Header Ads
Showing 180001 words to 183000 words out of 227252 words

Chapter 61 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1384

Ads at the middle of Article

da Dr.Erena sosai ta firgita yau kimanin wataninta biyu kenan a gidansa amma ta rasa kwamciyar hankali da natsuwa.
"Maama don Girman Allah ki zo ki fiddo ni daga cikin wannan gidan zan mutu".
Cewar Areefa a wani talatin dare da tayi wani mugun mafarki da yayi matukar tsorata ta.
"Wai me ke damunki ne Areefa eyee ba na ce miki ina nan zuwa ba amma kin ki kwatar da hankalinki ki natsu mana ina nan zuwa gobe da safe".
Wani kuka ta sake rushewa dashi matsanancin sai faman zarya take yi a tsakiyar dakin daga ita sai kayan barci kanta duk a hargitse kamar sabuwar mahaukaci.
"Allah Maama mutuwa zanyi ba zan iya jira har gobe da safe ba don Allah ki zo ki fiddo ni daga bakin gidan nan...".
Bata karasa maganar da take yi ba taji an hau dukar kofar dakin nata kamar za a karyata wani tsalle tayi ta ɗane saman gado idanu a warwaje.
"Maama kina ji ko kin gan shi nan fa ya zo yana dukar min kofa wayyo Allah na zai kashe ni".
"Innalillahi wa inna ilaihr raji'un".
Hajiya Layla ta fadi cikin sauti don tana jiyo sautin bugun kofar da ake yi sosai ta firgita ita kanta ta fara tsorata da yanayin da take jin Areefa a ciki sosai take fargarbar abin da zai je ya dawo kai kawo kawai take yi tsakiyar falon tun lokacin da Areefa ta bugo mata waya tana kuka gabadaya ta fice hayyacinta bata son abin da zai cutar da Areefa bata so a kuma yin na biyu bata so ace ta dalilinta Areefa take fadawa cikin kunci da bala'in rayuwa.
Hannayenta ta saka ta dafe kanta tana jin yarda yake juya mata a hankali ta ja kafafuwanta da take jin sun yi mata nauyi sosai ta zauna bakin kujera jikinta sosai yake rawa.
"Areefa kina jina".
Ta fadi cikin kwantacciyar murya mai cike da rarrashi.
"Ina jinki Maama ni dai don Allah ki zo ki fidda ni daga cikin gidan nan na roke ki".
Ta fadi tana mai sake rushewa da kuka a daidai lokacin kuma ya balla kofar ya shigo habawa ba ta san lokacin da tayi cilli da wayar ba ta yi hanyar toilet da gudu tana shiga ta mai da kofa ta rufe.
"Areefa!!".
Taji ya ambaci sunanta cikin wata murya wacce ta tabbatar bata sa bane gabadaya sautin ta ya cika mata kunnuwa yake yi kamar gidan ma rawa yake yi gabadaya lokaci guda ta sake rikicewa sosai.
Kara kankame jikinta tayi sosai idanuwanta a runtse ba abinda take ambata sai sunayen Allah hawaye sai faman sauka suke a kuncita zuciyarta na kara rikicewa.
A kunnuwanta take jin taku wanda yake ansawa a dukkanin bangwayen gidan ko ta ina kasa da sama zubewa tayi ta zauna kasa cikin yanayi na yanke tsammani abin da yake kokarin faruwa da ita.
Bata san mai ya kai ta yarda da auren nan ba, bata san wani tsautsayi bane yasaka ta amincewa dashi, tana cikin bala'i. wanda bata san ya za ta fidda kanta ba tsoro take kar abin yayi yawa ga duka ga mari gami da tsinka jaka.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo mata daidai lokacin da taji takun kafafuwansa na takowa zuwa toilet din fargabarta ta dadu da sauri ta shiga ja da baya domin kafafuwanta take jin suna kokarin kasa daukarta handle din kofar da aka rike hakan ne ya sanyata dauke numfashi gabadaya na dan lokaci kafun ta ji an saki a juya kuma an fara tafiya a hankali jin shirun da tayi na ɗan lokaci ya sanyata sakin gwauron numfashi tana dafe kanta da yake faman sarawa kamar zai rabe gida biyu numfashi take fizga zuciyarta na kara rikicewa da wannan lamarin wanda bata san yarda zata kwatantashi ba.
Haka ta cigaba da zama cikin wannan talatin daren har zuwa wani lokaci wanda ita akaran kanta ba zata iya cewa wani lokaci ta dauka ba domin barci a lokacin bata san ina ya nufa ba idanuwanta sun kekeshe kiran sallar assalatu ne ya fargar da ita daga duniyar tunanin da ta lulaka cikin kasalallan yanayi ta mike tana jan kafafuwanta da take jin su kamar zata zubda ita kasa ta isa wajan famfon Toilet bayan ta yi tsarki ta daura alwala zuciyarta na ta nazarin ta yarda zata fice daga dakin don gabadaya ta gama firgicewa bata san abin da zai faru ba in ta fita daga toilet din nan bata so ta hadu dashi ta tsane shi sosai take jin tsanarsa na kara samun gurbi a zuciyarta sosai take ganin wautar kanta da ta yarda har ta amince akayi wannan auren gashi yanzu tana cizon yatsa.
Sai da ta gama tsalle tsalle da zuciyarta kafun ta tunkari kofar jikinta na faman bari ta buɗe kadan ta leka ganin ba kowa a hankali ta shiga takawa ta fito ganin tabbacin ba kowa ta karasa kusa da kofar ta mai da ta kulle gami da sargafa key wani irin numfashi ta ja gami da jingina da kofar ta runtse idanuwanta zuwa wani lokaci kafun ta buɗe ta ja kafafuwanta sallaya ta dauko ta shimfiɗa gami da saka hijab ta shiga bada nafilfili zuwa wani lokaci tana kai kukanta wajan Allah ya rabata da wannan mugun mutumin ya tsare mata rayuwa ya kare ta sosai take zubda hawaye zuciyarta na kara karaya da tashin hankalin rayuwar da take ciki a yanzu faragaba take bata san abin da zai faru ba tana tsoron abun da zai faru ya hada har da ita shiyasa tun farko ta so Maama ta fada mata komai da zai faru da ita a wannan gidan domin ta shirya amma bata yi haka ba ga shi yanzu tana ganin bala'i....
Ringing din wayar tace ya katse mata dogon tunanin da ta zauna tana ta faman yi bayan ta sallame da gudu ta mike don har ta tsoro amma jin wayarta ne ya hakan ya sanyata shiga dubanta in da ta cillar da ita jiya can ta jiyo sautin bayan loka din gadon ta da hanzari ta isa ta rarumo ta ganin Maama ne ya hakan ya sanyata sauri daga kiran muryarta na rawa.
"Maama kin taho ne kina ina yanzu?".
Ta fadi da ɓarin jiki numfashi Hajiya Layla ta ajje jin muryar Areefa alamu ya nuna ba abin da ya same ta.
"Areefa dafatan dai kina lafiya ba abin da same ki?".
"Ni dai kawai ki taho Maama don Allah ki zo ki fiddo ni daga cikin gidan nan...".
Da sauri Hajiya Layla ta tare ta.
"Ba maganar zuwana Areefa in har na zo Dr.Erena zai gane ke wacece kuma zai gane ni kin ga kuwa in ya san waye ke ai da matsala...".
"A,a Maama ni ba damuwa ta ba ce ya san ko ni wacece in har zan fice daga cikin gidan ba zan iya zama ba ki zo ki cece ni".
Ta karashe muryarta na kara karyewa da kuka sosai durkushewa tayi a wajan jin Hajiya Layla ta ce ba za ta zo ba kenan duk abin da zai faru da ita sai dai ya faru kenan.
"Areefa".
Hajiya Layla ta fadi amma Areefa bata ansa ta ba sake kiranta tayi nan ma bata ansa ta ba sai ma kashe wayar da tayi ta cillar da ita kan gado zuciyarta ta shiga hasaso mata wani lamari mai girma wanda take kokwanto akan sa tsakaninta da Hajiya Layla tana SHAKKA akan kalaman da take furta mata tana shakka anya ba yaudararta tayi ba domin wani kudiri nata anya kuwa ba GADAR ZARE ta saƙa mata ba ta rufta ciki.
Girgiza kai ta shiga yi kamar wata kadangaruwa cikin tsayin lokaci kafun ta mike tana kai kawo cikin falon da matsanancin tashin hankali mai girman gaske sosai take jin zuciyarta na son gasgata abin da take sanar da ita sosai take jin girman lamarin a ko ina na sashin jikinta.
Bata son hasashenta ya tabbata bata son maganar zuciyarta ya zama gaskiya tana tsoro akan abin da zai je ya dawo in har hasashenta ya tabbata to tabbas da matsala wanda bata san ya zata fuske ce ta ba.
Zame jikinta tayi ta zauna bakin gadon hadi da zabga tagumi zuciyarta da kwanyarta sai faman hayaniya suke yi suna kokarin kamawa da wuta domin gabadaya ji takeyi komai ya rikice mata ta kasa samun tunanin da zata yi.
Ihu taji gami da tsayuwar mota a lokaci guda bata san lokacin da ta zabura ba tana kokarin kwasa da gudu tayi hanyar bayi taja tunga ta tsaya tana faman rarraba idanu bata san gari yayi haske haka ba daga kai tayi daidai inda agogon dakin yake karfe bakwai har da minti hamsin 7:50 mamaki hakan tayi domin bata san lokacin ya ja haka ba nan tsaye take tana jiyo sautin ihun nata shi yana kusantowa cikin gidan sosai daidai lokacin da ka buɗe kofar falon aka shigo ta tsinkayo faduwar abu mai karar gaske har sai da ta sanya hannu ta toshe kunnuwanta gami da runtse idanunta...




*_KAMALA MINNA_*😘
[10/16, 10:12 AM] DEENY MINNA🙋‍♂: UKU BALA'I


NA.


KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.




BABI NA HAMSIN DA HUDU


Cikin hanzari ta fito daga cikin Toilet din jikinta daure da ta shawul kallo daya zaka yi mata ka hango tsantsan tashin hankalin da take ciki idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kamar wacce tayi KUKAN DOLE kai kawo kawai take yi gabadaya kanta ya gama kullewa ta rasa me ya kamata tayi a yanzu wanda ya dace a daidai wannan lokaci amma ta rasa gaɓadaya gaboɓin jikinta ji take yi kamar an lakaɗa mata duka ta ko ina.
Da hanzari ta isa bakin gadon dakin nata ta zauna tana mai da numfashi kamar wacce tayi gudun fanfalaki wayarta da ke yashe gefe guda ta janyo tana mai dubanta tana jujjuyawa har na tsayin dakiku kafun ta shiga latsata tana binciko lamba ta danna mata kira amma ina! Wayar akashe taji ta hakan ba karamin kara rikita mata kai yayi ba mikewa tayi da sauri ta nufi sif din dake dakin buɗewa tayi ta janyo doguwa riga baƙa ta zurawa jikinta gami da yin rolling da mayafin ta janyo flatshoes ta sanya key din motarta da ke kan Mirrow ta dauka tare da dauko wayarta sai da ta karewa dakin kallo kafun ta fice cikin hanzari zuciyarta na kara tsinkewa da tashin hankali mai girman gaske.
Cikin hanzari ta fice zuwa tsakar gidan motarta kirar 406 mai launi ruwan toka ta shiga tare da yi mata key bayan ta buɗe get din gidan ta fice ziciyarta na kara rikicewa ba abin da take jiyowa sai sautin muryar Areefa da yarda take kuka tana ihu akan ta zo ta taimake ta zata mutu bata san mai za tayi mata ba ba ta san abin da ya kamata tayi a daidai wannan lokacin ba tana tsoron Dr.Erena ya sake maimaita abin da ya zama shine sanadi a yanzu tana tsoron a sake komawa gidan jiya za tafi kowa bakinciki zata fi kowa takaici a duniyar nan domin komai ya faru da Areefa a yanzu da lokacin baya duk ita ce sila ta hanyarta komai ya ke tabbata.
Wasu hawaye ne ta ji sun sauko mata da sauri ta sanya hannu daya tana dauke su tana mai tuki jikinta a sanyaye zuciyarta ne ta shiga kai kawo tana so ta samo wanda zai taimaka mata da abin yi sosai kwanyarta take hayaki tana kokarin kamawa da wuta.
'Alhaji Abdulwahaab'
Sunan da ya zo mata kai kenan da sauri ta runtse idanunta kafun ta buɗe su tana jin wani irin yanayi a zuciyarta mai girma gaske da sauri ta gangara bakin titi tayi parking tana mai hada kanta da sitiyarin motar na dakiku sai faman sauke numfashi take kafun ta dago ta dubi wayarta lambarsa ta binciko jikinta har rawa yake yi ta danna masa kira gami da karawa a kunne cikin kankanin lokaci ta shiga ruri amma ba a daga ba har ta katse sai da tayi haka sau uku a na hudu Allah ya taimaka ya dauka wani irin ajiyar numfashi tayi mai karfi tana mai cewa.
"Don Allah kana ina Alhaji Abdulwahaab akwai matsala fa sosai ina bukatar ka yanzu yanzun nan ko ina kake ina kan hanyar gidan Dr.Erena mu hadu acan".
Mamaki sosai ya cika shi jin abin da take fadi.
"Ban fahimce ki ba Hajiya Layla meke faruwa ne?".
Dafe kai tayi kafun ta sake nisawa.
"Ba mu da lokaci don Allah ka zo yanzun nan akwai matsala ce".
numfashi ya sauke cikin wani yanayi.
"Amma Hajiya Layla kin mata yanayin da muke ciki ne da Dr.Erena kin san za a samu matsala in har ya gane mu din ne muke tare da Areefa...".
"Alhaji Abdulwahaab!".
Hajiya Layla ta kira shi tana mai katse shi zuciyarta na kara hargitsewa.
"wannan lokacin ya dade da shafewa na manta dashi yarinyata nake bukata Abdulwahaab duk wani boye-boye ya kare tsakani na dashi zan fuskace shi komai zai faru zan tunkare shi sai dai duk abin da zai faru ya faru".
"Hajiya Layla da kin yi hakuri man...".
Katse wayar tayi jin yana kokarin bata mata lokaci wani kuncin taji ya tokare mata wuya mai Alhaji Abdulwahaab yake nufi da nuna halin ko in kula akan wannan lamarin da ta sanar dashi anya kuwa ya san abin da yake yi anya kuwa ya ji abinda ta fada masa sosai dafe kai tayi na dan lokaci kafun tayi wa motar ki ta fizge ta da karfi zuciyarta cike da zullumi.
Tafiya sosai tayi sannan ta isa unguwar da Dr.Erena yake nesa da gidan tayi parking zuciyarta ta na bugawa da sauri sauri bata san mai zata yi ba sosai take fargaba da tsoro a zuciyarta Areefa take so ta gani so take yi ta ga halin da take ciki runtse idanu tayi gami da kashe motar ta fito ta mai da kofar ta rufe a hankali ta shiga takawa zuciyarta na kara sautin bugu har ta isa bakin get din gidan lekawa ta shiga yi ko zata hango cikin gidan amma ba ta hango komai ba gefe ta ja kadan tana duban layin amma ba kowa sit kake ji kamar mutuwa ce ta gifta hakan ya dan kara tsorata ta amma cikin karfin hali da nuna rashin tsoro ta shiga kwankwasa Get a hankali idanuwanta na saitin karamar kofar zuciyarta na kara sautin bugun ta.
"Waye a nan?".
Ta ji an fadi da sauri ta juya don jin muryar tayi kamar daga sama domin gabadaya a firgice take sai da ta saita kanta sannan ta lura ashe Maigadi ne wanda ya buɗe kofar a daidai wannan lokacin.
Yak'e ta shiga yi shikuwa sai faman gaisuwa yake watsa mata ganin Babbar mace ce mai suffar naira.
"Yawwa Alhaji na ciki kuwa?".
Ta fadi tana mai kokarin saita kanta sai da ya kare mata kallo don ya so gane rikicin da ke idanunta kafun ya gyaɗa kai alamun eh wani rugugin tashin hankali ne ya dirar mata a zuciya amma ta danne tana mai kara faɗaɗa yak'enta kafun ta numfasa.
"Ok ni mahaifiyar matarsa ce Areefa".
Da sauri ya kara ladab yana mai bude mata kofar domin ta shiga sai da tayi addu'a kafun ta saka kafafuwanta cikin gidan tana takawa tana bin ko wani sashi da lungu na gidan tana kara tsorata da Dr.Erena irin dukiyar da ta ga an zuba a gidan ta fitar hankali ba ta lura da motar dake gabanta ba har ta kusan cin karo da ita san nan tayi baya da sauri motar tabi da kallo ganin yanayin da take da sauri ta zaro idanu waje ganin yarda motar tayi gilashin fitilun duk sun fashe mamaki ne ya cika ta da tsoro a zuciyarta tana tambayar mai ke faruwa Allah yasa ba Areefa ba ce tayi accident wani irin bugawa taji gabanta yayi da sauri ta yi cikin falon tana zuwa ta tadda shi a bude ba tare da fargabar komai ba ta fada ciki baje ta hango mutum tsakiyar falon sai faman murkususu yake yi idanuwansa a kankafe da sauri ta ja baya tana mai kiran Areefa da karfi gidan gabadaya ya dauka sautin muryarta.
Hancinta ta toshe jin irin warin dake tashi a tsakar falon gabadaya taji zuciyarta tana sama da kasa kamar zata yo waje rarraba idanu ta shiga yi tana faman kiran Areefa ganin ba alamunta hakan ya sanyata nufar cikin falon sosai tana buɗe daku har ta haye saman benan dakunan da ta gani ajere guda uku ta nufa tana kiran Areefa kamar wacce makoshinta zai yo waje.
Ita kuwa Areefa da take can kulle cikin daki kamar daga sama ta tsinkayo Muryar Hajiya Layla bata gasgata ba ta dauka kawai halin firgicin da take ciki ne take jiyo sautin kamar na ta amma kuma sai taji sautin na daduwa da sauri ta mike ta buɗe Toilet din kamar daga sama ta ji ana kwankwasa kofar dakin da take muryar Hajiya Layla na tashi da gudu ta fito har tana tuntuɓe ta nufi kofar ta buɗe da sauri Hajiya Layla ta gani a tsaye da sauri ta isa gareta ta rungume ta tana faman sakin ajiyar zuciya mai karfi idanuwanta sai zubda hawaye suke.
"Areefa me ke faruwa ne haka?".
Dago kanta tayi daga kafaɗarta ta dube da jajayen idanuwanta.
"Maama Dr.Erena zai kashe ni ba zan iya zaman gidan nan ba wallahi na hakura ba zan iya zaman aure dashi ba don Allah ki fidda ni daga cikin gidan nan ji nake kamar numfashi zai katse".
Dubanta take yi sosai ta na hango rashin hayyaci a idanuwanta gami da firgice janta tayi cikin dakin gami da mai da kofar ta rufe bakin gado suka zauna Hajiya Layla tana dubanta kafun ta nisa lura da tayi ba abin da ya same ta.
"Amma me ke faruwa dake haka duk na ganki a wannan matakin AREEFA?".
Runtse idanu tayi hawaye suka zubo.
"Maama baki jin warin da nake ji ne?".
Ta fadi muryarta da rauni a ciki tana faman girgiza kai.
"Tun ranar da na zo gidan nan nake jin wannan warin har izuwa yau kuma wallahi daga jikinsa ne warin nan ke fitowa da farko nayi zaton

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads