila ita take sanya ni".
Da sauri ta sake rufe bakinta tana mai girgiza mata kai.
"Nace kiyi shiru ko bana son jin komai daga gareki...".
"Umma ki bari na fadi domin ni dai na san rayuwata ta kare gwanda na fadi komai domin ki rokar min afuwa wajan mahaifina da wanda ya zama ina da hannu cikin faɗawarsu hukubar rayuwa".
Nisawa tayi tana mai da numfashi kafin ta gyara zaman da tayi dirshan akasa ɗan cikinta take ji yana ta faman juyawa yana tokare mata kirji laɓɓanta ta ciza gami da runtse idanu hakan da Abulle ta gani ya sanyata ware idanu tana tambayarta ko lafiya amma ta kasa bata ansa sai da ta dauki lokaci a haka kafun ta nisa wasu zafafan hawaye suka zubo mata.
"Duk halin da su Mariya suka shiga da Ummanta Goggo ce sila haka bacewar Abban su Mariya Goggo ce sila ita taja ni muka je wajan wani mutumi a dajin kauyen Sulalla akayi masa kurciya...".
"Innalillahi wa inna ilair raji'un".
Abin da Abulle ke maimaitawa kenan tana dafe kanta da take jin yana kokarin rabewa biyu lokaci guda idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir wata irin tsanar kanta take ji tana tsanar zaman ta a duniyar nan a daidai wannan lokacin wani takaici ne da bakin ciki ya turnuke ta bata san tsanar da Goggo tayi ma su Bello har ta kai haka ba ta san kiyayyar da take masu takai haka ba.
Mikewa tayi kan kafafuwanta tana duban Hafsat kafin ta fidda hannu cikin zafin nama ta dauketa da Mariya hagu da dama har sai da ta tuntsira ta bugu da bango hancinta da bakinta duk sun fashe suka dinga zubda jini da sauri ta ja jiki zuciyarta na suya ta fice daga cikin soron zuciyarta take ji tana kara ya mutsewa gabadaya taji ta tsani zaman ta a duniyar ina ma numfashinta zai dauke ta rabu da wannan takaicin da bakinciki da uwarta da 'yarta suka cusa mata a zuciya.
Hafsat ganin yarda Abulle tayi mata ta sake rushewa da kuka tana hada kanta da bango kamar ba a jikinta yake ba sai da tayi kuka ma ishinta sannan ta mike tana faman hade hanya ta nufi cikin gidan.
********
Fizgo shi yayi suka isa kofar gidan sai faman cin magani yake yi Alhaji Abdurrazaq ya kwala sallama hannunsa rike da Huzaif da gabadaya ya gama kumbura ji yake yi kamar ya fashe don takaici da bakin ciki wai mahaifinsa ya yi masa irin wannan cin zarafin akan wata banza wacce bai ganin ta da wata kima ko daraja.
Abban su Mariya ne ya fito yana duban su daya bayan daya don bai san su ba Alhaji Abdurrazaq ne yayi masa sallama ya ansa shi cikin yanayi na son karin bayani.
"Kai ne mahaifin Hafsat?".
Bello ya gyaɗa kai yana duban Huzaif ganin yarda aka riƙe shi kamar wanda yayi sata shi abin har dariya ya so ya bashi.
"Sunana Alhaji Abdurrazaq ni ne mahaifin Huzaif wanda ya ci zafin 'yarku ya keta mata haddi".
Zaro idanu yayi sosai yana duban su zuciyarsa yake ji tana bugawa da sauri-sauri wani takaici ya kume shi da sauri ya juya cikin gidan dakin Goggo Marka ya nufa ba ko sallama ya shiga tadda ita zaune yayi ta hada tagumi can gefe kuma Hafsat ce ta dukunkune sai faman numfashi take ja tana saukewa.
"Kunyi baki ku taho suna jiranku"..
Yana fadin haka ya fita daga cikin dakin zuciyarsa na raɗaɗi gami da zafi ya jima yana takaicin wannan lamarin tun lokacin da ya gane wa idanuwansa ya tambaya amma Goggo Marka ta so ci masa mutunci tun daga wannan lokacin bai sake magana ba sai dai yaje har gidan Abulle ya hadu da mahaifin Hafsat suka zauna sukayi magana a nan ya san komai yayi bakin ciki sosai yayi takaici.
Tabarma ya dauka yanufi soro da ita ya shimfiɗa sannan yayi musu iso har lokacin Huzaif na hannun mahaifinsa ya ki sakin sa zama sukayi amma shi Huzaif ya tsaya kerere a tsaye a daidai lokacin suka iso su kuma Hafsat tun da ta hango huzaif ta ji gabanta ya yanke ya fadi wani kallo ta ga ya watsa mata ita ma kallon ta watsa masa daga nan ta kau da kai.
Alhaji Abdurrazaq ne ya muskuta ya dubi Goggo Marka da tayi wiri-wiri da idanu sai hada gumi take yi abi duniya duk yabi ya addabeta.
"Maganar da mukayi kwana ki dake na cewa zan aurawa ɗana jikarki domin kuwa cin zarafin da yayi mata ba zan yarda dashi ba domin ba zan yarda ko 'yata ayi wa haka ba don haka shine nake so ku bashi aurenta domin ba wanda zai aureta bayan shi in kuma ba ku yarda ba ni zan shigar da wannan maganar kotu kuma zan tsayawa Hafsat kai da fata har in ga an kwatar mata hakkinta".
Bello ne ya dube shi sosai yanayin sa ya burgesa yarda ya nuna ba yarda ba akan cin zarafin da ɗansa yayi wa Hafsat ba ya ji dadin haka sosai ko ba komai ya nuna shi mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata duban Goggo Marka yayi kafun ya kau da kai.
"Ba sai maganar taje kotu ba ni ina bayanka nima a matsayin uba nake ga Hafsat in dai ta haihu ni na aminci ya aureta sai dai kuma magana daya akwai sharaɗi na lura kamar dole kayi wa ɗan naka don haka zan masa gargaɗi in har ya aureta ya ci zarafinta ko ya kuntata mata wallahi tallahi ni da kaina zan shigar da maganar nan kotu sannan a sake tada tsohon duk wani cin zarafi da yayi mata".
Wani kuka ne ya zo wa Hafsat mikewa tayi ta dubi Huzaif da yayi tsiru-tsiru da idanu sosai take jin har yanzu tana son sa bata jin zata iya rabuwa dashi duk da abin da yayi mata son sa ya zama jinin jikinta wanda hakan har yanzu ya kasa sanyata ganin laifinsa duban su tayi dukkan su kafin ta ja kafafuwanta da sukayi mata nauyi ta shige cikin gida....






*Kamala Minna*💞💞😘😘
[10/26, 9:20 AM] DEENY MINNA🙋‍♂:  UKU BALA'I


NA.


KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.




BABI NA SITTIN DA BAKWAI.


Gumi ne kawai ke ta faman keto mata kamar wacce aka juyewa diron ruwa sai faman yamutse fuska take yi tana cizon laɓɓa gabadaya ta gama galabaita ta fice daga hayyacinta lokaci-lokaci take ajiyar zuciya ita kadai tasan bala'i da masifan da take ciki yau kusan kwana uku kenan tana jin ciwon a tsaitsaye amma na yau ya shafe na kwanakin da tayi.
Jikinta har karkarwa yake yi buɗe idanuwanta tayi da suke runtse sun kaɗa sunyi jajir jijiyoyin goshinta sun fito sosai kamar shirya su akayi kan fatar goshinta hawaye ne suka kwaranyo mata karo na ba a dadi duban dakin tayi gani take yi yana juya mata sama na dawo kasa kasa na dawo sama sake runtse idanun tayi gami da yin wani yinkuri da ya sanyata sakin wata kara mai razanarwa kafun lokaci guda tayi luf! kamar ba ita bace tayi ihun ba.
Goggo Marka ce ta fado dakin cikin hanzari tana dubanta ganin yanayin da take ciki ya sanyata saurin isa gareta rikota tayi tana faman duddubata kafun lokaci guda ta gano abin da ke wakana da sauri ta gyara mata zaman dirshan da tayi tana mai rike mata kafadu da sauri ta fizge kanta daga hannun Goggo Marka tana faman sakin wani wahalallan numfashi hawaye sai ambaliya suke mata a fuska.
Sake kai hannu tayi zata rikota a daidai lokacin cikin nata ya sake juyawa wata irin zabura tayi gami da wancakalar da ita gefe guda kan ta ya hadu da gadon karfen dake gefen su da sauri ta ja da baya tana riko goshinta don sosai ta bugu lokaci guda wajan ya kumbure sosai duban Hafsat ta shiga yi idanuwanta suna kawo kwalla gabadaya ta gama rikicewa kanta gabadaya ya gama shiga duhu tunda Hafsat ta fara nakudar nan a tsaitsaye hankalinta ya kai kololuwa ba ta san lamarin zai kai ga haka ba wai yau Hafsat ce za ta haife musu abin kunya ɗan shege na gaba da fatiha ba ta taba dana sanin wannan lamarin da kaico ba kamar yau zuciyarta gabadaya ta gama karyewa da tashin hankali bata san yarda za tayi ba bata san wa za ta kai wa kukan ta a daidai wannan lokacin ba kowa ya juya musu baya musamman Abulle da gabadaya ta dauke musu kafa ta daina bi ma ta kansu ga gidan yanzu ita kanta kunyarsu take yi ta rasa dalili ko da yake ita kadai ta san abin da ta aikata a garesu sosai take jin zuciyarta na kara karye da komai na duniyar ma.
Ihun da Hafsat ta kuma yi ne ya sanyata dawowa hayyacinta dubanta ta shiga yi a tsaye take sai faman ya kice kayan jikinta take yi tana jifa dasu laɓɓanta cikin baki sai faman cijesu take yi kamar ba a jikinta ba idanuwanta a rufe da sauri Goggo Marka ta ja gefe ganin al'amarin ya girmama waje tayi da hanzari tana faman hada hanya Umma ce ta fito ta dubeta ganin yanayin da take ciki ya tabbatar mata ba lafiya isa tayi gareta tana riko hannayenta ba abin da jikinta ke yi sai karkarwa.
"Habeeba Ban san abin da ke faruwa da Hafsat ba ga ta can cikin dakin sai fizge-fizge take yi".
Zaro idanu tayi tana ambaton innalillahi wa inna ilaihir raji'un da sauri ta saki Goggo ta nufi daki durkushe ta same ta sai faman nishi take yi ga wani mahaukacin gumi da ta hada gabadaya tayi jagaf! duban kasan ta tayi ganin ruwa na kwarara ya tabbatar mata haihuwa ce da sauri ta fice ba tare da ta taba ta ba can ta hango Goggo sai safa da marwa take yi hannu aka hakan yayi matukar bata mamaki yau kuma girgiza kai tayi gami da komawa daki mayafinta ta dauko ta yi hanyar waje.
Tana sanya kai kofar gida ta hango su da sauri ta yo baya tana mai da numfashi ita gabadaya ta manta ma Mariya na waje lekawa tayi a daidai lokacin ita kuma Mariya idanuwanta na kallon kofar gidan don ta ga lokacin da Umma ta fito ta koma da sauri ya fito ta tayi da hannu sannan ta koma cikin soron sai faman kai kawo take yi don yanayin da ta ga Hafsat a ciki yayi matukar tsorata ta ba abin da ta tuna sai lokacin haihuwar Mu'azzam sosai zuciyarta ta karye lokaci guda hawaye su ka zubo mata a daidai lokacin Mariya ta iso ganin Umma da hawaye a fuska ya tsoratar da ita da sauri ta iso gareta tana tambayarta lafiya numfashi ta ja kafun ta runtse idanu jin yarda zuciyarta ke mikata wani yanayi.
"Mariya Hafsat na cikin wani yanayi matuka haihuwar ce na ke zaton lokaci yayi amma yanayin da take ciki yana bani tsoro".
Gaban Mariya ya yanke ya fadi idanuwa a waje.
"Haihuwa!?".
Ta fadi tana dafe kirjinta Umma ta gyaɗa mata kai da sauri ta juya tayi kofar gida wajan Dr.Karami ta koma kallo daya yayi mata ya gano tashin hankalin da take ciki da sauri ya iso daf! da ita kamar zai koma jikinta bakinsa har rawa yake yi wajan tambayarta lafiya runtse idanu tayi kafun ta buɗe su da kwalla hakan ba karamin kara tayar masa da hankali yayi ba.
"Hafsat ce take wani mataki na haihuwa amma lamarin sai a hankal...".
Tun kafin ta rufe baki yace da ita.
"Muje!".
Da sauri ta juya yana biye da ita suna shiga cikin soro suka tadda Umma wata irin kunya ce ta lullubeta shima Dr.Karami sadda kai yayi kasa don ba su yi tsammanin tadda da juna ba da sauri Umma tayi cikin gida shikuwa sai kokarin buɗe baki yake yi don gaishe Mariya ce tayi masa jagora zuwa cikin gidan dakin Goggo suka nufa wacce take bakin kofa lokaci-lokaci take daga labule tana duban Hafsat sai hawaye su zubo mata shar-shar.
Daga labulan yayi ya shiga da sauri ya isa gareta ya dago kanta da ke sunkuye yana kiran sunanta amma ina ta kasa ansawa da sauri ya kalli inda take durkushe shiru yayi na dan lokaci kafun ya mike ya leka waje Mariya ya yafito dake tsaye ita ma cikin yanayin fargaba da hanzari ta iso gareshe.
"Ku kamo ta kawai mu wuce asibiti ina ganin hakan zai fi dace wa don kin ga dai yanzu ko nace zan yi wani abu ba komai na aiki a wajena da zan taimaka mata domin ba a san yarda haihuwa zata kaya ba duk da dai gaf! take da yinta...".
Wani ihu ne ya cika musu kunnuwa da sauri Dr.Karami da Mariya suka faɗa dakin a daidai lokacin kan jaririn ya sanyo kai ware idanu yayi kafun yayi waje da sauri cikin sakanni ya dawo hannayensa da safa a ciki duban Mariya yayi wacce ta runtse idanu har da rufe fuska da mayafin jikinta girgiza kai yayi kafun ya isa wajan Hafsat wacce sai faman nishi take yi na wahala da taimakon Dr.Karami cikin ikon Allah Hafsat ta haihu bayan ta gama kururuwa jaririn na fadowa ta ta baje a kasa numfashinta na fita kadan-kadan.
"Mariya anso mani reza wajan Umma".
Da sauri tayi waje ta isa inda Umma ke tsaye sai faman Addu'a take yi idanuwanta sun kaɗa Mariya na isa ta dubeta jiki a sanyaye.
"Umma reza ake bukata".
Da sauri ta faɗa daki ta binciko sabuwar reza ko buɗeta ba ayi ba ta mikata mata zuciyarta na rage fargaba tunda ta ga an anshi reza da alamun an haihu da sauri Mariya ta juya ta koma dakin tana mika masa ya buɗeta ya yanke cibi a daidai lokacin kuma mahaifa ta fado dauke jaririn yayi wanda ya kasance namiji kyankyawa dashi dube-dube ya shiga yi.
Mariya ta lura dashi kuma ta gane abinda yake nima don haka da sauri ta kara so ciki dakin can gefe ta nufa inda wata akwaku take budewa tayi ta zaro wani sabon zani da alamun ko daura shi ba a taba yi ba ta mika masa goge jaririn ya shiga yi dashi sai da yayi masa tsaf! Sannan ta sake dauko wani ta mika masa ya nannaɗe shi a ciki ya mika mata komawa yayi wajan Hafsat ya dubata ganin yanayin da take ciki ya sanya shi yin waje da sauri Goggo Marka ya duba da ta gama firgicewa can gefe Umma ce ganinsa ya sanya ta yin kasa da kai.
"Alhamdulillah ta sauka".
Yana fadin haka yayi waje da sauri su kuwa har rige-rige sukeyi wajan fadawa dakin duban juna suka shiga yi kafun Umma ta shiga tsaftace dakin ta gyarawa Hafsat jikinta sosai ta tsorata ganin yarda ta karu a kasan ta hakan ya fadar mata da gaba duban Mariya tayi wacce itama idanuwanta na kanta gyaɗa mata kai tayi ba tare da tace komai ba a daidai lokaci Dr.Karami ya yi sallama suka ansa shi shigowa yayi hannunsa dauke da dan karamin kwanati (First Aid Box) cikin taimakon Allah yayi mata dinkin inda ta karu gami da allurai duban Umma yayi bayan ya ajje kunyar gefe.
"Jininta ya hau sosai kar ku saka mata ruwan zafi yanzu a dai samu mai dumi ta wanke jikinta dashi sannan ga wannan magangunan...".
Ya mikawa Mariya ledar yana mai cigaba da fadin.
"In ta ci abinci sai ku bata ta sha tsarin na nan a ciki Mariya sai ki duba ki gani Allah ya raya ya ɗayyaba".
Yana gama fadin haka ya mike yana duban Hafsat wacce ta dawo hayyacinta idanuwanta sai zubda hawaye suke yi ta kasa kallon kowa ma a cikin dakin yana kokarin fita yaji muryar Umma nayi masa godiya gami da Addu'a murmushi yayi gami da cewa 'Ameen' azuciyarsa sosai yaji dadin addu'ar a ransa.
*****
A wulakance ya anshi jaririn

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads