Showing 75001 words to 78000 words out of 227252 words
Chapter 26 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
bugun motar tasa kamar daga sama lokaci guda ya ji an balle murfin wani irin haske ya ga an dalle masa idanuwa dashi wanda hakan ya karasa rufe masa ganin nasa da jini ya wanzu a fuskar sa gabansa ne ya cigaba da faduwa yana ji ya na gani aka fizgo shi waje aka watsar tsakiyar titi kamar wani kayan wanki sosai ya bugu a bayansa wanda hakan ya sanya shi sakin kara mai sauti bai kai ga dire karar ta sa ba yaji an kwaɗa masa wani abu mai girma a tsakar kai wanda hakan ya kara sanya shi bajewa a tsakiyar titi yana mai sakin numfashi wahalalle wata tsawa kayi mai dan karan haske hakan ya baiwa Mr.Ekele damar ganin mutanan dake tsaye akansa gabza gabza har su biyar ko wanne rike da mugun makami a hannunsa hakan ya kara tsinkar masa da gaba ya sadakar shi tashi ta kare a filin duniyar nan a hankali ya mai da kansa ya langwaɓar jira kawai yake yi yaji saukar wani makamin wanda zai tafi masa da rai daga gangar jikinsa.
"Kai dan uban baban ka shine don ka raina wa oga sense shine zakayi masa eya ne ko to yau zaka bar duniyar nan dan kundun uba jikan oduduwa mai katon ciki".
muryar dake wannan zantukar kadai in ka saurara zaka gane tsantsar rashin imani da tausayi daga ji kuma zaka gane ma'aboci zuke-zuke ne zauna gari banza da ake amfani da su wajan cutar da jama'a da ba su ji ba su gani ba.
"Bobby kawai yi masa eya ne kamar yarda ya yi wa Oga shi ya yaji inda dadi".
Wata muryar ce ta daban ta sake fadin haka.
A wahale Mr.Ekele ya motsa yana mai sakin numfashi mai tsananin ciwo.
"ki taimake ni kin ji karki kashe ni zan baki duk abin da kike so Allah...".
Wani bugun bazata yaji ya saukar masa a baki wanda ya sanya shi zubewa a kasa yana kiran jesus ya cece shi za su kashe shi.
Wata irin shaka ya ji anyi wa wuyansa kafun lokaci guda a durkusar dashi a dage masa kai yana ji yana gani aka daura masa wata irin sharɓebiyar wuka wanda walwalin ta ke haske duhun daren da suke ciki kafun yayi wani yinkuri tuni an sauke kan sa a kasa yabi titi yana ta tintsirawa yana tsartuwar jini gangar jikin kuwa nan suka yi cilli da ita kafun daga bisa suka dauke ta sukayi cikin motar shi da ita suka banka masa wuta lokaci daya kamar an kunna wutar auduga haka ta kama ranga ranga.
A hankali suka shiga motocin su fuskar su na bayyanar da tsantsar murna da farincikin samun damar cika wannan aikin domin sun tabbata da ba su samu wannar sa'ar ba Allah kadai ya san abin da Dr.Erena zai musu domin sun lura sosai Mr.Ekele ya bata masa rai wanda ya kasa boyewa har sai da ya fiddo a muryarsa suka fahimta kuma yayi musu gargaɗin kar su sake a samu akasi akan aikin nan sannan ga kudin da ya saka musu masu auki wanda tun da suke yi masa aiki bai taba basu kudi haka ba.
*****
"Yaa Allah! Dr.Erena kasan me ke faruwa kuwa yanzun nan muna kan hanyarmu ta dawo wa daga Abuja mu kayi kaci ɓus da wani abun tashin hankali Mutumin ka Mr.Ekele an kashe shi an kona gawarsa har da motarsa sai dai kuma kansa da aka yanke kafun a ko ne shi shine yasa muka gane shi ne".
Numfashi mai karfi yaja kafun ya saki Murmushi mai cike da mugunta har sai da Alhaji Abdulwahaab yaji sautin.
"Ni na sanya aka kashe shi?".
"What! kai fa kace akan mi?".
"wannan ba damuwar ka bace abin da kake bukata na fadi maka don haka ka rabu dani kawai a wuce wajan domin ni har na manta da wani mai irin wannan sunan a filin duniyar nan".
"Yaa Salam! Me ya sa kayi haka Dr.Karami haka sam bai dace ba Mr.Ekele komai yayi maka bai dace ace ka sanya anyi masa wannan mugun aikin b...".
"Ya kamata ka kiyaye lafazun ka Alhaji Abdulwahaab na rantse da Allah ko kai ne kayi mani abin da Waccen mataccen yayi mani sai na sanya a kau da min da kai a filin duniyar nan wallahi don haka ka kiyaye lafazinka".
"Dr.Erena ni ka ke wa ikirari haka Allah ya baka hakuri ban san lamarin zai taba maka zuciya har haka ba".
"Da dai yafi haka wallahi don haka mu yi wani batun na daban in kana dashi in kuma babu mu sauke wayar".
Murmushi Alhaji Abdulwahaab ya saki mai zafin gaske kafun ya nisa.
"Ni ba ni da wani abin cewa dama akan waccan maganar ce kuma kace ba ka so komai ya wuce".
Bai jira cewarsa ba ya sauke wayar yana mai mamakin Dr.Erena da irin rayuwar da yake yi wa kansa tanaji ko da yake bai kamata ya zauna tunanin sa har haka ba tun da shi ma akwai tasu a tsakaninsu....
Nisawa Alhaji Abdulwahaab ya yi sosai lokaci guda gumi ya karyo masa duk da sanyin A-c dake busawa cikin Office din tausayin Areefa yake yi akan yarda lokaci guda ta daukar wa kanta wannan aikin mai cike da hatsari da tarin kalubale shi kansa tsoron Dr.Erena yake yi kuma yana tsoron ranar da zai san yana bibiyarsa ya san tabbas shima wani abu zai faru dashi sai dai zai wa kansa Alkawarin ajje duk wani fargaba da tsoro akan Dr.Erena ya fuskance shi ya marawa Areefa baya domin ganin sun cin ma abin da suke bukata akan sa sosai yake jin zafi da raɗaɗi a zuciyarsa duk lokacin da ya tuno da kunci da bakin cikin da Dr.Erena ya cusa masa a zuciya dama filin duniyar rayuwarsa gabadaya.
*KAMALA MINNA*😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA UKU.
Sosai take jin maganganun Alhaji Abdulwahaab na mata kuwwa a kunne ta rasa mai yasa haka, ta rasa mai yasa zuciyarta take koƙarin dauko mata abin da bata shirya tarbarsa ba, kokari take ta kau da komai a zuciyarta wanda sam bata muradin ace sun shigo har suna ƙoƙarin sanyata wani hali Dr.Erena mutum ne da ya kama ace ta ajje komai nata ta fuskance shi sosai da sosai sannan duk wata fargaba ko SHAKKA gami da tsoro ya dace ma ace babu su a filin rayuwarta.
Nisawa tayi tana mai jan numfashi mai zafi tana fesawar wasu lamura ne masu matukar tasiri a rayuwarta taji suna dawo mata kamar yanzu ne suke fado duniyarta ji take yi kamar yanzu ƙaddara ta hadata da Dr.Erena komai taji ya sanko mata lokaci guda a zuciyart da sauri ta ja burki a gefen titi tana mai hada kanta da sitiyari zuciyarta taji tana wani lugudan bugu wasu hawaye masu tsananin zafi da kokarin yayyaga zuciya suka shiga zubo mata...
*******
*JANUARY 2004.*
*KADUNA GIDAN MARAYU.*
"Alhaji Mati ba wai ban yarda da kai ba ne, kawai dai ka san sha'ani na rayuwar a wannan zamanin sosai yara irin wadannan suke shiga kuncin rayuwa a hannun wanda suke daukar su anyi ba sau daya ba, ba sau biyu ba a nan gidan shiyasa kaga gabadaya yanzu ba ma yarda da mutane sam! da suke zuwa daukar marayu da sunan rike su wasun su da yawa ba saboda Allah suke daukar su ba su da tasu manufar akan marayun da suka dauka...".
Nisawa yayi yana kara gyara glass din fuskarsa kafun ya dubi Alhaji Mati da yayi masa kuri da idanu yana dubansa kamar zai cinye shi danye sosai yake jin zafi da raɗaɗi a zuciyarsa sosai da sosai yake jin zuciyarsa na wani irin zugi ji yake yi kamar ya tashi ya makure wannan mutumin da yake kokarin yi masa sakiyar da ba ruwa ba zai yarda ba da wannan gangancin ba ba zai lamunci wannan haukar da wannan mutumin ke kokarin yi masa ba.
Nisawa yayi yana kokarin boye bacin ran dake kokarin bayyana kansa a fuskarsa wani shu'umin murmushi ya kalato ya sauke kafun ya kau da kai yana hirji kasa-kasa.
"a zamanin nan da muke ciki da yawa marayun da ake dauka suke shiga gararin rayuwa suke shiga tashin hankali sai mutane su zo da sunan ba su da 'ya'ya Allah bai basu haihuwa ba a taimaka a ba su za su rike tamkar 'ya'yan cikin su amma daga baya bayan sun samu cikar burin su sai su canza alkibla akan 'ya'yan da aka ba su da KUDIRI da sukayi niyya a zuciyarsu ba zan boye maka ba Alhaji Mati ka ganni nan nayi kuka da idona da girmana da kake gani a haka akan tashi hankalin da marayu suke shiga a hannun masu daukar su da sunan riko ban san adadin yawan marayun da suka bata ba ban san adadin marayun da aka bata wa rayuwa ba ban san adadin marayun da aka ciwa zarafi ba ban san adadin marayu mata da aka KETA HADDI a garesu ba haka ma mazan su ma ba a bar su ba...".
Shiru yayi yana jan numfashi zuciyar na wani irin bugawa ransa na kara ɓaci a hankali ya ja glass din idanunsa ya dauke wasu kwalla da suka tarun masa kafun ya sake nisawa yana duban Alhaji Mati da izuwa wannan lokaci ya kosa da dogon sharrin da yake yi masa wanda shi dai a karan kansa ba abin da suke yi masa domin bi sukeyi ta bayan kunnan sa suna wuce wa ba abin da ya kawo shi kenan a zaunar dashi ana karanta masa halin marayu ba shi zuwa yayi a bashi abin da yake bukata ko nawa ne zai biya a zuciyarsa ba wai marayu ya zo dauka ba siyar maraya ya zo yi da kudin sa domin bukatarsa ce ta taso a filin duniyar rayuwarsa.
"MARAYU MA 'YA'YA kamar ko wani ɗa a filin duniyar nan suna da gata da galihu gami da 'yanci a rayuwarsu kawai dai har yanzu ba a san wanene maraya ba duk marayu da ka ga ana ajje su a wannan gidan to in ka bincika ba su da laifin ko miskala zarratin a filin duniyar su da yawan su haihuwar su ake ana yasar da su a titi ba tare da sun sani ba da yawan su iyayen su da suka haife su ba wai ta hanyar sunna bace ake samun su ya kamata a daina ganin laifin marayu ba su suka halicci kan su ba haka ƙaddarar su ce ta zo a hakan in da suna da iko wallahi ba yarda za ayi su bar iyayensu su haife su ta wannan gurbatacciyar hanyar...abin takaici yawan mutanan mu ba sa duba ga hakan kawai yankewa maraya hukunci suke yi da bahagon tunani ya kamata ace an daina ganin laifin maraya maraya rauni gareshi maraya mai bukata ne a filin duniyarsa maraya shima ɗa ne kamar ko wani ɗa a filin duniyar nan...".
Nisawa yayi muryarsa a lokacin ta kara rauni.
"...don Allah Alhaji Mati ka dubi girman Allah da Annabi kayi mani alkawari ba zaka zamo daya daga cikin mutane da masu cin zarafin marayu ba...".
"Ba sai ka roke ni ba Uban Marayu".
Alhaji Mati ya fadi da murmushi kwance a fuskarsa kafun ya cigaba da cewa.
"Bana cikin irin wadannan mutanan masu tauye hakki har haka ka yarda dani Alkawari nayi maka ba zaka samu matsala dani ba domin nasan darajar maraya domin nima na ɗanɗani irin rayuwar tasa kuma ban ji dadi ba ka ga kuwa ba yarda za ayi ace na so wani dan uwa nawa ya shiga irin wannan halin".
Ya karashe da yanayin rauni a fuskarsa.
"Naji dadin haka sosai da sosai Allah yayi mana jagora".
Bai amsa ba illa yatsine fuska da yayi cikin yanayi kamar akwai abin da ke damun sa yana mai duban yarinyar dake zaune can gefe da su ta takure waje daya a shekarun ta ba za su hau goma zuwa sha daya ba fara ce tas! kamar shuwa bata da jiki sosai kallo daya zakayi mata ka gane irin matan nan ne ma su tsayi da kirar jiki.
Duban ta sosai Alhaji Mati yayi zuciyarsa na wani irin zullon farin ciki KUDIRI da burinsa gaf! suke da cika komai na duniyarsa ya kusan zamar masa sabo filin a leda.
Takardun da yaji Uban Marayu ya turo masa gabansa ne ya tsinke masa tunanin da yake yi cikin yanayi na son abin da aka turo masa ya dauki takardun yana yawatawa da idanuwansa kan su yana mai sakin wani Shu'umin murmushi.
Takardu ne na yarjejiniyar da sukayi a tsakaninsu zuwan sa na farko da suka je kotu komai da komai gashi nan a rubuce har da sanya hannun lauya da shi uban marayun.
Duban sa yayi kafun ya numfasa.
"Uban marayu na ga komai kuma hakan yayi daidai sosai da sosai"
ya fadi yana mai dauko Biro yana sanya hannu a wajan da Uban Marayun ya nuna masa da hannunsa.
"Godiya muke sosai Uban Marayu".
Alhaji Mati ya sake fadi yaka mai mika masa hannu suna gaisawa duk kan su da murmushi a saman fuskarsu.
Matar da take gefen sa zaune ya duba yana murmushi.
"Hajiya kiyi masa godiya ta tabbata yau dai mun samu 'ya".
Tsukankiyar matar mai kama da muciya da zani fuskar nan ta ta tasha mai sai kyalli take da wani kala-kala kallo daya zakayi mata ka kau da kan ka.
Yak'e ta saki tana mai washe hakoranta da suka gama dafewa da dattin hayakin sigari godiya tayi kamar bata so ba kafun ta mike tana sabar jakarta.
Dama tuntuni sunyi komai da komai jira kawai suke su samu damar tafiya daga wajan Uban Marayu.
"Khairiyya shikenan kuma kin bar mu kin ga yanzu ga iyayenki nan da za ki koma wajan su da zama ina yi miki fatan alheri a rayuwa".
Khairiyya dake kwakumi da jikinta da sauri ta dago idanunta da suka ci taf! da hawaye tana dubansa sosai yaji ta bashi tausayi a ransa kau da kai yayi don ya san tabbas in ya cigaba da kallon ta shima hawaye zai yi gaban sa yake ji yana bugawa amma bai kawo komai a kai ba kawai tunanin sa kamar yarda ya saba rabuwa da marayu cikin damuwa yau ma haka ne yake ji dalilin rabuwa da Khairiyya.
Kuka sosai take yi har suka fito daga cikin gidan bayan sun yi BANKWANA da yan uwanta sai kuka suke yi suma tana ji tana ga aka sakata cikin motar Alhaji Mati cikin yan mintina kalilan suka bar harabar gidan kallon gidan take yi tana ji a ranta ba za ta sake dawowa ba kallon gidan take yi kallo na karshe a filin rayuwarta tana ji a ranta bazata sake zuwa cikin gidan nan ba in ba wani iko na Allah ba sosai take ji gabanta na faduwa duk lokacin da ta kalli Alhaji Mati ko kuma taji amon muryarsa mai razana ta.
Tafiya mai nisa sukayi tun tana hango gidaje har suka fara shiga dazuka masu bishiyoyi kala daban-daban izuwa nan lokaci ta tsaigaita da kukan da take sai jan numfashi take tana ajiyar zuciya.
Awanni Hudu sukayi a hanya kafun su iso cikin Garin Sulaje suna kokarin shiga cikin gari Alhaji Mati yayi parking gefen titi yana duban matar dake gefensa zaune murmushi yake saki mai dauke da mugunta a ciki.
"kin gama aikin ki don haka ga tukuicin ki".
Ya fadi yana sanya hannu cikin aljihunsa yana zaro bandir din yan dubu dubu guda biyu ansa tayi tana mai kau da fuska kamar bata so ba.
"Sannan kuma wannan lamarin ya kasance tsakanina da ke in har naji labari mai kama da shigen wannan lamarin kin san Allah sai kin bar filin duniyar nan".
Ya karashe fuskarsa a daure kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa.
Ko a jikin ta bata nuna damuwa da maganganunsa ba illa tsaki da tayi can kasar makoshi ta na balle murfin motar ta fice Khairiyya dake takure bayan mota ta duba da wani irin yanayi na tausayawa tana faman gyaɗa kai kafun ta dubi Alhaji Mati.
"batar da sunanka sananne ka aro na banza ka sakawa kan ka akan wani KUDIRI naka na daban...Uhmm ba na ganin wanda ya isa rikakken mutum mara tsoro zai fito da wannan salon na boye sunan sa domin duk wanda yake so ya fado DUNIYAR SHAHARA a wani fanni da sunan sa ya kamata a san shi ko an rufe babin sa ba za taba mantawa dashi ba da abin da ya aikata".
Tana gama fadin haka ta buga murfin motar da karfi yan yatsunta biyu ta dagawa Khairiyya wacce a wannan lokacin ta dago da kanta tana dubansu su duka biyun cikin yanayin na rashin inda suka dosa a tsakanin su.
"Hajiya Layla"
Ya fadi da murmushin mugunta a laɓɓansa kafun ya dora.
"...abu daya zai sa na kyale ki a filin duniyar nan shi ne wannan yarinyar da kika bada takomashin taimako har na same ta saboda ita ce hanyar samun arzikina da nake burin cimma wa wannan dalilin zai hanani yi miki komai amma duk da haka ki tsumaye ni ina nan tafe".
yatsine fuska tayi kafun ta juya ta fara takawa kan kafafuwanta.
Dariya yake yi sosai da sosai har yana buga sitiyarin motar kafun ya tsagaita kamar daukewar ruwan sama fuskar nan tashi ya haɗe ta waje daya kafun yayi wa motar ki ya fizge ta kamar mai kokarin tashi sama.
tafiya yayi mai dan tsayi mai makon ya shiga gari kawai sai ya ratse ya yanki daji hakan da Khairiyya ta gani ya dan tsoro ta ta ware idanu tayi tana duban hanyar da suke shiga daji sosai da sosai tun suna hango gidaje har suka daina sai bishiyoyi kala kala can nesa kadan ta hango wani gida shi kadai kwallin kwal! a tsakar daji ba ka jin kukan komai sai na tsintsaye da sauran halittun daji gida dan madaidaici ne anyi masa farin fenti gabadayansa haka kwanon rufin ma fari ne aka saka. A hankali Alhaji Mati ya isa kofar gidan yayi Parking ita dai Khairiyya gabanta sai faduwa yake yi ta saki baki tana kallon gidan tana jin sa lokacin da ya buɗe kofar ya fita kafun taji amon muryarsa akanta a dan razane ta dube shi kafun tayi kasa da kai gabanta na