Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 227252 words

Chapter 2 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1366

Ads at the middle of Article

kula da hakan sai ita kadai kau da kai tayi, tana duban mahaifin nata wanda hankalinsa gabadaya yana kan matarsa, yana dubanta yana kallon yanayin da take ciki na tsananin wahala, zai so ace sun tafi asibiti da ita yana ganin haka shine kawai yafi dacewa, sai dai maganar Goggo Marka tayi masa katanga da hak,a ba don ya so ba ya dubi Mareeya da take ta faman ajiyar zuciya, hawaye sun cika mata idanu ya ja hannunta suka fice daga cikin dakin, zuciyarta sai faman azalzala take yi da tsoro don tana fargaban barin Goggo Marka da Uwarta ta kar tayi mata wani abu, domin irin kiyayyar da ta hango a idanuwanta komai za ta iya aikatawa.


Can nesa da dakin ya ja ta ya zaunar da ita, yana mai rarrashinta da ta bar kuka In Sha Allah uwarta za ta samu lafiya, ita dai gyada masa kai kawai take yi, amma ba ta hango hakan ba. hankalin ta gabadaya ya karkata izuwa wajan uwarta da kuma Goggo Marka da aka bari tare da ita, tsoro take ji.


Ba su jima da fitowa ba, Goggo Marka ta fito daga cikin dakin duk ta hada gumi kamar gaske. dubansu tayi gami da rausayar da kai ta wuce dakin ta, an jima kadan ta fito hannunta dauke da kullin abu, ba tare da tayi wa kowa magana ba ta samo kwano ta kwance kullin da ta ɗanko daga dakinta, wasu sauyoyi ne a ciki kwasa tayi ta zuba cikin kwanon mai dauke da ruwa ta shiga jujjuyawa, gaban Mareeya ya yanke ya fadi, ta zaro idanu tana kallon abin da take yi gabadaya hankalinta bai gamsu da abin da take yi ba, nan ta dubi Babanta, shima Goggo Marka yake kallo. sai da ta gama motsawa sannan ta mike ta nufi cikin dakin. da sauri ya tare ta da cewa.


"Goggo wannan kuma menene?".


Murmushi tayi gami da margaya kai.


"magani ne mace dake kan gwuiwa ake baiwa, domin samun sauki da kuma haihu sumulkalau ba tare da an samu matsala ba, yanzu ina bata shi in dai haihuwar ta zo to nan da nan zaka ga ta haihuwa abinta".


Ba ta tsaya jin abin da za su ce ba ta fada cikin dakin. izuwa wannan lokacin Habeeba sai faman numfashi take yi da nishe-nishe lokaci lokaci, gumi ya gama game mata jiki gabadaya. isa tayi gareta ta rangwafa gami da tallabo haɓarta dake kasa, ba tare da komai ba ta tura mata kwanon mai dauke da jikanken sauyoyin, wani hamami ne da daci suka dake hancinta da harshenta da sauri ta kau kai, duk da tsananin da take ciki bai hana ta tsanar wannan abin da ake kokarin ba ta ba.


Goggo Marka ta na ganin haka ta sake kakaba mata tana mai kashe murya.


"hakuri zakiyi ki sha Habeeba, shi zai taimaka maki wajan samun saukin nakudar. duk wani ɗaci nashi daure wa zakiyi haka".


ta sake kai maka shi baki nan ma kau da kai ta sake yi, cikin tsananin kin abin ta shiga numfarfashi, a lokacin nakuɗar ta sake motsa mata ji take yi kamar bayanta da kwankwasonta za su karye, ta dago da jajayen idanuwanta cikin rashin hayyaci ta dubi Goggo Marka wacce ta ke ganinta tana kasuwa gida bibbiyu a gareta, ta mai da kanta kasa tana mai sakin numfashi. ita kadai ta san halin da take ciki, ita kadai ta san azaba da raɗaɗi da take ji a kowa ni sashi na jikinta...
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU BALA'I
NA


KAMALA MINNA.


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.




BABI NA BIYU.


Awa daya tsakani amma shiru kake ji, ba wani cigaba wanda za ace na a zo a gani, har hankula su saka ran samun natsuwa.
Malam Bello zuciyarsa ta gama karaya matuka, ji da yayi shiru ba alamun haihuwar, anyi ta ko ba ayi ta ba, ya rasa matsayar da zai ajje zancen zucin sa.
Numfashi yake ta faman ajjewa, sai ka rantse shima nakuɗar ce akan sa, ya dubi Mariya wacce ta ke cikin yanayi na faduwar gaba da rikitar zuci da ruhi, duk hannaye biyu ta saka ta tallabe haɓarta, idanuwanta sun yi jajir hakan ya kara tsinke masa natsuwar zuciyarsa, sai faman bugu take yi tana yaso masa wani banzan zance wanda ba shi da muradin ace ya tabbata cikin duniyarsa, in kuwa haka ya tabbata ko shakka ba ya yi zai fi kowa ruɗewa cikin duniyarnan. a hankali ya shiga ajje numfashi, yana kallon dakin da Matar tasa take wanda ya tabbata izuwa wannan lokacin mutuwa ta zo kusa da ita. Da wannan zancen zucin ya kokarta mikewa yana faman hirji kamar zai ci babu, ya doshi dakin cikin bugun zuciya da ruhi.
Yaye labulan yayi cikin rashin tabbacin abin da zai gani, duk da dai zuciyarsa tana yi masa kuwwa akan ba sauki sai wajan Allah. idanuwa da numfashinsa gami da bugun zuciyarsa a lokaci guda suka shiga rudu, ganin yanayin da ya ga Habeeba a ciki, da hanzari ya fada dakin ya dubi Goggo Marka, wacce ke zaune can gefe ta zubawa Habeeba idanu, ba wani alamun tashin hankali tattare da ita, maganar Malam Bello ne ta dawo da ita duniyar rauni, da kokarin yafawa fuskarta yanayin tausayi, ta shiga duban shi.
"ka gani ko, har yanzu ba alamun haihuwar ina ga dai lokaci ne baiyi ba, ko kuma juyi ne".
Ta fadi cikin yanayi na kara narkewa a tausayi.
Gyada kai kawai yake yi, kamar wani kadangare yana faman jan numfashi yana ajjewa, idanuwansa da hankalinsa har da natsuwarsa duk suna kan matar sa, sake ajje numfashi mai kauri yayi.
"Goggo kawai mu tafi Asibiti".
ya dasa aya yana kokarin isa wajan Habeeba. Da sauri ta tare shi.
"a,a mana Bello, mai yasa zaka nuna gajen hakuri ne, na fada maka in haihuwar nan ta zo yin ta za ayi, amma na ga alamun taurin kai za kayi. haba don Allah ko fa Asibitin muka je hakance zata kasance".
Bai amince ba, bai yarda ba da maganar ta sam. bai hango ɗa mai ido ba cikin wannan lamarin, don haka ya dube ta sosai, cikin karyar da murya.
"Goggo zuwa Asibitin shine ya fi dacewa, domin zaman gidan ba karimin hatsari zai farar ba".
Duban sa tayi, cikin shan kamshi.
"me ka ke nufi Bello, kana nufin a matsayina ba zan iya amsar haihuwar ba ne ko yaya?".
Girgiza kai ya shiga yi, cikin yanayi na rashin natsuwa.
"ba haka bane Goggo, ya kamata ki fahimta wani abu, kin ga can asibiti in muka je ko ba haihuwa ba ce su sun san abin da ya dace suyi mata, domin ganin komai ya zo yarda ya dace, amma zaman gidan ba abin da zai haifar sai dai ya je fa mu a ruɗu da rashin abin yi kawai, sai dai mu sata gaba muna kallo".
"ba in da za a kai ta Bello, na fada maka ka duba fa ka ga yanayin da take ciki, alamun ya nuna haihuwar gaf take da yin ta yanzu, in muka dauke ta cikin wannan halin komai zai iya faru a hanya, za ta iya haihuwa a titi me kenan akayi?".
ta fadi cikin yanayi na rashin jin dadin maganganunsa, ta yafa wa fuskarta yanayin kamar gaske ta shiga cizon laɓɓa, sai ka rantse zage ta yayi tas.
Wani marainin nishi Habeeba ta saki, wanda da kaji amonsa kasan wahala ce tsagwaronta ba mis a cikin ta, hakan ya kara ruguza 'yar natsuwar Bello, ya shiga dubanta sai faman fadin "Sannu" yake yana ji azuciyarsa har da can kasar ruhinsa kamar bai yi mata adalci ba, in har ya yarda da batun Goggo. sai dai kuma a wani bangaren in ya ki amsar maganar Goggo, kamar kin biyayya ce a gareta. duban Goggo yayi ya sake juwa wajan Habeeba, wanda ko tantama ba yayi mutuwa tana kurkusa da ita, in kuwa mutuwa ba ta zo ba to tabbas bakar izaya da wahala tana ɗawainiya da gangar jikinta da zuciyarta.
"kiyi hakuri Goggo, mu kai ta asibiti...".
Wani kallo ta watsa masa, kafin ta fara magana cikin ɗaci.
"wai shin in tambayeka yau ta fara haihuwa ne a duniyarta, na dauka ta haifi Mariya kuma a gidan nan ta haifeta, ba tare da zuwa wani waje ba. to bari kaji na fada maka ba in da zata, a gida zata haihuwa kana kallo fa na bata magani rage zafin nakuda, da zuwan komai a sannu kuma da ka kalle ta za ka san maganin yayi aiki..."
Da sauri ta katse batunta, lokacin da taga wani ruwa ya fara gangarowa daga kasan Habeeba.
"ka gani ko. har faya ta fashe haihuwar ma ta zo nan kurkusa, sai ka fice ka bamu guri ko a nace".
Ta kareshe tana galla masa harara. da sauri ya dubi Habeeba, yana kallon yarda ruwan da bai san na menene ba, yake zubowa daga jikinta wanda ya tabbatar da zancen Goggo din, amma bai amincewa kan sa ba, har can kasar ruhinsa. ba yarda ya iya haka ya fara jan jiki yana kallon Habeeba, yarda take wani irin nishi da murkususu kamar za a zare mata rai.
Zuciyarsa ta kara yin rauni, ganin yarda Habeeba ke shan wahala. in da yana da yarda zai yi da ya dauke mata wannan azabar ya daurawa kan sa, amma ina! ba hali, haihuwa mace ce kawai take da wannan alhakin nayin ta, wanda ba komai bane a cikin ta sai tsatsar azaba da wahala, tausayinta ya kara tsargar masa a jiki. da wannan yanayin ya isa inda Mariya take zaune, ta na ganinsa ta mike idanuwanta akansa, sai nar-nar suke alamun son zubda hawaye, tana kokarin yin magana ya yi saurin riketa ganin kuka na kokarin kufce mata, ya shiga girgiza kai kamar wani d'an kadangare.
"karki yi kuka Mariya, komai tsanani yana tare da sauki da yardar Allah, kuka sam bai ka mata ba..."
da sauri ta tareshi, tana mai gyada kai, hawayen da take boye su suka shiga zubowa, kamar an murde kan rubabben famfo.
"Abba Umma ta ina son ta, bana so na rasata don Allah ka taimaka mani ka taimaka mata, mu kai ta asibiti kar ta mutu ta bar mu cikin duniyar nan, ba zan iya rayuwa ba na rokeka".
Ta karashe tana mai zubewa a kasa, kamar wacce aka bugewa gwiwowi ta shiga sakin kuka mai cin rai da tsuma zuciyar mai sauraro.
Kallonta yake yi, cikin wani irin hali na tausayawa zuciyarsa gabadaya ta gama raunacewa ji yake yi kamar ya daura hannu saman kai, ya zunduma ihu. wani radadi da zafi gami da zugi yake ji suna taso masa, tun daga kasar ruhi har zuciya gabansa sai amsa wani irin bugu yake yi mai dauke da kayan tashin hankali cikin sauri-sauri. dafe kai yayi da duk hannayensa ya rasa mai ya kamata yayi, ya rasa mai ya dace yayi, domin samo mafita akan wannan lamarin dake kokarin janyo masa tashin hankali. ya rasa da mai zai ji, ya sani Habeeba na cikin halin wahala dole ya nemi mafita, dole ya kai ta asibiti, in da yake tunanin nan ne kawai ya dace ace a halin da take yanzu tana can. sai dai wani hanzari ba gudu ba, Goggo Marka ta hana yin haka, ya rasa mai yasa ta kasa fahimtarsa, ya rasa mai ya sa taki yarda ta amshi rokonsa, ya rasa mai yasa take kokarin janyo masa abin da zai haifar masa da tashin hankali, taki fahimtarsa, taki gane matsalar da yake hangowa za su fad'a, ya kamata ta fahimta zamanin da da yanzu ba daya bane, komai ya sauya kamar yarda komai na cikin duniya ya sauya, haka zamani yake sauyawa da abubuwa masu dauke da karin haske ga duniyar dangin rai sai dai taki amincewa da cewa ZAMANI YA CANZA.
"Abba don Allah kar ka bari maganar Goggo tayi tasiri a zuciyarka, har ta hanaka ceto rai".
Mariya ta fadi cikin rawar murya, tana duban mahaifin na ta, cikin kasalallan yanayi.
Gyada mata kai ya shiga yi, kafin ya ja jiki ya fice daga cikin gidan, ya bar ta nan tallabe da haɓa.
Bakin titi ya nufa, mai Napep ya dauko ya dire kofar gidan, ya ce dashi ya jira shi cikin gidan ya fada cikin jarumar zuciya, a daidai lokacin Goggo Marka ta fito daga cikin dakin a firgice saura kadan suyi karo, idanu ya zuba mata yanayin da ya ganta ya sanya gabansa tsananta bugawa, ita kanta Mariya ba karamar razana tayi ba da sauri ta bi bayan mahaifinta, ganin yanayin da yake ciki yana fadawa cikin dakin yayi daidai da karar da Habeeba ta saki, gami da bingirewa jini na malala ta karkashin ta, ga kan jariri ya yo waje bai san lokaci da ya isa gareta ya durkushe gami da tallabo haɓarta, zuciyarsa ta buga lokaci guda ganin da yayi ba alamun numfashi a jikin ta, hakan ya kara masa firgici, zabura yayi gami da ficewa waje, cirko-cirko ya tadda da su, Goggo Marka tallaɓe da haɓa kallo daya zakayi mata ka hango rashin gaskiya da firgici kwance a cikin idanuwanta, ita kuwa Mariya hannu ta daura akai ganin yarda mahaifinta ya fito, ta kurma ihu gami da zubewa kasa tana fadin.
"Shikenan rayuwa ta gurgunce a duniyata, shikenan na bani na lalace a rayuwar duniya, shikenan tsanin rayuwata ya karye...".
Da sauri ya isa gareta, ya dago ta.
"Mariya daina fadin haka, wa ya sanar dake ta mutu, ta na nan da ranta".
ya fadi yana mai juyar da kallon sa wajan Goggo Marka da tayi wuki-wuki kamar wacce tayi wa sarki karya, girgiza kai yayi, da sauri ya koma cikin dakin dalilin wasu lamura da zuciyarsa da kwakwalwarsa suka shiga sanar dashi, cikin jarumtar zuci da na jiki ya shiga gyara mata jiki, idanuwansa cike da hawaye ya dagota gabadaya ya rungume ta, ya fice daga cikin dakin cikin hanzari ba in da ya direta sai cikin Napep, shi kansa mai Napep din ya tsorata da yanayin da ya ganta aciki, da sauri ya shiga ciki gami da tayarwa, Malam Bello gabadaya ya gama ficewa daga hayyacin sa. kwalla da suka taru masa a idanu sai shatata suke kamar wani karamin yaro. har Napep ya fara kokarin tafiya, sai ga Mariya ta fallo a guje tana kuka, tana mai cewa da mai Napep din ya tsaya don Allah, amma Malam Bello ya ce su tafi kawai don yasan in har Mariya ta biyo su, kafin su kai sai hankalin su ya kara tashi musamman in da take nan a firgice, yana hangota tana daga masu hannu tana kiran su cikin muryar kuka. kai ya shiga girgiza mata, yana mai daga mata hannu alamun ta koma gida. amma ina kuka ta sake rushewa da shi gami da durkushewa, ta saki wani sabon kukan mai cin rai da tsuma zuciya, kuka take yi kamar ranta zai bar jikinta, wani zafi take ji tun daga kasar ruhinta har zuwa inda zuciyarta ke ajje. ta gama yanke tsammani akan sake ganin mahaifiyarta a duniyar rayuwarta dauke da numfashi, zuciyarta ta gama yarje mata sun yi rabuwa kenan har gaban abada, ba za su sake haduwa ba.
ta ji ma cikin wannan halin. kafin ta kokarta cikin jan jiki ta mike tana faman tangadi, duniyar gabadaya ji take tan juya mata, komai ya kwance mata, komai ya lalace cikin duniyarta, kayan farinciki tuni suka guje suka barta, ji take kamar zuciyarta zata tarwatse, kwakwalwarta ta na faman kai kawo cikin duniyar tashin hankali da rashin tsammanin samun sa, sannu a hankali take tafiya idanuwanta a rufe jefa kafa kawai take yi a duk in da taji kafar ta ta, ta bata damar haka, cikin ikon Allah ta isa kofar gida, tana kokarin sanya kai cikin soron, sukayi karo wani irin zafi da raɗaɗi ta ji goshin ta ya dauka, da sauri ta buɗe idanunta tana dafe goshinta, wasu zafafan hawaye suka zubo mata. Goggo Marka. ta gani tsaye idanuwanta akan ta, sai faman tsume fuska take yi. kau da kai Mariya tayi, tana mai jin zafi rai suns dago mata da duk wani numfashinta, ta fara kokarin rakuɓeta za ta wuce, wani wawan cafka ta yi wa wuyanta, ta dawo da ita gabanta.
"ke mai uwa ko, shine saboda rashin sanin darajar kai, ki ka zube a titi kina kwarar baki. to dan uban ki in ba duniyar kika dauke da ihu ba, za a kashe miki uwa ba ki cika Mariya jikan Lamiɗo ba shegiya bakar munahika kawai.
Girgiza kai ta shiga yi,hawaye na sake balle mata sam maganganun Goggo ba su taba mata zuciya ba, domin tashin hankalin da take ciki ya zarce duk wata bakar magana ko zagi da za ayi mata, hannu ta sanya ta dauke hawayen da suka cika mata idanu ba tare da ta sake bin ta kan Goggo ba, ta sake yinkurin shigewa cikin gidan. a wannan karon ba ta hanata ba, sai kwaɓa da tsaki da ta bi ta dashi.
Tunda suka dauki hanyar Asibiti, Malam Bello ke rungume da Habeeba. ba abin da yake yi sai zubar hawaye, har zuwa wannan lokaci jini bai daina zuba a jikinta ba, gabadaya shimfidar cikin Napep din ta baci shi kasan direban lokaci-lokaci yana juyowa ya dube su, domin ba karamar firgita yayi ba, sai faman zabga gudu yake yi kamar zai tashi sama, burin sa kawai su isa Asibiti, domin ceto ran Habeeba.
Mintina goma kacal ya kai su Asibitin baban alis, yayi Parking gami da direwa, da gudu yayi cikin Asibitin yana mai sanar da Nurses su taimaka wata ce ba ta da lafiya, yanayin da yake ciki na rashin hayyaci, sai ka rantse uwarsa ce ba lafiya amma Nurse din ba wanda ya bi ta kasan, kowa harkar gabansa yake yi, mutanan da suke zazzaune sai faman bin sa da kallo suke, cikin yanayi na tausayi, domin sun tabbata ba abu ne mai sauki zai firgita duniyar tunanin wannan matashin ba. tun yana neman daukin su, su kula shi amma ba wacce ta kulashi, sai da ya isa kusa da wani teburi ya shiga duban matar dake zaune,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads