Header Ads
Showing 153001 words to 156000 words out of 227252 words

Chapter 52 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1401

Ads at the middle of Article

ya nuna Dr.Karami dashi.
"Ka sani in akwai wanda yafi cancanta ya zama makusancinta da komai nata ni ne nan!".
Ya fadi yana nuna kansa yana dukan kirjinsa da karfi cikin sauti mai ansa amo sosai har jijiyoyin kansa na fitowa duk da duhun fatar da yake da ita.
"Bana tunanin a filin duniyar nan akwai wanda ya dace da ita kamar ya ni ka sani Dr.Karami ta dalilina kasanta ta dalilina kansan wacece ita kafin kasanta ni ne nan na fara saninta kuma tare ka ganmu!".
Ya sake fadi cikin hargagi kamar zai kaiwa Dr.Karami duka ya juya ya dubi likitan yana kokarin yin magana Baseera ta daga masa hannu cikin tsananin haushi da takaici.
"duk wannan abin da kake yi IHU BAYAN HARI ne mutuniyar da kuka kashe har kake da karfin zuciyar da zaka zauna kana dambe akan ta mutuniyar da kuka zama ajalinta har kake ikirarin kai ne makusancin ta mutuniyar da ku ka birkitawa rayuwa har kuke tsammanin akwai wani lalen kati da za ku buga akanta kaico!".
Ta kareshi da murmushin takaici a fuskarta kafin ta shiga nuna dakin da Mariya take kwance.
"ko wannan ku ya kamata yaje ya tanaji duk wani kaya da ya sani ana jana'iza dashi domin shine kadai abin da ya kamata a daidai wannan lokaci Bala'in da kuka daurawa rayuwarta ya zama ajalinta..ko da yake dama ta fadi tun da dukkanku son ta kuke sai ku je ku dandatsata ko ya dauki ka sonsa".
kuka ne ya kawo mata hari amma ta hana zuciyarta karaya ta hana idanuwanta zubda kwalla ta hana kanta yin rauni so take yi ta kwatarwa ƙawarta 'yancinta sai yau ta kara tabbatar da so bala'i ne so masifa ne sai yau ta kara tabbatarwa ba komai bane a cikin so sai tashin hankali duk wani kauɗi da ganɗoki da ake fadi da kambawa so na dashi na kayan jindadi da kwanciyar hankali ta karyata a so in dai haka so yake to gwanda ta zauna batayi aure ba in har sai anyi soyayya za ayi aure.
numfashi take ajjewa idanuwanta izuwa lokacin sun gama cika da kwalla jingina tayi da bango tana zamewa har ta zube a kasa kamar wata kayan wanki nishi take yi so take yi hawaye su zo mata amma ina zuciyarta taki aminta mata wani zafi da raɗaɗi take ji tausayin Mariya yana kara ratsa jinin jikinta sosai take ji a jikinta in har mutuwar Mariya ya tabbata to ita kam ba zata taba yarda tayi so da wani ba domin ta tabbata SO AJALI ne ba komai ba.
"Bata mutu ba".
Runtse idanuwa tayi jin sautin kalmomin da suke ansa kuwwa a kunnuwanta ji take yi kamar a mafarki ji take yi kamar kalmar ta fito ne don kar ta sanya wa kanta abin da zai nakasta mata rayuwa laɓɓanta duka ta tura cikin bakinta tana cizawa zafin da taji ne ya sanyata buɗewa idanuwanta da saurin abin da ta ganine ya sanyata mikewa da hanzari.
Dr.Karami, Dr.Aqeel,Huzaif gabadaya taga sun cikwuikuye likita kamar zasu raba shi gida Uku.
Wani murmushi ne mai tafe da hawaye ya kufce mata kamar wata zautacciya haka ta tunkaro inda suke sai faman jinjiga shi suke 'wai ya tabbatar musu da gaskiya' duk kansu ta shiga duba da mamaki gami da wani irin farinciki mai girma gaske hadiye miyau tayi mai tauri kafin ta shiga nuna shi likitan da yatsa tana kuma nuna dakin da Mariya take.
"Are You Sure?".
gyaɗa mata kai yayi runtse idanu tayi.
"Yaa Allah...wayyo Allah na me ma ya dace nayi..yawwa....likita kasan mi...kawai mu je na ganta...please".
Ta hade hannayenta bayan ta gama rawar baki wajan furta kalaman rokon ja da baya yayi domin kwace kasan daga rikon da firgitattun mazajen har uku sukayi masa sai faman ajiyar numfashi yake yi.
"Sosai take cikin matsala ba zan boye muku ba zuciyar tace ta kusan bugawa saboda tsananin damuwa da tashin hankali da take ci ban san mai yasa a kananun shekarunta ba ta fuskancin wannan matsalar har haka sosai naji tsoron yanayin da na ganta bani da tabbacin a halin da ake ciki a yanzu yarda zata farfado numfashinta dai yana harbawa nayi irin kokarina yanzu dai tana bukatar hutu sosai kafun muga yarda Allah zai yi".
Dukkansu ajiyar numfashi suka saki mai karfi gabadayansu har sai dashi likitan ya dube su da mamaki Baseera ce tayin hanzarin dubansa.
"Please Doctor zamu iya zuwa muganta?".
Dubanta yayi kafin ya dube su Dr.Karami ya girgiza kai.
"A,a wannan ta'addacin da naga anayi a nan in kuka shiga tayar mata da hankali zakuyi har abin da ake gudu ya afku".
Yanayin da yayi maganar a dake ya sanya su zuba masa idanu suna kallon ikon Allah juyawa yayi ya koma cikin dakin kafun cikin mintina ya fito ya kama gabansa ba tare da yace da su komai ba.
Nan suka shiga kai komo a tsakaninsu Baseera kuwa sai kwaɓa take yi da tsaki kamar zata tsinke harshenta tana faman zabga musu harara kamar idanuwanta za su fado kasa lokaci-lokaci take isa kofar dakin tana lekewa amma bata hango komai dalilin labulan da yayi wa kofar shamaki.
Cikin wannan yanayin suka ji sautin takun takalma akan tayal din da yake malale cikin asibitin dukkansu suka jiyo jin sautin wajensu yake tunkarowa gabadayan su sakin baki sukayi musamman Huzaif da yayi fakare da idanu kamar wani gaula Hafsat ce take taku cike da isa da yanga sai faman taunar cingam take yi kamar wata Magajiyar karuwai daidai inda Huzaif yake tsaye ta tsaya ita ma ta karewa su Dr.Karami kallo kafin ta dubi Baseera da ita mata ta kalle ta ta watsar cikin nuna ban san ma Allah yayi halittar mai kama dake a nan ba hakan yayi wa Hafsat zafi domin dama can basa jituwa sam! a tsakaninsu duban Huzaif tayi wanda shima ita yake duba gabadaya jikinsa yayi la'asar sosai sai faman gyaɗa kai yake yi kamar wanda aka kama da laifin da bashi ya aikata ba.
Dage laɓenta na sama tayi kamar wacce taci karo da kashi tana wani dakune hanci kafun ta hura cingum din bakinta tayi katon kwai ta fasa masa a fuska.
"ban san mi yasa in ana gayyar tsiya nake ganin ka ba ban san min da yake sanyawa kake gangancin shiga ciki ba kai gabadayanka ba ka hada hanya da tsiya ba amma in ka ganta jikinka har wani ɓari yake yi kamar tsoho ya samu danyen jini budurwa danya sharaf a daren farko".
Gyaɗa kai yayi cikin rashin abincewa Dr.Karami jin abin da Hafsat take fadi sai abin yayi matukar bashi mamaki ba yau bane farkon haduwarsa da ita da kuma yarda take rashin kunyarta amma yau yayi matukar mamaki da yanayin da ta nuna musamman ganin halin-ko-in-kula da ta nuna akan 'yar uwarta Mariya da halin da take ciki wani yawu mai tauri ya hadiye kafun ya kau da kai cikin kunar zuci.
"Ban san mai yasa kake wahalar da kanka a inda ba a yin ka ba ance ba a sonka an tsaneka amma kaki daukar zuciyarka kayi nisa da inda ba ayi da kai haba sai kace mai MATACCIYAR ZUCIYA wanda ya yada kare ya dauke ya cinye tas!".
Kuri yayi mata da ido ba tare da yace komai ba kuma da alamun bashi da niyar cewa din.
Murmushi tayi na wulakanci kafun ta dora da cewa tana nuna shi da dan yatsa.
"Wai kai ma so kake yiwa biyayya ko? ka biyo wannan zugar ta mara sa zuciya kai ma ka yaɗa hajar son ka ko za a saya kaico!".
"ni ban san wata ƙaddara bace ta sanar dake ki dauko shanyayyun kafafuwanki ki zo wajan nan ba in ban da rashin zuciya da rashin aikin yi me ye naki a ciki ko akwai wani wanda kuke alaƙar mutunci dashi ne a nan da kika zo?".
Baseera ta fadi cikin takaicin kalaman da Hafsat din ta fadi dubanta tayi shekeke kamar taga kashi
"Ke kuma a soyuwa zaki sako min kazamin bakin ki mai dan banzan wari".
"Ke dalla rufewa mutane baki yan fashi da makami kawai ke ko kunya baki ji ba ko da yake dama ba a gaje ta ba shiyasa tunda ba aji kunyar kwacen saurayi ba ai ba za aji kunyar biyo saurayi ba".
Baseera ta sake fadi tana kau da kai daga kallon Hafsat da ta gama cika da bakin ciki da kalaman Baseera din duban Huzaif tayi wanda gabadaya kallo daya zakayi masa kasan yana cikin rashin hayyaci da kwanciyar hankali tsaki tayi rai a bace ta wurga masa wani kallo kafin ta juya cikin sassarfa ta bar wajan.
Ba wanda ya bi ta kanta nan suka ji gaba da jajen zuciyoyinsu har zuwa wani lokaci mai tsayi da ya kwasar musu awanni uku cir!.
Sannan likita ya sake zuwa zuwan nasa da ya kasance na biyar kenan yana dubata ba tare da ya bari sun shiga ba tausayin su yaji matuka da yanayin da ya gan su a ciki hakan ya ba su damar zuwa ganinta amma a bisa sharaɗin ba wanda zai yi ko da magana ne ta a zo a gani hakan suka yarda suka shiga yarda take haka take sai Oxgyen da yake taimakawa numfashinta yana kai kawo kirjinta na faman dagawa kamar zai faso waje sosai suka tsorata da yanayin da suka ganta don Baseera sai da ta toshe bakinta kuka ne ya kusan kufce mata kallon Mariya take cikin tausayi wacce lokaci daya duk ta zube dama yaya lafiyar kura balle kuma ta balle da gudawa duk fuskarta faɗa sai kwarmin idanu ruwan da aka saka mata sai faman tafiya yake yi Dr.Karami ne ya isa gareta idanuwansa na zagayawa a kanta da wani irin yanayi na rauni da tausayi gami da matsanancin so kau da kai yayi jin zuciyarsa na tsalle kamar zata faso kirjinsa ta fito gaban na'urar da take nuni da yanayin tafiyar numfashinta ya isa ya shiga kallo na dan lokaci yana faman ajiyar zuciya kafin likitan ya shiga yi musu bayani akan komai da yake afkuwa da ita na damuwa da kuma bugawa da zuciyarta take kokarin yi sharuɗa ya kafa musu sosai akan matsa mata da ake yi da kuma sanya mata damuwa da sanyata gaba ana mata rigimar da zata firgita mata zuciya sosai suka anshi sharuɗar kafun ya ba su dama kowanne yayi waje Baseera da Dr.Aqeel da Huzaif ne suka tafi gida amma shi Dr.Karami ya zauna akanta a matsayin wanda zai kula da ita duk wani abun da za a bukata duk da likitan yace ba sa bukatar mai kulawa daga wajan majinyaci amma ya ki yarda akan haka dole likitan ya kyaleshi bayan yayi masa ikirarin shima likita ne...




*_Makaranta na masoyana na wannan labarin ina so a daidai wannan gabar kuma daidai wannan shafin ina bukatar gyara da kuma shawara sannan kusa ni tafiya ba tsokacin makaranta sosai take taba wani sashi na tafiyar zuciyar marubuci ya ji ba dadi don Alalh kuyi min tsokaci ta hanyar sako ko ta whatsapp domin raayoyinkun na da amfani sosai a gareni ga lambata nan ta whatsapp ina tsumayenku a ko ina kuke masoyana ina son ku so na sosai da sosai❤ 08076708191_*
[9/14, 4:59 PM] DEENY MINNA🙋‍♂: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA BIYU.


Sunkoyawa yayi da zubar debo ruwa a gorarsa har ya nitsar da ita sosai yana kokarin dagowa yaji ta maƙale gabadaya taki daguwa hakan yayi matukar daure masa kai shiru yayi kamar mai tunani wani abu kafin ya sake dago gorar tasa amma ina! sai yaji kamar an kara daura mata gingimeman dutse.
"Ja'e zo ka taya ni gorata ta ki hidduwa daga ruwa".
Ja'e dake tsaye yana gabzar danyen Mangwaro ya juyo ya dube shi kafin yace.
"Ban fahimce ka ba me kake nufi?".
"Zo ka gani mana don Allah".
Ba tare da ya sake cewa komai ba ya tako zuwa wajen ya dube shi sannan ya dubi gorar da tayi kasa amma ga bakinta nan.
"Jayota mana kai ma sai kace wani sakakke ya za ayi gora ta makale a ruwa?".
Sake janyota yayi amma ina taki daguwa da karfin gaske ya fizgota gabadaya yayi baya ya zube a kasa gorar tayo waje sagale da ruwan rigar mutum hadi da kansa duk sunyo waje Ja'e dake tsaye bai san lokaci da ya kwala ihu ba ya ari na kare ya falle kamar wani zomo da yan farauta suka biyo shi Iro da ya baje cikin ciyayi mai taɓo ganin abin da Ja'e yayi ya tabbatar masa akwai abin da ya gani shima cikin tsorata da firgice ya k'urma da gudu shima ko tsayawa ganin abin da ke faruwa bai yi ba gudu ya shiga yi da yake irin siraran mutanan nan ne marasa jiki ga tsayi nan da nan ya kamo Ja'e da ke ta fama haki kamar wanda ya ɓalle daga lahira ya fado duniya.
Ba su tsaya tambayar juna ba suka sake arcewa gudu sukayi sosai har sai da suka fara hango bunkokin rugar su kafin su tsagaita suna mai da numfashi Ja'e ya sunkoya riƙe da kafafuwansa yana duban Iro da yake gabansa.
"Aradun Allah Iro lahira na hango".
Ya fadi yana mai waige-waige cikin tsananin firgici da razana Iro da yake can nesa dashi ya dube shi cikin rashin fahimta.
"Ban gane ba kaifa baka da hankali wa yace maka ana hango lahira daga nan duniya".
Nishi Ja'e ya saki na wahala kafin ya tashi tsaye sosai ya dubi bayansa sa'an nan yace.
"mutum ne fa kamar gawa na gani rike da Gorar...wai hala kai baka gani bane?".
Iro da yayi shiru yana sauraron Ja'e jin abin da yace ya sanya shi ware idanu waje.
"Aradu ban gani ba kawai biyo ka nayi don na tabbata abin da ka gani bala'i n...".
A guje suka sake kwasa suna zunduma ihu kamar wasu zararru sai faman tsalle-tsalle suke kawai don sun ji motsi abu cikin ciyayin da suke kusa da ita da wannan yanayin suka karasa cikin rugar ihun da suke ya firgita mutanan cikinta nan da nan kowa ya shiga kallon su ana tambayar dalili amma ba wanda yayi kokarin tsayawa balle ya basu ansar abin da ya jefa su cikin firgicin da suka samu kan su.
Da yake rugar ba mai girma bace kallo daya zakayi mata ka gane ZURI'A DAYA ce ta hadu a wajan don bunkokin na su tsilli tsilli suke a lissafe ba za su haura goma ba.
"Iro wai kalau kuke kuwa? Wannan wani irin wauta ne da girman ku da komai amma kuna wannan shiriritar".
Tsohon da suka gilma gindin wata bunka ya shiga fadin haka cikin yanayi na jin haushin abin da ya ga sunayi don mafiyawancin lokaci haka suke indai suka dawo kiwo sun dinga nuna yarintar su ke bayan kuma a shekaru ba wanda bai haura ashirin ba kuma ko wanne da matarsa ta aure.
Ba su bi ta kan sa ba sai da suka karasa shiga cikin jerin bunkokin da suke kafun kowa ya faɗa bunkarsa cikin halin firgici nan da nan matan da suke wajan su ma suka tashi suna kokarin kwasa da gudu amma tsohon nan ya hana su .
"Mariye jurɗe don Allah karku biyewa shiriritar su Iro kun san dai halin su ba sai na fada muku ba indai daukar hakki ne sun iya shi wajan tayar da hankalin mutane".
Cak! Suka tsaya suna duban sa zuciyoyinsu na harbawa domin sun tsorata da yanayin da suka ga su iron.
"Amma Baffa kamar wannan yanayin da suka shigo dashi ya bambanta da sauran lokuta alamu ya nuna kamar akwai dai abin dake faruwa".
Gyaɗa kai yayi yana murmushi kafun ya gyara tsayuwar malfarsa akai yana duban surukan nasa
"Nikam zan ga ranar da za ku daina daukar lamarin su Ja'e...".
Ihun da suka ji an kurma ne gabadayan su suka juya da sauri suna duban Bunkar Ja'e Asiya ce ta yo waje a guje kai ko dan kwali babu zani na kokarin kwance mata sai faman mazurai take gabadaya ta firgice.
Jurɗe ce tayi sauri isa gareta tana rukota sosai a hannunta ganin yanayinta da firgici.
"Lafiyarki kuwa Asiya meke faruwa mai ya samu Ja'e?".
Jikinta na mazari ta shiga nuna bunkar kafun taja numfashi mai karfin gaske.
"wai gawa suka gano a bakin kogi".
Ta ida tana mai kokarin rike zanin jikinta dake kokarin subuce mata.
"Gawa!!!".
Su ka fadi su duka cikin yanayi na zaro idanuwa waje Baffa da ke tsaye tun dazu da sauri ya kwaɗawa Ja'e kira yana tunkarar bunkar cikin hanzari.
Ja'e dake makale cikin bunka sai faman mazurai yake yi jin muryar Baffa ya sanya shi takowa a hankali kamar wanda aka ce gawar tana biye dashi sai da ya leko kafun ya fito wani kallo Baffa yayi masa kafun ya dube shi sosai.
"Wai shin me ke faruwa ne naji matarka tace wai gawa kuka gano bakin kogi ya abin yake ne ina shi Iron yake?".
Cikin yanayi na firgici Ja'e ya hadiye numfashi mai tauri kafun ya dubi Baffan nashi.
"Aradun Allah Baffa Gawa ce Iro yaje debo ruwa a garo kawai sai ya ganta".
Cikin rashin fahimta Baffa ke duban sa kafun ya kwalawa Iro kira cikin hanzari ya fito shima yana faman mazurai har yafi Ja'e firgici ya tako ya iso matarsa na biye dashi sosai da sosai Baffa ke dubansa cikin yanayi na nazarinsa kafun yace.
"Ina jin ka me ya firgita ku?".
Rarraba idanu ya shiga yi kamar mai tsoron yayi magana gawar ta riko shi numfashi yake ja a hankali kafun ya dauke gumin da ya tsattsafo masa a goshi.
"Baffa gawa ce na gano bakin kogi naje debo ruwa to shine gorar tawa ta makale nayi-nayi ta fito amma takiya sai da nayi daƙyar sannan na jayo ta a nan ne sai ga gawar mutum ta biyo gorara".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!".
Gabadaya suka dauki salallami suna duban Iro da yayi firgai-firgai kamar wanda suka karawa firgici Baffa yayi ajiyar numfashi mai kwari cikin rashin aminta da zancen domin shi dai ba ya ganin wannan lamarin zai tabbata tunda ba yarda za ayi ace a tsinci gawa a bakin kogi shi dai ya san tun da yake zaune a nan sama da shekaru ashirin kogin nan bai taba cin mutum ba balle yace gawar wani dan rugar tasa ce sake duban su yayi ganin har yanzu suna cikin firgici ya sanya shi nazarin son zuwa ya je ya gani

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads